Sashe 91
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yadda ya so yakice takaicin Islaha daga idanunsa amma sai ya kasa. Shi mutum ne da yi rayuwa a cikin turawa, lokacin da yana makaranta suna sha ganin mace da namiji suna abinda suke so, ya gani sau babu adadi musamman a school, amma bai taɓa jin takaici akan hakan ba, bai taɓa jin ya tsani wanda ya aikata ba, bai taɓa jin haushi ko zafin abin ba.
Amma yanzu kam ya ji takaici da baƙin ciki wanda bai taɓa ji ba tunda ya zo duniya. Shi kansa tunani yake yi, meyasa ya damu da ita har haka? Amsar itace; bai sani ba, amma yana tunanin dan ta kasance bafulata kamar sa ne, shiyasa yake jin haka.
  Islaha kuwa ta ɗan ji sauƙi babu laifi, a haka ta yi bacci sanin ba sallah zata yi ba ta sa ki jiki ta yi baccinta, dan Sunaira da ta ga bata da lafiya bata takuta mata ba kuma daman masu gidan basa nan.
Cikin bacci ta ji ana kiran sunanta, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda ta ji maganar, da hanzari ta miƙe ganin Labiba a durƙushe a gabanta.
Da mamaki mai yawa Islaha take bin Labiba da kallo ta ce, "Labiba!."
Labiba ta kifa kanta a kan gado, cikin ciwo da tsananin azaba ta ce, "Islaha, ki taimaka min mu je asibiti, taimaka min ki raka ni don Allah. Zan mutu, zan mutu Islaha!."
Hankalin Islaha ya tashi, tsoro da firgici suka shige ta, ta riƙe Labiba ta ce, "meyasa same ki? Me ki ke ji?."
"Marata! Ki taimaka min zan mutu."
Ta diro daga kan gadon, ta shiga baÉ—aki ta wanke baki a gaggauce ta fito ta saka hijjab.
Ta kalli Labiba ta ce, "za ki iya tashi?." Labiba ta É—aga mata kai kawai, dan ita kaÉ—ai ta san azabar da take ji.
A haka suka fita Islaha ta tsayar taxi ta ce a kai su asibiti ma fi kusa. Labiba tana jikin Islaha tana ta yi mata sannu, sai shafa fuskarta take yi ganin yadda take gumi kamar wacce zata haihu.
Nana HaleemaâœðŸ»â¤ï¸
[7/19, 10:59 AM] KRBBK: RDB2P66
Nana Haleema.
Islaha jin abu mai ɗumi yana taɓa ƙafarta ya saka ta kalli ƙafarta, ganin jini ya saka gabanta ya faɗi, sai take tunanin wanne irin jini ne wannan a jikinta? Ita ba mai haihuwa ba mai zai saka ta ga wannan jinin?."
A lokacin suka iso asibitin, da hanzari aka zo aka shiga da Labiba ganin yadda jini yake zuba a jikinta duk ya ɓata Islaha.
Sai bayan an shiga da Labiba, a lokacin Islaha ta bi jikin Labiba da kallo, ta duba jikinta ta ga ba daga jikinta jinin ya zo ba, daga jikin Labiba ne. Ta kalli kayanta duk hijjab ɗin ya ɓaci, ta biya mai taxi ta shiga ciki da sauri.
Bata ga inda suka shiga da Labiba ba, ta zauna a reception ta dafe kai tana tunanin abinda yake damun Labiba har haka. Ta sake kallon jinin, ta ga yadda ya ɓata, ta yi tsaki ta rasa me zata yi.
Sai ta miƙe ta ƙarasa reception ta tambayi inda zata ga Labiba aka faɗa mata tana emergency. Aka tambayi details ɗinta a wajan Islaha ta faɗa sannam ta wuce can.
A tsaye ta tsaya tana kai kawo cikin rashin sanin abinda yake faruwa, sai da likita ya fito ta ƙarasa wajan sa ta ce, "me yake damunta Dr?."
Zuwa lokacin har an turawa Dr details É—in Labiba, dan haka ya kalle ta ya ce, "Labiba?."
Ta É—aga kai alamun eh, Dr ya ce, "she had miscarrige!."
Wani irin bugawa ƙirjin Islaha ta yi, ta maimaita kalmar miscarriage a ranta, tana tunanin meye ma take nufi, dan kanta ya manta meye ma kalmar misscarrige take nufi.
Dr ya ce, "ta samu bacci yanzu, za ki iya zuwa wajan ta" ya faɗa yana nuna nata ɗakin.
Har ya ɓace Islaha ta kasa motsin kirki, sai daga baya ta shiga a sanyaye tana ji kamar ta yi kuka saboda yadda take ji zuciyarta tana bugawa.
Ta tsaya tana kallon Labiba tana tuna kalmar ɓarin ciki da aka faɗa mata, har an canja mata kaya zuwa uniform na asibitin, tana kwance tana bacci an saka mata ruwa.
Islaha ta zauna a gefenta tana kallon ta cikin wani irin yanayi na bugawar zuciya. Sai maimaita kalmar take a ranta, ta rasa wanne irin tunani ya kamata ace ta yi.
Sai bayan azahar Labiba ta farka, suka haÉ—a ido da Islaha da take zaune ta yi tagumi tana kallonta, amma ta cire hijjab É—in ta ajjiye a gefe.
Islaha ta ce, "Sannu."
Labiba ta É—aga kai ta ce, "me ya same ni?."
Islaha kai tsaye ta ce, "kin samu miscarrige ne."
Labiba ta kasa É—auke ido daga kan Islaha jin abinda ta ce, sai kuma ta sunkuyar da kai tana jin kunya ina ma bata kira Islaha É—in ba, ina ma ita kaÉ—ai ta zo da Islaha bata san sirrinta ba.
A lokacin nurse ta shigo, aka tafi da Labiba É—akin scanning, Islaha dai tana zaune a É—akin bata je ko ina ba.
Gajiya ta yi da zaman, ta miƙe tana kallon abayar jikinta, sai ta shiga banɗaki ta wanke inda jinin ya ɓata, tana yi tana mita ta ce, "Aikin banza, ni ba yin ciki ba ni da wanke jinin shege. Allah ka kiyaye mu, ka cigaba ba mu kariya gaba da baya."
A haka ta ɗan wanke, sai kuma ta ga rigar ta jiƙe da yawa, kawai sai ta ɗauki uniform na asibitin ta saka, ta shanya rigar a kan ƙofar banɗakin, ta fito ta hau kan gadon da niyar in Labiba ta dawo zata tashi.
Tunani take akan lamarin Labiba, tana mamakin ciki, kuma a ƙasar Saudia aka same shi, kuma yadda Labiban ta sunkuyar da kai ya bata tabbacin ta san da cikin, ta girgiza kai tana jin babu daɗi a ranta. Bata taɓa ganin wacce ta samu ciki ba ta hanyar aure ba ido da ido sai Labiba, shiyasa abin yake ɗaure mata kai sosai.
A lokacin aka buɗe ƙofar ɗakin, ta juya ta kalli wanda ya shigo dan a tunaninta su Labiba ne, bata gane waye ba dan scrub ne a jikinsa irin na likitoci, sannan ga hular tiyata ga face mask.
Kafin Islaha ta yi magana an juya an fita daga ɗakin an rufe ɗakin, sai ta taɓe baki ta koma ta yi kwanciyar ta, dan gaskiya bazata tashi ba sai Labiba ta dawo.
Rehaan da ya yi mistake É—in É—aki ya tsaya bayan ya fita ya yi shiru, ya tafi tunani yana girgiza kai, yana sake tambayar kansa kamar yarinyar can ya gani, yarinyar da ya taimaka mata a train. Sai zuciyasa take faÉ—a masa me ya same ta har haka? Ko ciwon train É—in ne har yanzu bai bar ta ba?.
Ya shiga office yana cire hular kansa ya zauna yana tunanin da bai san dalili ba. Ya kalli landline yana tunanin ya tambayi reception amma yana tunanin ina ruwansa? In ma itace ina ruwansa da zai damu?.
Ya sauke numfashi, ya girgiza kai yana so ya kawar da ita daga ransa amma sai ya kasa, ya tallafi haɓa yana tunani, sai kuma ya yi tsaki ya ɗauki wayar ya kira reception.
Daman sun san daga inda kiran yake, suna É—auka ya ce, "what happened to the patient in room 202 of the emergency ward?"
"Wait a minute."
Ya yi shuru yana ji ana danna computer sannan aka ce, "She had a miscarriage Sir, She was three weeks pregnant... and she took the wrong medication without knowing it was harmful to her condition."
Rehaan ya ji wani irin dummm a tsskiyar kansa, ya runtse ya furzar da iska, ya haÉ—É—iye yawu don son tabbatarwa ya ce, "Are you sure it's the patient in room 202 who had the miscarriage?."
"Yes Sir. There is no mistake, her name is Maddibo Mu....."
Rehaan kafin ta kai ƙarshe ya dakatar da ita ya ce, "is okay, thnak you."
Ya ajjiye wayar yana tuna sunan Islaha Muhammd Maddibo, ya shafa kansa yana ji kamar wutar tsanar ta ake hura masa a zuciyarsa.
Kenan condition É—in da ta shiga a train ciki ne? Ya É—aga kai sama yana jin wani irin yanayi, kuma ya tuna abinda Ubaid ya tura masa.
A bayyane ya ce, "Oh Allah! Meyasa nake haɗuwa da yarinyar nan ne? Meyasa ƙaddara take haɗa mu da ita ko yaushe?" Ya faɗa yana dukan table, yana ji ina ma bai taɓa saninta a duniyarsa ba.
"Kuma cikin Ubaid ne!."
Ya rufe ido ya buÉ—e, sai ya sauke numfashi ya ce, "bazan sake ganin ta ba daga yau, in sha Allah!" Ya faÉ—a yana jan numfashi, sai kuma ya É—auki kayansa ya fita daga asibitin.
Labiba ta kasa yiwa Islaha magana itama bata ce komai ba, sai dare sannan aka aka yi discharging É—insu Labiba da kanta ta biya duk wani bill.
A taxi suna tafiya Labiba ta kalli Islaha ta ce, "Don Allah kar ki faÉ—awa kowa wannan maganar, tsautsayi ne, kuma baza a sake ba."
Islaha ta wani kalle ta ta ce, "ina ruwana Labiba? Lokacin da ki ka yi na sani, In ba dan neman taimakona da ki ka yi a lokacin ba kin taɓa nema ne?. Nima saboda zuciyar musulunci ya saka na kalle ki, kuma ina kallon ki a matsayin ƙanwar Hamma.
Labiba bata ce komai ba, itama ta share ta suna zuwa ta fita daga motar bata sake kallon ta ba.
Haka Islaha ta kwana da wannan tunanin, da ta motaa abin take tunawa tana ganinsa kamar a mafarki. Da safe bayan sun gama komai ta nufi gidan Rehaan dan yin aiki, da kuma sake yi masa godiya akan abinda ya yi mata.
Tana shiga ta ji falon shiru babu kowa, lokacin sallar azahar ne ta tabbatar bacci yake yi. Ta dafa tea ta ajjiye, tana zaune ita kaÉ—ai har aka yi sallar la'asar.
Da yake ba sallar zata yi ba bata tashi, tana zaune a kitchen tana danna waya ta ji an shigo falon. Ta ɗago kai, sai kuma miƙe a sanyaye ta fito tana fitowa falon suka haɗa ido.