← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 133

Sashe 116

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jafar ya ce, "kana ji, ni ba wai aurenta nake so ka yi ba, ba goyan bayanta nake yi ba, ina faÉ—a maka ka daina yi mata zato akan abinda ba ka da tabbas a kai, sannan ka yarda babu wani plan a lamarin yarinyar nan, sannan ka amince ka yi abinda Abba ya ke so. Bayan nan babu wani abu a raina, babu wani dalilin da zai saka na ce ka amince saboda ra'ayin kaina. Kuma na ba ka shawara ka daina kiranta da karuwa, kuma kar ka faÉ—awa kowa wannan maganar, bai kamata a jita a bakin ka ba. Ba class É—in ka bane, in aka ji maganar karuwa a bakin ka za ka zubar da class É—in ka."

Ya sauke numfashi ya ce, "a ko yaushe ra'ayinmu É—aya da kai, meyasa yanzu ka canja?."

"Ban canja ba Ray, ina faÉ—a maka abinda ya kamata ka yi ne kodan saboda mahaifinka. Ka daina kiran yarinyar nan da karuwa, ko da karuwar ce bai kamata ka dinga faÉ—a ba, tunda ba gani ka yi ba, hasashe ne."

"sai ka ce na daina cewa haka, ka san abinda na gani da idona meyasa ka ke ce min haka? Irin wannan yarinyar ka ke cewa na aura?. Rehaan Yola ne, ko ka manta ne?."

"Ban manta ba mana."

"Abba bai yi bincike a kanta ba, bai ga halayen ta ba?."

"Ya ce shi bai ji wani hali mara kyau a kanta ba, in ka faÉ—a masa a yanzu zai ga kana yi mata sharri ne dan ka gudu daga auren."

Ya dafe kai cikin takaici ya ce, "wai na gudu! Oh my god."

Jafar ya yi masa bai ce komai ba. Rehan ya dinga sauke numfashi kamar wanda ya yi gudu, ya rufe ido yana ji kamar ya kurma ihu saboda takaici da ɓacin rai. Da wata daban ce ba Islaha ba sai ya yarda da auren, amma tunda aka ce Islaha ce sai ya ji bazai iya ba.

Jafar ya ce, "yanzu sai mu je gidansu ku tattauna ko? In ka yi mata ta ga zata iya auren ka sai ta taimaka maka ta aure ka, in ba ka yi mata ba a kai kasuwa" ya faÉ—a yana gimtse dariya dan so yake ya sake tsokano sa.

Sai kuma ya kalle sa, saboda takaici ma bai ce komai ba sai numfashi da ya sauke yana cize lips ɗinsa kamar zai fasa shi da haƙora.

Jafar ya yi dariya ya ce, "Ango! Ango!!." Yana faɗa yana dariya, sai wayarsa ta yi ƙara, yana dubawa ya ga Abba ne yake yi masa waya, ya ɗauka ya saka a kunne ya yi magana sannan ya kashe.

Jazy ya kalli Rehaan ya ce, "Abba ya ce ka same shi a ɓangaren Daaada, ni dai zan wuce gida, Ba kasafai na cika gaisawa da kakar nan ta ku ba, in ka fito ka same ni sai mu tafi gidansu budurwarta ka, in ba ka same ni ba...."

Kallon da ya ɗago yana yi masa ya hana Jafar ƙarasawa, ya yi dariya sosai harda tafa hannu ya fita, ya bar Rehaan da kayan takaici..........

Nana Haleema.
[7/27, 11:49 AM] KRBBK: RDB2P87
Nana Haleema.

Walking slowly ya shiga falon kansa a ƙasa, ɓacin ran da yake ciki bazai barsa ya ɗaga kai ya kalli mutanen falon ba, ya nemi waje ya zauna bai kalli kowa ba.

A hankali ya ce, "Ina yini."

Daada ta bisa da kallo ganin ya É—an rame, ta ji labarin ya yi ciwon ciki kuma gashi nan ta gani a kan fuskarsa.

Amma duk da haka sai ta ce, "Gaisuwar tawa ce ko ta iyayenka?."

Ya yi shiru baice komai ba, kuma ya ƙi ya ɗaga kai ya kalli kowa dan duk haushi suke bashi.

Daada ta ce, "na yi maka uzurin raahin lafiya. Ka ji maganar auren ka ai ko?."

Bai motsa ba balle ya amsa mata, bata damu ba ta ce, "Ranar juma'a mai zuwa za a É—aura aurenka Muhammad, sai ka fara shirye shirye, in za ka yi shagali ka yi, in baza ka ba dai kai ka sani."

Nan ma bai ce komai ba sai Mama da ta ce, "Shagali kai Daada, bikin Rehaan guda in ba a yi shagali ba a bikin wa za a yi?."

Daada ta kalle ta ta ce, "kin san halin nunƙufurcinsa, bazai bar shi ya yi abinda ya kamata ba. Da ya yi shagali, da kar ya yi duk ɗaya ne, aure ne wallahi sai an yi."

Ta sake kallonsa ganin ko kallon ta bai yi ba ta ce, "batun gidan da za ka zauna, umarni ne ba wai shawarar wani nake nema a nan ba. Ban ce kowa ya ce min komai ba, ban ce kowa ya kawo min shawararsa akan hukuncina ba...." Ta faÉ—a tana kallon kowa.

Kowa ya yi shiru yana jira ya ji me zata ce, har shi Rehaan É—in so yake ya ji abinda zata faÉ—a.

Daada ta ce, "Ban amince Rehaan ya fita daga gidan nan zuwa wani gida daban ba, ban damu da gidajen da yake dasu a garin nan da wajen garin nan ba, ban damu da yana da gidaje masu yawa ba, umarni ne ba shawara ba, a cikin gidan nan nake so ya zauna. Ɓangarensa ya ishe sa ya zauna da matarsa, dan haka a nan zai zauna ban amince ya fita ba."

A lokacin ya É—aga ido yana kallonta, suka haÉ—a ido ta ga yadda fuskarsa da idanunsa suka canja, ya É—an lumshe ido ya buÉ—e a kanta.

Ta ce, "ka ke kallona da wasu idanun ka masu kama da na maguna, ka ji abinda na ce ai ko?."

Ya ɗan ɗaga kai yana kallon ta, muryarsa a sanyaye ya ce, "meyasa bakya sona ne Daada? Duk abinda zan yi farin ciki a duniya sai kin hana shi, duk abinda zai saka min walwala sai kin hana. Abinda zai saka ni baƙin ciki a ko yaushe shine burinki, abinda zai ɓata min rai ya hanani walwala shine burin ki. San....."

Abba ya dakatar dashi ya ce, "Rehaan!."

Ya kalli Abba ya ce, "Abba ka bar ni na faɗa mata, ta ce aure zata yi min da wata yarinya, duk waɗanda suka yi aure a gidan nan kowa an bashi dama ya auri zaɓinsa, amma ni da yake ba a sona an ce ban isa ba, sai dai na auri wacce aka zaɓa min. Ka ce na yi haƙuri kuma na yi, ka ce na yi haƙuri na karɓi auren na haƙura na karɓa, yanzu kuma kana ji tana cewa na zauna a nan..." ya ƙarasa faɗa cikin ɓacin rai, amma maganarsa a hankali take fita, kuma a kakkatse.

Mama ta ce, "Rehaan ba ka da kunya ashe? Daada da mahaifinka ka ke faÉ—awa haka?. Daadan ba ita ta haifi mahaifinka ba, bata isa da kai ba kenan?."

Ya kalli Mama zai yi magana Abba ya ce, "Ya isa haka Rehaan, kar ka ce komai."

Ya ɗaga kai ya mayar da kansa ƙasa, muryarsa a sanyaye ya ce, "a yaushe haka ka ke cewa kar na ce komai, na yi shiru Abba."

Daada ta saki baki tana kallonsa, sai kuma ta gyaÉ—a tana girgiza kai tana kallonsa ta ce, "lallai jinin indiyawa wuyan ka ya isa yanka....."

Ta sake kallonsa ta ce, "Na isa ɗin ne, shiyasa nake yanke duk abinda na ga dama a kan ka. Kuma wallahi sai anyi auren nan, ko za ka sha fiya-fiya ka kashe kan ka sai an ɗaura auren nan da gawar ka. Kuma billahillazi in ka ƙure ni ka ɓata min rai, a yanzu zan kira iyayen ka a ɗaura auren kowa ya huta!. In kana musu ka nuna min ban isa nayi hakan ba."

Yana jin yadda Abba yake kallonsa shiyasa bai ce komai ba, ya sunkuyar da kai yana ji kamar ya tashi ya fita amma ba ya son yi saboda Abba, kuma ya san ƙarshe zagin a kan Mamy zai ƙare duk da bata wajan.

Mama ta girgiza kai ta ce, "ai sai ya nuna miki shi ba jinin fulani ne gabaÉ—ayansa ba, sai ya nuna miki akwai baragurbi a cikin jininsa."

Abba ya ce, "Saddiƙa ya isa...." Ya faɗa yana kallon ta.

Abba ya kalli Daada ya ce, "Daada ki cigaba da yanke hukuncin da ki ka ga dama, dole kowa ya bi."

Daada ta ce, "daman abinda zan faÉ—a kenan, kuma dole ayi wallahi, in kuma ban isa ba zan gani."

Abba ya ce, "kin isa, tunda ki ka faɗa hakan za a yi." Kafin a sake yin magana Rehaan ya miƙe ya fita daga falon.

Yana fita ya ji wayar ta yi ƙara ya ɗauko ya duba, ganin Abba ya kiransa kuma ta katse duk a lokaci ɗaya, sai ya fahimci saƙo ne dan ya dakatar dashi daga barin gidan, ya koma da baya ya tafo ɓangaren Abban ransa a ɓace sosai.

Bai jima da zama ba Abban ya shigo ya ga ya jingin da kujera ya lumshe idonsa.

Abba ya ƙarasa ya zauna akan kujera yana kallonsa, cikin sanyin murya ya ce, "Rehaan da mahaifiyata ka ke sa'in sa?."

Ya É—ago a hankali ya kalli Abba ya ce, "bata yi min adalci ne Abba, bata sona."

Yadda ya yi maganar sai dai Abba ya ji tausayinsa, ya san Rehaan ya wuce irin wannan auren, ko a ƙauye an daina irin wannan aure balle a cikin birni, a cikin birnin ma namiji mai kyau da aji da kuɗi kamar Rehaan. Shi da in ya tashi aure zai iya ɗauko ko wacce mace a faɗin duniya ya aura, saboda abinda Allah ya mallaka masa, amma ace shine zai yi irin wannnan auren da ko matar ma bai sani ba.

Abba ya tausasa harshe ya ce, "tana sonka mana Rehaan, ya za a yi ta ƙi ka bayan kaima jikan ta ne?."

A hankali ya ce, "saboda ni jinin Mamy ne, kuma bata son Mamy."

Abba ya É—an dafe kai cikin rashin jin daÉ—i ya ce, "ka daina faÉ—ar haka Rehaan, babu wanda Daada bata so a gidan nan." Ya yi shiru bai ce komai ba, dan ya san Abba yana kare mahaifiyarsa ne kawai, amma duk dinga kowa ya san bata son Daada.
Chapter 116 · 0% Book details