Sashe 21
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Saheer ya ce, "tunda baki da dalili ba za a rufe case ɗin nan ba Islaha, har Ummin baza ta fita ba. Domin zamu je ayi rubutu nida iyayenta, duk abinda ya same ki wallahi sai na ɗaure ta. Kuma dole ki basu bayani mai gamsarwa akan maganar nan, baza a ƙyale case ɗin ya tafi a banza ba wallahi, kin ji na rantse ko?."
Ta É—an girgiza kai cikin rashin mafita ta ce, "To Hamma."
Sai a sannan ya kalli Sadik da Saleem ya ce, "ku yi haƙuri, ashe bamu gaisa ba" ya faɗa yana basu hannu.
Suka gaisa suna dariya, Safeera ta ce, "ta ya zamu gaisa, ka ga Islaha ai dole ka manta damu."
Ya yi murmushi ya ce, "Hankalina ne a tashe, sai da na baro ƙasar nan sannan na samu nutsuwa. Ina labarin waɗanda suka yi waya akan kuɗin fansar ta?."
Sadik ya ce, "Amfani aka yi da ɓatanta aka kira dan a damfare mu, suma za a yi bincike a gano waɗanda suka yi wayar."
Ya É—aga kai ya ce, "babu wanda zai sha a cikim case É—in nan wallahi, ko shi wanda ya É—auke ta É—in ne sai mun yi shari'a dashi indai ina da rai."
"Hakan ne ya kamata daman" Saleem ya amsa yana kallon Islaha.
Saheer ya ce, "Ya kuÉ—in aikin Baffa? An gama haÉ—awa ne Sadik?."
Sadik ya É—an kalli Islaha yaga ta zuba masa ido alamun kar ya faÉ—a, ya É—auke kai daga kallon ta ya ce, "uhum an samu, har an biya ma. Sai dai mu yi fatan Allah ya sa a yi a sa'a."
"Amin. Amma baka faÉ—a min an gama ba."
"Ina gama biyan kuÉ—in islaha ta bayyana shiyasa na manta."
Ya É—aga kai, ya juyo yana kallon Islaha ganinta tsaf da ita kamar babu abinda ya faru da ita ya ce, "babu alamun wahala a tare dake, kin dai É—an rame kaÉ—an, amma kwata-kwata baki yi kama da wacce aka sace ba."
Ta sunkuyar da kai ta ce, "kaina ciwo yake yi min Hamma" ta faÉ—a dan ta kawar da waccan maganar.
Ya bita da kallo cike da kulawa ya ce, "muje ki huta" ya faɗa yana miƙewa, ya riƙe hannunta suka shiga ciki.
Sadik ya kalli Safeera ya ce, "ƙawar ki akwai abinda take ɓoyewa wanda bata so mu san dashi."
Safeera ta girgiza kai ta ce, "nima na gani, zan je naji ko meye, dan na tabbatar zata faÉ—a min. Ina zuwa" ta faÉ—a tana bin bayansu da sauri......
Nana Haleema.
[6/22, 9:42 AM] KRBBK: RDB2P014
Nana Haleema
Rehaan yana zaune a falon Mamy yana danna wayarsa, magana yake akan sabuwar order da ya yi gabaɗaya ya yi busy har su Mamy suka zauna bai sani ba. Ƙaramin tsaki ya yi yana dafe kai, sai kuma ya kira waya ya saka a kunne ya fara magana cikin turanci.
Ya fi mintina arba'in yana waya, sai ya sauke wayar ya yi ajiyar zuciya, sannan yaji Mamy ta ce, "Mr Busy."
Ya hankali ya juyo suka haɗa ido, suna haɗa ido ya yi murmushi ya ɗan langwaɓar da kai cikin shagwaɓar da ya saba yi mata ya ce, "neman halak da wahala Mamy."
Ikram da take zaune ta ce, "awwwn! Bruh ashe ka iya karin magana?."
Ya ɗaga ido ya kalle ta suka haɗa ido, a lokacin ta ƙaraso ta basa hannu alamun su gaisa. Bai musa ba ya bata hannu suka gaisa, ya ɗan yi murmuahi ya ce, "Ikram, ya Mummy?."
Ta zauna a gefensa tana kallonsa ta ce, "tana gaishe ka." Ya É—an É—aga kai yana kallon falon sannan ya ce, "Ina Riyya da Kiddo?."
A guje Kiddo ta taho ta zauna kusa dashi tana riƙe hannunsa tana kallonsa ta ce, "My love."
Ya shafa kanta ya ce, "My love bakya yi min waya."
Cikin shagwaɓa ta ce, "na kira ka baka yi picking calls ɗin ba."
Ya ɗan buɗe ido, sai ya ɗauki waya ya shiga recent calls ɗinsa, a nan ya yi karo da kiran ta har sau biyu. Ya ɗaga ido ya kalle ta, sai ta fara kukan shagwaɓa kamar bata girma ba ta ce, "kana gani ka ƙi ka ɗauka. Ka daina sona."
Ya riƙo ta ya ce, "I'm sorry Kiddo, banga kiran ki ba, da zan yi pecking."
Ta turo baki ta ce, "ni dai a'a."
"Me ki ke so?."
"Mu tafi Jeddah tare."
"sai kin je Jeddah zaki haƙura?."
"Eh."
"Kiddo ni kaÉ—ai ne a Jeddah, Jazy baya nan, in na tafi aiki da wa zaki zauna?."
Sai ta É—an yi jim kaÉ—an ta ce, "to yaushe zaka je danii?." Ya ja hancinta ya ce, "zan turo a zo a tafi dake."
Ta É—aga kai ya yi murmushi sannan ya ce, "Ina Riyya?." Banisha ta ce, "Tana school."
"Janan fa?."
"Tana wajan aiki."
Ya gyaɗa kai bai ce komai ba, a lokacin Riyya ta dawo daga makaranta. Mamy ta miƙe ta ce, "tunda ga Riyya ta dawo muje muyi lunch gabaɗaya."
Tare suka hau kan dining har Ikram aka fara cin abinci, rabin zaman nasa amsa waya yake yi, ko ka ji shigowar saƙo ya mayar da amsa ya cigaba da cin abincin. Mamy ta zuba masa wani abu ta miƙa masa, ya kalla yana kallonta ya ce, "meye wannan?."
Mamy ta ce, "moimoi."
"Moimoi!."
Mamy ta ce, "in baka ci ka daina harararsa."
Ya É—an ture ya ce, "bana so Mamy. Kema sun koya miki cin wannan abun" ya faÉ—a yana cigaba da shan tea É—insa yana danna waya. Mamy ta ce, "Kai kuwa dole na koya ai, zaman da nayi a nan ban yi shi a inda aka haife ni ba."
Ikram aka kira a waya, ta ɗaga waya tana magana kafin ta kashe ta ce, "Mamy zan je gida yanzu, zan dawo in anjima." Mamy bita da kallo tana murmushi ta ce, "To Ikram, a gaishe da Mummy."
"Zata ji. Byee Riyya, byee Hamma" ta faÉ—a tana É—aga masa hannu ta fita.
Mamy ta kalle sa a lokacin ya ce, "gobe zan yi tiyata Mamy, sannan a daren zan tafi Jeddah."
Riyya ta ce, "Jeddah!"
Ya kalle ta ya É—aga kai alamun eh. Riyya ta ce, "Hamma why are you always traveling? We don't get enough time to spend with you. We really need you in our family. Daga Uk sai Jedda, kullum baka nan."
Ya kalle ta ganin cikin yanayin damuwa take maganar, hakan ya tabbatar masa har zuciyar ta take yi ba wasa take yi ba. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Riyya akan aiki, zan je wani asibiti for three months contract."
Riyya ta yi fushi ta miƙe tsaye ta ce, "meyasa ko yaushe kana kan aiki? Meyasa baza ka tsaya a nan ba? meyasa lallai sai ka je can?."
Ya riƙo hannunta ta zauna ya ce, "calm down Riyya, ba abin ɗaga hankali bane." Idonta ya ciko da ƙwalla ta ce, "Muna son ka dinga zama a kusa damu, muna so mu dinga hira da kai. Kai kaɗai ne Yayanmu, su Hamma Sameer yayansu su Janan ne, kaine namu. Don Allah ka dinga zama a kusa damu, ka ji?."
Rehaan ya kalli fuskar ta cikin damuwa ya ce, "ko yaushe muna tare, kar ki damu."
Riyya ta miƙe ta tafi ɗaki bata sake kula shi ba, ya bita da kallo cikin damuwa. Gabaɗaya ahlin Mamy babu wanda yake si yaga ɗaya yana fushi, sun fi so kowa ya kanace cikin farin ciki da walwala. Ba dan aiki ne zai kai shi Jeddah ba, tsaf zai iya fasa zuwa saboda fushin da Riyya ta yi, sun san darajar kansu, suna ƙaunar junansu, suna yiwa juna abinda ɗaya yake so.
Mamy ta kalle shi ta ce, "su ma ƴan uwanka basa son zaman ƙasar wajen nan da ka ke yi, balle kuma ni mahaifiyar ka. Duk dani wani lokacin nafi son zaman ka a can ɗin, kafi zama lafiya kana sakewa fiye da zama a nan ɗin."
Ya yi shiru bai ce komai ba, dan baza su fahimta ba. Ita Mamy ta san baya son zaman ƙasar gabaɗaya, takura yake yi kuma baya sakewa, shiyasa da aka kawo masa contract ɗin ma ya karɓa kawai, dan baya son abinda zai haɗa shi da zama a nigeria ko kaɗan. In haka akwai ne Abba baya bari ya zauna, amma in aiki yake yi bai cika takura masa akan ya dawo ba.
Mamy ta sake kallonsa ta ce, "Banisha tana son zama tare da kai, kaga da kana da aure sai ku je tare ku dawo."
Bai ce komai ba dan bai san amsar da zai faÉ—awa Mamy a wannan maganar ba. Kamar ta fi kowa sanin bashi da aure, kuma bai yi niyar yi a nan kusa ba.
Mamy a tausashe ta ce, "meyasa baza ka yi aure ba?."
Ya kalli Mamy cike da gajiya da maganar ya ce, "Aure Mamy! Na auri wa?."
"Why Ikram?."
Ya É—an buÉ—e ido cikin mamaki ya ce, "ikram!."
"eh ita. Tana sonka, kuma zaka iya aurenta, dan kaf cikin cousins ɗinka babu kamar gidansu Jafar. Suna sonka tsakani da Allah, ba dan wani abu da ka ke daahi ba. Kuma Ikram tana da kirki da hankali, zan yi farin cikin karɓarta as my daugher inlaw."
Ya sake kallon Mamy yana girgiza kai ya ce, "i'm not interesting."
Mamy ta dafa kafaÉ—arsa ta ce, "Why? Meye aibu dan ka auri Ikram?."
"Mamy a matsayin Riyya nake kallon ta, bazan iya kallonta a matsayin matata ba. Infact duk wata cousin sistera É—ina bazan iya kallonsu a matsayin matan aure ba, Æ´an uwa ne kawai. Yadda babu aure tsakanina da Riyya ko Banisha, suma babu. Bazan iya kallon cousin sister as my wife ba."
Mamy ta girgiza ta ce, "Haka Jafar ma ya dinga cewa, amma yanzu saura few days bikinsa da Riyya. Zaka iya auren Ikram kaima, kamar yadda zai auri Riyya."
Ya girgiza kai ya ce, "shi ya ga zai iya Mamy, amma ni bazan iya ba. Dan zai auri Riyya ba hakan yana nufin zan auri Ikram ba."
"Amma ka san Ikram tana sonka ko?."
"Na sani, nima ina sonta as my sister, soyayyar da nake yiwa Riyya nake yi mata, ba wacce zan aura ba."