Sashe 87
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Safeera ta yi dariya, dan ta san halin Islaha da kishi, in itace a matsayinta baza ta yi ba. Safeera ta ce, "Wallahi ni ko a jikina, murna nake yi Baba ya samu sabuwar matar da in na tafi aiki ƙannena suna makaranta zata kula dashi yadda ya kamata. Kuma dan ba ki san irin kyautatawar da ta dinga yi mana bane, mahaifiyarmu ta ajjiye mu ta bar ƙasa, ita kuma ta kamo hannunmu ta riƙe. Ai wallahi ta cancanci Baba ya aure ta, ko Umma tana nan ta cancanci su yi zaman kishi, balle bata nan, kuma ba a san ranar da zata dawo ba."
Islaha ta ce, "Allah ya sanya alkhairi."
Ta amsa da amin kafin ta ce, "bara na kira Sadik na ji in an É—aura na ki, yadda zan dawo na tsokane ki son raina" ta faÉ—a tana kashe wayar Islaha ta bi wayar da kallo cikin wani irin yanayi.
Tana idar da Sallah Sahir ya kira ta, ta É—auka cikin faÉ—uwar gaba, amma yadda ta ji maganarsa a sanyaye ya saka ta ce, "Hamma ya dai?."
Ya ce, "kin ji shiru ko? Baba ne ya ce a dakata da ɗaura auren sai kin dawo. Gabaɗaya raina a ɓace yake a akan hakan."
Ta yi ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, yanayinta ta ya canja zuwa na jin daɗi ta ce, "meyasa ya ce haka?."
"Wai gaggawar me ake yi, a jira ki dawo."
"To ai shikenan, Allah ya sa zamu gani."
"Amin. Amma ni ba haka naso ba gaskiya."
"Wataƙila yanzu in aka ɗaura bazai zama alkhairi ba."
"Haka ne."
Islaha ta ce, "Hamma ya batun Zainab?."
"Bana so na faÉ—a miki ki tayar da hankalin ki, shiyasa na yi shiru."
"Bazan tayar ba, ka faÉ—a min don Allah."
"Ba a ga Zainab ba, duk inda nake tunanin zan ganta ban ganta ba. Har gidan Æ´an uwanku na gidan na je aka ce bata je ba, har Barr na tambaya ya ce shi ya jima bai ga Zainab ba."
Ta yi shiru bata ce komai ba, ya san ta daman zara damu sosai akan hakan, sai ya tausasa murya ya ce, "amma ki yi haƙuri, kafin na koma zan sake dubawa, in sha Allah rayuwar Zainab zata salwanta ba, Allah zai yi riƙo da hannunta, zai kare ta a duk inda take."
"Allah ya shiga tsakanina da wanda ya zama munafuki a tare dani" ta faÉ—a hawaye yana sakko mata.
Ya tausasa murya cikin rarrashi ya ce, "ki yi haƙuri, in sha Allah zan nemo miki ita."
"Hamma in wani abun ya same ta ni ce sila, Allah bazai yafe min ba."
"Ki yi haƙuri, Allah ya gani ya san taimako ki ke yi, ko dan hakan bazai bari ki wulaƙanta ba."
Kuka take yi masa sosai yana rarrashinta, sai da ya ji ta ɗan nutsu sannan ya ƙyale ta. Abin ya haɗar mata, ga jin daɗin an fasa ɗaura aure ga tunanin Zainab.
Daƙyar ta iya miƙewa, ta wanke fuskar ta ta fito tana kallon kanta, kallo ɗaya za ka yiwa idanunta ka san ta yi kuka. Ta ɗauki facaemask ta saka, ta saka hijjab ta fita zuwa gidan Rehaan.
Tana shiga falon gabanta ya faɗi, dan yana zaune shi da wani bature yana nuna masa abu a file shi kuma yana gani. Tana ƙarasa shiga falon Baturen ya tashi da file ɗin ya fita.
Sai ta ji zuciyarta ta yi nauyi sosai, haka kawai take ji kamar tana jin nauyinsa akan abinda ta dinga yi, ta lumshe ido ta buÉ—e ta kalle sa ta ga kamar bai ganta ba ta ce, "Good day."
Ya É—ago ido ya kalle ta, ta yi saurin kawar da kai tana mamakin wannan faÉ—uwar gaban da take yawan ji indai zasu haÉ—a ido.
Ya miƙe tsaye ya harɗe a hannu a ƙirji yana kallon ta, ya ɗan riƙe kai ya ce, "ohhh my god, na gaji sosai."
Ta kalle sa ta ƙasan ido, ta turo baki gaba tana hararasa ta ce, "rago kawai, shi komai ya gaji."
Bata faɗa yadda zai ji ba, ita kaɗai take maganarta. Rehaan ya ji ta, ya yi kamar zai yi magana sai kuma ya ɗauke kai ya taɓe baki ya ɗauki wayarsa zai bar wajan.
Daƙyar ta iya buɗe baki ta ce, "kana buƙatar wani abu ne?."
Sai ya tsaya ba tare da ya juyo ba, sai kuma ya juyo ya dawo da baya, ya saka hannu aljihu ya É—auko kuÉ—i ya ajjiye a gefen kujera kusa da ita, ya É—an fara tafiya da baya sannan ya ce, "no need, you can go" ya faÉ—a yana bar mata wajan ya hau sama.
Ta bi sa da harara ta ce, "Ɗan rainin hankali, kar ka so ɗin, da na san haka ne ai da ban fito na zo inda ka ke ba. Dan ka kasance Rehaan yola babu ruwana wallahi, baza ka yi min na ƙyale ka ba."
Ta kalli kuÉ—in ta ga riyal É—ari biyar biyar da yawa, ta harari kuÉ—in ta ce, "ba dan ina son kuÉ—in ba wallahi bazan É—auka ba, kawai dan amfani dasu ya zama min dole, ko dan na biya su Mama kuÉ—in da suka kawo ni na wuce gida" ta faÉ—a tana É—aukar kuÉ—in tana kallonsu.
Ko bata lisssfa ba ta san da yawa, dan gani take kamar sun fi waÉ—ancan yawa. Ta yi ajiyar zuciya tana kallon kuÉ—in tana tunanin aikin me take yi masa da yake bata waÉ—annan uban kuÉ—in?.
Sai kuma ta taɓe baki, a bayyane ta ce, "ba sata na yi ba, ba kyauta ya bani ba, ba roƙonsa na yi ba, aiki na yi masa kuma ya biya ni, haƙƙina ne, kuma halak ɗina ya bani" ta faɗa tana saka kuɗin aljihun rigarta ta fita daga gidan tana takawa a hankali.
After two days...
Nana Haleema.
[7/17, 7:20 PM] KRBBK: RDB2P63
Nana Haleema.
Suna zaune a falon Maleek suna faÉ—a musu zai yi tafiya shi da matarsa. Islaha tana zaune ta yi shiru bata ce komai ba, sai da ya gama sannan ta É—aga kai ta ce, "zan iya faÉ—ar wani abu?."
Maryam ta ce, "za ki iya."
Islaha ta ce, "ina so na je Madina na yi kwana biyu, amma ban san ta inda zan fara ba."
Maleek ya kalle ta ya ce, "Is okay, duk lokacin da za ki je sai ku je da Sunaira ki yi ticket É—in train ki je."
Islaha ya yi murmushin jin daÉ—i ta ce, "na gode."
Ya kalli Sunaira ya ce, "Ku je da ita station ta siyi ticket duk lokacin da zata tafi." Sunaira ya amsa ya bawa Sunaira kuɗin ticket ɗin. Ita dai Islaha godiya take yi dan ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Basu jima ba suka tafi aka bar gidan a hannunsu.
Daman kwana biyu ba zuwa gidan Rehaan take yi ba, rabon ta da zuwa tun washe garin da ya bata kuÉ—i, daga nan Maleek ya ce mata ya yi tafiya baya nan.
A washe garin ranar ta siyi jaka ta baya, irinta ta ƙaramar tafiya, ta saka doguwar riga guda ɗaya a ciki, ta saka kayan amfani in za ka iya kwana dasu, ta goya jakar ta fito zasu je statiom ɗin kamar yadda ya faɗa.
A hanyar su ta tafiya Islaha ta ce, "Sunaira ina na ne unguwar Khadiyya a Madina, ya zan yi?."
Sunaira ta yi mata typing kamar ko yaushe, Islaha ta dub ta ga ta ce, "in kin sauka ki tari mota ki faÉ—a musu, zasu kai ki ko ina ne. In kuma za ki je masallaci, kawai ki cewa masu mota haram zasu kai ki."
Islaha ta gyaÉ—a kai tana murmushi, a haka suka si yi ticket Sunaira, ta bata da sauran kuÉ—in da zata siyi na dawowa. Sai da Islaha ta shiga train sannan Sunaira ta koma.
Islaha kallon jirgin kawai take yi, dan ticket É—in first class aka siya mata, gashi nan kamar jigin sama saboda kyau. Babu jimawa jirgin ya fara gudu dasu a ciki.
Tana zaune da facemask a fuskar ta tana ta kalle kalle, wani abun ta yi video wani abun ta ajjiye wayar. Awa É—aya da wani abun suka É—auka suna gudu, kafin ta ji sanarwa sun iso station É—in Madina.
Suna fita ta ga inda mutane suke bi, da yawa matafiya ne waɗanda suka shigo ƙasar, ita dai su take bi har aka fito inda motoci suke, ta samu taxi ta faɗi sunan da Umma ta ke, ya faɗa mata kuɗin da zata biya ta shiga suka tafi. Sai da suka zo sannan ta bashi location ɗin da Umma ta tura mata, ai kuwa har ƙofar gidan da Umma take ya kai ta.
Islaha ta bi gidan da kallo, gidan babba ne babu laifi, ta fita daga motar ta bashi kuɗinsa ta ƙarasa. Gate ɗin bashi da tsayi, sannan lock ɗin yana saman gate ɗin kana saka hannu zaka cire. A hankali ta cire, ta taka a nutse ta ƙarasa wajan ƙofar tana danna door bell. Ba jimawa aka buɗe, ana buɗewa suka haɗa ido da Umma da take tsaye sanye da ƙaramin Hijjab.
Umma ta buÉ—e ido cikin tsananin mamaki ta ce, "Islaha ke ce?."
Islaha ta É—aga kai tana murmushi ta ce, "Ni ce Umma."
Umma ta ji wani irin daɗi yana mamaye mata zuciyarta, ta rungume Islaha tana ji kamar ƴarta Safeera ya gani. Daman kuma duk wanda ba ya ƙasar sa in ya ga wanda ya sani sai ya ji kamar ya yi me saboda murna, Umma ta gigice tana jin daɗi kamar ta mayar da Islaha ciki.
"Me ki ke yi a nan! Baza ki dawo ciki ba!?." Muryar matar gidan ya ratsa su cikin yaren ta, zuwa lokacin Umma tana fahimtar wani abun a arabic sosai.
Ta saki Islaha tana cewa, "Wannan masifaffiyar mata, Islaha mu je Allah ya sa ta bari ki zauma."
Tare suka shiga falon, ta yi kan Umma kamar zata dake ta tana masifa da arabic. Umma ta bata haƙuri da larabci, ita kuma ta nuna Islaha tana tambayar wacece.
Islaha ta bi matar da kallo, ganin ta yar ƙarama da ita bata da jiki, kuma a haife ma ta san Umma ta haife ta, amma ji yadda take yi mata wannan masifa har da ƙoƙarin duka.