Sashe 65
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Safeera ta ce, "zan yi, zan je wajan Maman Kausar ta bani lambar Umman ta saudia sai na kira ta."
"Ko ke fa, Allah ya cigaba da bamu ikon jure jarabawar rayuwa."
"Amin Bestie. Ina Labiba kuwa?."
"Tunda na zo au É—aya na ganta, na fita na ganta ita da wata mata sun hau taxi."
"Lallai an samu duniya. Hanan tana nan itama tana cin karen ta babu babbaka, Mama kullum cikin saka mata albarka take yi."
"ke baki san gasa suke yi akan kawo kuÉ—i ba? In wannan ta kawo dubu goma yau, gobe sai wata ta san hanyar da ta bi ta samo ashirin. Gasa suke yi akan nemo kuÉ—i ba ta hanyar halak ba."
"Uwarsu ce ta É—ora su akan hakan ai, kuma ita wai gani take haka kawai mazan suke É—aukar kuÉ—i su basu."
Islaha ta taɓe baki ta ce, "Su suka sani dai, matsalar su ba tamu ba. Zainab fa? Tunda na tafi kun yi magana da ita kuwa? In na kira ta sai na ji wayar bata zuwa."
"Wallahi ba mu yi magana ba har yanzu, Brr Suraj dai mun haÉ—u mun gaisa."
"Don Allah ko za ki je ki duba min ita?."
"Shikenan, zan je in Allah ya yarda. Ya batun binciken ki akan gidan?."
"Shine na ce ki je ki ganar min ita ai, itace makamina."
"To shikenan, zamu yi magana in Allah ya yarda." Daga haka suka yi sallama suka kashe wayar.
  Lokacin da Baba ya dawo suka nuna masa duk abinda Maman Kausar ta yi.
Baba ya girgiza kai ya ce, "Safeera ƙawar babar nan ta ku hidimar da take yi ta yi yawa sosai, kar na hana ta ga kama bana yabawa da kulawarta gare ku, amma ta ɗora kanta nauyin ku wanda Allah bai ɗora mata ba."
"Wallahi nima haka na ce Baba, in na yi magana sai ta ce ai duk an zama É—aya."
Baba ya sauke nunfashi ya ce, "Allah ya saka mata da alkhairi."
"Amin Baba."
"Zan yi tafiya kwananan Safeera, ina ta tunanin inda zan bar ku. Gaskiya bazan bari ku zauna wajan Atika ba, hidimar zata yi mata yawa sosai."
Safeera ta ce, "Ka je ka dawo Baba, zamu zauna a wajan nata, in ya so kafin tafiya ta gaba sai a É—auki mataki."
Ya kalli Safeera ya ce, "wanne mataki kenan?."
Safeera ta sunkuyar da kai ta ce, "Baba kamar yadda Gwaggo ta ce, me zai hana baza ka auri Mamansu Kausar É—in ba kawai?."
Baba ya girgiza kai tana kallon ta ya ce, "ƙawar babar ki ce fa Safeera, kina ganin hakan ya dace?."
"Baba ko Unma tana nan dan ka aure ta ai ba damuwa bane, kuma ko da auren tsakanin ka da Umma ba laifi bane balle babu auren. Kawai in dai akwai hali ka aure ta ɗin Baba, ka ga baka da fargaba in zaka yi tafiya, sannan itama zata dawo ƙarƙashinka, babu batun hidimar ta ta yi yawa."
Baba ya sauke numfashi ya ce, "Shikenan Safeera, zan yi shawara akan hakan."
Ta gyaÉ—a kai ta ce, "To Baba, sai anjima" ta faÉ—a tana tashi ta fita ya bita da kallo yana tunanin mafita akan hakan.
   Hajiya Karima suna kan waya ita da Mama suna tattaunwa akan Islaha, Hajiya Karima ta ce, "Labiba ta ce min yarinya ta waye, har gidajen larabawa take shiga. Gidaje manya manya. Ke kin san yarinyar zata yi farin jini, ga kyau ga gashi."
Mama ta ce, "ai na san za a rina, na san karuwanci kawai zata je tana tafkawa a gidajen larabawa wallahi."
"To ki kwaɓi Saheer, babu shi babu ita koda zata dawo. Aure tsakaninsu a dakatar dashi babu batun yinsa. Baza mu zuba ido ya ɗauko mana ita a matsayin sirika ba, shine kaɗai namiji da ki ka mallaka, in ya kawo ta mun shiga uku."
"Har sai kin faÉ—a ma, ai yadda ta tafi É—in nan ta bar zuri'a ta har abada, daman ba so nake yi ba, zan amince ne saboda wani burina. To yanzu bazan amince ya auri ragowar larabawa ba wallahi."
"Hakan shine ya kamata. Kar ki bashi fuskar da zai ce zai aure ta wallahi, ki rufe ido ki ce in ya aure ta sai kin tsine masa. Ke da ina da yarinya mace ma ai da Saheer ya yi mata, matsalar da aka samu bani da ita. Yanzu ba abin na yi hanyar yaran ƙawaeye ba, yarinya ta zo ta ƙoshi ta zama ƴar iska."
Mama ta ce, "Bar ni dashi kawai Karima. Daman Iskaha ta ga babu Idon Saheer ba sai abinda Allah ya yi ba? Ni fa shiyasa na ji daɗi da ba a haɗa su gida ɗaya da Labiba ba, dan ɓata min yarinya zata yi wallahi."
"Tsaf zata lalata ta wallahi, kin ga yanzu kowa ya san inda dare ya yi masa. Ke Alhaji Musa ya faɗa min wai Maimuna ta ce ita so take ta dawo, na sheƙe da da dariya na ce waye ya faɗa mata borno a gabas take."
Mama ta ce, "Bata san ita da dawowa sai ta biya kuÉ—in nan cif ba, in ba haka ba ta wuce gidan yari."
"Bar ƴar wahala, ta ɗauka zuwan ai sauƙi ne dashi. Ina zuwa" ta faɗa tana kashe wayar.
A lokacin Saheer ya shigo, Mama ta bi sa da kallo ta ce, "yauwa zauna, ina neman ka daman."
Ya zauna ta ce, "kana da labarin abinda budurwar ka take aikatawa a Jeddah?."
Gabansa ya yanke ya faÉ—i, ya kalli Mama ya ce, "na me kenan?."
"Na iskanci mana, Labiba ta faÉ—a min gida gida take bi na larabawa dan ta tara kuÉ—i. Ka ga sai ka cire ta daga ranka, dan wallahi bazan bari ka auri ragowar wasu ba."
Saheer ya yi shiru ƙirjinsa yana bugawa sosai ya kasa cewa komai, dan bai san abinda zai cewa Mama ba, ya san duk abinda zai faɗa baza ta yarda ba, gwara ya yi shiru zai fi alkhairi.
Mama ta ce, "ka saka a ranka babu kai babu Islaha, wallahi baza ka aure ta ba ka ji na ce wallahi!."
Ya ɗago ya kalle ta jin ta rantse, suka haɗa ido ra ce, "Gwara tun wuri ka nemi wata, da in na faɗa maka na ce ƴar iska ce ai baka yarda, yanzu in ta dawo maka da cikin balarabe ai ka amince. Ka ji da kunnen ka, babu kai babu ita indai ina da rai da numfashi, zan ga da ni da ita waye ya fi mahimmaci a rayuwar ka!." Mama ta miƙe ta shiga ɗaki ta barsa da bugawar zuciya.........
Nana Haleema.
[7/8, 11:05 AM] KRBBK: RDB2P45
Nana Haleema.
_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L
••••••••
Islaha tana kashe wayar Saheer ya kira ta, ta yi murmushi sannan ta É—auka ta ce, "yanzu nake shirin sake kiran ka Hamma."
Ya yi murmushi ya ce, "gashi nima na kira ki."
"Muna ta waya da Safeera ne. Ka san me ta ce?."
Saheer ya ce, "sai kin faÉ—a."
"Wai na yi creating content na dinga yi daga nan, saboda kar a manta da fuska ana ta, yan social media suna ta tambayar inda nake. Shine na ce mata Hamma ya faÉ—a min."
Saheer ya ce, "Hakan shawara ce mai kyau, zai saka kowa ya san kina nan kuma zaki dawo in sha Allah."
Islaha ta yi murnushin jin daɗi da farin ciki, Hamma yana bata goyan baya a duk wani abu na cigaba rayuwar ta, yana ƙara mata ƙarfin guiwa yi ko da bata so. Koda ta sare yana ƙarfafa mata guiwa har ta ji zata iya, ko da zata yi sanyi yana sakawa ta ji zata iya.
A sanyaye ya ce, "Shine na ce mata sai na tambaye ka, in ka bar ni sai na yi."
Ya yi Æ´ar dariya ya ce, "Ki yi Islaha. Ki samu topics masu kyau ki dinga tattaunawa a kai, hakan zai taimakawa aikin ki harda gidan tv ku."
"To Hamma, zan yi tunani in sha Allah."
"Allah ya taimaka."
"Amin Hamma. Na gode da bayan goyan bayan ka, ko yaushe kana riƙo da hannuna ka kaini inda nake son zuwa."
Ya murmusa yana sauke ajiyar zuciya sai ta ce, "ka san me? Na fara tara kuÉ—in nan fa."
"Har nawa ki ka samu?."
"riyal dubu bakwai, in ka yi converting kuÉ—in zuwa naira sun kai miliyan biyu da É—ari shida a yanzu."
Saheer ya ce, "a ina ki ka same su? Ko albashin na ki ne?."
"A'a ba albashi bane. Kasan akwai gidan da nake zuwa ina ɗan dafa musu tea na dawo, can ba zama nake yi ba, ina dai zuwa na ɗan yi na dawp asalin inda nake. Shine....shine matar gidan ta bani kuɗin" Ta samu kanta da ɓoye masa asalin wanda ya bata kuɗin.
Ya É—an yi shiru yana nazari, maganar Mama tana sake yi masa yawo a kansa, yana tuna yadda Mama tace tana yawo a gidanjen larabawa, amma bai bari tayi tasiri ba ya ce, "har gida nawa ki ke zuwa?."
Ta ce, "nan ne fa kawai, shima kawai tea nake dafawa na fito. Matar gidan tana da kirki sosai, shiyasa ta yi min kyauta."
Saheer ya É—an kausasa murya ya ce, "Islaha!."
Jin yadda ya kira ta sai ganbanta ya faÉ—i sosai ta ce, "Na'am Hamma."
"Kin san ba son aikin nan nake yi ba ko?."
"Na sani Hamma."
"Na yarda kina zaune ne dan babu yadda zan yi, kuma tun farko ban san da maganar ba, da baza ki je ba."
"na sani Hamma."