← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 133

Sashe 132

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya ce, "ka je kawai, duk abinda ya kamata aje ayi." Jafar ya amsa da girmamawa sannan yana miƙewa ya fita.

Gidansu Rehaan É—in shiru, duk baccin gajiyar dinner suke yi, shi kansa ba dan Abba ya kirasa ba bazai fito ba dan sai biyu na dare aka tashi daga event É—in jiya, kowa a gajiye yake yi.

Sanin Rehaan yana can yana baccinsa na ƙa'ida shiyasa bai shiga wajansa ba, ya fita daga gidan yana aiyyana yadda zai tsokane sa in anjima.

Garin Allah yana wayewa Islaha bata jira kowa ba ta wuce asibiti, a can ta tarar da Sadik ne kawai a wajansa.

Tana shiga suka haÉ—a ido, Saheer ya yi mata murmushin da gabanta ya faÉ—i. Yana zaune ya idar da sallah, ya yi wanka ya canja kaya amma ya rame sosai, ya yi wani iri, kamar wanda ya jima yana kwance cikin ciwo, damuwa ta bayyana akan fuskarsa sosai. Islaha ta tsaya cak tana kallonsa kamar yadda yake kallon ta.

Cikin nutsuwa ya miƙe a hankali, ƙafarsa ciwo take yi masa sosai, saboda ɗaurin da ya sha a wajen mutanen, hannunsa ma kamar har lokacin a ɗaure yake haka yake ji, amma saboda murnar ganin Islaha haka ya miƙe a kan ƙafarsa ya matso kusa da it ya ce, "Matar Hamma!."

Yadda ya faÉ—i sunan, da yadda muryarsa ta fita, da yadda yake kallon ta, da yadda yadda yanayinsa ya koma ya saka gabanta ya faÉ—i, ta lumshe ido ta buÉ—e hawaye suka taru a idonta.

Ganin tana hawaye sai ya miƙa hannunsa kan fuskarta ya goge mata ya ce, "ki amsa mana, ba ki ji na kira sunanki ba?."

Islaha kasa magana sai ta fashe da kuka mai sauti, zuciyarta gabaɗaya ta gama karyewa, jikinta ya yi sanyi, zuciyarta tana rawa kamar zata faɗo ƙasa. Tana tunannin shikenan ta cuci kanta, ga Hamma ya dawo amma ita zata tafi, zata tafi gidan wani matsayin matarsa ba Hamma ba, zata tafi wani wajen da zata zauna da wani namiji a matsayin mijinta ba Hamma.

Saheer ya riƙe hannunta duka biyun, cikin wani irin yanayi na rauni da gajiyar da take jikinsa ya ce, "Islaha zan tsallaka iyaka, i want to hug" Ya faɗa yana a hankali yana kallon ta.

"Saheer me ka ke yi haka?" Sadik ya faɗa da sauri dan ya dakatar dashi, dan shi ya san akwai auren wani a kanta, riƙe hannunta ma da ya yi sai dai Allah ya yafe, amma ba ƙaramin zunubi aka aikata ba.

Saheer ya juyo ya kalle sa ya ce, "iya yau ne kawai, in ban jita a jikina ba zan iya mutuwa Sadik. Ina tsananin kewar ta, ni kaina bazan ce ga adadin kewar ta da nake ji ba.”

A lokacin Baffa ya shigo ɗakin ya raba gardamar, da sauri Islaha ta ƙwace hannunta ta koma gefe tana cigaba da zubar da hawaye.

Baffa ya bita da kallon mamaki, dan shi bai san ta fito daga gida ba balle ta zo nan ya ce, "Islaha har kin ƙaraso?." Ta ɗaga masa kai ta yi bata iya cewa komai ba.

Baffa ya ƙarasa wajan Saheer ya ce, "barka da fitowa Saheer, Allah ya cigaba da kiyaye mu."

Saheer cikin jin daÉ—in ganin mahaifinsa ya ce, "Amin Baffa. Ina Mama?."

Baffa ya ce, "suna hanya, yanzu zasu ƙaraso."

Saheer ya É—aga kai yana kallon Islaha da take kuka, ya kalli Baffa ya ce, "Baffa ka ce ta daina kuka don Allah."

Baffa ya kalli Islaha, ya juya ya kalli Safeera da ta shigo lokacin ta ke tsaye daga bakin ƙofa ya ce, "Safeera ki rarrashe ta." Safeera ta ƙarasa inda Islaha take ta dafata kawai dan ta san baza ta daina kuka ba.

Saheer kam idanunsa yana kanta, duk inda ta motsa ita yake kallo. Ya kasa samun nutsuwa, ji yake kamar ya riƙo ta jikinsa ya rarrashe ta daina kuka. Duk da abubuwan da yake tunawa wanda suka faru a can, bai saka sun danne kewar Islaha da yake ji ba.

A lokacin Mama suka ƙaraso, suka riƙe Saheer suna kuka, shi kansa sai da ya yi kukan na kewar ƴanuwansa da iyayensa.

Likita ya sallame su, bayan ya ba shi magani, ya kuma ce ya dinga yawan shan ruwa, sannan ya dinga cin abinci mai gina jiki. A lokacin da suka tafi, rana ta yi sosai dan har an yi sallar azahar.

Ita dai Islaha kasa komawa gidan ta yi, tana gidansu Safeera tana kukan da ya ƙi tsayawa. Sai da Baffa ya kira ta a waya ya ce ta dawo gida sannan ta koma.

Baffa kaɗai ta samu a zaune ta ƙarasa ta zauna, Baffa ya ce, "Ƙarfe huɗu zasu zo tafiya da ke Islaha. Ki yi haƙuri, ki bar wannan koke-koken. Za ki ta fi gidan mijin ki in sha Allah.

Nana Haleema.
[7/31, 11:42 AM] KRBBK: RDB2P100
Nana Haleema.

Islaha ta É—ago ta kalle sa cikin rauni, murya tana cracking ta ce, "Baffa, Hamma!."

"Zan yi masa bayani da kaina."

Tana girgiza kaita ce, "Don Allah kar ka faÉ—a masa, kar ya sani don Allah Baffa!."

Ya yi murmushi ya ce, "ai kuwa dole ya sani, ba abinda za a ɓoye masa bane."

Ta cigaba da kukan da ya zamar mata ɗan uwa Baffa ya ce, "kina da matsalar sarƙewar numfashi, ki dakata da wannan kukan, ki tashi ki je."

Islaha ta kasa tashi saboda kuka, Baffa ya ce, "Islaha ya isa, ki bar wannan kukan kar ki jawowa kan ki matsala. Ba ke ki ka halicci kan ki ba, Allah ne ya yi ki, kuma tun ka fi ki zo duniya ki ka rubuta ƙaddarar ki, kuma ba ki isa ki tsallake abinda ki ka rubuta da hannun ki ba. Babu Saheer a cikin rayuwar ki, halaccin da ki ke tunanin ya yi miki don Allah ya yi ba don ki aure shi ba, ba ki isa ki yi abinda Allah bai nufa ba. Dan haka ki daina kuka, ki tashi ki je ki shirya."

Duk da Baffa wa'azi yake yi mata amma ba ji take yi ba, Hamma kaɗai take hangowa a idanunta. Ta miƙe ta fita daga falon, tana fitowa ta haɗa ido da Hamma da Sadik a ƙofar ɗakinsa, Sadik yana riƙe dashi saboda bashi da ƙwari sosai, yana miƙa ledar maganinsa.

Ganin ya tsayar da idanunsa a kanta sai ta ƙarasa wajen da suke har ta je yana kallon taya ce, "me yake damun ki haka? Wannan koke-koken da ki ke yi na meye?. Ba gani na dawo ba, gani a gaban ki a tsaye ina yi miki magana, meyasa ba ki nuna farin cikin ganina ba ki ke kuka?."

Ta goge idanunta ta ce, "Ka yi haƙuri Hamma, don Allah ka yi haƙuri!." Abinda ta iya faɗa kenan, ta juya a guje ta bar wajan tana kuka.

Hankalinsa ya tashi sosai ya kalli Sadik cikin muryarsa da bata fita sosai ya ce, "me ya same ta, me ya faru ta ke bani haƙuri?."

Sadik ya ce, "ban sani ba, ka jira ta nutsu sai ka tambaye ta."

Saheer cikin damuwa ya ce, "na lura tana da damuwa sosai, akwai abinda ya faru da bana nan?.

"Ka sha magani ka ka huta, likita ya ce ka samu bacci mai tsaho, sai ka yi bacci jinin ka zai sauka. Ko wacce magana ce zata biyo baya, amma ba a yanzu ba. Ka tabbatar ka sha maganin nan, dan ya kashe maka ƙananun cuttukkan da suka shige ka."

Saheer ya yi shiru, Sadik ya raka shi É—aki, ya ba shi abincin da Mama ta aiko dashi ya É—an ci kaÉ—an, ya ba shi magani sannan ya kwanta.

Sadik ya bi shi da kallon tausayi sannan ya fito, ya rufe masa ƙofar cikim rauni ya ce, "Allah Sarki Saheer, sai dai ka yi haƙuri, amma Islaha yanzu ba ta ka bace, bazata taɓa zama ta ka ba har abada. Dan ni na san babu yadda za a yi Islaha ta dawo, ta tafi kenan."

Islaha da kuka ta koma gidansu Safeera, Safeera ta runtse ido dan ita har ta gaji da wannan koke-koken da Islaha take yi.

Ta yi tsaki cikin fusata ta ce, "in kin san za ki damu har haka meyasa ki ka amince? Da kanki ki ka ɗauki ƙafa ki ka je ki ka saka hannu, ba wani ne ya yi miki dole ba. Kukan me ki ke yi bayan ke ki ka kai kan ki?."

Bata ce komai ba sai kuka, itama Safeera ta yi mata banza bata sake ce mata komai ba, dan wallahi haushi take bata. Sai da suka jima a haka, sai daga baya Safeera ta ce, "Ki cigaba har ki samu attack."

Zazzaɓi ya rufe Islaha, kanta ya yi nauyi yana ciwo sosai. Cikin rauni da sanyin jiki da ciwo ta ce, "Wai ƙarfe huɗu za a zo a tafi dani, ni dai bana son tafiya ko ina Safeera, ina son zama tare da Hamma."

Safeera ta ce, "me ki ke so na ce miki yanzu?." Islaha bata ce komai ta cigaba da goge hawaye.

Safeera ta ce, "tunda ki ka yi aure zancen zama da Saheer ya ƙare, haka za ki yi haƙuri zuwa lokacin da komai zai yi daidai."

Ta goge ido ta ce, "da wacce fuska zai fahimce ni?."

"Zai fahimta, amma za a sha wahala."

Islaha ta ce, "daman ni marainiya ce, amma ban yi tunanin haka aurena zai zama na marasa gata kamar wannan ba."

"Oh da gaske auren ki ka yi kenan?."

Ta girgiza kai ta ce, "Ba haka nake nufi ba, kawai abin ne babu daÉ—i."

Safeera bata ce komai ba ta cigaba da danna wayarta dan bata san me zata ce mata ba kuma, ta gaji da rarrashinta. Sun jima a haka a zaune, har aka yi sallar la'asar, Baffa da kansa ya kira Safeera ya ce ta saka Islaha ta shirya ta rako ta gidan.

Jazy bai haÉ—u da Ray ba sai bayan sallar la'asar, ya same sa a zaune a falo yana video call a laptop, ya zauna a gafensa har ya kammala ya rufe laptop É—in.

Jazy ya ce, "a ina Rolls Royce take?."

Ray ya ce, "Ka tambayi Shams."
Chapter 132 · 0% Book details