← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 133

Sashe 71

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daada ta washe baki jin an fasa mata kai, ta gyara zama ta ce, "ni fa a idon mutum ina gane munafuki, ina gane maƙaryaci da ɓarawo. Da za a ɗauke ni aikin ɗan sanda da na taimakawa aikin su sosai, ba sai an sha wahalar bincike ba, ina ganin idon mai laifi zan ce mai laifi ne wannan. Wannan baiwar tun yarinta, har nemo ni ake yi na nuna ɓarawo."

Mama ta yi mata hararar ƙasan ido, amma a zahiri ta yi murmushi ta ce, "ko shakka bana yi akan hakan."

"Ina jin ki, ya aka yi?."

"Yariya ce mai kirki, ta sauke alkur'ani guda, sannan cikakkiyar ma'aikaciyar jarida ce. Gata da shigar mutumci, ga ta da hankali da girmama mutane. Sa....." kafin ta ƙarasa Daada ta dakatar da ita tana murmushi, tana hararo fuskar Islaha tana jin daɗi na mamaye ta.

Daada ta ce, "ni shaida ce, in dai tarbiyya da girmama na gaba ne tana dashi wallahi. Yarinyar da ta ganni a akan titi ta tsaya, ta sauko ta riƙe ni ta kawo ni har nan. Ai a iya nan an nuna tsantsar girmama ɗan adam da sanin martabar na gaba."

"Gaskiya tana da hankali, dan ma ance ta je ƙaro  ilimi."

"Kai ma sha Allah! Ashe dai irinsa ce Æ´ar boko."

"Irinsa ce kam Daada, kin ga itace daidai shi."

"Ai bari kawai. Wannan aure kamar an yi sa an gama, babu wanda ya isa ya dakatar dashi."

Mama ta É—an yi jim sannan ta ce, "amma sai nake gani kamar babarsa baza ta bari ayi auren nan ba, dan bata so."

Daada ta wani kalle ta ta ce, "a ƙarƙashin wa take?."

Mama ta ce, "mai gidan."

"Shi kuma a ƙarƙashin wa yake?."

"Wajan ki Daada."

Daada ta haÉ—e rai ta ce, "in ina magana ki daina saka min ita a lissafi. Wallahi Allah, kin ji na rantse ko? Babu wanda ya isa ya saka a fasa auren Ishlaya da Muhammad, ko mutuwa na yi sai an tabbatar dashi. Ko shi mijin nata bai isa ba balle ita kanta, dan haka ki É—auka auren nan kamar rubutu ne a kan dutse."

Mama ta murmusa cikin farin ciki ta ce, "har na ji daɗi, da na yi bincike akan yarinyar ba ki ji yadda ta shiga raina ba wallahi. Ta burge ni, ina son mace nutsatstsiya wacce za ki ji kowa yana yaba mata. Ance in ka mutu ma da shaidar bakin mutane mala'iku suke amfani. Shaida mai kyau ai rahama ce, tunda na ji yadda ake ta yabonta na ce wannan matar aure ce. Kuma daman na san Daada da kaifin basira, baza ki taɓa yi masa zaɓen tumin dare ba."

Daada ta yi murmuahin jin daɗi ta ce, "wannan gaskiya ne Saddiƙa, shiyasa nake sonki, dan kin fi su fahimta da saurin gane haske. Yanzu ki je a cigaba da shiri, aure babu fashi. Ke kafin auren Juwairiyya da Jafar za a yi bikin nan nasu, tunda uwarsa ta fara nuna bata so tsaf zata saka matsafan ƙasarsu su tsafe auren a kasa aikata komai."

"Da hakan ma ya fi Daada, dan komai zai iya faruwa wallahi."

"Matsala ɗaya, ance bata ƙasar, kuma an ce babanta yana asibiti."

"Gaskiya ne, amma da ta dawo ba sai ayi a wuce wajan ba."

Daada ta É—an yi jim ta ce, "zan san yadda zan yi. Jeki abin ki, na gode."

Mama ta miƙe ta fita ta koma ɓangarenta. Tana shiga ta ɗauki waya ta saka a kunne ta ce, "auren nan bazai fasu ba, na gama da batun auren a yanzu."

Wanda take magana dashi a wayar ya ce, "in kina hali da dama, za ki iya zuwa gida?."

Mama ta ce, "yanzu kuwa Malam, in zuwa." Tana kashewa ta kira Abba ta faɗa masa zata fita, bai hanata ba, ta saka Saleem ya ɗauke ta a mota suka fita. Daman indai fitar wajan malamai ce Saleem ne yake kai ta ba driver ba, saboda tana buƙatar sirri, bata so a san inda zata je.

*Madinah.*

Umma tana ta murna an bata albashinta na wata a hannu, duk da babu abinda ta rasa a gudan amma ta ji daÉ—i sosai. Duk ta rame saboda wahala, Allah ya taimake ta tunda ta yiwa mai gidan barazana bai sake zuwa inda take ba sai shegen kallo kamar maye.

Tana tsaye tana aiki sai ga kiran Hajiya Shafa ya shigo wayar ta, ta É—auka ta saka a kunne ta ji me tace sai ta kashe wayar.

Umma ta koma ɗaki ta saka hijjab ta fita zuwa ƙofar gidan, ta ga Hajiya Shafa da Alhaji Musa a tsaye.

Umma ta ƙarasa ds fara'a ta ce, "barkan ku da zuwa."

Alhaji Musa ya ce, "barka. Ina albashin?."

Umma ta yi sak tana kallon su, kafin ta ce"Yana ciki, É—azu aka bani."

"Jeki ki É—auko mu gani." Bata musa ba ta juya ba jimawa ta dawo dasu.

Ya karɓa ya ga riyal ɗari bakwai ne, ya zari riyal ɗari biyar ya bata ɗari biyu ya ce, "wannan itace tamu ta kamfani, wannan kuma sune naki."

Kafin Umma ta yi magana Hajiya Shafa ta ce, "bani riyal tamin É—in da na ranta miki, ki ka siyi layin waya."

Kafin Umma ta yi magana ta zare riyal É—ari a hannunta, ta canja ta bata riyal ashirin ta ce, "sai ki adana waÉ—annan."

Umma a ɗan zaman da ta yi tana ɗan gane kuɗin ƙasar, tunda haka kawai yaran gidan zasu aike ta kuma dole sai ta je, ta haka take ɗan fahimtar kuɗin kaɗan kaɗan. Ta juya kuɗin a hannunta ta ce, "Daga riyal ɗari bakwai na dawo riyal ɗari ashirin, shine kuɗina?."

Alhaji Musa ya ce, "shine naki mana."

"Amma ni nake shan wahalar aikin nan, gwara Hajiya Shafa na san bashi ne na ci dole na biya ta. Ina laifin ku É—auki riyar É—ari biyu ku bar ni da É—ari biyar É—in? Ni nake shan wahala, kalli hannuna duk ya goge saboda yi musu wanki, duk da akwai injin wanki amma wani abun dole sai ka saka hannu ka wanke. Ta ya riyal É—ari da ashirin zata kai ni wata? Bakwa jin tausayina ne?."

Nana Haleema.
[7/10, 11:05 AM] KRBBK: RDB2P50
Nana Haleema.

Alhaji Musa ya bita da harara ya ce, "ban gane ba ma tausyain ki ba? Tun farko ba an faÉ—a miki yadda tsarin yake ba? Me ki ke siya da za ki raina kuÉ—in hannun ki? Kim san naira nawa ne wannan?."

"Duk da haka, na san da batun za a dinga rabawa uku, na É—auki kashi É—aya ku É—auki biyu, amma cemin aka yi riyal dubu É—aya da É—ari biyar za a bani, yanzu kuma na ga riyal É—ari bakwai, ko dubu bai kai ba."

Hajiya Shafa ta riƙe baki ta ce, "Ke ɗin za a bawa riyar dubu ɗaya da ɗari biyar? Bakya jin turanci, babu larabci, ga ƙorafi, a haka za a baki wannan kuɗin?."

Hajiya Shafa ta kuma cewa, "Kuma ƙarya suka yi miki, tun farko da aka ce ana neman ki ba dubu da ɗari biyar aka ce musu ba. Su ma na Jeddah da za a basu haka ne saboda yara ne, kuma suna jin turanci, kuma a gidan ma'aikata suke. Ke kuwa har yanzu zo bakya ganewa da larabci, a haka za a baki kuɗin da ki ka ambata?."

Umma ta ce, "Amma ni ba haka suka faÉ—a min ba, dubu da É—ari biyar suka ce."

"Roman baka ne, dan ki yarda ki zo kuma kin zo."

Umma  ta yi shiru bata ce komai ba saboda takaici, Alhaji Musa ya ce, "saboda haka na zo a canjata tun a Yola, irin waɗnan matan buri ne dasu, gani suke in suka bar nigeria kamar kuɗi zasu yi, sun baro ƙasar su sun zo nan inda zasu yankewa talauci cibiya. Ki gode Allah, na rantse da Allah da riyar ɗari bakwan da aka baki sai kin kawo ta, ruwanki ne ki nemi kuɗin kashewa ta wata hanyar, ruwank ki zauna haka. Babu ɗaga ƙafa a lamarina, tunda ka ki ka amince sai abinda ki ka gani."

Umma kamar zata yi kuka ta ce, "amma babu adalci a lamarin nan. A kuÉ—in nan zan si yi magani in bani da lafiya, ga abubuwan amfanin yau da kullum."

"Ke ki ka san adalci, wani watan in Allah ya kaimu zan zo na karɓa, kuma dole ki bayar, in ba haka ba yan sanda su kama ki. Shaafa mu je."

Umma tana gani suka tafi, ta koma jiki a sanyaye tana duba kuÉ—in. Ashe daman roman baka su Mama suka yi mata a harkar nan, ita bata ga jin daÉ—i da tara kuÉ—in da suke cewa zata yi ba, ina tara kuÉ—i tana fama da wahala kamar jaka? Kullum ana tula mata aiki kamar wata mara galihu. Kuma duk wannan aikin ace a iya kuÉ—in da zasu tsaya kenan?.

Ta juya kuÉ—in kafin ta ajjiye, ta yi tagumi tana tuna Æ´aÆ´anta da ta tsalleke ta baro saboda neman kuÉ—i, gashi kuÉ—in baza su taru yadda take tunani ba.

*Jeddah.*

Yadda suka je wajan Umma suka karɓa haka suka je wajan Islaha, ita bata musa ba ta bayar dan ta san daman haka aka ce.

Labiba kuwa gabaɗaya ta ce su riƙe suka dinga yi mata godiya.

Islaha bayan sun rabu, sabon content ta ɗauka ta gama editing ta yi sharing. Ta sauke numfashi, tana son komawa gida kuma tana son zuwa Madina ta ga Umma, haka kawai take so ta je ko dan amanar ƙawarta.

Ta saka hijjab da niyar zuwa gidan Rehaan, kwana biyu ko ga je bata ganinsa, bata san ina yake zuwa ba, amma bata ganinsa kwata-kwata.

Hakan yana yi mata daÉ—i, dan ita ganinsa ma fusata yake yi, sai ta dinga tuna abinda ya yi mata ta ji kamar ta zane sa. A haka ta shirya ta nufi gidan tana tafiya a hankali.

Rehaan yana sama, suna zaune shi da Jafar da ya gama hutun gajiya yake hutawa a zaune.

Rehaan ya ce, "sai yanzu ka ga damar zuwa, bayan na faÉ—a maka ina da abubuwan da zamu yi?."
Chapter 71 · 0% Book details