← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 133

Sashe 92

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta É—an yi murmushi, da son nuna masa ta gode akan taimakonsa, ba dan haka ba shi ya isa ta kulasa. Islaha ta ce, "ina yini" ta faÉ—a da hausa tana kallonsa.

Ya yi shiru bai ce komai ba, yana kallon fuskar ta sau É—aya ya É—auke kai, domin yanayinta da komai na ta ya yi kama da wacce ta samu miscarrige É—in.

Islaha ta ce, "na gode da taimakona da ka yi."

Ya juyo ya kalle ta, sai kuma ya dawo da baya ya zo kusa da ita yana kallon ta ya ce, "I don't ever want to see your face again. Stay away from this house. Your face is the first face I've ever hated seeing in my life......"

Ya dakata yana kallon ta kamar yadda take kallonsa, ya girgiza kai ya ce, "Bana so na sake ganin ki, daga yau!."

Islaha ta bi sa da kallo tana mamakin kalamansa, daman yana da guts É—in cewa ya tsane ta? Ta yi tunanin itace zata ce ta tsane sa ba shi zai faÉ—a ba.

Sai ta ga ya ja bayac ya ajjiye kuɗina inda ya taɓa ajjiye mata ya ce, "ki ɗauka, ki je ki cigaba da abinda ki ka saba. But I don't want my name dragged because of you."

Da mamaki take kallonsa ta ce, "Dragged your name? Akan wanne dalili kenan."

Bashi da lokacin bata amsa, ya wuce ta sai ta ga kamar in ta bari ya tafi bata tanka ba ya gama ci mata fuska.

Ta ce, "Ji mana! Dan na zo gidan ka ina aiki ba haka yana nufin kana da ikon faɗa min abinda ka ga dama ba. In kana so kace na daina zuwa gidan nan ka faɗa kai tsaye, ba sai ka yi ƙoƙarin ci min mutunci ba. Ka ke zancen ka tsane ni, kai ka ɗauka nima sonka nake yi? Wallahi nima babu wanda nake jin haushi kamar ka, in ba ka sani ba yau ka san da hakan. Ina zuwa gidan nan saboda wani dalili, kuma na samu mafitarsa, dan na daina zuwa kai zaka ragu da rashin zuwana, ba ni ba."

Ya waiwayo ya kalle ta yana mamakin ƙarfin hali da rashin kunyar yarinyar nan.

Ya record É—in miscarrige É—inta ya zo har office É—insa, amma ta dinga faÉ—a masa wannan maganar banzar?.

Kamar bazai kula ta ba, sai kuma ya É—an É—aga kai ya ce, "Thank God you've found your solution. Now leave! I don't want to see you again. Go and continue your filthy prostitution."

Islaha ta wani zaro ido, cike da tsiwa da rashin kunya, da tafasar zuciya ta ce, "Kar mu zo nan, kar ka kuskura ka kira ni da kalmar karuwa!" Ta faÉ—a da hausa tana kallonsa.

Ya ɗan buɗe ido, wani irin haushinta yake ji ba kaɗan ba, sai ya ya jingina da staircase yana yi mata kallon ƙasƙanci ya ce, "Let me say it again, you're a prostitute and a thief. Za ki dake ni?.."

"Bazan dake ba, amma harshena zai dake ka. Ni ba karuwa bace, kar ka sake kirana da wannan sunan. Sannan ni ba ɓarauniya bace, sau ɗaya na taɓa ɗaukar abinda ba nawa ba, kuma saboda shi nake a ƙasar nan. Ba ka isa ka faɗa min magana wacce bata yi min ba na ƙyale ka. Kar ka yi tunanin saboda kai ne Rehaan Yola zan saurara maka, wallahi bai dame ni ba, ko kai waye a duniyar nan ba ka isa ka ɗaga min murya na ƙyale ka ba."

Sai ya ga kamar yana zubar da ajinsa in ya tsaya yana magana da ita. Ya ɗauke kai ya ja tsaki ya fara hawa sama, sai kuma ya tsaya ya kalle ta kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya hau sama bai sake waiwayonta ba, dan Allah ya sani ba ƙaramin haushinta yake ji ba.

Ta kalli kuɗin da ya ajjiye, ta kalle sa tana ganin a lokacin zai shiga bedroom, ta zubar da kuɗin a ƙasa ta ce, "bani da buƙatar kuɗinka, kuma Allah sai ya saka min ƙazafin da ka yi min...bazan yafe wannan kalma ba, sai Allah ya tsayar damu a ranar hisabi, ka yi bayanin sunan da ka kira ni dashi."

"Kuma ka jira Rehaan Yola, wallahi sace ni É—in da ka yi bazai tafi a banza ba, sai na nuna maka waccece Islaha!."

Yana jin duk abinda take faɗa, ya shiga ɗaki ya rufe ƙofa, ta tsaya tana kallonsa cikin wani irin baƙin cikin da bata taɓa jin irinsa a rayuwar ta ba.

Ta kasa tafiya saboda takaici, bata san ta fara hawaye ba, sai ɗuminsu ta ji akanfuskarta. Ta goge ido, ta sake kallonsa sai ta fashe da kuka, tana tunanin wacce halitta ce a jikinta da ake yi mata kallon karuwa?. A haka ta ja ƙafar ta ta fita daga gidan, tana ji a ranta ta fita kenan har Allah ya tashi duniya baza ta dawo ba.

Rehaan fan's yaneee🤣🤣🤣

Nana Haleema.
[7/20, 10:26 AM] KRBBK: RDB2P67
Nana Haleema.

Islaha ko da  ta koma gida Maleek sai kawai ta sake fashe da kuka, kuka ta yi sosai, kuka mai mai tsuma zuciya da baƙin cikin da bata san na meye ba.

An daɗe ana kiran ta da karuwa, ba yau aka saba kiran ta da sunan ba, sunan ba baƙo ne a gare ta ba. Bata san dalilin mutane na faɗa mata ba, amma bata taɓa jin zafi da haushin kalmar kamar yau ba.

Ko dan Rehaan Yola ne ya faɗa mata bata sani ba, amma yadda kalmar ta yi mata zafi a ranta ko kalaman Mama basu taɓa yi mata zafi haka ba. Tunanin ta ɗaya ko yaushe, wacce halitta ce a jikinta da ya saka ake yi mata kallon karuwa? Aikinta ne ya jawo ko kuma ina ta tashi? Haka ake yiwa waɗanda suka tashi a gidan marayu kallon karuwai ko kuma ita kaɗai ta fita zakka?....

Ta yi kuka ta gode Allah, kalmar ɓarauniya tana sake tsaya mata a zuciyata. Ta lumshe ido tana goge idanunta, tana jin zafi da ɗaci yana mamaye mata ko ina na jikinta da jinin jikinta. Ashe da ƙaryar haushin sa da take yawan faɗa take yi, sai yanzu ta san meye asalin jin haushi, bata taɓa jin ta tsani abu kamar yadda take jin ta tsani Rehaan ba, yanzu ta san meye tsana da jin haushi, da bata san komai ba.

Ta goge idonta ta kanta a hankali tana ji hawaye yana sake sakkowa.

Bata san lokacin ta kwashe a haka ba, tana ji wayar ta tana ƙara amma bata iya ɗauka ba saboda yadda jikinta yake a sanyaye, haushi da baƙin ciki ya gama mamaye mata zuciyarta. Gabaɗaya zaman ƙasar ya fita daga ranta, komawa gisa take da buƙatar yi cikin gaggawa, bata son zaman ko kaɗan.

Ta jawo waya ta ga wanda ya kira ta, bata bi kiran ba ta kira Alhaji Musa. Bata jima tana ringing ba ya É—auka, suka gaisa sannan ta ce, "Don Allah zan iya ganin ka zuwa gobe?."

Alhaji Musa ya ce, "wani abun ne ya faru?."

Islahs ta ce, "eh, ina so na ganka don Allah."

"Zan shigo zuwa dare, ina garin Jeddah, amma ina airport, zuwa anjima zan zo."

Ta amsa ta kashe wayar ta koma ta kwanta, sai kuma ta miƙe ɗauko kuɗin da suke hannunta gabaɗaya. Wanda ya bata a ƙarshe suna nan bata taɓa su ba, ta bi kuɗin da kallo, da tana da dama da iko da ta ƙona su ko ta yi sadaka dasu, dan bata buƙatar amfani da abin hannunsa, amma tana buƙatarsu dole zasu yi mata amfani.

Riyal dubu sha bakwai ta irga, sune gabaɗaya  kuɗin har albashinta. Ta ɗauki waya ta yi converting kuɗin zuwa naira, ta ga kuɗin suna da yawa sosai, ya ishe ta ta biya su Mama ta koma gida da duk abinda zata yi. Ta sauke numfashi tana kallon kuɗin, a haka gasu ƴan kaɗan, amma a kuɗin nigeria kuɗi ne masu yawan gaske.

_Ƙarfin kuɗin nan dai shine ya ba ki, a cikin sha bakwai shine ya ba ki sha huɗu. Kin ga kenan da kuɗinsa za ki kashe wutar gabanki. Kuɗin mara mutunci, wanda ya ce miki karuwa. Kawai ki watsar!._

Abinda zuciyarta take faɗa mata kenan, ta rutse ido tana ji kamar ta yi hauka saboda takaici da ɓacin rai, tabbas kuɗinsa ne, ba dan ta haɗu dashi ba da bata samu kuɗi masu yawan waɗannan ba. Daƙyar ta rarrashi zuciyarta bata watsar dasu ba, ta haɗe su ta ajjiye ta yi tagumi tana tuna Labiba ta zubar da ciki.

Zuwa dare ya yi mata waya ya ce gashi ya zo, ta fita zuwa ƙofar gidan suka shigo compound ɗin tare.

Ya kalle ta ya ce, "Ya dai?."

Ta ssuke numfashi ta ce, "yanzu misali, in zan biya kuÉ—in da ku ka kashe ku ka kawo ni nan,
nawa zan bayar?."

Ya kalle ta ya ce, "a cure wai?."

Ga É—aga kai ya ce, "Miliyan uku ne da wani abun, a nan kuma zai kama riyal dubu takwas kenan."

Ta É—an yi shiru kafin ta ce, "in na bayar shikenan na biya gabaÉ—aya?."

Shi dai kallon ta yake yi ya ce, "eh."

Ta gyaÉ—a kai ta ce, "ina zuwa" ta faÉ—a tana komawa ciki.

Ba jimawa ta dawo ta bashi kuÉ—in, ya kalli kuÉ—in ya kalle ta ya ce, "Wai kin biya gabaÉ—aya kenan?."

Ta É—aga kai ta ce, "gasu ina ba ka."

Ya miƙa hannu zai karɓa sai ta fasa bashi, ta ce, "shaida nake so ka bani, wacce in na bayar kowa zai san na biya ka, bazan ba da kuɗin nan ba tare da shaida ba."

Ya murmusa ya ce, "buɗe idon ki da kyau yarinya, na fi ƙarfin na cuce ki, na wuce na damfare ki na karɓi wannan kuɗin. In ki ka je makka ki sha shiga kasuwar mai zogale, ki ka ce Alhaji Musa ki ke nema, babu wanda bazai nuna miki ni ba. Nawa riyal dubu takwas take a wajena da har zan cuce ki?."

"Nima ban ce zaka cuce ni ba, abu ne na shaida, ka saka hannu nima na saka hannu. Ina zuwa" ta faÉ—a tana sake komawa shi dai ya bita da kallo.
Chapter 92 · 0% Book details