← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 133

Sashe 97

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     A jirgi suka yi sallar asuba, ƙarfe tara na safe jirginsu ya dira a Abuja. Bayan ta gama komai ta ɗauki kayanta kuma ta zauna jiran jirgin da zai kai ta Adamawa state.

Sai ƙarfe sha biyu sannan komai ya zama ready, mota ta ɗauke su zuwa inda stairs ɗin jirgin yake. Awan su uku a sama sannan suka sauka, tun a airport ta canja wasu kuɗin zuwa naira, ta yo drop ɗin taxi zuwa gida zuciyarta tana bugawa, dan bata san abinda zata tarar a wajan Mama ba, bata san yadda zasu kwashe da Hamma ba, wacce irin amsa zata bashi in ya tambaye ta? Ta bashi labarin Rehaan Yola ko kuma ta yi shiru?. Da wannan tunanin aka cigaba da tafiya, tana kallon Yola cikin yanayin kewa.

Ya ku ke ganin Hamma zai karɓi maganar Rehaan? Mama zata bari ta zauna a gidan ta? Ana ta shirin auren Rehaan, ya abin zai kasance?
Drama don start🔥❤️❤️

Nana Haleema✍🏻❤️
[7/21, 12:04 PM] KRBBK: RDB2P71
Nana Haleema.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_

Islaha a ƙofar gidansu Safeera aka sauke ta, daman ta yi canjin riyal zuwa naira tun a airport, ta biya kuɗin mota aka sauke mata kayanta aka shiga dasu gidan su Safeera.

Da sallama Islaha ta shiga cikin gidan, Safeera da Kausar da Rukayya suna zauna a tsakar gidan suka ji sallama sai kuma ga kaya an shigo dasu.

Safeera ta yi wani ihuu ta miƙe cikin gigicewa, a guje ta ƙarasa ta ƙanƙame Islaha tana ihun murna.

Islaha tta ce, "Dallah za ki cillar dani" ta faÉ—a tana murmushi.

Safeera ta riƙe hannun Islaha tana kallon ta cikin wani irin yanayin murna da ɗimaucewa ta ce, "Islaha ke ce?." Ta harare ta bata ce komai ba ganin Mama ta fito daga ɗaki.

Islaha ta ƙarasa kusa da Mama ta ce, "Mama ina yini."

Mama ta bita da murmushi ta ce, "Ai dole Safeera ta yi ihu, ina ciki na jiyo ihunta, ashe kece a tafe. Sannu da zuwa Islaha."

Islaha ta murmusa ta ce, "yauwa Mama."

Kausar ta ce, "Kin ga yadda ki ka yi kyau? Kin sake zama kalar madara."

Ta yi dariya bata ce komai ba Rukayya ta ce, "Adda Islaha ina Umman mu? Tare ku ka dawo?."

Islaha ya girgiza kai ta ce, "Ni kaɗai ce, Umma tana can, amma tana gaishe ku, akwai saƙo ta bani na kawo miki."

Sai jikinsu ya yi sanyi ta ce, "ita meyasa bata dawo ba?." Islaha bata iya bata amsa ba, dan bata san me zata ce musu ba, gwara ta yi shiru ya fi zama alkhairi.

Mama ta ce, "Ku bar ta ta huta, shiga ciki Islaha." Islaha ta shiga É—akin Safeera, tana shiga ta cire mayafin kanta, ta cire ribbon É—in kanta tana barbaza gashinta dan zafi take ji a cikin gashin.

Safeera ta shigo mata da kayan da aka shigo dasu ta ce, "Kin dawo ƙasar mu mai zafi, gashi nan har kin fara cire ribbon."

Islaha ta kalli Safeera ta ce, "bacci nake ji, taimaka min za ki yi da ruwan zafi na yi wanka na yi sallah na kwanta."

Safeera cikin murnar ganinta ta ce, "An gama mutanen Jeddah." Babu jimawa ta kawo mata Islaha ta yi wanka haÉ—e da alwala.

Tana fitowa Safeera ta shigo mata da abinci, Safeera ta bita da kallo tana zama kusa da ita ta ce, "ke kin ga yadda ki ke wani shining na kyau? Kin ga yadda skin É—inki ta yi kyau?."

Ta harare ta ta ce, "ki bar abincin nan Bestie, sai na tashi daga bacci."

Safeera ta bita da kallo ta ce, "Wallahi na kasa gasgatawa ke ce É—in, gani nake kamar mafarki nake yi."

"Ki cigaba da mafarkin."

Safeera ta yi dariya sosai ta ce, "kawai sai na gan ki, ba labarin za ki dawo."

Islaha ta ce, "daman na ce babu wanda zan faÉ—awa sai na dawo, har Hamma ban faÉ—awa ba."

Ta girgiza kai tana murmushi ta ce, "To ki sauri ki kwanta ki tashi, ki bani labari." GabaÉ—aya zumuÉ—i ganin Islaha ya cika mata zuciya, ji take kamar kar ta bar ta ta yi bacci.

Islaha ta yi dariya ta tayar da sallah, bayan ta idar da sallah kwanciya ta yi bacci ya É—auke ta.

Har aka yi magrib bacci take yi, sai bayan sallar i'sha ta tashi. Kai tsaye banÉ—aki ta shiga ta yi alwala ta fito ta yi sallah.

Safeera ta shigo tana faÉ—in, "kin sha bacci, tun É—azu nake shigowa sai in ga ba ki tashi ba."

Islaha ta ce, "na gaji ne Safeera. Daga Jeddah na zo Abuja, ban wani huta sosai ba na taho Yola."

"Na kawo miki abincin ko za ki fito falo?."

Islaha ta ce, "kawo min nan. Baba ya dawo?."

"eh ya dawo."

"mu je na gaishe sa sai na dawo." Ta saka hijjab ya fito har É—akin Baba.

Baba yana ganin ta ya murmushi ya ce, "Islaha saukar yaushe?."

Ta yi murmushi suka gaisa sannan ta ce, "saukar É—azu Baba."

"Sannu da zuwa."

"Yauwa Baba. Ina yini?."

"Lafiya lau Islaha, ya hanya?."

"Alhamdu lillah."

"Ma sha Allah.."

Khadija autarsu Safeera ta ce, "Adda Islaha Umma bata dawo ba, yaushe zata dawo?."

Islaha ta kalle ta ta ce, "ta kusa dawowa, ki kwantar da hankali ki."

Sai kawai ta fara kuka ta ce, "ina so na ga Umma, ki kaini wajanta." Islaha ta riƙe hannunta ta ce, "kar ki kuka, ki bari in zan koma zan tafi dake wajanta, kina so?."

Ta yi murmushi tana É—aga kai, Islaha ta ce, "Yauwa, to daina kuka." Ta daina kuka Islaha tana murmushi ta koma É—aki.

Mama har É—akin ta shiga ta kaiwa Islaha abinci sannan ta bar su ita da Safeera suna hira.

Islaha bata ce komai ba ta buÉ—e abincin ta ga shinkafa da miyar kifi, ta yi ajiyar zuciya ta ce, "kai amma na ji daÉ—in abincin nan, saura shinkafa da wake da mai da yaji" ta faÉ—a tana ci a hankali har ta ci rabi.

Safeerata kawo mata ruwa ta sha ta sauke numfashi alamun ta ƙoshi.

Islaha ta ce, "Na ƙoshi wallahi, miyar nan ta yi daɗi sosai."

Safeera ta ce, "sai na gan ki ƙwatsam, ni ki bani labarin ya aka yi ki ka dawo."

Islaha ta kalle ta ta ce, "Kai bestie, kin cika gulma wallahi, lallai sai na ba ki labari? Ki jira na gama hutawa mana, ko gidansu Hamma ban shiga ba fa."

Ta yi dariya ta ce, "Ai tunda na gan ki a nan na san ba ki shiga ba."

"wallahi matsalar Mama ce bana so, shiyasa na zo nan na huta, in Baffa ya dawo sai mu gaisa, na fi jin daÉ—in gidan in Baffa yana nan."

Safeera ta harare ta ta ce, "wai baza ki faÉ—a min ba, sai ja min aji ki ke yi."

Islaha ta yi dariya ta ce, "zan faÉ—a miki, abin ne kamar tatsuniya wallahi, kar ki ce na raina miki hankali."

Safeera ta ce, "Ke wallahi harshen ki ya fara komawa na larabawa, har wani la la ki cewa."

Suka yi dariya gabaÉ—aya Islaha ta ce, "Wallahi ban san ya shiga bakina ba, kuma zama da Sunaira ne, amma dan ta Maleek larabci bazai zauna a bakina ba, saboda da turanci mu ke magana."

"Ina jin ki, bani labari."

"Kar na faÉ—a miki ki ce drama ce."

"Kema in dramar ce ai kin sani."

Islaha ta yi murmushi tana ɗaukar wayarta tana dubawa ganin chaji ya kusa ƙarewa. Ta kalli Safeera ta ce, "na gama abinda ya kai ni, shiyasa na dawo."

Safeera da mamaki ta ce, "kin gama kamar ya kenan, Har kin samo kuÉ—in?."

Ta É—aga mata kai alamun eh, da mamaki Safeera take binta da kalko kafin ta ce, "ta ya kenan? Ko duk wata miliyan biyar ake ba ki, bai ci ki haÉ—a wannan kuÉ—in ba, dan ba ki yi wata uku ba har yanzu."

Ta furzar da iska ta ce, "Ba na faÉ—a miki akwai gidan da nake shiga na yi aiki bayan wanda nake ciki ba?." Ta É—aga kai alamun ta sani.

Islaha ta ɗan yi shiru dan bata san ta ina zata fara ba, kar ta ga kamar ta raina mata hankali tana ɓoye mata wani abun.

Safeera ta ce, "ina jin ki."

Islaha ta ce, "A gidan da nake zuwa na samu kuÉ—in da na biya bashin, kuma na dawo gida."

"ban gane ba, a gidan da ki ke zuwa ki ka samu wannan kuÉ—in?."

"Ke ba wani kuÉ—in na kuma É—aukowa ba, na ga kina yi min kallon tuhuma."

"Ai dole na yi miki, abin da mamaki ai. A cikin wata biyu da Æ´an kwanaki har kin haÉ—a miliyoyin kuÉ—i?."

"Ke dallah, ko yankan kai nake yi ai bai ci na haÉ—a kuÉ—in nan ba. Biya min aka yi.

"Waye ya biya miki? Wa ki ka sani a Jeddah da zai biya miki wannan kuÉ—in?."

Islaha ta miƙe tsaye tana share zancen ta ce, "bar ni na fara buɗe kayan nan, na bar na ajjiyewa a nan, san bana so Mama ta saka ni a gaba da tambayoyin banza. Bani reza na farka silling ɗin nan." Ta faɗa tana zuwa wajan kayan da suke a ajjiye.

Safeera ta bata reza ta farke kayan tana fitowa dasu daga ciki.

Safeera cikin tuhuma ta ce, "kin share maganar da muke yi Islaha, kin saka min ayar tambaya akan ki."

Ta kalli Safeera ta ce, "ban san ya za ki É—auki maganar ba, bana so ki sake zargina, dan maganar bata yi kama da hankali ba, ina faÉ—a miki za ki ji kamar na raina miki hankali."

"Shirun na ki ne zai saka na zarge ki, gwara ki faÉ—a min kin san ni mai fahimtar ki ce."

Islaha ta dakata da fito da kayan ta ce, "gidan wanda nake shiga aikin, shine wanda ya sace ni É—in nan, har na É—auko masa kuÉ—insa....." ta É—an ja numfashi sannan ta ce, "Kuma a gidan na samu kuÉ—in da na biyasa har na dawo gida."
Chapter 97 · 0% Book details