← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 133

Sashe 47

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safeera ta kalli Sadik ta ce, "Ka daina zarginta, ni na yarda da ita, na san bazata taɓa aikata wani abun mara kyau ba. Tana da ilimi, ta san duk abinda take yi, wallahi baza ta yi abinda zai lalata tarbiyyar ta ba."

Sadik ya ja tsaki ya ce, "lalata tarbiyya na nawa kuma? Ai tunda ta saka ƙafa ta bar ƙasar ta, zancen tarbiyya ya ƙare. Ni ta saka ni a tsaka mai wuya, ko me zan cewa Baffa yanzu oho."

Sai kuma ya É—an gyaÉ—a kai ya ce, "babu amfanin tsayuwa a nan, tunda dai bata nan ta je duk inda zata je. Allah ya kiyaye hanya" ya faÉ—a yana bar wajan.

Saleem ya kalli Safeera ya ce, "ƙawar ki bata kyauta ba Safeera, abinda ta aikata bai kamata ba ko kaɗan. Hakan bai yi daidai da tarbiyyar ta ba ko kusa."

Safeera bata ce komai ba dan ba yarda zasu yi ba, gwara ta yi shiru da bakinta tunda zargin Islaha suke yi, kome zata faÉ—a musu ba amincewa zasu yi ba. Safeerata kalle sa ta ce, "bara na shiga ciki, zamu haÉ—u zuwa gobe ina sha Allah." Ya É—aga mata kai ta juya ta shiga gidan a sanyaye.

Safeera a sanyaye ta koma gidan, ta tarar da Rukayya ta shirya ta fito zata tafi makaranta ta ce, "Adda ina ta neman Umma ta whatsapp bana samu, ya kamata ace zuwa yanzu mun ji yadda ta sauka ko?."

Safeera ta ce, "in kin dawo sai mu neme ta, sai kin dawo."

Ruƙayya ta fita ita kuma islaha ta tsaya tana tunanin abinda ya kamata ta yi, dole ta ajjiye aikinta ko dan saboda Baba, bazata so ya dinga dawowa daga wajen neman halak babu abinci ba.

Sannan ga ƙannenta, in suka dawo daga makaranta waye zai dinga basu abinci? A ina zasu dinga zama tunda zata rufe gidan ta tafi da key ɗin? Ta sauke numfashi ta shiga ɗaki tana tunanin mafita a cikin lamarin, dan mahaifinta da ƴan uwanta suna buƙatar zaman ta a gidan ko dan saboda abinci.

Mama suna tsaye ita da Hajiya Karima suna jin voice note É—in Labiba na jiya.

Mama ta yi dariyar jin daÉ—i da farin ciki ta ce, "kai amma na ji daÉ—i, ke daga jin muryar Labiba kin san tana cikin farin ciki mai yawa wallahi."

Hajiya Karima ta ce, "ita da take tamu kenan, ki duba tun da muka ajjiyewa ƴar riƙon can taku saƙo, amma har yanzy bata duba ba balle ta bamu amsa ba. Kuma Oga Musa ya ce mana gidan da aka kaita gida ɗaya ne ya raba su da Labiba, Maimuna aka kai Madina su suna Jeddah. Mai yarinyar nan take nufi damu?."

Mama ta ce, "kar ki damu, na san halinta zata yi magana. In bata yi magana ba ai daidai mu ke da ita, tunda har ta riga ta bar ƙasar nan ta tafi a ƙarƙashin mu ai duk ahinda muke so kuma sai ta yi."

Karima ta ce, "yarinyar nan ba a gane gabanta fa, Æ´ar iskan kanta ce."

Mama ta yi dariya ta ce, "kar ki wani damu, zamu yi magana da ita. Ai wannan ba abin damuwa bane, tunda har ta tafi ai iskanci da iyayi ya ƙare."

"Kuma Alhaji Musa ya ce zasu iya ƙarawa Islaha kuɗi, dan yace mai gidan yana da kirki sosai, in ga in aka ƙara gaba ta kaimu."

Suka tafa da Mama ta ce, "ke da yarinyar nan zata saki jiki ta nemi kuɗi a ƙasar nan, zata yi saurin samu a hannun karɓuwa a wajen mutanen ƙasar wallahi. Kin san kalar ta mai ɗaukar hankali ce, su da suka saba ganin farare ƙal ƙal kalar Islaha zata yi saurin ɗaukar hankalinsu."

"Za ta yi fa, ba dai ta je ba? Ki jira dai mu gani, na tabbatar tana daga cikin waɗanda zasu maƙale su ƙi dawowa." Suka sake tafawa cikin nishaɗi mai yawa dan suna cikin farin ciki mai yawa.

Mama ta kalli wayarta da ake ta kira, ta taɓe baki ta ce, "Saheer ne fa, da alama ya samu labarin bata nan, shine yake kirana zai fara yi min ƴar murya kamar ni ce uwar Islahan."

Karima ta ce, "Ki É—auka, baki san me zai ce ba."

"Allah akan Islaha ne, bara kuma ki ji."

Ta faɗa tana ɗauka suka gaisa sannan ya ce, "Mama da gaske Islaha ta tafi wata ƙasar aiki?."

Mama ta kalli Karima alamun kin ji ko, sai ta yi Æ´ar dariya ta ce, "ta tafi Saheer, tana can gidan wani balarabe, dan an ce ko aure ma bashi dashi. Tun a kallon farko ta burge sa har ya amince ya É—auke ta. Ka san budurwar taka ba dai É—aukar ido ba, yanzu zata burge namiji ya É—auke ta ko bai yi niya ba"

Saheer ya ji zafi a ransa, kishi yana mamaye masa zuciya, haushin Islaha ya mamaye masa zuciya, ya daure ya kawar da fushin ya ce, "Mama meyasa za ki tura islaha don Allah?."

"kai malam dakata, Islahan yarinyar goye ce da zan ɗauke ta na tura ta ba tare da amincewar ta ba? Sau nawa ina yi mata tayi tana guduwa, sau nawa ina cewa tazo tana watsa min ƙasa a ido?. Wannan ma da kanta ta same ni tace tana da buƙatar tafiyar nan. Ina ruwana dan ta nema na kai ta? Ko wuta Islaha tace min tana son shiga, da hannuna zan riƙe hannunta mu je ta shiga na dawo. Ko kana so ka ce min ta ƙarfi na ɗauke ta ana kai ta?."

"Mama wai harda Labiba, yanzu Mama hakan daidai ne? Dan sun nuna suna so kawai sai a basu dama su yi ahinda suka ga dama?."

"Ka ga malam bana son surutan banza, ka dakata da wannan maganar. Tafiya dai an riga an yi ta, babu dawowar su a yanzu."

"In sha Allah sai na dawo da Islaha, ina dawowa gida Islaha zata fara shirin dawowa gida itama."

Mama ta yi tsaki ta ce, "sai ka dawo da ita ai" ta faÉ—a tana yanke wayar.

Ta kalli Karima ta ce, "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, shi a tunaninsa dawowar Islaha yanzu zai yu? Bai san sai ta gama biyan kuÉ—in da aka kaita ba, sannan take da Æ´ancin yin duk abinda ta ga dama?."

Karima ta ce, "ki ka sani ko duk zai biya? Yadda yake magana cikin gadarar nan na san zai iya biyan kamfani kuÉ—insu ya dawo da ita."

"ina ya ga kuÉ—in?."

"Ki ka sani?."

"Ai ko yana dasu wallahi bazai biya ba, sai ta biya da kanta, ai ba a banza ta hau jirgi ta bar ƙasar ba." Karima ta yi dariya suka cigaba da tattaunawa akan batun.
[7/2, 10:41 AM] KRBBK: RDB2P33
Nana Haleema.

A hankali ta ji ana tashinta daga bacci, Islaha ta buɗe iso a sanyaye ta kalli Sunaira da take tsaye a kanta tana murmushi. Sai a lokacin Islaha ta tuna a inda take, ta bi ɗakin da kallo sannan ya miƙe zaune a lokacin take jin ana ta kiran sallar asuba.

Ta kalli Sunaiha ganin har ta shirya cikin uniform, Islaha ta miƙe tsaye tana ɗan murmushi, kafin Suhaira ta yi typing a waya ta bata.

"Barka da Safiya Islaha, lokacin sallah ya yi, sannan lokacin haÉ—a breakfast ya yi."

Islaha ta gyaÉ—a tana murmushi ta shiga banÉ—aki tana tafiya kamar bata so.

A sanyaye ta yi wanka ta fito ta saka uniform sannan ta tayar da sallah, tana idarwa ta fito ta tarar da Sunaira tana ta aiki itama ta shiga tana taya ta.

A lokacin suka gama haÉ—a lafiyayyen tea, suka haÉ—a simple breakfast kamar yadda aka saba da taimakon Sunaira.

Suka jera a dining a lokacin ƙarfe bakwai na safe, suna tsaye a jikin dining ɗin ya sakko daga sama yana amsa waya cikin shirin fita aiki.

Sai da ya zauna sannan ta ji Sunaira ta gaishe sa cikin harshen larabci, itama ta gaishe sa cikim english.

Maimakon ta ji ya amsa kamar yadda ya yiwa Sunaira, sai ta ga ya kalle ta sannan ya ce, "morning, Islaha...Right?."  Ya faɗa yana kallon ta da sigar tambaya.

Ta É—an yi murmushi tana gyaÉ—a kanta, tana mamakinsa na kallonta har yana maimaita sunanta. Bai ce komai ba Sunaira ta yi serving É—insa sanann suka bar wajan.

Kitchen suka koma a lokacin Sunaira ta fara karyawa, ita dai Islaha tana tsaye dan lokacin ya yi wuri da yawa, baza ta iya cin komai a lokacin ba, tafi so sai rana ta fito.

Tashin motarsa suka ji alamun ya fita, Sunaira ta fito itama ta fito, suka kwaahe kayan da ya gama suka shiga aka wanke aka ajjiye.

Sunaira ta yiwa Islaha typing ta bata dan ta karanta, Islsha ta karɓa ta ga ta ce, "Ki je bedroom ɗinsa ki gyara."

Islaha ta kalle ta Sunaira, sai ta rubuta da turanci ta mayar dashi arabic ta bata. Sunaira ta karanta sannan suka fita ta raka ta har bedroom É—in ita kuma ta koma.

Islaha ta sauke numfashi ta shiga ɗakin tana kallon ɗakin hotonsa da wata balarabiya da yaro ta gani, ta ƙarasa tana kallon hoton ganin matar kyakykawa ga yaronsu mai kyau.

Ta É—auke kai a bayyane ta ce, "Ko ya Hamma yake? Na san zuwa yanzu ya ji labarin abinda yake faruwa. Na san zai ji babu daÉ—i, zai yi min hukunci mai tsauri" ta faÉ—a tana kallon bedroom É—in.

A sanyaye ta gyara É—akin, ta buÉ—e bathroom shima ta gyara sannan ta fito a lokacin Sunaira ta shigo.

Ta kalle ta taga ta buÉ—e wani waje ta É—auko kaya masu yawa sosai. Ta yiwa Islaha alama da ta taho, ta bi bayanta suka tafi laundry room ta bawa Ilsaha alamun ta wanke.

Islaha cike da mamaki ta ce, "kutumelecy, wankin ma ni zan yiwa wani ƙato?."

Sunaira ta yi murmushi alamun bata ji abinda Islaha ta ce ba, Islaha ta karɓa suka kunna washine machine aka wanke su. Lokacin da ta gama ta kalli kayan ganin duk basu fita ba, ta yi tsaki ta wanke inda bai fita ba da hannu, ta yi drying kayan sannan ta goge.
Chapter 47 · 0% Book details