← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 133

Sashe 49

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Labiba ta juya ta bisa da kallo tana dafe ƙirji, sai suka haɗa ido da Aysha da take tsaye a wajan. Labiba ta ruɗe ta kasa magana, har Aysha ta shigo kitchen ɗin ta kasa cewa komai.

Aysha ta bita da kallo kafin ta ce, "kin zo ƙasar nan saboda ki tara kuɗi ko saboda ki yi asarar kuɗi?."

Labiba a diririce ta ce, "ni ban san ma ya shigo ba, kawai na ji...."

Aisha ta dakatar da ita ta ce, "kawai ki bani amsa."

Labiba ta ce, "ina so mana, kuÉ—i na fito nema."

Aisha ta ƙare mata kallo sannan ta ce, "Amma ki ke tsaye a nan?."

Da mamaki ta ce, "Ina zan je to?."

"meyasa baki bi shi É—akin ba kamar yadda ya ce?."

Labiba ta bita da kallo alamun ƙarin bayani, Aisha ta ce, "ta wannan hanyar zaki fara tara kuɗin irin wanda baki yi tunani ba. Ubaid mutum ne mai kuɗin gaske, wallahi kuɗin da yake dashi zan iya cewa bai san adadinsu ba, kuɗin da yake dashi da a nigeria yake zai zama na farko a ƙasar. Indai zaki yi abinda yake so babu abinda bazai yi miki ba...."

"Ni ɗin nan da ki ke gani nabu abinda baya bani, na canjawa iyayena gida, na siya musu mota, na kawo su umra duk da kuɗin da nake samu a gidan nan. Kema dan jinin mu ya zo ɗaya ne ya saka har na bar ki a gidan nan, har nake faɗa miki sirrin gidan, amma da wallahi bazan taɓa bari ki raɓe sa, ba saboda ni kaɗai na san alkhairi da nake samu tare dashi."

Labiba ta É—an yi shiru tana tunani kafin ta ce, "Aysha kuma kina ganin babu matsala?."

"Wacce matsala ana zaune lafiya? Kuɗi ki ka zo nema kuma su zaki samu, Ba shikenan ba?. In ki ka biye ta albashi kuɗin kayan sakawa ma gagarar ki zai yi, dan kayan ƙasar nan shegen tsada ne dasu wallahi. Amma in ki ka saki jiki shikenan zaki ga kin zama hajiya, kina daga nan kina turawa gida abin arzuƙi ana bin ki da albarka. In ki ka saki jiki, Ubaid ƙasar waje zai ɗauke ki ya tafi dake."

Labiba ta yi shiru bata ce komai ba, har lokacin jikinta a sanyaye yake ta kasa aikata kataɓus balle ta amsa ta amince ko bata amince ba. Aysha ta bita da kallo tana dariya a ranta, tana ayyana bata san dawar garin ba, dan inda ta san waye Ubaid da bata tsaya a wajen ba. Aishata girgiza kai suka cigaba da gyare gyarensu.

Labiba da ta shiga É—aki waya ta É—auka ta shiga lambar Mama ta ganta online sai ta kira ta ta inda Aisha ta koya mata.

Mama tana É—auka ta ce, "ke kuma haka ake yin abu? Daga tafiya sai a jiki shiru babu wani labari?."

Labiba ta ce, "ina nan lafiya Mama, ya jikin Baffa?."

"Da sauƙi. Ya aikin?."

"Mama aiki ake yi kamar jakai, akwai gajiya a aikin su wallahi."

"amma akwai damun kuɗi ba, kar ki bada ni mana, kar ki saka na yi danasanin tura ki, dan Hanan da take nan gida kuɗin da take kawowa yana da yawa, ke gaki a can har kin fara ƙorafi. Kar ki saka zuwan naki ya zama bashi da amfani."

Ran Labiba ya ɓaci sosai ta ce, "Mama wai ko mai sai ki ce Hanan, me take baki wanda ni bana bayarwa?."

"To itace take kawo min abin arzuƙi, ba dole na dinga ambatar sunanta ba?."

"Nima zan aiko miki da kuÉ—in da sai kin ce gwara ni akanta."

"Dakyau! Kina yin hakan kin tabbatar min da ke ɗin mai ƙaunata ce, ke jinina ce, ke mai kishi ce."

"Zan yi Mama, indai zaki daina yabonta a kaina."

"Tuni zan daina, indai zaki yi abinda ya fi nata ita ɗin banza. Ai ni duk wacce ta fi kawo min kuɗi itace ta gaban goshi a wajena. Ke dai kawai ki riƙe kan ki."

Labiba ta murɗa baki kamar tana wajan ta kashe wayar. Sai ga kiran Hannan tana ɗauka ta faɗa mata abinda ya sake ɓata mata rai ta kashe tana.

Aysha ce ta shigo ta bita da kallo ta ce, "ki tashi mu je mu ƙarasa aikin can."

Labiba ta miƙe a sanyaye ta fito, bayan sun gama Aysha ta ce, "zan je na yi wanka, kema ki yi."

Ta É—aga kai ta shiga É—aki, ta shiga wanka tana yi tana tsakin abinda Hanna ta ce mata har ta fito, tana fitowa ta ga an kashe hasken É—akin.

Abin ya bata mamaki, dan ta san ita a kunne ta bar sa da zata shiga. Ta ƙarasa wajen switch, zata kunna kenan ta ji an riƙo ta, ta firgita zata ƙwace ta ji muryarsa a kunnenta.

Ya kunna hasken ya bita da shegen kallo ya ce, "ke mai kyau ce."

Gabanta ya faɗi, amma da ta tuna ƙudurinta akan nsman kuɗi sai ta ɗan yi murmushi tana kallon sa. Ya ɗago da fuskar yana kallon idanunta ya ce, "i’m waiting for you" yana faɗa ya fita daga ɗakin.

Yana fita Aysha ta shigo ta bita da kallo ta ce, "zan je mall na dawo."

A sanyaye ta ce, "nima zani."

"A'a ki zauna, ba ya ce ki same sa a É—aki ba?."

"Ni tsoro nake ji fa."

"Tsoron me? Kina so ki ce min baki taɓa yi ba?."

"ban taɓa ba, sai dai ƙananun abubuwa. Amma ban taɓa bada kaina ba."

"Dakyau! Tunda kin saba da ƙananun abubuwa sai ki fara da manyan yau, kuma tukwicin babba ne tunda shine na farko. Ki saki jiki ki je a wuce wajen, in ba haka ba wallahi zaki yi danasani mai yawa."

“Zan je, kawai ina ganin kamar abin zunubin ya yi yawa saboda a ƙasar saudia nake."

Aisha ta taɓe baki ta ce, "Sai me da a ƙasar ki ke? Ai ba a makka ko Madina ki ke ba, nan Jedda ce. Allah na tuba ko a Makka da Madina nan ki ke meye a ciki? Mu sau nawa muna yi a can? Akwai abinda ya same mu?."

Labiba ta ce, "ni tunani nake yi wallahi."

"Mtsww! Ke ki ka sani, ni na fita."

Labiba ta koma gefen gado ta zauna tana tunani, tana son tara kuÉ—i masu yawa sosai, tana so ta yiwa Mama abinda Hanan bata yi mata ba, ga hanya ta samu amma zuciyarta tana rawa sosai.

Ta saba ƙananun abubuwa da maza, babu abinda namiji bai taɓa yi mata ba, babu inda hannun namiji bai je a jikinta ba. Ta saba da hakan sosai, kuma ta ƙware a kai kawai bata taɓa bada kanta ba, sun yi da wani alhaji akan hakan tafiyar nan tazo. Duk da ba wai faruwar abin take jin tsoro ba, tsoron ta ɗaya Ubaid ba ɗan ƙasar su bane, sai take ganin kamar bai dace ta saka masa jiki ba.

Ta tuna kalaman Aysha, sai ta samu ƙarfin guiwa mai yawa, tana ji a ranta lokacin zaman ta hajiya ne kawai ya yi, shiyasa Allah ya jinkirta mata har aka zo yanzu.A sanyaye ta shirya ta saka kaya ta nufi ɗakin nasa. 

Zaune ta same sa daga shi sai short, ta bi sa da kallo dan fatarsa kaÉ—ai ma abin kallo ne, fari ne sosai ga kyaun larabawa.

Tana shiga ya taso ya riƙo ta yana kallon ta ya ce, "kina jin tsoro?."

Ta ɗaga kai a sanyaye ya ce, "Sau nawa ki ka taɓa yi?."

Ta girgiza kai ta ce, "Ban taɓa ba."

"Kin tabbatar?."

Ta É—aga kai alamun eh, ya murmusa ya ce, "nawa ki ke so na baki?."

Ta kalle sa suka haÉ—a ido ya ce, "ki faÉ—a."

Labiba bata ce komai ba, ya sake ta ɗauko kuɗi riyal ya buɗe hannunta ya saka mata, kallon kuɗin take yi dan bata taɓa ganin Saudi riyal ba tunda take, bata san riyal nawa bace, kawai kallon ta kawai take yi ta ga dai ɗari biyar a rubuce.

Ya yi converting kuÉ—in da ya bata to naira ya nuna mata wayarsa, zaro ido ta yi ganin kuÉ—in mai yawa a kuÉ—in nigeria, ta kalli hannunta ta gansu É—an kaÉ—an ba wani yawa ne dasu ba, amma a kuÉ—in nigeria da ywa sosai.

Suka haɗa ido, kafin ta ce wani abun ya jawo ta ya ƙanƙame yana zare rigar jikinta a hankali.

•••••••••

      Umma tana zaune tana kallon hannunta cikin gajiya, hannunta duk ya yi ja saboda wankin yaran da ta yi. Ta sauke nunfashi mai tsaho, gidan shiru duk sun fita sai ita kaɗai shiyasa ta samu damar hutawa.

A gajiya yake jinta sosai, gaɓoɓinta duk sun gaji saboda aikin da ta sha a gidan. Ko abincin kirki bata samu ta ci ba saboda aiki, sallah ma ba a nutse take yi ba saboda ihun su.

A sanyaye ta jawo wayar ta kunna data amma data taƙi yi kwata kwata. Ta sauke ajiyar zuciya ta kira lambar Safeera, wayar ta shiga dan ta saka kati sosai a layinta.

Wayar tana ta yi ba a É—auka ba, ta sauke ajiyar zuciya ta rasa wanda zata kira. Kallon lambar Baba take yi abinda ya faru yana dawo mata a ranta, ta rufe ido ta buÉ—e ta nemo, dan baza ta iya kiransa ba, sai ta kira lambar Atika. Bata jima ringing ba Atika ta É—auka, Umma ta ce, "Atika kina jina."

Daga can ɓangaren Atika ta ce, "Ina jinki, Hajiya Maimuna mutanen makka da madina. Ya ki ke?."

Umma ta sauke numfashi ta ce, "lafiya lau, kowa lafiya?."

"Lafiya ƙalau. Ya aka yi wayar ta shigo? Na ji ance fa layin nigeria ba ya yi."

"Eh da yake na saka kati sosai a wayar, kema kuma yanzu zasu É—auki katin wayar ki."

"Allah sarki. Ai da kati sosai a wayar tawa,
É—azu na saka na dubu uku shiyasa ta shigo."

"Na kira Safeera bata É—auka ba, ban yi magana dasu ba tunda nazo. Don Allah ki duba min su."

Atika ta ce, "kar ki damu zan duba miki su in Allah ya yarda. Da fatan komai lafiya dai ko? Aiki ya samu ko?."
Chapter 49 · 0% Book details