← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 133

Sashe 51

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Shafa ta ce, "ki dakatar da wannan shirmen, ki saki jiki ki yi aiki. Tunda ki ka zo baza ki samu ƴanci ba sai kin gama biyan bashin kuɗin da yake kan ki, yanzu a ƙarƙashin kamfani ki ke, dole ki nutsu. Zan kira Alhaji Musan, zan faɗa masa ya yiwa waɗanda suka yi miki hanya magana, bazan ɗauki wannan shirmen ba wallahi, na gaji da kawo ƙara."

Umma dai bata ce komai ba dan an kulle nata baki. Hajiya Shafa yi tsaki ta ce, "ki fito ki yi musu aiki, ki daina wanna É—ari É—arin, ba jin yaren ki suke yi ba. In kina É—arare jiki zasu zargi baki da gaskiya, in suka yi miki wani abun ke ki ka jiyo" ta faÉ—a tana yin gaba.

Umma dai tana tsaye kamar an dasa ta a wajan cikin tashin hankali, Hajiya Shafa ta juyo ta ce, "ki zo mu je."

Umma ta tako a hankali ta biyo bayanta cikin yanayi na ruÉ—ewa da tashin hankali.

••••••••

Mamy tana zaune tana waya da yan ƙasar su, bayan ta gama wayar Abba ya kira ta ya ce ta zo yana neman ta. Mamy tq miƙe ta nufi apartment ɗinsa ta same sa a zaune.

Ta ƙarasa ta zauna ta ce, "gani Abba."

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Daada ce."

Mamy ta É—an murmusa ta ce, "akan maganar Rehaan ko?."

Ya É—aga kai ya ce, "ta ya ki ka canka?."

Ta yi murmushi ta ce, "indai har aka ce Daada to tabbas na san maganar Rehaan ce. Me ya faru?."

Ya yi murmushi sannan ya ce, "akan auren sa da yarinyar can ne, ta matsa a kai sosai ma kuwa. Dan yau ta ce min ko ta mutu na tabbatar ya auri yarinyar, hakan shine zai saka ta kwanta a kabarinta lafiya."

Mamy ta ce, "ikon Allah! Wai a ina ta san yarinyar nan haka?."

Ya girgiza kai ya ce, "Ke dai ki bar girma Nadira, Daada ta girma shekaru sun ja, shiyasa take fama da rigima kala kala."

Mamy ta ce, "to yanzu kun yi magana da iyayen yarinyar ne?."

"Na faɗa min ance mai riƙonta yana kwance a asibiti, da wa zan yi magana?."

"To sai ka faÉ—a mata hakan ko?."

"Na faÉ—a mata, ta sake maimaita min ko bata da rai na tabbatar an yi auren nan. Tana son yarinyar, kuma ita take so Rehaan ya aura. Ko yau ta mutu, gobe a É—aura musu aure."

Mamy ta yi murmushi ta ce, "To me zamu ce tunda Daada ce ta yanke? Sai mu yi fatan Allah ya sa ta gari ce."

Abba ya ce, "Amin ya rabbi. Zan saka a yi min bincike mai ƙarfi a kanta.”

Mamy ta ce, "ni wallahi Ikram nake yi masa sha'awar aure, yarinyar tana da hankali sosai, kuma ni na lura kamar itama tana son shi."

Abba ya yi dariya ya ce, "za a ki saka a maimaita Juwairiyya da Jafar kenan. Ke kin san yadda aka kai ruwa rana akan auren nan, yanzu in aka sako maganar Ikram da Rehaan ai babu zaman lafiya."

Mamu ta ce, "Inda zai amince ɗin da sauƙi, yadda ta amince dana Riyya shima zata amince."

Ya yi murmushi ya ce, "indai har Rehaan É—in zai amince da Ikram É—in sai ya aure su duka, Ikram itace tamu, mun san halinta ta san namu. Ita kuwa wannan bamu san daga ina take ba."

Mamy ta ɗan taɓe baki tana jin takaici a ranta ta ce, "ni tun kafin tazo ma bana sonta, sam bata yi min."

Abba ya É—an buÉ—e ido ya ce, "akan me? Yarinyar da baki santa ba zaki ce baki so bata yi yi miki ba?."

Ta yi shiru bata ce komai ba, Abba ya girgiza kai ya ce, "Saboda Rehaan baya so ko?."

Mamy ta kalle sa ya ce, "Na san halin ki ai, duk abinda yake so shi ki ke so, abinda baya so kema bakya so. Kefa koda kina son abu, da ya kushe sai ya fita daga ranki. In kuma bakya so, shi kuma yana so sai ki so kema."

Ta É—an yi murmushi dan tasan haka É—in ne, ko me Rehaan yake so tana so, in baya so bata so.

Abba ya ce, "yanzu dai kin san dole nayi abinda mahaifiyata take so ko?."

Ta girgiza kai ta ce, "gaskiya ne."

"To ki ba da haɗin kai akan auren nan, na fahimci Daada da gaske take, babu wasa ko rikicin tsufa. Ki yi haƙuri."

Mamy ta girgiza kai bata ce komai ba, amma ko kusa bata son auren nan, haka kawai yarinyar bata yi mata ba, bata santa bata taɓa ganinta ba, amma tana jin ƙinta a ranta, saboda tana ganin ta silarta za a yiwa ɗan da ta fi so a duniya dole, bata taɓa yiwa ɗanta dole akan komai ba, amma akanta za a yi masa dole. Wannan dalilin ne ya saka Islaha bata yi mata ba.

••••••••

Mama tana tsaye a ɗaki riƙe da waya ta ce, "ina jin ki, ya ake ciki yanzu?."

Daga wayar aka ce, "an tabbatar min da yarinyar nan ta tafi ƙasar waje aiki, kin ga tayi daidai da wacce mu ke nema."

"Aikin gwamnati ko na kamfani?."

"Aikin gidan turwa mana. Aikin da ake lalata rayuwar mata, shi nake nufi."

Mama ta buÉ—e ido ta ce, "da gaske ki ke?."

"Wallahi da gaske nake. An tabbatar min da yarinyar bata ji, tana ɗan taɓa abubuwan zamani. Dan gidan da take zaune ma babu tarbiyya, ana yiwa mai riƙonta take da woman leader. Ƴaƴanta ne jarinta, sune suke fita su kwana a waje su kawo mata kuɗi, kuma itama a gidan take."

Mama ta ƙyalƙyale da dariya ta ce, "ina zuwa."

Ta faɗa tana kashe wayar, bata ɓata lokaci ba ta kira lambar malam, suna gaisawa ta ce, "Malam akan batun auren Rehaan da yarinyar nan, ina so a yi aikin da ko ba yaso sai an yi auren nan ta ƙarfi da yaji."

Malam ya ce, "kar ki samu damuwa. Ki É—auka kamar an yi wannan aikin an gama, in kin ga ya tsallake auren to zai iya tsallake mutuwarsa."

Daɗi ya mamaye zuciyar Mama, cikim farin ciki da jin daɗi ta ce, "yauwa Malam, yarinyar tayi daidai da ra'ayina, tayi daidai da wacce nake nema. A taimaka ayi aikin nan Malam, in ba a yi auren ba hankalina bazai taɓa kwanciya ba."

Malam ya ce, "kar ki damu Hajiya Saddiƙa, wannan ƙaramin abu ne, kawai ki ɗauka an gama. Dan wallahi sai an yi auren nan, auren nan babu fashi."

Mama ta ce, "zan turo da abin sakada a rabawa almajirai, sannan akwai naka ka yi cefane." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar.

Mama cikin farin ciki ta ce, "dakyau! Kai wannan lamari ya yi min daÉ—i, bana so Rehaan ya auri mace ta gari domin hakan ma amfaninmu ne. Dole na tabbatar da auren nan ya yu, ko koda zai mutu akan ba ya so sai dai ya mutu, amma auren nan kamar an yi sa an gama!!" ta faÉ—a cikin nishaÉ—i, dan ita kaÉ—ai ta san amfanin da hakan zai yi mata.

Mu je zuwa. 💃🏻
[7/3, 2:05 PM] KRBBK: RDB2P36
Nana Haleema.

Kamar yadda Umma ta faɗawa Atika bata yi ƙasa a guiwa ba ta shirya ta nufi gidan. Da sallama ta shiga suka amsa suna kallon ta cikin sakin fuska.

Safeera ta ce, "sannu da zuwa Mama Atika." Atika ta murmusa ta zauna ta ce, "Yauwa Safeera, ya gida ya ƙannen naki?."

Saferra ta ce, "Lafiya lau. Ina Kausar?."

"Tana gida, ta ce na gaishe ki."

"Ina amsawa."

Atika ta ce, "Mun yi waya da da Umman ku, ta ce ta kira ki baki É—auka ba, shiyasa ta ce nazo na ga lafiya."

Rukayya da ƙannenta suka haɗa baki suka ce, "Mama Atika don Allah ki kira mana ita."

Atika ta murmusa ta ce, "to bara na gwada, kun san yanayim ƙasar da take sai a hankali" ta faɗa tana ɗaukar wayar ta kira wayar Umma amma ba a ɗauka ba.

Ta kalle su ta ce, "ba a É—auka ba, amma gobe zan kira muku ita da kaina."

Jikinsu duk ya yi sanyi alamun ba haka aka so ba. Atika ta kalli Safeera ta ce, "Ya aikin naki?." Safeera ta ce, "Alhamdu lillah."

"Amma za ki cigaba da zuwa ko?."

Safeera zata yi magana Baba ya yi sallama ya shigo. Mama Atika ta sauka har ƙasa ta gaishe sa, ya amsa ya ce, "yau ke ce a gidan?."

Cikin fara'a ta ce, "Ni ce. Mun yi magana da Maimuna ne ta ce don Allah nazo naga ya yaran suke, shiyasa na fito."

Baba ya gyaÉ—a kai ya ce, "kin kyauta" ya faÉ—a yana shiga É—aki.

Atika ta ce, "Safeera kar ki ce zaki ajiiye aikin ki akan wannan abun, ki yi haƙuri ki cigaba da zuwa."

Safeera ta ce, "Mama Atika in na tafi waye zai dinga kula da gidan? Sannan in Baba ya dawo abincinsa fa?. In suka dawo daga makaranta ban dawo ba Baba bai dawo ba ina zasu je?."

Mama Atika ta ce, "ki ji wata magana, ni ba uwa ce a wajen ku ba kenan ko Safeera?." Safeera ta É—aga kai ta kalle ta Mama Atika.

Mama Atika ta ce, "kalle ni da kyau, ni ba uwa bace da baza su iya zama a wajena su ci abinci kafin ki dawo ba? Kina tunanin akwai abinda bazan iya yi muku ke da ƙannen ki ba?."

"A'a Mama, kar a É—ora miki nauyi ne shiyasa."

"Babu batun nauyi, yadda Kausar take ƴa a wajena haka kuma ku ke gabaɗayan ku. Babu yadda ban yi da babar ku ba amma ta ƙi ji tace sai ta tafi, ni daman ku nake ji ba wani abun ba. Mahaifin ku yana yin tafiya wani lokacin, in ya tafi da wa zai bar ku?. Wanna dalilin ya saka na ce tunda ita bata yi wannan tunanin ba ni nayi, duk abinda ya samu kizo ki faɗa min, in tafiyar ta kama Baban ku, sai ku taho wajena mu zauna. Danginta ba a garin nan suke ba balle ace ku je can, kinga ni kaɗai ku ke da ita."
Chapter 51 · 0% Book details