Sashe 126
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Safeera ta ce, "Ai na faɗa miki ki ƙa ji, yanzu da muka dawo ma na sake maimaita miki. Kin yi gaggawar yanke hukunci babu dogon nazari gaskiya, amma tunda kin bawa Allah zaɓi wataƙila shine alkhairin ki."
Ta É—ago a fusace tana hararar ta ta ce, "Ta ya wannan auren zai zama alkhairi a gare ni?."
"ki daina faÉ—a, ba ka yankewa kan ka hukunci akan abinda ba kai za ka yiwa kanka ba. Kawai ki cigaba da addu'a Allah ya shiga cikin lamarin."
Islaha ta yi shiru, ta yi forwading acc detaila É—in zuwa ga lambar Jafar da ko saving ma bata yi ba.
Ta jima a zaune a wajan daga ita har Safeera babu mai cewa komai, sai daga baya Safeeta ta ce, "Su wai ƴan gidan nan ɗauka suke yi ɗansa da akace yana da taɓin hankali za ki aura? Da yake ga ki ƙarshen mara gata, sai kawai Baffa ya ɗauke ki ya aurawa mahaukaci."
"don Allah Safeera mu bar maganar nan haka, kin yi min alƙawarin babu wanda za ka faɗawa."
Safeera ta yi ziping bakinta ta ce, "shikenan, bara na koma gida."
Tana miƙewa wayar Islaha ta fara ƙara, Islaha ta ga kiran Sadik ne sai ta ɗauka ta saka a kunne. Daga can ɓangaren ya ce, "Islaha an saka min kuɗi fa, an saka kuɗi har naira miliyan hamsin. Fito ina waje."
Ta kalli Safeera da take tsaye ta ce, "An saka kuɗin, mu je waje mu same sa" ta faɗa tana miƙewa ta yafa mayafi.
Suna fita basu tarar da babu kowa a falon suka fita zuwa ƙofar gida. A jikin motarsa suka sake shi a tsaye, suka ƙarasa dan wajan da ya tsaya rana sosai.
Tana zuwa wajen Sadik ya ce, "Islaha kuÉ—in waye wannan?."
Islaha ta ce, "kuÉ—in fansar Hamma ne, ya za a yi a mayar dasu cash, ka yi musu waya kace musu an haÉ—a kuÉ—in? Amma bana son Baffa ya san kuÉ—in aka samu."
Sadik ya dakatar da ita ya ce, "in na yi magana sai ki ce ina yi miki wani kallo na daban, yanzu meye wannan?. Wancan lokacin na gan ki da rafar daloli, yau kuma ga ki da naira miliyan hamsin. Islaha kina so kaina ya tarwatse ne?."
"Ai na faɗa maka abinda zan yi ko? Ban ɓoye maka ba na faɗa maka saboda gudun zargi. To shi na aikata, ga kuɗi nan sun zo ni kuma na ƙulla yarjejeniya."
"Na shiga uku ni Sadik!...." ya faÉ—a yana dafe kansa tare da juya musu baya.
Sai kuma ya waiwayo ya ce, "Islaha ba mafarki bane ba wannan, rayuwa ce ta zahiri wacce take faruwa a gaske ba a mafarki ba. Ki É—ago kai ki kalle ni da kyau, a gabanki nake a tsaye ba a cikin mafarki nake ba..... Ki daina raina min hankali, ki faÉ—i abinda zai yu don Allah. Wanne irin mutum ne zai É—auki wannan kuÉ—in ya ba ki saboda auren contract."
Islaha ta ce, "Na dai faɗa maka gaskiya, ka daina yi min tambayoyi akan wannan abun da ya riga ya zama tarihi, abinda na sani shi nake faɗa maka. In ba ka yarda ba ga Safeera nan, a gaban idanunta aka yi komai, wataƙila in ita ta faɗa maka baza ka ƙaryata ba."
Safeera ta ce, "Hamma Sadik a gabana aka yi komai, har takardar yarjejeniyar na karanta. Ta ƙulla aure na wata biyar saboda kuɗin fansar Hamma."
"in aka je yarjejeniya ana nufin yarjewa akan abinda kowa yake da ra'ayinsa. Na ji ita akan Hamma ta yi, shi kuma akan me ya bata kuÉ—in dan ya aure ta?."
"Mahaifinsa. Zai aure ta saboda mahaifinsa" Safeera ta ta bashi amsa tana kallonsa.
Ya kalli Safeera ya ce, "wai waye wannan mutumin ne? Waye wanann da akan mahaifisa sai yi aure ta harda wannan kuÉ—in matsayin na yarjejeniya?."
Islaha ranta ya fara ɓaci ta ce, "bazan tsaya na tsara maka ƙarya ba, in ma abinda ka ke tunani na je na aikata babu wanda zai bani waɗnanan kuɗin a lokaci ɗaya saboda na bashi kaina. Abinda nake so da kai kawai ka amince, a je a yi abinda ya kamata."
Ya kalle ta ya ce, "Ba ki amsa min ba, waye shi?."
Islaha ta ce, "In na faÉ—a amfani me hakan zai yi?."
Sadik ya ce, "Ki faÉ—a min."
Islaha ta É—an yi jim tana tunanin ta faÉ—a ko kar ta faÉ—a, ta kalle shi ta ga ita yake kallo alamun yana jiran amsa, ta sake tafiya dogon tunani kafin ta ce, "Rehaan AbdulAziz Yola, wanda ka fi sani da Ray!.
Nana Haleema.
[7/29, 12:06 PM] KRBBK: RDB2P95
Nana Haleema.
Sadik sai da wayar hannusa ta kubce ta faɗi ƙasa saboda yadda sunan ya ratsa kunnensa ya shiga har ƙwaƙwalwa. Safeera ce ta duƙa ta ɗauko masa wayar, tana murmushi tana aiyana inda shine ya gansa ido da ido da bata san ya zai firgice ba.
Sadik ya zuba mata ido yana kallon ta cikin rashin sanin abinda zai ce mata. Sunan Ray kawai yake maimaita a ransa, da Raay ta ƙulla auren contract take nufi ko me? Da Ray zata zauna a matsayin miji da mata ko kuma dai wasa take yi masa?
Ya kasa magana sai tunani yake yi, duk da ta faÉ—a masa sunan mahaifin wanda za a yi auren amma ko kusa bai kawo Rehaan bane. Ya É—auka sauran yaransa ne tunda ance yana da yara da yawa, bai yi tunanin babbar giwar ne da kansa ba.
Sadik ya kalle ta ya ce, "Ray fa ki ka ce?."
Islaha ta nuna masa Safeera ta ce, "ka tambaye ta, a gabanta aka yi komai."
Ya kalli Safeera ya ce, "Da gaske shine ko AI ne?."
Ta É—an yi dariya kaÉ—an ta ce, "shine. Yadda ka shiga wannan firgicin haka nima na shiga, lokacin da na haÉ—a ido dashi sai da na ji kamar ba a duniyar nake ba. Mr Ray da muke gani a tv da magzine, shine na zauna a falonsa har na haÉ—a ido dashi. Har ya yi mata magana da yaren da nake ji, ban É—auka ya iya wani yare in ba turanci ba, sai gashi na ji ya yi har zan ba da shaidar ya iya ko ina. Rehaan shine wanda ya saka hannu Islaha ta saka hannu, shine ya tura kuÉ—in da aka turo maka."
Sadik ya karɓi wayarsa a hannaun Safeera, ya duba bank name ɗin wanda ya turo kuɗin, amma sai ya ga sunan kamfani ne kuma bai yi kama da sunan Ray ba.
Ya kalli Safeera ya ce, "Bank name É—in ba nasa bane."
Safeera ta ce, "Kaima kamar ba mai ilimi ba, ta ya zai turo maka kuÉ—i da kansa? Sai dai ya saka a tura."
Sadik kalli Islaha yana girgiza kai ya ce, "Abokina ya yi haƙuri, ko da ya dawo daga hannun masu garkuwa Islaha kin fi ƙarfin....."
Islaha dakatar dashi a fusace ta ce, "kar ka ƙarasa!."
Ta nuna kanta da yatsa ta ce, "Har abada ni matar Hamma ce, babu wani namiji da zan kasance a ƙarƙashinsa a matsayin mijina sai Hamma. Auren wata biyar ne kawai, daga ya ƙare kowa zai kama gabansa kamar ba a zauna ba. Na auresa saboda Hamma, kuma zan zauna da shi saboda Hamma, zan dawo saboda Hamma. Zan dawo a ɗaura mana aure da Hamma, mu zauna a matsayin ma'aurata kamar yadda muke mafarkin halam, shi kuma ya je ya cigaba da rayuwarsa kamar yadda yake yi!" Ta faɗa cikin fushi tana kallonsa.
"Amma Islaha ko da ace kun rabu za a ce ex wife É—in Ray ce, iya wannan matsayi da ki ka samu na ex É—insa babban mataki ne a duniyar nan. Kuma ta ya zai sake ki? Ni bana hango rabuwa a zaman ku."
"Na faɗa maka auren wata biyar ne kawai, ya san mahimmacin rules tunda a turawa yake rayuwa, ya san meye contract marriage tunda a cikin masu yi ɗin yake zama ko yaushe. Bazai karya ɗaya daga rules ɗina da na ba shi ba, zai yi komai base on yadda muka gina auren ni da shi, bazai taɓa breaking ko guda ɗaya ba, dan ya san illar yin hakan. Zan kiyaye rules ɗinsa, shima zai kiyaye nawa, lokaci yana yi komai zai ƙare."
Sadik ya girgiza kai ya ce, "Islaha ya kamata ki tuna, bayan contract akwai aurensa a kan ki. Mu musulmai ne, ba a kan contract mu ke gina aure ba balle mu ce da an yi canceling shikenan auren ya ƙare. Dole sai ya sake ki ta hanyar furta miki ko ya rubuta miki."
Islaha ta ce, "Na san da wannan, kuma zai yi É—in kamar yadda na faÉ—a maka."
"Yanzu yau laraba, jibi kenan É—aurin auren ku dashi?." Ta masa É—aga kai alamun eh.
Sadik ya ce, "Baffa ya sani?."
"ya sani, amma bai san batun yarjejeniya ba. Don girman Allah ka yi min alƙawari babu wanda zai sani, daga kai sai Safeera ne ku ka san maganar nan, don Allah ka riƙe min amana. Ko Hamma ne zai dawo kar ka faɗa masa, ni zan san abinda zan ƙirƙira na faɗa masa amma ba aure ba. Kuma ko da wasa kar ka faɗawa wani ka san Rehaan ya yi auren contract dani ko da wata, wallahi bana so a san da auren nan kamar yadda ba ya so."
Sadik ya ce, "Na yi miki alƙawari babu wanda zai sani in sha Allah."
Ta ce, "Sai batun waÉ—anda za a kira domin kuÉ—in fansar Hamma, Baffa suke kira yanzu ba kai ba, ya za a yi yanzu?."
Sadik ya ce, "ni suka fara kira kafin Baffa, zan kira su gobe, sannan zan je a ciro kuÉ—in a bank sai a kai musu. In Allah ya yarda Saheer zai fito lafiya."
Ta É—aga hannu sama ta ce, "In sha Allah." Sadik har lokacin bai fita daga shock ba, ya kalle ta alamun yana son yin magana amma ya ga ta haÉ—e rai alamun babu tambaya, dole ya yi shiru ya shiga mota yana tunani akan wannan lamari mai É—aure kai.