← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 133

Sashe 130

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kalli Baffa jin abinda ya ce, muryar ta a shaƙe ta ce, "ka shiga kawai Baffa."

Baffa ya murmusa ya ce, "ki shiga, Safeera ki raka ta." Safeera ta riƙe hannunta suka shiga ciki.

Suna shiga ta hange shi a kwance yana bacci, hawaye ya cigaba da ambaliyya daga idanunta, ganin yadda masoyinta ya canja kamar ba shi ba.

Ta ƙarasa gaban gadon tana kallonsa, an saka masa ruwa yana shiga jijiyoyin jikinsa, kayan jikinsa duk sun lalace, fuskarsa ta yi duhu sosai, ga goshinsa an ɗaure da bandage, fatar jikinsa duk ta yi wasu ƙananun baƙaƙen ƙuraje.

Islaha ta miƙa hannu da niyar dafa kansa Safeera ta riƙe hannunta, duk da ba saba taɓa shi ta yi ba, amma yanayin da ta gan shi a ciki ne ya saka take so ta dafa kansa. Ta juya suka haɗa ido Safeera ta girgiza mata kai alamun kar ta taɓa shi. Bata fahimci dalilin Safeera na hanata taɓa shi ba, sai ta janye hannunta suka fito a sanyaye.

Ko da suka fito bata daina kuka ba, Safeera bata ce mata komai ba, sai da ta gama kukan son ranta sannan ta kalli Safeera ta ce, "meye dalilin da ya saka ki ka riƙe hannuna da zai taɓa Hamma?."

Safeera ta ce, "saboda ke matar wani ce, taɓa wanda ba muharramin ba babban zunubi ne da ba ki san girmansa ba."

Islaha ta yi sak tana kallon Safeera da ta kashe mata baki, ta kasa magana sai kallonta take yi, ta rasa wanne irin zagi zata yiwa Safeera da zata fahimci kuskurenta a cikin kalamanta.

Islaha ta ce, "Ina ma na iya zagi, ina ma na iya zagin maguzawa, zagin Æ´an iska, zagin karuwai, wallahi da sai na zage ki tas!......"

Ta nuna ta da yatsa ta ce, "Daman akan auren nan ki ka hana ni?."

Safeera ta ce, "Laifi ne hakan, ke ba matar auren ba ce?."

"Safeera meyasa ki ka yi min haka, ɓeyasa ki ka fara canja min tun yanzu?. Ni na ɗauka saboda haramcin hakan ki ka hana ni, ashe akan wancan banzan auren da ban ɗauke sa a matsayin aure ba ki ka hana ni taɓa Hamma?."

Ganin ta fara fusata tana masifa a cikin mutane sai Safeera ta tausasa murya ta ce,  "Aure ya wuce ace masa banza aure, ki daina faɗa, sunna annabi ne ba a zaginsa. Kuma akwai haramci a ciki taɓa shi, ko babu aure a kan ki taɓa Saheer haram ne balle ke matar aure....."

Hannu Islaha ta ɗaga kamar zata mare ta, sai Safeera ta yi shiru dan ta san a fusatar Islaha tsaf zata mare ta akan kalamanta. Islaha ta nuna ta da yatsa ta ce, "Na rantse da Allah in ki ka ƙarasa sai na gaggaura miki da mari." Safeera ta yi murmushi bata ce mata komai ba.

Baffa ne ya ƙaraso wajan da suke tsaye, hakan ya hana Islaha magana.

Ya kalli Islaha ya ce, "Islaha."

Ta ɗaga kai ta kalle shi tana jiran ta ji me zai ce, a daidai lokacin Adda ta ƙaraso wajan ta tsaya a kusa da Baffa.

Baffa ya ce, "Yauwa ga Yayarki nan, ku je ta ta ya ki abubuwan da ya kamata ki yi, kafin gobe ki tare a gidan mijin ki."

Wani irin abu ya soki Islaha a zuciyarta, ta runtse ido da ƙarfi tana jin yaji yana tasowa daga zuciyarta yana mamaye idanunta. Saboda zafin yajin har ruwa idonta ya tara, ta rasa inda zata saka kanta saboda baƙin ciki. Ga shi bata iya yiwa Baffa musu balle ta ce bazata je ba.

Adda ta kalli Baffa ta ce, "Baffa wai sai da aka yi auren nan, yanzu me za a faÉ—awa Saheer?."

Baffa ya kalle ta ya ce, "wannan duk zai biyo baya, ya kamata ku fara shirin da ya kamata."

Islaha ta kalli Baffa tana hawaye ta ce, "Baffa don Allah ka bari zuwa anjima sai mu tafi, tunda ka ga sai gobe ne tafiyar ba yau ba."

Baffa ya murmusa yana kallon ta, yana karanto rauni da soyayyar Saheer a idanunta. Shi kuma wannan dalilin ne ya saka yake so ya nisanta ta a Saheer dan ita yanzu matar wani ce, zama inda Saheer yake bai kamace ta ba. In ya bar su tare za a tafka saɓon Allah, ko iya magana ta yi da Saheer da fuskar masoya babban zunubi ne.

Baffa ya ce, "ku je Islaha, har shida na yamma ta yi. Ku tafi kawai." Babu yadda zata yi da Baffa, ta miƙe a sanyaye Safeea ma ta miƙe suka fito tare da Adda.

Ray tunda aka ɗaura aurensa ya daina walwala, yana sakewa ne kawai zaboda Jazy zai ji babu daɗi in yana ƙin sakewa a bikinsa, amma gabaɗaya komai ya tsaya masa ba ya jin daɗin komai. Yana zaune a falo ya canja kaya zuwa na shan iska, hannunsa riƙe da mug na tea yana sipping a hankali.

Jazy ya shigo yana hararsa ya ce, "Mamy tana ta neman ka, É—an family picture É—in nan na biki baka tsaya an yi ba. Haba Ray, baka kyautawa Riyya ba, gabaÉ—aya bata ji daÉ—in haka ba."

Bai ce masa komai ba ya dai kalle sa kafin ya É—auke kai. Jazy ya zauna bayan ya cire babbar rigar jikinsa, ya É—auki wayar sa yana dannawa sannan ya ce, "media gabaÉ—aya a kan ka take magana yau, hotunan ka kamar ruwa. Amma na yi mamaki da maganar auren ka bai fita ba."

Ya juyo ya kalle sa ya ce, "ka daina cewa aurena, please."

Ya yi murmushi ya ce, "Ray she is your wife, auren contract ne ko akasin wannan kai ta dama ba mu ba."

Bai ce masa komai ba ya kuma yi masa shiru dan bai san me zai ce ba. Jazy ya kalli agogo ya ce, "ƙarfe nawa zamu tafi dinner party?."

Ray ya buɗe baki zai yi magana Jazy ya ce, "wallahi bazan karɓi uzurin ka ce min baza ka je ba, gwara ma na faɗa maka tun kafin ka furta. Kar ka wahalar da bakin ka ka ce min baza ka je ba."

Sai ya fasa faɗar abinda zai faɗa ya ajjiye kofin hannunsa ya miƙe ya shiga bedroom.

Bayan sallar magrib Jazy ya shirya cikin ash men lace, yana saka agogo a hannunsa ya shiga É—akin Ray ya same sa sanye da bathrobe ko kaya bai saka ba.

Ya bi shi da ya ce, "kasan akwai pictures before event ko?."

Ya yi tsaki ya ce, "kai wa da me zan ji ne? Ka ce sai na je, kuma ka ce min photoshoot?."

Jazy baice komai ba sai danna waya da yake yi, ya kira Riyya ya saka a speaker ya ce, "Riyya É—an uwanki ya ce ba zai yi attending event É—in ki ba, ki yi masa magana yana jin ki."

Riyya ta ce, "Ray please, tunda ba ka tsaya an yi pictures É—azu ba yanzu ka zo mu yi, ka ji?."

Jin muryarta kamar zata yi masa kuka sai ya ce, "Riyya zan je event É—in, meye wani pics brfore event?."

"Please!."

"Okay, i will be there"

"Thank you. I love you."

"I love you" ya furta yana kallon Jazykafin Jazy ya kashe wayar.

Ray ya yi ajiyar zuciya yana kallon Jazy da ya yi kyau cikin shigarsa ta angwaye. Kafin ya yi magana Jazy ya ce, "ka shirya mu je." Bai ce komai ba ya É—auke kansa sai wayarsa da ya É—auka jin ana kiransa.

Jazy ya ƙwace wayar bai bari ya ɗauka ba ya ce, "in ka fara waya akan business sai a tashi daga event ɗin ba ka gama ba. Don Allah ka tashi ka shirya."

Nan ma bai ce masa komai ba Jazy ya ce, "Abba ya ce na tura a É—auki Islaha ta je event É—in, ni kuma na manta."

Sai lokacin ya ce, "wace?."

Ya wani kalle sa ya ce, "É—an rainin hankali, da ina yi maka magana ka yi banza amma ina ambato sunanta ka yi magana."

"Ita wa?."

"ba ka san ta ba?."

Ta girgiza kai alamun bai santa ba yana miƙewa tsaye.

Jazy ya ce, "matarka nake nufi." Ya dakata daga kwance igiyar bathrobe É—un da yake niyar yi yana kallonsa, sai kuma ya ce, "point of correction, contract wife za ka ce, ba matata ba."

"Kai ka san wannan, ni a matarka nake kallon ta."

"As who will she go to the event?."

"Amaryar Ray."

Bai ce komai ya ƙarasa yana kallon kayan da zai saka.

Jazy ya ce, "ni fa murna nake da auren nan, ko babu komai Alma zata ƙyale ka." Ray ya sake yi masa shiru, sai da ambaci Alma ya tuna masa kwana biyu ko kiransa bata yi, yadda take damunsa da waya da texts yanzu duk bata yi.

Bai ce komai ba ya shirya cikin men lace amma na sa brown colour.

Jazy ya kalle shi bayan ya gama ya ce, "ka yi kyau fa." Bai ce masa komai ba wrist watch yake É—aurawa sannan ya saka takalmi.

A hankali ya É—ago yana yatsine fuska ya ce, "cikina."

Jazy ya buÉ—e ido waje ya ce, "ciwo yake yi maka?."

Ya É—an girgiz kai ya ce, "ina jin alamun ciwon."

Jazy ya ce, "don Allah ka taimaka mana kar ciwon cikin nan ya tashi, in ya tashi a wannan lokacin ai mun shiga uku." Bai ce komai ba ya ƙarasa shiryawa suka fito tare, suka hau mota suka tafi ayi hotunan kafin event.

Mama tana tsaye ta shirya cikin lace mai kyau, fuskar ta ta sha makeup kamar ba ita ba. A kan idanunta motar Mamy ta fita zuwa wajan event É—in.

Ta girgiza kai ta ce, "an dai ɗaura aure, wannan aure shine target ɗina na ganin bayan Rehaan. Wallahi indai ina da rai sai na ga bayan Rehaan, wallahi sai na kai shi ƙasa."

"Mama" Sameer ya faÉ—a yana shigowa.

Ta juya tana kallonsa ya ce, "Za mu tafi tare ne?."

Ta É—aga kai ta ce, "mu je mu tafi tare kawai." Tare suka fito suka shiga mota zuwa wajan event É—in.
[7/31, 11:42 AM] KRBBK: RDB2P99
Nana Haleema..
Chapter 130 · 0% Book details