← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 133

Sashe 78

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ɗan taɓe baki yana ɗan girgiza kai ya ce, "Islaha Muhammad Madibbo, right?."

Ganin ba ita yake kallo ba sai ta ce, "Haka ne."

"A jounlist, working in toran giwa channel.  You are from Adamawa state?" Ya faɗa yana kallon ta.

Ta É—aga kai ta ce, "Eh."

Ya É—an girgiza kai ya ce, "so fulani is your tribe?." Nan ma ta É—aga kai alamun eh.

Ya É—an zuba mata ido yana nazarinta, sai ya ga ta buÉ—e baki zata yi magana amma ta fasa. Jazy cikin yaren hausa ya ce, "faÉ—i, ina jin ki."

Islaha ta ce, "Watannin da suka gabata, a cikin Diamond hotel, an kawo maka katin gayyatar Mr Rehaan Yola for interview. Miss Islaha."

Ya É—an zuba mata ido alamun yana tunawa, sai ya É—an É—age gira yana É—aga kai ya ce, "Yes na tuna. Ke ce Miss Islaha da ta bani katin gayyatar Rehaan a Diamond hotel?." Ta É—aga kai alamun itace tana kallonsa.

Ya ɗan jingina da kitchen island ya harɗe hanunsa a ƙirji ya ce, "neman Rehaan Yola ne ya kawo ki Jeddah kenan?."

Ta É—an buÉ—e ido kaÉ—an ta ce, "No, i'm here for a job."

"A job!"

Ya maimaita yana kallon ta, kafin ya miƙe tsaye sosai ya dafa kitchen island ɗin yana kallon ta ya ce, "which job?."

Islaha ta É—an lumshe ido ta ce, "it's my personal issue Mr Jafar."

Ya É—an É—age kafaÉ—a alamun bai damu ba, sai ya ce, "Kin haÉ—u da Rehaan É—in akan hakan?."

Ta girgiza kai ta ce, "Ni ban haɗu dashi ba, ba da kai muka yi alƙawari akan zaka neme ni in lokaci ya yi ba, ko ka manta?."

Ya girgiza kai ya ce, "Fuskar ki na manta, ba alƙawarin ba. Amma kin taɓa ganin Rehaan? Ina tunin kafin yanzu kin taɓa ganin Rehaan Yola?."

Ta girgiza kai alamun  ta ce, "ban taɓa ganinsa ba had yanzu."

Ya É—an buÉ—e ido yana binta da kallo cikin mamaki, dan ya san raina masa hankali kawai take yi. Ya É—an girgiza kai ya ce, "Wow!." Sai kuma ya É—an murmusa ya fita bai ce komai ba.

Jazy yana fita daga kitchen É—in sama ya hau har É—akin Rehaan, ya same shi a tsaye yana amsa waya.

Sai da ya gama wayar sannan Jazy ya ce, "a ina ka san housemaid É—in na da take zuwa gidan nan?."

Rehaan ya kalle sa ya ce, "Gidan Ubaid."

Jafar ya ce, "ka san Æ´ar Nigeria ce, kuma Æ´ar Yola?."

Ya É—an juyo ya kalle sa sannan ya ce, "me ya dame ni da sanin hakan?."

Jafar ya ce, "Ya kamata ya dame ka, a yadda ka ke ya kamata ka dinga tantance waɗanda zasu raɓe ka. Dan a biyata kuɗi daga Nigeria, ta zo Jeddah ta fara aiki a gidan Ubaid, daga baya ta shigo nan abu ne mai sauƙin faruwa. Za a iya haɗa baki da ita a cutar da kai."

Ray ya ɗan sauke numfashi bai ce komai ba. Jazy ya ce, "Lokacin da ka shiga Nigeria ka sauka a diamond hotel, itace ƴar jaridar dana faɗa maka mun yi magana da ita, har na yi mata alƙawarin itace zata hira da kai. Me ya baro ta daga garinsu duk da aikin da take dashi mai kyau?. Sannan ta zo Jidda ta fara aiki a kusa da gidan ka, sannan daga baya ta fara yi maka aiki......"

Jazy ya yi shiru yana girgiza hannunsa, ya gyaÉ—a kai ya ce, "Akwai alamar tambaya akan yarinyar nan, zuciyarta bata amince da ita ba..." sai ya yi shiru, ya shiga video da ta yi, ya yi screenshot fuskar ta, ya tura ya ba da umarnin bincike a kan Islaha a take.

Rehaan shi kansa ya ɗan ji wani iri, musamamn da ya tuna itace dai wacce ya sace, ya tafi tunanin  meyasa ta shiga rayuwarsa har haka?.

Ya kalli Jazy ya ce, "Sannan itace yarinyar da na É—auke ta, har ka dinga cewa in ban sake ta ba zaka faÉ—awa Mamy."

Jazy ya zaro ido waje ya ce, "what! Kana nufin itace?."

"Itace."

Jazy ya furzar da iska, ya tafi tunani sannan ya ce, "da farko ta fara haÉ—uwa da kai a diamond hotel, ta zubar maka da tea har ta faÉ—a maka magana, kafin ta haÉ—u dani. Daga baya ta haÉ—u dani ta ce tana so ta yi hira da kai. Daga nan ka sace ta, sannan sai gata a Jeddah a kusa da gidan ka tana aiki, sai kuma gata a gidan ka a matsayin housemaid....."

Ya girgiza kai ya ce, "Ban yarda da ita ba, in ta aikata wani abu mara kyau wallahi i will have her arrested" ya faɗa zai fita sai kuma ya fasa ya ce, "bara na ƙyale ta. Amma ta san kaine Rehaan Yola?." Ya ɗage kafaɗa alamun oho, Jazy ya fita daga ɗakin ya koma wajan Islaha.

A zaune ya same ta kamar yadda ya bar ta, sallamar sa ya saka ta kalle sa, ya gyara tsayuwa ya ce, "Miss bani labarin a inda ki ka san me gidan nan."

Ta É—an kalle sa jin wata tambaya ta rainin hankali ta ce, "Mr Jafar meyasa ka ke yi min wannan tambayar?."

Maimakon ya amsa sai ya ce, "ina jinki."

Ta É—an yi tsaki kaÉ—an ta ce, "ni ban san shi ba, a diamond hotel na fara ganinsa, daga nan na gansa a Nadira hospital and medical center, daga nan ya sace ni, daga nan na gansa a gidan nan. Shine kawai."

Ya girgiza kai ya ce, "me ki ka yi masa har ya sace ki?."

Ta miƙe tsaye ta ce, "Wannan shi zaka tambaya, nima ban sani ba."

"HaÉ—uwar ku a hotel kafin ki haÉ—u dani, me ya haÉ—a ku?."

Ta ɗan dafe kai cikin ƙosawa ta ce, "why me? Ka je ka tambaye sa mana, lallai sai ni?."

Ya zuba mata ido ganin ko nauyinsa bata ji ta fara yi masa rashin kunya. Islaha ta juya ta ce, "na faɗa maka iya abinda na sani, meyasa zaka takura min da tambaya?" Ta faɗa zata wuce sa ya riƙe gefen mayafinta.
[7/14, 2:53 PM] KRBBK: RDB2P56
Nana Haleema.

Islaha ta mayafinta ta juyo ta ce, "Mr Jafar me ka ke so nace maka? Ƙarya ka ke so na yi maka?."

Ya zuba mata ido yana sake karantar yanayinta ya ce, "kin haɗu dashi a hotel, kin haɗu dashi a asibiti, ya sace ki, sannan ya ƙyale ki. Sai kuma ga ki a Jeddah, kin fara aiki a kusa da gidan nan, daga baya kin fara a nan. Meyasa rayuwar ki take haɗuwa da ta sa har haka?."

"Bani na halicci kaina ba balle na sani, Kuma wannan ai ba yin kaina bane, yin Allah ne. Ni kaina inda ina da dama, ko wanda ya san shi ma bazan nuna na sani ba balle shi da kansa. Hanya bazan so ta haÉ—a ni da wani nasa ba, balle shi É—in."

Ya É—an murmusa yana kallon idanunta ya ce, "Miss Islaha in na gano wani abu akasin haka a kan ki, wallahi i will have you arristed."

Da mamaki ta ce, "akasin abinda na faɗa, au har ni zan tsaya na yi maka ƙarya akan mutumin da ban san shi ba? Kawai sai na yi maka ƙarya dan na burge ka, ko dan ka bar ni na cigaba da aiki a gidan nan?....."

Ya yi shiru bai ce komai ba, ta cigaba ta ce, "Ni ban ce zan saka a kama shi ba sai kaine zaka ce zaka saka a kama ni saboda shi? Kai ga mai aboki, ni da sace ya sace banza kenan, tunda shi mai kuɗi ne ni kuma talaka ce. Ban san shi ba, ban san ko sunansa ba, kuma bani da buƙatar na sani. Aikina a gidan nan ma wani dalili ne kawai ya saka nake yi, in ba da dan dalilin ba da ban zo ƙasar nan ba balle har na zo gidan nan. Kuma ina so ka sani, shine dalilin, shine dalilin da ya saka na zo ƙasar Jeddah. Dan haka ni nake da bakin da zan ce ya shiga rayuwata, ba shi ba."

Jazy dai ya yi shiru yana kallonta ganin yadda take yi masa tsiwa cikin rashin tsoro.

Ta ce, "inda na yi niyar cutar dashi da baka zo ka same sa lafiya ba, tunda har in na dafa na bashi yana ci, da yanzu sai dai ka ji labarin mutuwarsa. In da ina niyar cutar dashi da ban taimake sa daga wajan wata ƙoɗaɗɗiyar baturiya ba, da na bari ta aikata ƙudurinta na jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Wallahi bai kai na baro ƙasata da iyalaina na zo nan saboda shi ba, ko biyana za a yi na bibiyi rayuwarsa bai kai wanda zan tsaya na ɓata lokacina na bibiye sa ba. Babu wanda nake jin haushi a duniya kamar shi ɗin, ina so ka faɗa masa, bai isa na zo dan na cuce sa ba wallahi, bai kai matsayin da zan riƙe sa a rai har na cuce sa ba" tana gama faɗar hakan ta nufi exit door.

"Wanne irin taimako ki ka yi masa, mai Alma zata yi masa ki ka taimake sa?."

Ta juyo ta kalle shi ta ce, "don Allah na yi, na yi saboda kasancewarsa musulmi É—an uwana, bayan wannan babu wani abun. Dan haka no need sai na faÉ—a maka" tana gama faÉ—ar hakan ta fita daga kitchen É—in.
Chapter 78 · 0% Book details