Sashe 111
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita dai ta kasa magana ta zubawa Baffa ido, tana jin abin kamar a mafarki. Sai maimaita an ajjiye maganar Saheer a gefe kawai take yi a ranta, ga tashin hankalin da take ciki, ga wata magana da ta kasa gane mata gabaÉ—aya.
Ganin Baffa yana kallonta sai ta sauke ido ƙasa, Baffa ya ce, "na yi hakan dan cigaban rayuwarki da samun rayuwa mai inganci, kuma kowa yana son cigaba a rayuwarsa, za ki so ki auri wanda ya fi Saheer wani abu a duniya."
"A'a Baffa, ni bana son komai daga hannun kowa, kuɗi ko mulki basa gabana, ko shi wanda ka ke faɗa ɗin bazan iya zaɓarsa na bar Hamma ba."
Baffa ya murmusa ya ce, "a yanzu ba za ki gane abinda nake nufi ba Islaha, ba za ki fahimci abinda nake gujewa rayuwar ki ba. Amma indai kin ɗauke ni a matsayin uba, kin yarda bazan cutar dake ba, kin yarda bazan kai ki inda za ki sha wahala ba, kin yarda bazan hana ki auren Saheer saboda son zuciya ba, to ki kalli maganar da na kawo miki da zuciya ɗaya, kar ki kalle ta ta fuskar kuɗi ko na zaɓi wanda ya fi kuɗi akan ɗana. Duk wanda zai so auren ki da Saheer wallahil azim a bayana yake, ko ke da kan ki bana tunanin kina so ki aure shi kamar yadda nake so ki aure shi. Tunda ki ka ga na ja baya, ki amince da abinda nake faɗa miki kawai."
Ita dai bata san me zata ce ba, ta yi shiru kawai tana tunani dan ba wani jin kalaman Baffa take yi ba, tana cikin tashin hankalin rasa Hamma ana yi mata wani abu na daban.
Baffa ya ce, "Kina jina?."
Ta É—aga kai ta kalle sa ta ce, "Wallahi Baffa bana fahimtar komai, ni tunanin Hamma kawai nake yi."
Ya yi murmushi yana kallon ta ya ce, "Tashi ki je Islaha."
Ta miƙe kamar jira take yi, da gaske bata fahimtar abinda Baffa yake faɗa.
Mama duk ta ji abinda suke faɗa ta yi shiru tana tunanin wannan lamari cike da tashin hankali. Da hanzari ta koma ɓangarenta ta tarar da Karima da Hanan a zaune.
Nana Haleema.
[7/24, 9:52 AM] KRBBK: RDB2P83
Nana Haleema.
Mama tana shiga suka bi ta da kallo har ta samu waje ta zauna sannan Hajiya Karima ta ce, "Kun yi magana kuwa?."
Mama cikin wani irin yanayi ta ce, "Waye ma Alhaji AbdulAziz Yola?."
Hanan ta yi caraf ta ce, "Shine mahaifin Rehaan Yola."
Ta zaro ido cikin bugawar ƙirji da tashin hankali ta ce, "kan bala'i! Kun san me na jiyo a falon mai gidan nan?."
Hajiya Karima cike da zumuÉ—i ta ce, "FaÉ—i muna jin ki."
Mama ta ce, "Magana na ji ana yi akan ya turo a nemawa É—ansa auren Islaha."
A tare suka zaro ido waje Hanan ta ce, "ÆŠansa fa! Wanne daga cikin su?."
Karima ta ce, "Ke Zulaiga bana son ruɗewa, ƴaƴansa fa ance kaf sun yi aure, kuma tsakani da Allah me za su yi da Islaha? Su da suke auren ƴaƴan masu kuɗi me zasu yi da tashin gidan marayu? Ai sun fi ƙarfinta Islaha, mai gadin gidan ma ya fi ƙarfinta balle kuma ɗam gidan da kansa, anya kin ji da kyau?."
Mama cikin tabbatarwa ta ce, "Wallahi da gaske nake. Har Baffa ya amince da batun auren, itama yana saka mata ra'ayin ta amince ta bar Saheer."
"Danƙari!."
Mama ta gyara zama cikin baƙin ciki ta girgiza kai ta ce, "aiki ja Karima, na hana auren ta da Saheer kuma ta auri wanda ya fi Saheer? Ina wallahi bazai yu ba, dole na san abinda zan yi, AbdulAziz Yola fa."
Hanan ta ce, "Amma kuma akwai wani mahaukaci a gidan, shima ɗansa, kuma an ce ya girma sosai ana nema masa matar aure, amma yana da taɓin hankali. An ce in haukan ya tashi sai ya yiwa kowa duka, har mai aikin gidan ya taɓa kashewa kuma ya kashe banza. Ina jin shi ake so a aura mata."
Mama ta kalli Hanan ta ce, "Yana da ɗa na cikinsa wanda yake da taɓin hankali daman?."
Karima cikin tabbatarwa ta ce, "yana dashi, na taɓa ganinsa. Ya girma sosai, dan zai girmi Saheer amma babu hankali sam."
Sai kuma Karima ta kuma cewa, "Irinsa ne daidai da islahan ai, irin wanda zai kashe ta ya kashe banza shine daidai ita."
Mama ta kalli Karima ta ce, "bazai yu ba, in ta auri É—an gidan dole za a ce matar É—an uwan Rehaan Yola ce."
"Amma kuma matar mahaukaci ba.... Islaha bazata taɓa samun kwanciyar hankalin aure ba, kullum cikin fargaba da tunani take, kuɗin mahaifinsa bazai amfane ta da komai ba sai danasani. Kin ga kin samu hanyar kuɓutar da Saheer daga auren ta cikin sauƙi. Kar ki manta, in ya kashe ta ya kashe banza har lahira."
Mama ta yi shiru ta kalli Karima ta ce, "ni ban damu da wanda zata aura ba, ko waye ta aura ban da É—ana. Kawai wanann ne na ji ya yi girma da yawa, ta wuce class É—in Saheer fa."
Karima ta ja tsaki ta ce, "To wannan ɗin ya kai Saheer hankali ne? Ana faɗa miki mahaukaci ne tuburan kina kawo wata magana. In za ki amince da auren nan ki amince kawai, ta je can ta ƙarata, meye amfanin kuɗi babu farin ciki?."
Mama ta sauke numfashi cikin jin daÉ—i ta ce, "Ni dama zai kashe É—in ai da zan so hakan, É—ana ne wallahi baza ta aure shi ba, akan ta aure shi zan iya zama ajalinta. Ta je ta auri duk wanda zata aura amma ban da É—ana, dan nasan Alhaji AbdukAziz bazai bawa É—ansa mai hankali auren ta ba."
Hanan ta ce, "kin ga matan da Æ´an gidan suke aure kuwa? Kyawawa, farare tass, kuma Æ´aÆ´am masu kuÉ—i, dan har da wanda yake auren yar gwamna. To ban da abin ki Mama waye zai É—auki Islaha in ba mahaukacin ba?."
Karima ta ce, "Bar Maman nan ta ki, ko kuma tana so ta ce Rehaan É—in ne zai aure ta?.â€
Hanan ta ce, “Bar faÉ—a, ai ko a mafarki bazai taÉ“a faruwa ba balle a zahiri. Wai! Ina ita ina ganin Rehana balle aurensa?. Ban Æ™i ba ta zo a wankewa matarsa toilet.â€
Hajiya Karima ta yi dariya ta ce, “Ba ki da kirki Hanan. Amma a wajea mai wankin toilet É—in ma matsayi ne, ta Æ™are a a matar mahaukacin ya fi riba.â€
“Wallahi ya fi. Ban da abin Mama tunda har aka zo neman aurenta ai kin san ba abin kirki bane, basai an faÉ—a ba kowa ya san mahaukacin zata aura.â€
“Maman ta ki ma na ga ta ɗau haske." Suka yi dariya suka tafa.
Hanan ta sake yin dariyar mugunta ta ce, "duk wannan iyayin a matar mahaukaci zata ƙare, duk wanann gashin har baya, da wannan idanun, da shagwaɓa duk na mahaukaci ne."
Karima ta ce, "ta yi masa shagwaɓa ya ci kutmar ubanta, ya kashe ta ya kashe banza, ta mutu tana amsa sunan matar mahaukaci." Suka ƙyalƙyale da dariya a tare suna tafawa.
Baffa yana tsaye ya zo kiran Mama akan maganar Saheer ya jin duk abinda suke faɗa, ya sauke numfashi yana girgiza kai yana mamakin wannan ƙiyaya da suke yiwa Islaha. Ya dawo da baya ya kira lambar Alhaji Rufa'i dan shaida musu amincewar Islaha.
   •••••
"Mamy Hamma Rehaan bashi da lafiya." Riyya ta faÉ—a a gigice tana shigowa É—akin Mamy a guje.
Mamy gabanta ya faɗi, ta miƙe da gaggawa ta ce, "me ya same shi?." Ta faɗa suna fita a guje zuwa apartment ɗinsa.
Dawowarsa kenan daga Jeedah, ko wanka bai yi ba, yana zaune ya ji cikinsa yana yi masa ciwo sosai.
Mamy ta shiga da hanzari ta ƙarasa ta tallafo shi jikinta, ya kwantar da kansa a ƙirjinta tana shafa kansa ta ce, "Rehaan ciwon cikin ne?..."
Bai iya bata amsa ba saboda ciwo Mamy ta ce, "Sannu. Riyya je ki ki É—auko min pcm injectiom da sauri."
Ta koma da sauri ita kuma ta kwantar da shi a jikinta ta ce, "Banisha shiga É—aki ki É—auko towel, ki taho da ruwan sanyi."
Banisha ta je ta dawo, Rehaan yana ta juya kansa a ƙirjinta tana riƙe dashi cikin azabar da take addabarsa.
Banisha ce ta fara dawowa, Mamy ta kwantar da kansa a cinyarta, ta jiƙa towel ɗin da ruwan sanyi, ta ɗaga rigar jikinsa tana goga masa a cikinsa da ya ɗauki zafi kamar bakin wuta.
Ya ɗan riƙe hannun Mamy, dan wani irin ciwon ciki yake yi da ba ya so a taɓa masa cikin ko kaɗan, ko ya aka taɓa cikinsa ko aka motsa shi sai ya ji kamar za a zare masa rai.
Mamy cikin tausayi ta ce, "Yi haƙuri, zai daina."
Bai ce komai ba idonsa yana rufe yana kwance akan cinyarta tana shafa kansa da hannu É—aya, hannu É—aya yana kan cikinsa da towel dan ya ji sanyi.
A lokacin Riyya ta dawo da abinda Mamy ta saka ta É—auko. Mamy ta saka Riyya haÉ—a mata allurar, ta gama haÉ—a mata allurar ta bawa Mamy.
Mamy ta karɓa ta riƙo hannunsa guda ɗaya, ta cire masa agogon hannunsa, ta kalli Riyya ta ce, "cire takalmin ƙafarsa." Riyya ta cire masa ta ajjiye.
Mamy da dabara ta yi masa allurar a jijiyar hannunsa, daƙyar take motsawa saboda kar ta motsa ta motsa shi ciwo ya dawo baya.
Mamy ta kalli Riyya, murya a can ƙasa yadda baza ta dame shi ba ta ce, "kawo min ruwa a cup."
Riyya ta kawo mata ruwan, Mamy ta yi masa addu'a a cikin ruwan kamar yadda ta saba, ta tallafo kansa ta ce, "ÆŠago ka sha."
Ya ɗago a hankali ta zuba masa kaɗan a bakinsa, yana haɗɗiyewa a hankali, ruwan yana sauka cikinsa ya saurin runtse ido, saboda in wani abun ya shiga cikinsa kamar saukar garwashi haka yake ji. Daƙyar ya sha kaɗan, sauran ta zuba masa a fatar cikinsa tana gogewa da towel a hankali. Shi dai ya riƙe cinyarta sosai, ya kifa kansa a kai tana shafa gashin kansa tana yi masa tofi a hankali.