← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 133

Sashe 120

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ashe shine ya aiko shi wajena. Har yana faɗa min mahaifinsa ne yake son auren ba shi ba, shi bazai aure ni dan yana so ba, dan haka zai aure ni saboda mahaifinsa ya ce ya aure ni. Mtsw! Sai ka ce an faɗa masa nima aurensa zan yi, ko maza sun ƙare a duniya ba gwara na mutu babu aure ba, balle ina da Hammana."

Sadik ya ce, "Ba ki faÉ—a mana waye ba."

Ta É—an sake yin shiru kafin ta ce, "ba shi da wani mahimmaci, ku manta kawai. Mu caigaba da neman kuÉ—in fansar Hamma." Suka cigaba da tattaunawa akan yadda za a yi.

Islaha abu kaÉ—an sai ta yi tsaki saboda takaicin Rehaan, a haka suka gama zaman basu samo mafita ba, ta shiga gida Safeera ta tafi shima ya tafi gida.

Rehaan tunda ya shiga gidan da dangin babarsa suke yake jin kansa cikin Æ´anci da walwala. Dukkansu indiyawa ne, gabaÉ—aya basa jin wani yare in ba hindi ba sai english. Har gwara Yayar Mamy tana iya yin hausa kaÉ—an-kaÉ—an.

Suna ta hira gabaÉ—aya, sun hanashi motsi kowa yana bashi labari ana bashi tsarabar da aka kawo masa. Shi dai tana kusa da Mamy a zaune, sai Yayar Mamy a zaune a gefensa sun saka shi a tsakiya.

Yana murmuahi ya ce, "Fateema bata zo ba?."

Mamy ta ce, "Tana wajan aiki, ta ce aiki ya yi mata yawa, amma ta ce zata zo."

Ya É—an gyaÉ—a kai bai ce komai ba yana kallon su gabaÉ—ayansu. Yayar Mamy mai suna Sanah ta ce, "ga mu gabaÉ—aya mun haÉ—u, amma babu Sofia, ko tana da rai, ko bata da rai Allah ne ya sani."

Rehaan ya ce, "Mama wai meye silar barinta cikin ku? Ya aka yi ta ɓata har aka neme ta aka rasa?."

Wacce ya kira da Mama ta ce, "Tunda mahaifiyarka ta auri ɗan Nigeira kuma bafutalani take sha'awar auren irinsu. Gabaɗaya sai aka ƙi bata goyan baya kamar yadda aka bawa Mamy goyan bayan auren mahaifin ku...."

Ta É—an sauke nunfashi kaÉ—an ta ce, "Shine aka wayi gari ta bar gida, daga baya sai ta tura mana hotunan É—aurin aurenta da mijin. Amma ita mijin ta É—an Kano ne ba nan ba, mun nemi ta dawo bata dawo ba, kuma bata faÉ—a mana inda take ba. Tun muna samunta a waya har muka daina, mu neme ta ko ina bamu samu ba. Gashi bamu san mijinta da ahlinsa ba balle mu neme ta. Shekarun da yawa, dan ba a jima da haihuwar ka ba aka yi hakan.

Rehaan ya É—an yi shiru sannan ya ce, "in tana da rai za a ganta wani lokacin, in bata da rai kuma Allah ya nuna mana ahlinta in ta bari."

Ya riƙe hannun Mama da Mamy ya ce, "ku cigaba da addu'a, Allah zai bayyana ta."

Sanah ta shafa kansa ta ce, "Allah ya sa." Ya É—an yi murmushi kawai.

Sanah ta ce, "ashe da kai za a haÉ—a ayi auren."

Ya ɗan sauke kai ƙasa kafin ya ce, "Mama bana so kowa ya san da maganar nan, zan bi umarnin Abba ne ba dan ina so ba."

Sanah ta É—aga kai tana shafa kansa ta ce, "Allah ya cigaba da É—aukaka ka." Suka amsa da amin kafin ya yi musu sallama ya tafi bayan ya ci abinci.

Da daddare Baffa ya kira Islaha akan maganarsu, Islaha ta shiga da sallama ta zuna akan carpet.

Ya kalle ta ya ce, "Islaha mun yi magana ranar nan ba ki ce min komai ba, ni kuma ina jiran amsar ki na ke yi."

Islaha ta kalli Baffa ta ce, "Baffa wacce magana kenan?."

"Akan auren ki da É—an AbdulAziz Yola, ranar juma'a suke son É—aura auren."

Ta sunkuyar da kai ta ce, "Baffa don Allah ka daina faɗar maganar nan, in wani laifi na yi maka ka ke so ka aurar dani ga wanin Hamma don Allah ka yi haƙuri ka yafe min. Baffa in kuma shine ya yi maka laifi har ka ke so ka aurar ga waninsa don Allah ka yafe masa, amma ka daina faɗar maganar auren don Allah."

Baffa ya É—an yi shiru yana kallon ta sai ya yi sauke ajiyar zuciya ya ce, "Islaha Saheer ba ya nan, babu lallai ya dawo, ni a jikina nake jin Saheer ya tafi kenan, sai dai mu yi masa fatan Allah ya sa ya cika da imani."

Islaha ta É—ago kai ta kalli Baffa hawaye ya sakko daga idonta, ta girgiza kai ta ce, "Baffa Hamma bazai mutu ba, ka daina faÉ—a don Allah."

Baffa ya ce, "Islaha kalle ni."

Ta ɗago a hankali ta kalle sa sai ta sauke kai ƙasa saboda biyayya bata son kallon idanunsa.

Baffa ya ce, "A wanne matsayi ki ka É—auke ni a duniya?."

Muryar ta tana cracking ta ce, "a matsayin mahaifina, ban san waye ya haife ni ba, kai nake kallo a matsayin mahaifi wanda ya kawo ni duniya."

Baffa ya ji daɗin amsar ta sannan ya ce, "To ki yarda bazan yi miki zaɓi wanda zai cutar dake ba. Na fi kowa ƙaunar auren ki da Saheer, na fi kowa son ki auri Saheer saboda yadda nake son tarbiyyar ki, ina ƙwaɗayin ki amsa sunan ƴata kuma matar ɗana, in ƙwaɗayin na samu iri daga jinin ki. Islaha tunda ki ka ji na janye kalamaina akan auren, tunda ki ka ji na ce ga wani ba Saheer ba, kin san ina da hujja mai ƙarfi akan hakan. Ko kina ganin zan cuce ki ne?."

Ta girgiza kai tana hawaye, ta kasa magana sai hawayen da yake sakko mata, kalaman Baffa hr jininta take jinsu.

Baffa ya ce, "To ki saka a ranki ina guje miki faɗawa inda za ki sha wahala ne shiyasa na zaɓi wani na bar Saheer. A matsayina na uba a gare ki, bazan so na ga za ki faɗa wuta na ƙyale ki ba, duk yadda zan yi zan riƙe hannun ki na tabbatar kin wuce ba tare da wutar ta taɓa ki ba."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba tana goge hawaye ta kasa magana kwata-kwata.

Baffa ya ce, "Ki yi haƙuri, na san kina son Saheer, kuma kina burin mallakar Saheer a matsayin mijinki. Kuma na san abin zai zo miki bazata, amma nan gaba za ki gane abinda nake hango miki a yanzu. A yanzu bazan amince da auren ki da Saheer ba, ko da yana nan bazan yarda ya aure ki ba balle kuma baya nan. Masu garkuwa da mutanen nan in suka kama kashewa suke yi, ni jikina yana bani bazasu taɓa sakin Saheer ba. Shiyasa nake so ki amince da abinda na zo miki dashi, dan ni na ari bakin ki na ci albasa, na sanar da su kin amince."

Iskaha ra fashe da kuka mai sauti ta rarrafa ta riƙe ƙafar Baffa ta ce, "Baffa Hamma ba ya nan, an sace Hamma, an yi garkuwa dashi ana neman kuɗin fansa. Don Allah Baffa ka bar maganar nan, ni bazan iya auren wani in ba Hamma ba, bazan iya yin aure Hamma ba ya nan ba, ko da yana nan bazan iya kallon wani namiji a matsayin mijina ba in ba shi ba. Don Allah Baffa ka daina faɗar za ka aurar dani ga wani, don Allah ka bar maganar nan, tana saka min bugun zuciya."

Baffa ya bita da kallo ganin yadda take kuka da zuciya da jikinta, sai ta ba shi tausayi mai tsanani, amma duk da haka ba ya tunanin a ransa zai amince ta auri Saheer.

Ya shafa kanta ya ce, "Shikenan, ki yi shiru ki bar kuka. Na ji na bar maganar sai Hamman ki ya bayyana. Ki daina kuka." Ta kifa kanta a guiwar Baffa tana kuka sosai.

Ya yi shiru ya ƙyaleta tana kukan, sai da ta gaji dan kanta sannan ta ɗago ta goge idonta, ta kalle sa ta ce, "Na gode Baffa."

Ya yi murmushi ya ce, "tashi ki je." Ta miƙe a hankali ta fita daga ɗakin.

Baffa ya sauke numfashi ya ce, "A haka za a yi auren, bazan zuba ido rayuwarta ta lalace ba. Zuwa nan gaba zata saba, in bata so nan gaba zata so, in bata gane ba nan gaba zata gane” Baffa ya faɗa yana kallon Inda Islaha ta bi, dan bazai taɓa bari ta auri Saheer ba, duk hanyar da ya san zai bi dan kuɓutar da Islaha daga auren Saheer zai yi, bazai taɓa bari rayuwarta ta lalace ba.

Nana Haleema
[7/28, 12:20 PM] KRBBK: RDB2P90
Nana Haleema.

"Ki gudu Sudaisa, kina da damar da za ki gudu yanzu, ki tafi bana so wani ya yi nasarar amsa sunan mijin ki."

Sudaisa tana kuka ta ce, "bazan iya ba, bazan iya tafiya na bar ka ba."

"Za ki iya, ki tafi Sudaisa."

"A'a, bazan iya tafiya ba bar ka ba."

Kafin Sudais ya yi magana aka damƙo wuyansa ana jansa a ƙasa, Sudaisa ta bi yo bayansu tana kuka ta tarar an ajjiye sa a gaban Arɗo da yake zaune.

Aka nuna maaa Sudais ya ce, "Shawara yake bawa amaryar Black akan ta gudu."

Arɗo ya kalli Sudaisa ya kalle ta, bai ce komai ba sai ƙarar sautin bingida suka ji, Sudais ya faɗi a ƙasa alamun shi aka harba, ita kuma ta zube a ƙasa a sume.

Arɗo ya kalli kowa na wajen ya ce, "Na jima ina tausayinsa, amma shi ba ya tausayin kansa. Ƙarshen mara jin magana kenan, duk wanda ya bawa wani shawarar gudawa ƙarshensa kenan."

Ya kalli Sudaisa sa take a sume ya ce, "Ina É—ayan nan da nake ganin su a tare? A je a zo dashi."

A lokacin aka je aka ɗauko Saheer, ganin gawar Sudais bai san ya fara kuka ba, ga Sudaisa a ƙasa a sume. Hankalinsa ya tashi sosai, ya duƙa akan guiwarsa yana kuka. Arɗo ya ce, "Matar Black ta suma saboda rashin ɗan uwanta, na ga kuna shiri da ita, ka rarrashe ta."
Chapter 120 · 0% Book details