← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 133

Sashe 8

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To daman ai so nake ka fasa min kan, akan me zan yi shiru? Mutuwa nake so na yi, kawai ka kashe ni. In ka kashe ni ka haƙa rami ka binne ni a wajen nan ƙarewar sacewa."

"Mutuwa ki ke so ko?."

"Eh, ita nake so" ta faÉ—a tana kallon sa amma hawaye take yi.

Ya girgiza kai yana jan bindigar ya ce, "sai ki faɗi kalmar ki ta ƙarshe kafin bullet ya fasa miki kai" ya faɗa yana nuna mata bindigar a goshinta.

Sai ta fashe da kuka mai sauti, tana tuna yadda Hamma zai ji in ta mutu, tana tuna yadda Safeera zata ji in ta mutu, tana tuna su Zainab dasu Hafsa.

Ta ja numfashi da ƙarfi ta ce, "La'ilaha illahu Muhammadu rasullah, SAW."

"Kuma Allah ya isa ban yafe mu ku ba, zan tafi inda zak zo, kafin ku taho ayi mana hisabi" ta faÉ—a hawaye yana sakko, mata tana rufe idonta cikin wani irin yanayi.

Ya yi dariya ya jinjina girman taurin kan yarinyar, kawai sai ya juya ya fita yana kulle ta.

Duhu ta gani alamun an rufe ƙofa, ta ƙarasa buɗe ido, ta ga baya nan ta koma ta zauna tana kuka harda ihuuuu.

         *******

"Ranka ya daɗe na rantse da Allah bani da hannu a ɓatan Islaha, wallahi ni ban ɗauke ta ba" Ummi ta faɗa cikin tashin hankali.

Dpo ya kalli Safeera ya ce, "ki maimaita abinda ki ka faÉ—a."

Safeera ta ce, "ni shaida ce, a kan idona Ummi ta cewa Islaha wallahi sai ta ga bayanta, har tana cewa ta rubuta ta ajjiye. A lokacin har ni da Saleem mu ke cewa Islaha wannan ba kalmar wasa bace, ya kamata hukuma ta shiga cikin maganar, dan baka san me za a aikata maka ba. Sai ta yi dariya ta ce babu abinda zata iya yi mata, barazana ce kawai. Akwai cctv, ta É—auki komai."

Saleem ya ce, "gaskiya ne anyi haka ranka ya daÉ—e, ni da kaina na yiwa Islaha faÉ—a akan ta saka hukuma a maganar nan."

Ummi ta zaro ido t ce, "na rantse da Allah barazana ce kawai, wallahi Allah ni ban faÉ—a dan zan yi mata komai ba."

Dpo ya kalle ta ya ce, "kin yarda kin faÉ—a kenan ko?."

"Eh na faÉ—a, amma wallahi ba da wata manufa na faÉ—a ba. Tsabar kishi ne ya saka na faÉ—a."

"Kin faÉ—a dan za ki aikata, ko kin faÉ—a dan barazana wannan duk bai tashi ba. Kin furta sai kin ga bayan Islaha, yau ba a yi sati biyu ba an nemi Islaha ta rasa. Ko kece ko bake bace ba kece, in kin ga kin bar case É—in nan tabbaas anga Islaha, in ba a ganta ba, kotu zata yanke miki hukunci daidai da abinda ki ka aikata."

Ummi ta ɗora hannu a kai ta ce, "Kotu kuma yallaɓai?."

"Eh kotu, zamu cike muku FR mu tura ku kotu ranar monday in sha Allah. Kafin ranar zamu riƙe ki a nan."

Ummi ta fashe da kuka ta ce, "na rantse da girman Allah bani da hannu a case É—in nan ranka ya daÉ—e, wallahi ban aikata komai ba."

Dpo ya ce, "babu mai fitar dake sai Allah. Ke da kan ki kin amsa kin furta sai kinga bayanta, dan haka kina cikin case É—in nan tsamo-tsamo."

Wani ɗan sanda ne ya shigo ya ƙame kafin ya ce, "Sir ga wani Muslim yazo tare da wata shaida akan ɓatan Islaha."

Dpo ya ce, "su shigo."

A lokacin mahaifin Ummi da yake zaunse ya ce, "Dpo ayi mana alfarma a bamu belinta, duk abinda ya faru da kaina zan kawo ta."

Dpo kafin ya yi magana Muslim ya shigo shida mai napep É—in da ya so zuba mata acid.

Suka samu waje suka zauna Muslim ya ce, "Sunana Muslim, nima abokin aikin Islaha ne. Wannan bawan Allah ya zo gidan tv ya same ni ya ce ya ga lokacin da aka É—auke Islaha."

Dpo ya kalli mutumin ya ce, "Bawan Allah ya sunanka."

Mutumin ya ce, "sunana Muddasir ranka ya daÉ—e."

"Kana ina daidai inda abin ya faru?."

"ina kan titin da abin ya faru a cikin adaidaita sahu. Da farko ni ta fara tsayarwa zata shiga, sai na faɗa mata kuɗi ta ce ya yi tsada baza ta iya biya ba. Ta nemi nayi ragi sai naƙi yi. Muna wannan maganar sai ga wata baƙar mota mai zubin motar asibiti, tun kafin su ƙaraso wajan suka buɗe ƙofar motar, suna zuwa inda take aka ja ta ciki da ƙarfin gaske. Kafin na fito daga napep ɗin sun yi nisa sosai saboda gudu suke yi."

Ya girgiza kai ya ce, "Meye kalar motar ka ce?."

"Baƙa ce, mai zubin motar asibiti."

"Ka ga waÉ—anda suke a ciki?."

"Ban gani ba, ban farga ba kawai naga an ja ta ciki sa ƙarfi."

"Ka kula da lambar motar?."

"Gaskiya ban kula ba ranka ya daÉ—e, saboda ruÉ—ewar da nayi da lamarin, ban tsaya na kula ba."

Ya girgiza kai ya ce, "amma me ya hanaka kai repost a ofishin Æ´an sanda mafi kusa ba? Yadda abin ya faru a gaban ka ya kamata ka kai rahoto wajen hukuma. Meyasa baka yi ba?" Ya faÉ—a yana karantar yanayinsa.
[6/16, 10 AM] KRBBK: RDB2P05
Nana Haleema

Muddasir ya É—an yi ajiyyar zuciya ya ce, "ban yi wannan tunanin ba gaskiya, ranka ya daÉ—e."

Ya sauke numfashi ya ce, "hakan yana nufin da gaske sace Islaha aka yi..."

ya É—aga ido ya kalli Ummi da fuskarta ta yi gaje-gaje da hawaye ya ce, "Za ki iya faÉ—a mana waÉ—anda ki ka saka suka É—auke ta, bana so maganar nan ta bar wajan nan, in ba haka ba za ki sha wahala."

Ummi ta rushe da kuka ta ce, "wallahi bani bace, ban aikata komai ba wallahi."

Sadik ya ce, "ai koda Islaha ta bayyana, wallahi matuƙar tana da hannu sai kotu ta raba mu. Sai an yi mata hukunci daidai da abinda ta aikata, baza mu bar maganar nan ta tafi a banza ba."

Dpo ya ce, "kwantar da hankalin ka, a gaban hukuma ku ke, in sha Allah za a fitarwa da kowa haƙƙinsa."

Ya kalli Mudassir ya ce, "kai jeka. Ka bada sunan ka da lambar wayar ka a kan kanta, in amfanin hakan ya taso za a neme ka." Ya amsa da to ya miƙe a nutse ya fita.

Dpo ya kalli mahaifin Ummi ya ce, "kamar yadda na faɗa Alhaji, zamu riƙe Ummi a nan har sai ranar litinin mun aika maganar kotu."

Mahaifin Ummi ya ce, "ayi haƙuri ranka ya daɗe a bamu belin ta, in sha Allah duk abinda ya faru da kaina zan kawo ta. Baza a samu matsala ba, zan san duk abinda za a yi."

Dpo ya ɗaga kai ya ce, "Alhaji Ummi ta shiga cikin case ɗin nan gaba da baya, ta ko wanne ɓangare sai an nemo ta."

"Na yi alƙawarin bazan bari ta gudu ba, zan tsaya wajan ganin case ɗin ya zo ƙarshe in sha Allah."

Ajiyar zuciya Dpo ya yi, aka tsayar da magana aka ba da belin Ummi suka fito.

Sadik suna fitowa ya kira Sheer ya da ya addabe sa da yawa, ya faÉ—a masa duk yadda aka yi har wanda ya zo ya bada shaida ya faÉ—a masa.

Saheer ya ja tsaki ya ce, "akan me za a bada belita? Akan wanne dalili za a bada belin wacce ake zargi?."

"Don Allah ka kwamtar da hankalin ka,ko da an ga Islaha na faÉ—a musu baza mu bar case É—in nan ba, zamu tsaya wajan ganin an yi musu tsakani da Ummi."

"Yanzu ya ake ciki?."

"Babu komai a ƙasa, zamu jira mu gani zuwa wani lokaci, yanzu dai babu komai a ƙasa, amma in sha Allah zata bayyana."

"Shi wanda ya ce ya ga lokacin da aka ja ta motar, waye shi?."

"Mai napep ne kawai, sanarwa ya gani ya je ma'aikatarsu ya faÉ—a."

"Ni fa ban yarda ba, akwai wani abun a ƙasa wallahi."

"Kar ka damu, komai zai daidaita in sha Allah."

Saheer ya ce, "ya batun aikin Baffa?."

Sadik ya ce, "shima a nan ana ƙoƙari in Allah ya yarda, kar ka damu."

Saheer ya ce, "Babana bashi da lafiya, an sace min matata amma ka dinga cewa in kwantar da hankalina. In ban ganni a nigeria ba hankalima bazai taɓa kwanciya ba wallahi. Haka kawai an kulle ƙasar nan, ji nake kamar na haura na gudu wallahi."

"Sai haƙuri, zasu buɗe shigowa nan ɗin, matsala ce ta tsaro."

Saheer ya yi tsaki ya kashe wayar cikin wani irin yanayi na bugawar zuciya da tashin hankali.

******

A hankali Mansur yake tuƙa motar da Rehaan yake ciki, cikin salon tafiyar kwantar da hankali, babu ta hayaniya da wuce ƙa'ida.

Gab da zasu shiga gidan ya danna horn, mai gadi da yake yasan da zuwansu ya buÉ—e suka shiga da motar cikin gidan.

A hankali Rehaan ya fito, mai gadin ya ƙaraso yana duƙawa ya ce, "barka da zuwa ranka ya daɗe."

Ya É—an kalle sa ya ce, "ya aiki?."

"Alhamdu lillah. Ranka ya daɗe na ga saƙo, Allah ya saka da gidan aljanna."

"Amin. Baƙi sun zo?."

"eh ranka ya daÉ—e, suna ciki suna jiran ka."

Bai ce komai ba ya wuce cikin gidan Shams yana bayansa yana takawa a nutse.

Wani part ya buɗe ya shiga falon, mutanen da suke ciki ba su wuce biyar ba, suna ganin shogowarsa duk suka miƙe ya ƙarasa ya basu hannu duk suka gaisa, sannan ya zauna ya ce, "ku zauna." Ba musu suka zauna.

Ya kalli Bilal ya ce, "ɓangaren ka kun yi magana da Jazy?."

"Eh, mun yi magana dashi ya ce na sanar dakai bai san kan abun ba. Ga takardar da aka turo mana" ya faɗa yana miƙa masa, ya karɓa yana ɗan nazarinta kaɗan.

Ya kalli wata baturiya ya ce, "and you."

Itama ta faɗa masa abinda yake tafiya a ɓangarenta. Sun jima suna tattaunawa a akan abinda ya shafi kasuwancinsa. Sai da aka samu matsala da maganin matsalar sannan suka yi masa sallama suka fita daga falon.

Ya É—an sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa a lokacin aka yi kiran sallar i'sha.
Chapter 8 · 0% Book details