← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 133

Sashe 82

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta ce, "Baffa kana da dama da ikon yanke ko wanne hukunci a kaina, ba sai ka tambaye ni ba, kawai ka yanke min hukunci a matsayin ka na uba a gare ni."

"Na sani Islaha, na san na isa dake gaba da baya. Amma hakan bazai saka na tauye ki ba, dan kina yi min biyayya hakan bazai saka na cutar da rayuwar ki ba. Ki faÉ—a min ra'ayin ki, kina so a É—aura auren yanzu ko sai kin dawo?."

"Baffa wallahi na ba ka zaɓi, ka zaɓa min abinda ka ga ya yi daidai dani."

Baffa ya yi murmushi mai sauti, ya ce, "baza ki zaɓa ɗin ba ko?."

Islaha kamar tana kusa dashi, ta sake sunkuyar kai ta ce, "Baffa ka zaɓa min kawai, na san baza ka yi min abinda zai cutar dani ba."

Baffa ya yi murmushi cikin jin daÉ—i da farin ciki ta ce, "Shikenan Islaha. In Allah ya nuna mana jibi juma'a, bayan sallar juma'a za a É—aura auren ki da Saheer. Hakan ya yi miki?."

Gabanta ya faɗi, ta runtse ido ta ce, "Ya yi Baffa. Allah ya nuna mana, Allah ya ƙara maka lafiya da tsahon rai mai amfani."

"Amin Islaha. Allah ya yi miki albarka, ya cigaba da ba ki kariya a duk inda ki ke." Ta amsa da amin kafin su kashe wayar.

Baffa yana kashe wayar ya kalli Saheer da yake kusa dashi, ya yi murmushin jin daÉ—i ya ce, "Yarinya mai tarbiyya, ina ji a raina ina Islaha Æ´ata ce, ina ma ni ne na haife ta."

Saheer ya murmusa yana ji kamar ya miƙe ya taka rawa saboda murna, ji yake kamar ya jawo jibi ta zo Islaha ta zama mallakinsa.

Baffa ya ce, "gobe zan aika ka a siyo goro da alewa na É—aurin aure, jibi babu abinda zai saka a dakata daga É—aura muku aure in sha Allah."

Ya yi murmushin jin daÉ—i da farin ciki ya ce, "Allah ya kaimu Baffa."

Baffa ya ce, "Amin. Ka je ka sanar da waɗanda zaka sanar, dan lokacin ya ƙure ba sai an yi gayya gagaruma ba, in bikin ya zo sai a yi taro."

Cikin zumuɗi ya miƙe, yana ji kamar ya rungume Baffa dan daɗi da farin ciki. Saheer yana fitowa suka haɗu da Mama a tsaye da alama ta ji komai. Ya sunkuyar da kai ita kuma ta ce, "biyo ni."

Ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, ya bita a sanyaye zuwa falon ta. Suna shiga ta juyo ta kalle sa ta ce, "Ban amince da auren Islaha ba, ban amince ka aure ta ba Saheer. Ka je ka samu mahaifinka, ka faɗa masa baza ka aure ta ba."

Ya buÉ—e ba ki zai yi magana ta ce, "Wallahi in ka amince da auren nan sai na tsine maka, ka ji na ce wallahi, babu abinda zai saka na dakata dafa tsine maka albarka Saheer, in kana ganin bazan iya ba ka aikata Saheer!."

Saheer ya zare ido yana kallon Mama jin abinda take faɗa, ya haɗɗiye yawu daƙyar, yana ji idanunsa suna cikowa da ruwa, ya buɗe baki zai yi magana ta ce, "kar ka ce min komai, ikon da nake dashi a kanka nake so na gani. In har kana jin tsoron bakin uwa kar ka amince, in kuma baka jin tsoro tsinuwata ka aure ta ka ji!" Tana gama faɗar hakan ta shiga ɗaki.

Saheer ya bi ta da kallo, yana ji zuciyarsa tana girgiɗi kamar zata faɗo daga ƙirjinsa, ya sauke numfashi mai tsaho, yana ji kamar wuta ce a kusa dashi saboda tiririn sa yake ji, ya ja ƙafarsa daƙyar ya fita daga falon, yana ji kamar ya yi kuka.....

Ga ƙoshi, ga kwanan yunwa😩🤭🤣
[7/16, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P59
Nana Haleema.

Saheer a sanyaye ya fita ƙofar gida, ya tarar da Sadik a zaune a mota yana jiransa, ya shiga motar yana jan numfashi mai tsaho. Sadik bai kula da yanayin da yake ciki ba ya ce, "An kawo kaya, zamu tura zuwa inda ya kamata. Ka ga list ɗin mutanen da...." Maganar Sadik ta maƙale ganin ko kallonsa ma ba ya yi.

Sadik ya ce, "Yane?."

"Akan maganar É—aurin auren nan ne."

"Ba ka son auren nata ne kuma ko meye?."

Ya kalle sa ya ce, "a duniya akwai mai son auren Islaha in ba ni ba?."

Sadik ya ce, "to meye na damuwa akan hakan?."

Ya sauke numfashi ya ce, "Islaha ta amince auren....."

Sadik ya tari numfashinsa, bai bari ya ƙarasa ba ya ce, "daman ya za a yi ta ƙi amincewa? Ai dole ma ta amince da auren, tunda ta gama...."

Cikin tsawa ya ce, "ya ishe ka malam!."

Sadik ya murmusa ya ce, "to na yi shiru, ina ji."

Ya yi masa banza ya ƙi magana, Sadik ya yi dariya ya ce, "ina da abin yi, in baza ka faɗa ba na kama gabana."

Saheer ya sauke numfashi ya ce, "Baffa ya ce jibi za a É—aura aurena da ita, Mama kuma ta ce indai aka É—aura auren sai ta tsine min."

Sadik ya zaro ido cikin kiÉ—ima da mamaki ya ce, "kai! Abin har ya kai ga haka?."

Saheer bai ce komai ba sai lumshe ido da ya yi ya buÉ—e sannan ya ce, "ban sani ba, ban san me zan yi ba yanzu."

Sadik ya ce, "Haƙura za a yi zuwa lokacin da zata janye kalamanta, ai ba a yi auren ka Islaha tana wannan fushin ba, ga furucin da ta yi a kan ka, dole sai mun jira ta janye sai a san abinda ya kamata ayi."

Saheer ya É—an É—aga kai ya ce, "Sai abinda Baffa ya ce, ni wallahi kam kaina ya kulle."

Sadik ya ce, "Dole kan ka ya kulle, kana son Islaha, ga damar aurenta ka samu, amma Mama ta hana. Sai haƙuri, ka cigaba da addu'a kawai."

Saheer ya yi shiru yana kallon ƙasa, ya rufe ido ya buɗe zuciyarsa tana bugawa da sauri sauri. Ya kalli Sadik ya ce, "Ina son Islaha Sadik, rasata daidai yake da rasa rayuwata gabaɗaya."

Sadik ya ce, "Haka zalika Mama mahaifiyarka ce, tsinuwar ta daidai yake da tarwatsewar rayuwar ka."

"Na sani, ba ina nufin na zaɓi Islaha akan Mama ba, kawai dai ina faɗa maka yadda nake sonta, in na rasata ban san wanne hali zan shiga ba."

Sadik ya taɓe baki, dan shi gabaɗaya Islaha ta sire masa, da abokinsa zai yarda ma da ya ce masa ya nemi wata wallahi. Bai yarda da ita ba, akwai abubuwan da take ɓoyewa, kuma tana da ɓoyayyiyar ɗabi'a wacce bata so a san da ita.

Saheer bai kuma cewa komai ba ya fita, Sadik ya yi murmushi ya ɗauki waya yana dannawa yana jin daɗi, a bayyane ya ce, "Auren babu lallai ya yu, ni daman na fi son haka wallahi, dan zaman sa da Islaha ƴar ƙaramar matsala" yana gama faɗar hakan ya ajjiye wayarsa ya ja mota ya tafi.

                •••••••

Islaha tunda Baffa ya kashe wayar take jingine da gado cikin sanyin jiki, a kasa motsawa saboda rashin ƙarfin jikinta. Ta kasa yarda jibi juma'a za a ɗaura mata aure, ta kasa amincewa igiyar auren Hamma har guda uku zasu hau kanta nan da wasu awanni masu zuwa. Bawai bata son Hamma bane, tana sonsa so na tsakani da Allah, kawai bata shirya aurensa a lokacin bane, ta fi so sai ta gama abubuwan da suke gabanta, sai auren ya biyo baya.

Ta zame ta kwanta a wajan tana tunani, tana so ta faÉ—awa Safeera amma sai ta ji baza ta iya ba, ta yi shiru cikin tunanin da bata san dalilinsa ba. Ta yi tunanin Saheer zai kira ta, amma sai ta ji shiru, hakan ya yi mata daÉ—i sai ta ji bata so ma ya kira wayar ta

Sai dare mutanen gidan suka dawo, aka kira ta suka bata tsarabar doguwar riga baƙa mai kyau irin ta larabawa. Ta je ta ajjiye a ɗaki tana tunanin halin da Zainab take ciki, da kuma auren da Baffa zai ɗaura mata.

Washe gari bayan ta gama komai ta yi nufin zuwa gidan Rehaan, duk da bata so amma tana son samun kuɗi, tana ji a jikinta dole ta je ko dan kuɗin da take so ta haɗa ta bashi ta bar ƙasar da wuri. Ko dan saboda Zainab dole ta dage da neman kuɗi, dan hankalinta ya yi kan ta koma fa je ta ga halin da take ciki.

Tana typing code ɗin ƙofar ta buɗe, ta shiga a hankali da sallama. Babu kowa a a falon hakan ya saka ta wuce kitchen.

Sai da ta tsorata ganin Jazy a tsaye ya É—ora mai akan wuta zai soya irish.

Ya juyo suka haɗa ido ya ce, "Miss Islaha, ƙaraso mana."

Ta shigo a hankali ta kalle sa, kamar bazata yi magana ba sai ta ce, "ina yini."

Ya juyo ya kalle ta ya ce, "jiya sai ki ka ƙi zuwa, ina ta jiran zuwan ki."

Bata ce komai ba, ya miƙa serving spoon ɗin da yake juya dankalin dankalin ya ce, "za ki iya taimaka min?."

Ta gyaɗa kai ta karɓa, shi kuma ya ɗan matsa gefe ya ce, "na gode" ya faɗa ana fita daga kitchen ɗin.

Ta bi sa da kallo dan gabaɗaya ƙhamahinsa ya mamaye kitchen ɗin. A bayyane ta ce, "Ka rasa turaren dubu nawa suke siya, turare ya maƙale ko ina kamar yanzu aka saka" ta faɗa tana zuba dankalin a mai.

Man ya yi zafi sosai, hakan ya saka ya taso sama, ya yi hayaƙin da ya shiga hancinta kai tsaye ya sarƙe ta. Ta ɗan ja baya da sauri ta fara tari, ta ɗauka abin kaɗan ne tunda hayaƙin bai kai ya sarƙe ta haka ba, sai ta ji numfashinta yana neman tsayawa, ta miƙa hannu ta kashe wutar stove ɗin, ta fito ta zauna a falon tana jan numfashi da ƙarfi.

Ta sama Jazy ya hango ta ta fitoc ganin yadda numfashinta yake sauka sai ya sakko da sauri, ya ɗauki ruwa ya ƙarasa inda ta ke ya ce, "Sannu, ki nutsu."
Chapter 82 · 0% Book details