← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 133

Sashe 122

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadik dai kallon ta yake yi dan har lokacin bai yarda a nutse take ba. Ya ce, "wannan maganar bata da ma'ana Islaha, kina musulma ina ke ina auren yarjejeniya?. Kuma shi mahaukacin ina ne da zai É—auki kuÉ—i masu yawan waÉ—anan ya ba ki dan kawai ki aure sa?."

Ta kalle sa ta ce, "kai ka ce min a wajansu miliyan Hamsin ba komai bane."

"Dan na ce haka ai ba hakan yana nufin zai yu bane, kawai dan za ki auresa sai ya ba ki waÉ—annan kuÉ—in?. Islaha ki nutsu don Allah."

"A faÉ—a maka a nutse nake, kuma haka na yanke, kuma hakan zan yi. Bazan bar ran Hamma ya salwatanta a banza ba, tunda dai auren ba mai É—orewa bane zan jure saboda Hamma. Na riga na yanke hukunci akan zan yi É—in, ina faÉ—a maka ne dan ka zama shaida koda Hamma zai dawo ya ce ban kyauta masa ba. Ka zama shaida, na yi ne saboda shi, kuma zan dawo gare shi ba tare da komai ya same ni ba."

Sadik ya ce, "Islaha wannan ba shawara mai kyau bace, akan me za ki yi irin wannnan auren kamar a Kdrama ko american series?....."

"Akan Hamma zan yi, kana ganin yadda suke dukansa, kana ganin yadda Hamma ya rame kamar ba shi ba, kana ganin yadda Hamma ya koma kamar wanda ya shekara yana ciwo. A kansa zan sadaukar da kaina balle auren wata biyar."

"Islaha ke za ki aurar da kanki? Ko za ki cewa Baffa auren jarjeniya za ki yi saboda Saheer?. Ba Kdrama bane, ki nutsu ki fahimci a Yola ki ke."

Ta kalle sa ta ce, "ka ɗauka Kdrama ɗin ne kawai, ka ɗauka film ka ke kallo kuma ni ce jarumar ciki. Baffa ya amince da auren, zan ce masa na amince ba tare da ya san ƙudurina ba. In dai har zai bani kuɗin fansar Hamma zan yi, Hamma Sadik!."

"To shi waye wanda za ki aura É—in? A cikin Æ´aÆ´an Abdul Aziz Yola wanne za ki aura har da ki ke ganin zai ba ki miliyan hamsin lokaci É—aya?."

Islaha taÉ—an ja numfashi sannan ta lumshe ido ta ce,..

Nana Haleema.
[7/28, 12:20 PM] KRBBK: RDB2P91
Nana Haleema.

Ganin ya zuba mata ido yana jira ya ji sunan da zata faɗa sai ta ɗan ɗauke kai zuciyarta tana faɗa mata ba yanzu ba, kar ta faɗa masa sunan ko waye sai ta ce, "faɗar bata da wani amfani, na faɗa maka ƙudurina dan ka zama shaida, zan yi abinda nake ganin shine daidai."

Sadik ya ce, "Kar ki dakusa rayuwarki, ki jira mu ga abinda Allah zai yi."

Ta É—an murmusa ta ce, "akan Hamma zan iya yin komai, ba dakusar da rayuwata ba, in rasa rayuwata ne zan iya yi indai a kansa ne. Bazan iya jira ba, zan jarraba wannan É—in, in ya yu daman haka nake fata, in bai yu ba sai na gwada wani." Ganin ya shiru ya kasa magana, sai ta koma da baya ta koma cikin gidan da sauri.

Tunda ta koma take kai kawo a ɗaki, ɓangare ɗaya na zuciyarta yana faɗa mata abinda zata yi ba daidai bane, ɗaya ɓangaren ya faɗa mata hakan shine daidai, in ba ta aikata ba a ina za a samu kuɗin da za a karɓo Hamma?.

Ta kawar da tunanin kar ta aikata, ta ƙarasa jakar ta ta buɗe, ta ɗauki biro da takarda ta zauna tana rubutu a kai.

Bayan ta gama rubutawa ta karanta yadda ya kamata, ta ajjiye takardar tana ajiyar zuciya a hankali a hankali. Kamar lokacin da zata tafi Jeddah, haka wannan lokacin ma ko kaɗan ta ƙi bawa zuciyarta damar da zata ce tunaninta ba daidai bane, ta dage akan ƙudurinta, ta dage akan abinda take kai shine daidai, ta ƙi amincewa da ba kan daidai take ba.

Haka ta gama zamanta a ɗakin, sannan ta kwana a kan gadon ta yi shiru tana tunanin halin da suka ga Hamma a ciki. Sai kuma ta miƙe ta yi alwala ta zo ta tayar da sallah raka'a biyu, bayan ta idar ta karanta addu'ar da annabi ya koyar damu domin neman zaɓin Allah, ta nemi zaɓin Allah akan abinda ya zama alkhairi sannan ta kwanta.

Washe gari tana tashi wanka ta yi a gaggauce, ta saka hijjab ta É—auki handbag É—inta ta fita da sauri ta fita. Da farko gidan tv ta fara zuwa, ta É—an jima a can sannan ta tafi asibiti. A can ma ta É—an jima sannan ta fito ta dawo gidansu Safeera ta kira Saleem a waya.

Saleem É—auka ta ce, "Hamma Saleem don Allah email address É—in Jafar za ka bani."

Daga can ɓangaren ya ce, "Wanne Jafar?."

"Wanda mu ka gani a diamond hotel, lokacin da mu ke neman Rehaan Yola."

"Okay, bara na duba in na gan shi zan turo miki. Amma yana jimawa jafin ya buÉ—e mail, sai a kwashe sati É—aya bai amsa ba."

"Na gode" tana faÉ—a ta kashe wayar.

Safeera ta ce, "kin ce za mu yi magana kuma kin yi shiru, wani abun ne ya sake faruwa?."

Ta kalle Safeera sannan ta ce, "Jiya sun ce in ba a ba da kuÉ—in fansar Hamma za sa kashe sa, har video suka turo suna dukansa."

Safeera cikin damuwa da sanyin jiki ta ce, "WaÉ—nanan mutane Allah ya shiga tsakaninmu dasu......"

"Amin."

"Yanzu ya ake ciki, An samu kuÉ—in?."

"Ba a samu ba. Amma ni zan samo."

Safeera ta ce, "ban gane ba, a ina za ki samu miliyan É—ari?."

"Sun rage hamsin, miliyan hamsin ne yanzu."

"Ina za ki samo waÉ—anan kuÉ—in?.

Islaha ta yi shiru bata amsa ba, dan bata san da wacce fuska zata fahimta ba, kuma ta san halin Safeera in ta faÉ—a mata zata dinga kushewa, ta dinga yi mata wa'azi ita kuma bata so.

Safeera ta ce, "ko saudian za ki sake komawa ki haÉ—o kuÉ—in?."

Ta girgiza kai alamun a'a, sannan ta goge idanunta ta ce, "contract marriage zan karɓa, zai aure ni saboda iyayensa, ni kuma zan auresa dan ya bani kuɗin fansar Hamma."

Safeera ta buÉ—e baki saboda mamakita ce, "Ban gane ba, yi min bayani yadda zan kwashe."

Islaha ta rufe ido ta ce, "Shi wanda Baffa ya ce zan aura, dashi zan yi auren yarjejeniya."

"Islaha kina da abin mamaki, ko na ce kina da abin dariya wallahi. Kwana biyu kalaman ki kamar na waɗanda suke acting, yadda ki ke yin komai kamar rubuta miki aka yi ki ka karanta ki ke acting a kai."

"Shiyasa bana son faÉ—a miki, dan na san baza ki bani goyan baya ba."

"Akan me zan ba ki goyan baya akan abinda bai kamata ba? Auren yarjejeniya ki ke cewa za ki yi fa."

Islaha yi magana saƙon Saleem ya shigo wyar ta, ɗauki wayar bata cewa Safeera komai ba, ta buɗe saƙon ta yi copy ɗin email address ɗin Jafar, ta je mail ɗinta ta paste ta fara rubuta masa message.

Sai da ta gama ta tura sannan ta kalli Safeera ta ce, "Abinda na faÉ—a miki shi zan yi, zan je wajensa mu yi magana, in dai ya amince zai bani wannan kuÉ—in ni kuma zan aure sa na É—an lokaci kaÉ—an, daga baya sai mu rabu na dawo na auri Hamma."

Safeera da take kallon Islaha ta ce, "ban gane ba Islaha, wai aurensa za ki yi dan ya ba ki kuÉ—i, sannan daga baya ya sake ki ki dawo ki auri Saheer?." Ta É—aga kai alamun eh tana kallon ta.

Safeera ta zaro ido waje ta ce, "na shiga uku, Islaha me ki ke faɗa ne haka? Wannan wacce irin magana ki ke yi kamar ta masu taɓin hankali?. Contract marrige a addinin mu, kuma a al'adar mu ta fulani? Sunnar Annabin za ku gina akan bayan wasu kwanaki za ku rabu?."

"Dallah malama ki daina É—aga min murya, na san duk abinda nake yi, kuma auren gaske za a yi tunda Baffa ya sani. Ba wa'azi na ce ki yi ba, na riga na yanke hukunci, ko me za ki ce ba sauraren ki zan yi ba."

"Dan Baffa ya sani ai ba akan hanyar kirki ku ka gina auren ba. Kuma ke yanzu akan Saheer sai ki yi wannan kwamachalar? In ya fito ya ji kin yi aure nufin ki zai ji daÉ—i ne?."

"Akansa zan yi, in ma abinda ya fi kwamachala ne indai akan Hamma ne zan aikata. Kuma ko da ya fito É—in ma ba wani abun damuwa bane, dan ba jimawa aure zai yi ba ya watse, ni kuma na dawo na auri Hamma."

Safeera ta bita da kallon bata da hankali, amma sai bata yi magana a kai ba ta ce, "Shi kuma kawai sai ya ɗauki waɗannan kuɗi ya ba ki dan ki aure sa? Mahaukaci ne shi ko yana shaye-shaye?.”

Islaha ta ce, "ban sani ba, amma na san yana da kuÉ—in da zai bani. In ya bani fine, in bai bani ba za a yi soke yarjejeniya."

"Okay, mu yi tunani akan bai baki É—in ba, a ina za ki samu kuÉ—in fansar?."

Islaha ta É—aga kai ta kalle Safeera sai ta girgiza kai ta ce, "bani da hanyar da zan samu, balle ma a jikina nake jin zai bani."

Safeera ta ce, "saboda kawai zai aure ki sai ya É—auki waÉ—nanan kuÉ—in ya ba ki? Ke ga Æ´ar gold ko Æ´ar diamond da azurfa ko?. Miliyan hamsin fa ba dubu hamsin ba."

"Ba Æ´ar diamond ba ce, amma zan gwada na gani. A rashin ta yi ake barin arha, abinda ka ke ganin bazai faru ba in ka gwada sai ka ga ya faru."

"Shi wanda ki ke magana akan zai ba ki kuÉ—in, waye shi?."

Ta ɗaga ido ta kalle Safeera, kamar zata faɗa mata sai kuma ta ce, "ƙaryata ni za ki yi in na faɗa miki."

Safeera ta ce, "faÉ—i ina jin ki."

Islaha ta ce, "ki jira komai ya tafi yadda nake so, zan ɗauke ki muje tare dan ki gani da idon ki. Amma yanzu....." bata ƙarasa maganar ba wayarta ta fara ƙara, ta duba ta ga sabuwar lamba ce sai ta ɗauka ta saka a kunne.

Jafar ya ce, "Miss Islaha."
Chapter 122 · 0% Book details