← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 133

Sashe 113

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ArÉ—o ya ce, "ba sunana bawan Allah ba, ArÉ—o za ki ce, in da hausa ne ki ce Shugaba, inda turanci ne ki ce master ko ki ce leader."

Mama ta ce, "To ArÉ—o, don Allah kar ku kashe sa zamu kawo."

"Yauwa. A shirya kuÉ—in nan da kwana biyu, zamu sake kiran ku" yana faÉ—a suka kashe wayar.

Baffa ya yi shiru bayan an gama wayar ya kalle su sanyaye ya ce, "Ina zamu ga waɗanan kuɗin? Ai sai dai mu ce Allah ya gafarta maka Saheer, Allah ya sa ƙarshen wahalar ka kenan. Dan na san lokacin mutuwar ka ne kawai ya yi!."

100 millions ta fansar Saheer! Saheer fans a haɗo kuɗi kar a kashe mana bawan Allah😭
[7/24, 5:59 PM] KRBBK: RDB2P85
Nana Haleema.

Cikin tashin hankali da ruÉ—ewa suke kallon Baffa jin furuncin a kashe Saheer da yake faÉ—a. Mama ta ce, "Haba Baffa, ya ka ke faÉ—ar irin wannan kalaman, maimakon ka yi fatan Allah ya kawo mafita sai ka ce haka?."

Baffa ya kalle ta cikin yanayi na damuwa da tashin hankali ya ce, "A ina za ki samu naira miliyan ɗari? Ko gidan nan za a siyar baza a taɓa samun wannan kuɗin ba, in za a zaga dangina da na ki ana neman waɗanan kuɗi baza a samu ba, dan ba mu dasu, ba mu da dalilinsu. In aka bayar ɗin ma kashe mutane suke yi, gwara mu yi masa fatan cikawa da imani."

Mama tana girgiza kai tana kuka ta ce, "Baza su kashe Saherr ba, zai dawo in Allah ya yarda, bazai mutu ba."

Islaha kuka take yi kamar ranta zai fita, tunda ta ji muryar Hammanta shikenan ta gigice take kuka mai sauti, bata tare da nutsuwa ko kaɗan, Hamma kawai zuciyarta da ƙwaƙwalwarta take kira.

Baffa ya dafa Islaha ya ce, "ki daina kuka Islaha, ki cigaba da addu'a, in akwai rabon zamu sake ganawa zai dawo."

Mama ta yi tsaki cikin jin haushi, ita da take mahaifiyarsa bai ce ta daina kuka ba sai wata banzar Islaha. Baffa ya É—auki waya ya kira Sadik, babu jimawa sai ga shi ya zo gidan.

Baffa ya kalli Sadik da sanyin jiki ya ce, "Sun kira waya Sadik, suna neman kuÉ—in fansa har naira miliyan É—ari."

Sadik ya wara ido ya ce, "É—ari Baffa? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Miliyan É—ari!" Ya sake maimaita cikin tashin hankali.

Sai kuma ya girgiza kai ya ce, "dole hukuma ta shiga maganar nan, in Allah ya taimaka sai ka ga an dace."

Mama ta ce, "ni dai kar a faÉ—awa Æ´an sanda, kar su kashe min É—ana."

"Baza su kashe sa ba in sha Allah, za a san yadda za a yi a kuɓutar dashi in Allah ya amince." Sadik ya juya ya fita, Islaha ta zabura ta bi bayansa ko takalmi bata saka ba.

Sadik da ya fita gab da zai shiga mota ya ji maganar Islaha a bayansa. Ya tsaya ya waiwayo ya kalle ta, Islaha ta ƙaraso kusa dashi ta goge ido ta ce, "zan bi ka mu je."

Ya kalle ta ganin duk ta firgice, ta koma wani iri kamar ba Islaha ƴar gayu da aji ba. Sadik ya ce, "to ki koma ki saka takalmi." Sai a sannan ta san babu takalmi a ƙafarta, ta koma ta je ta ɗauko ta shiga mota suka tafi. Bayan sun dawo wajan Baffa Sadik ya shiga, ya same shi a zaune yana tunanin mafita akan wannan lamari.

Sadik ya zauna ya ce, "Gani Baffa."

Baffa ya ce, "Sadik akan maganar kuÉ—in nan ne, ya ka ke ganin za a yi?."

Sadik ya ce, "Wallahi kaina ya rufe Baffa, ban san me zan ce."

Baffa ya ce, "Akwai gonata guda biyu, kwanaki a ta ya É—aya miliyan biyar, É—aya kuma miliyan bakwai ban siyar ba, ka ga yanzu zasu iya yin miliyan asirin. Sannan ga wannan gidan, tunda a babbar unguwa yake, kuma yana da girma sosai, a tunanina zai iya zuwa miliyan hamsin zuwa sama haka. Ka ga an É—an samu kuÉ—in, sauran kuÉ—in sai a siyar da gidansa, da É—an abubuwan da za a rasa ba.."

Sadik a sanyaye ya ce, "Baffa in aka siyar da gidan nan ina za ku koma?."

"Sai mu koma ƙauye cikin ƴan uwa, ran Saheer ya fi komai mahimmaci Sadik."

Ya sauke numfashi ya ce, "kwana nawa suka ce?."

Baffa ya ce, "Kwana biyu suka bayar."

Sadik ya ce, "in sun kuma kira mu faÉ—a musu ba mu da halin wannan kuÉ—in su taimaka su rage, in aka yi sa a zasu rage. Tunda daman ciniki ake yi dasu, ba da sun faÉ—a ake É—auka a bayar ba."

Baffa ya sauke numfashi bai ce komai ba, dan bai san wanne irin tunani zai yi akan haka ba. Abinda suke ji a waje ga shi ya zo gidansu, har cikin ɗakinsu. Sadik ya dinga rarrashin Baffa ganin ya ɗaga hankalinsa sosai, shi kansa hankalinsa a tashe yake, amma yana ɓoyewa ne saboda halin da Baffa yake ciki.

•••••••

Suna kashe wayar suka kalli Saheeer ArÉ—o ya ce, "Baban ka ya ce basu da miliyan É—ari, kuÉ—i sun fi ranka kenan."

Saheer ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Basu da wannan kuÉ—in, basu da hanyarsa."

"Ba bafulatani bane? Ya siyar shanunsa mana."

"Ranka ya daÉ—e wanne shanu ne zasu yi miliyan É—ari a wannan lokacin?."

ArÉ—o da yake goge bindiga ya kalle sa ya ce, "in ba a kawo ba za a cilla ka cikin ramin marasa amfani."

A lokacin wani matashi ya ƙaraso wajen da machine, Arɗo ya kalle su har suka ƙaraso. Aka gurfanar da matashin a gaban Arɗo. Arɗo ya yi murmushi ya ce, "Barka da zuwa."

Mutumin ya É—an dake ya ce, "Barka ranka ya daÉ—e."

"KuÉ—in fansar Bala ka kawo ko?."

"Sune ranka ya daÉ—e."

"Nawa ne?."

"Miliyan biyar aka ce, da waya guda huÉ—u, da wannan machine É—in" ya faÉ—a yana nuna machine É—in da ya zo a kai.

ArÉ—o ya ja jakar ya buÉ—e ya ga dubu dubu ne a ciki, ya É—auke wayoyin ciki yana kallonsu sabbabi duk a kwalayensu. Ya tura masa kuÉ—in ya ce, "ka lissafa, naira É—aya in babu ka yi kuka da kan ka." Mutumin ya fara irga kuÉ—in kamar yadda aka ce, yana yi yana gumi jikinsa yana rawa sosai.

A lokacin Magaji ya ƙaraso wajen ya ce, "Arɗo mai cikin can da take cikin matan can ta haihu, ta samu ɗa namiji amma ita ta koma."

Arɗo ya ce, "Har yanzu ba a ɗauko mana likitoci ba? Har yanzu ba a samu mai amfani a cikin sanƙammmun ba?."

Kafin Magaji ya yi magana ya kalli Saheer ya ce, "Kai baka iya aikin asibiti ba?."

Saheer ya ce, "Ban iya ba."

"Mtsw! Ba ka da amfani."

Ya kalli baƙo da yake irga kuɗi ya ce, "Baƙo fa, ka iya likitanci?."

Ya É—ago ya kalle sa jikinsa yana karkarwa, ArÉ—o ya ce, "Kar ka ji tsoro, babu abinda za mu yi maka, in ka iya likitanci ka taimaka mana ka duba wacce ta haihu."

Murya tana rawa ya ce, "Na iya."

Ya yi dariya ya ce, "Dakyau baƙo...Magaji a ɗauke shi a je dashi ya duba ta, ina akwai wanda bashi da lafiya yau mun samu likita. Bar irga kuɗin, alfamar likitancin da ka iya ko nawa ka kawo mun karɓa." Aka tafi dashi inda matar ta haihu.

Ya je ya same ta a kwance kaca kaca cikin jini, ga matan sun zagaye ta suna kallo, ga jaririn an naɗe shi da ɗankwali yana ta kuka, ita kuma tana kwance tana jan numfashi daƙyar. Ya duba ta ya kalli Magaji ya ce, "Da ranta, ba mutuwa ta yi ba, gajiya ce da yunwa, tana buƙatar a saka mata ruwa."

"Mu je a faÉ—awa ArÉ—o."

Tare suka dawo wajen Arɗo aka faɗa masa, ya ɗan ɗaga kai ya ce, "Tunda bata mutu ba a ƙyaleta kawai, ina da ciwo a hannuna, me za a siyo a wanke min likita?."

Jikinsa ya yi sanyi tunawa da halin da matar take ciki, amma babu damar magana ya faɗi abinda za a siyo. Ya ɗauki waya ya kira, babu jimawa sai ga duk abinda ya faɗa an kawo masa, harda ƙarin maganin ciwon kai da ƙananun abubuwa.

Ya wanke masa ciwon kamar yadda ya ce, Arɗo ya kalli magaji ya ce, "Kukan jaririn can ya cika min kunne, a kawo waya a kira mijinta, in bazai kawo kuɗi ba duk mu kashe su, kar su zamar mana kaya." Shi dai yana duƙe yana wanke masa ciwo, ƙirjinsa yana bugawa har ya gama.

ArÉ—o ya ce, "A kawo amaryar Black ya wanke mata ciwon ta."

Aka je aka É—auko Sudaisa da kanta yake a fashe, yana wanke mata tana kuka bayan ya gama ya ce, "Za a iya bata magani?."

Arɗo ya ce, "ka bata komai, wannan ai ta gida ce." A cikin magungunan da aka kawo ya buɗe ya bata na zazzaɓi ta ce, "Arɗo a duba Hammana, da wannan Hamma" ta faɗa tana nuna Saheer.

Arɗo ya ce, "Ayi yadda take so...." Ya juyo ya kalle ta yana murmushi ya ce, "Amarya kuma amanar Black." Alfarmar Sudaisa aka bawa Saheer maganin ciwon kai da zazzaɓi, aka bawa Sudais aka wanke masa ciwukan jikinsa.

ArÉ—o ya bita da kallo ya ce, "Black ya yi min shigar sauri, kamata ya yi a ce ni na aure ki ba shi ba. Amma matar abokina matata ce, nima mijin ki ne, yau zamu yi daren amarcin mu" ya faÉ—a yana binta da shegen kallon da gabanta ya faÉ—i.

"An samu labarin shigowar sojoji nan da mintina goma, kowa ya shirya!."

Abinda aka faÉ—a ta over over hannun ArÉ—o kenan, ya kalli su Magaji ya ce, "A kwashe min kadarorina a killace su waje É—aya, kar a bar wani abu ya samu É—aya daga cikinsu, mu zamu ji da sojojin."

Magaji ya ce, "Ya za a yi da jaririn can? Kukan sa zai iya tona mana asiri."

Ya kalli Magaji ya ce, "A bashi ƙaramar gyaɗa kawai, a aika shi inda zai huta daga wannan wahalar."
Chapter 113 · 0% Book details