Sashe 103
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Bani labari, ya aka yi na ganki a nan bayan na san zaman ki a can bai isa kin tara waÉ—anan kuÉ—in ba."
Ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Hamma...."
Ya yi saurin dakatar da ita ya ce, "kar ki ɓoye min komai, in na same ki da ɓoye min wani abu kamar yadda ki ka dinga yi a baya zamu yi faɗa mai muni."
Ta girgiza kai ta ce, "bazan ɓoye maka komai ba, in sha Allah."
Ya É—aga kai ya ce, "ina jin ki."
Ta yi shiru kamar baza ta yi magana ba, dan bata san da wacce fuska zai É—auki maganar ta ba, ita kanta jin maganar take kamar wasan yara balle kuma shi. Ta sanyaya murya ta ce, "kamar yadda na faÉ—a maka ina samun kyautar kuÉ—i a gidan aiki, to a haka na tara kuÉ—in."
Ya sake kallon ta ya ce, "cikin wata biyun ki ka tara miliyoyin nan?."
Ta girgiza kai ta ce, "ba wannan ba, wanda na siyo ticket na dawo gida nake nufi."
"Okay, waÉ—ancan fa?."
Ta sake kallon sa ta ga ita yake kallo, sai ta daure saboda kar ya zarge ta ta ce, "Mun haɗu da Jafar ne, wanda muka taɓa haɗuwa dashi a Diamond hotel, lokacin da na je neman Rehaan Yola zamu yi interview. Shine ya ce min na dawo gida aikin bai dace dani ba, shi zai biya Rehaan kuɗinsa."
Saheer ya tsaya yana kallon ta jin wata magana mara kan gado, ta sako wasu mutane da bai san da su a cikin labarin ba. Ya ce, "Me ya kawo Jafar cikin maganar nan kuma? Ya aka yi ya san da batun kuÉ—in?. Sannan me ya kawo Rehaan Yola a ciki?."
Islaha ta É—an shiru sannan ta ce, "Shi wanda ya sace ni É—in, ashe shine Rehaan Yola ban sani ba, kuma..."
Saheer ya dakatar da ita ya ce, "ban gane ba, kamar ya shine Rehaan Yola, Rehaan Yola dai wanda na sani ki ke nufi?."
"Shi É—in dai Hamma. Shine ya É—auke saboda mun haÉ—u sau biyu na yi masa rashin kunya, sannan gidansa ne gidan da nake zuwa yin aiki a Jeddah. A nan muka haÉ—u da Jafar, ya yi bincike a kaina ya san wacece ni, shine ya ce aikin bai dace dani ba, ni kuma na faÉ—a masa dalilin zuwana Jeddah, shine ya ce na dawo gida zai biyasa kuÉ—insa. Shine kawai na dawo."
Saheer ya ce, "lokacin da kina Jeddah, kin ce min matar gidan ce ta ke yi miki kyautar kuÉ—i saboda tana da kirki, yanzu kuma kin ce Rehaan ne. Meye gaskiyar maganar?."
"Ƙarya na yi maka a wancan lokacin, bana so ka yi min faɗa kace ina zuwa wani gidan ne shiyasa na ce maka haka. Amma shi ko aure bashi dashi."
Ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, ita kuma ta ƙi kallonsa ta kawar da kai gefe tana jira ta ji amsar da zai bata.
Sun kwashe minitina ashirin a haka kafin ya ce, "Wanne series ne, waye ya ya yi directing film É—in?. Na san dai labari da tsarwa na ki ne, to waye ya ba da umarni?."
Ta juyo suka haÉ—a ido jin abinda ya ce, ya É—aga mata kai ya ce, "a wacce channle ake haskawa nima na gani, ko a youtube ne?."
Islaha ta sauke numfashi jin bai yarda ba, ta lumshe ido ta ce, "Hamma da gaske nake fa."
"Nima da gasken nake ai, ki faÉ—a min sunan series É—in na je na kalla. Ko sunansa rainin hankalin Islaha?."
"Hamma...!"
Ya dakatar da ita ya ce, "Ni za ki mayar ƙaramin yaro Islaha, ni za ki zauna kina rainawa hankali dan kin ga ina ɗaukar ko wacce damuwa daga wajen ki?."
Islaha ta ce, "Da gaske nake Hamma."
"Da farko kin ce min ba ki san wanda ya sace ki ba, kin ce ba ɗan ƙasar nan bane ba, aka yi ta fama dake akan ki ba da wata hujja da za a iya gano waye ki ka ƙi faɗa. Yanzu sai Rehaan Yola ya shigo cikin wasan kwaikwayon ki, sai ga Jafar ma ya shigo cikin wasan dan a yi acting ɗin dashi. Da yake kin mayar da Rehaan abokin wasan ki ko, An faɗa miki ƙaramin mutum ne shi?. Ko kina faɗa sunansa ne dan na ji a raina ai kina tare da mai kuɗi bara in bar magana? Ko kina faɗa min Rehaan ne dan na ji a raina baza ki yi min ƙarya dashi ba?."
Islaha zata sake magana ya hanata ya ce, "indai wannan shashancin za ki cigaba da faɗin min bana son ji, ki riƙe kalamanki kawai. Gwara ki fito fili ki faɗa ki ce Hamma bazan faɗa maka ba, ya fi min daidai akan ki dinga raina min hankali kamar wani sa'anki."
Islaha ta ce, "Wallahi da gaske nake, bazan yi maka ƙarya ba."
Ya kalle ta ya ɗauke kai sannan ya ce, "Da dai bakya yin rantsuwa akan ƙarya, amma yanzu kin fara. Ke da bakin ki kin ce ƙarya ki ka yi min dan kar na yi miki faɗa, wannan ma dan lin yi min ƙarya ba yau aka fara ba."
Islaha sai ta yi shiru dan bata san me zata ce masa ba kuma, tunda har ya yi tunanin ta rantse a kan ƙarya gwara kawai ta yi shiru da bakinta zai fi alkhairi.
Ta yi shiru shima ya yi shiru, ya zubawa ƙaramin titin masu ido ita kuma tana wasa da jakarta bata sake ce masa komai. Baza ta sake cewa komai ba tunda ya yace tana rantsuwa a kan ƙarya a je a hakan, gwara ta yi shiru kar ta yi masa rashin kunya tazo tana danasani daga baya.
Shi kuwa tunanin wannan rainin hankalin nata kawai yake yi, ji yake ba a taɓa raina masa hankali a duniya kamar yadda Islaha ta yi masa ba, ji yake ba a taɓa yi raina masa wayo da wulaƙanci kamar abinda ta yi a lokacin ba.
Zuciyarsa ta fara É—arsa masa abubuwa kala kala a kanta, ya fara zargin kalaman Sadik dana Mama gaskiya ne, tunda gashi ta saka shi a gaba tana raina masa hankali kamar wani yaro É—an shekara É—aya.
Ya yi ajiyar xuciya bai ce komai ba, sun jima a haka kowa ya yi shiru babu wanda ya sake magana a cikinsu. Sai daga baya ya ja motar suka tafi wajan aikin bai sake yi mata magana ba.
A bakin gate ɗin ma'aikatar ya tsaya baice mata komai ba, ta ɗauki handbag ɗinta sannan ta kalle shi, kamar kar ta yi magana sai kuma ta ce, "in na yi ƙarya da sunan Ray wacce riba zan samu Hamma? Wanne irin amfani hakan zai yi min da zan rasa da wanda zan yi maka ƙarya sai shi?. Amma tunda kana jin abinda na faɗa maka a matsayin ƙarya shikenan, har kana cewa ina rantsuwa akan ƙarya. Duk tunanin da zuciyarka ta baka a kaina ka yarda hakan ne, kar ka tilasta zuciyarka ta amince da gaskiya na faɗa, ka yi amfani da yardar ka ya fi" ta faɗa tana fita daga motar har lokacin bai ce mata komai ba.
_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.ðŸ™ðŸ»ðŸ˜_
Nana Haleema.
[7/22, 10:14 AM] KRBBK: RDB2P76
Nana Haleeema.
Sai da ya ga ta shiga wajan aikin sanann ya ja tsaki, a bayyane ya ce, "Islaha ƴar rainin hankali ce, ni zata saka a gaba tana bugawa kamar ball dan ta raina ni? Da farko an sace ta, ta biya kuɗin aikin baffa, ta saka aka kulle case, ta tafi Jeddah, ta yi min ƙaryar wata mace ce take bata kuɗi, yanzu ta dawo tana kallon idona tana faɗa min wai Mr Rehaan ne. Mtsww!"ya faɗa yana jan motar ya bar wajan.
Yana barin wajan da Sadik suka haɗu, Sadik ya shiga motar ya zauna ya ce, "Ya dai na ganka da ɓacin rai a safiyar nan, bayan jiya kace min akwai labari?."
Saheer ya kalle shi ya ce, "kalli fuskata Sadik, na yi kama da shashasha?."
Da mamaki ya ce, "ban gane ba, me ya faru?."
Saheer ya ce, "yarinyar nan Islaha ce take neman mayar dani mahaukaci."
Sadik ya yi yar dariya ya ce, "sai yanzu ka sani kenan....Hmmm me ya faru?."
"Na tambaye ta akan ya aka yi ta dawo gida bayan bata gama abinda ta je yi ba, a ina ta samu kuÉ—i, ka san me ta ce?."
"Sai ka faÉ—a."
"Wai Rehaan Yola shine ya sace ta, kuma dashi ta haÉ—u a can, Jafar ya biya mata kuÉ—in kuma ya ce ta dawo gida."
Sadik ya ce, "ban gane ba, wanne Reheen Yola É—in?."
"Wanda ka sani, wanda ta je hotel yin interview dashi kwanaki. Wai da shi ta haÉ—u dashi a can, daga nan suka haÉ—u asibiti, ya sace ta, ta sace masa kuÉ—i, ta je Jedda suka haÉ—u......." Sai ya ja dogon tsaki yana dukan motar, ya dafe kai ya ce, "Islaha ta mayar dani mahaukaci gabaÉ—aya."
Sadik ya ce, "bayan mahaukaci ta mayar da kai sakarai wanda bai san abinda yake yi ba. Ta rasa da wanda zata yi ƙarya sai da Ray? Kuma duk wannan shirmen da ta lissafa ta ce duk da shi ya fau? Ta rasa wanda zata ƙullawa sharri sai shi?."
"Hmm!" Ya faÉ—a yana jan numfashi kawai bai ce komai ba dan bai san abinda zai ce ba.
Sadik ya ce, "wannan maganar bata da kan gado balle makama, da sunan wani zauna gari banza ta faɗa ma sai a yarda, amma sunan wanda ta kira ba abin wasa bane. A ina zata ga Rehaan ma, mutumin da ko yaushe yana Uk? Ko da ma shi ɗin ne, ace bata taɓa ganin hotonsa ba balle ace har ya sace ta bata san shi bane?. Islaha fa ƴar jarida ce, kuma ƴar social media ce, duk wanda yake hawa kafafen yaɗa labarai ƙarya yake yi ya ce bai san Rehaan Yola ba. To akan me ma zai zubar da class ɗinsa ya ɗauke Islaha fisabinillahi?."
Saheer dai bai ce komai ba, dan gani yake Islaha ta gama katantanwa da hankalinsa gabaÉ—aya.