Sashe 76
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wanda ya yi maganar ya wara hannu ya ce, "meye amfaninta? A kashe ta kawai, itama ta ƙasar wajen in ta dawo a yi maganinta, a kashe su duka su biyun ai basu ƙarfin kisan ba. Saboda rai biyu zamu haƙura da aikin mu ne?."
Babban ciki ya ce, "gaskiya ne wannan, abinda ka faɗa shi ya kamata ayi. A ɓatar da yarinyar nan daga garin nan, in hakan bai yu ba a kashe ta!. Itama mai goya mata bayan, a wannan lokacin bana son kuskure, a tabbatar an yi maganinta!."
Mama a sanyaye ta ce, "kisa ya yi tsuri boss, a bani dama na san abinda zan yi."
Cikin faÉ—a ya ce, "sau nawa ana ba ki damar? Dama nawa aka ba ki ki ke wasa da ita?. Nan aka ba ki kwangilar sace yarinyar, nan ashe ba ke ki ka É—auka ta ba. Yanzu kuma kina so a sake ba ki dama dan ki É—auki mataki?...."
Ta yi shiru bata ce komai ba ya ce, "Na gama baki dama, a wannan karon da kaina zan ɗauki mataki, ai ba fin ƙarfina suka yi ba. Ke kin san muna yin komai saboda idanun mutane, amma yanzu bazan sake saurare ki ba. Kisa shine daidai da Zainab, dole mu tabbatar ta daina numfashi!."
Nana Haleema.
[7/13, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P54
Nana Haleema.
Mama ta kalle sa a sanyaye ta ce, "Tuba nake, amma a wannan karan baza a same ni da kuskure ba."
"Me za ki yi mata?."
"Daji zan aika ta kawai, yadda baza a yi zargin wani abu akan gidan ba."
"Kina nufin ta haukace kenan?."
"Ƙwarai."
ÆŠaya daga ciki ya ce, "in wata ran ta samu lafiya ta dawo daidai fa?."
Ta kalle shi ta ce, "ban da aikin wajen wanda zan je, in ya yi aiki tamkar rubutu akan dutse ne. Wallahi sai ta haukace."
Duk suka yi shiru Mama ta ce, "a bani wannan damar don Allah, bazan ba ku kunya ba in Allah ya amince. Kisa ya yi tsauri, ba mu san wa ta turawa recording É—in ba, in aka kashe ta za a yi zargin mu ne. Amma in ta haukace, ta shiga daji, shikenan mun huta."
Boss ya ce, "me ku ka ce?."
Suka ce, "duk abinda ka ce boss."
Ya kalli Mama ya ce, "An baki dama, amma in aka samu matsala..." kafin ya ƙarasaa ta ce, "wallahi babu matsala a harkar nan, ku bar komai a hannuna."
Cikin gamsuwa aka amince da shawarar haukata Zainab, suka cigaba da tattaunawa akan yanayin tsarin aikinsu, kafin kowa ya watse.
Mama tana barin wajan kai tsaye wajan bokan ta wuce. Ta yi bayani yadda ya kamata, sannan ta saka a yi aikin da zai ɓatar da hankalin Islaha daga kan su, ta manta da duk abinda yake faruwa ta yi harkokin ta, shi ya bata abinda ya kamata ta yi sannan ta koma orphange.
Tana shiga aka kira wayarta, ta ɗauka ta ce, "na gama komai, zuwa gobe za ku ji labari mai kyau. Zainab baza ta shura ba, tunda ta fitar da recording ɗin muryata ai ta shiga uku. Ku bar komai a hannuna, zan ɓatar da ita wallahi. In kuma nata haukace ba, zamu kashe ta!."
Zainab da ta ji komai, gabanta ya faÉ—i ta bar wajan da sauri. Hannunta yana rawa ta kira wayar islaha amma sai larabci ake yi mata. Jikinta yana karkarwa ta yi mata voice note tana hawaye, tana gamawa ta É—auki kuÉ—i a jakarta ta fita a guje.
      •••••••
Islaha bacci ne ya ɗauke tunda dare ya yi, bata farka ba sai sha biyu na dare, tana miƙewa zaune wayar ta ta jawo tana dubawa. Da voice note ɗin Zainab ta fara karo, ta buɗe tana sauraran abinda take faɗa. Bata san ta miƙe tsaye ba, a firgice ta tsaya akan ƙafarta jikinta yana rawa sosai.
"Innallahi wa'inna ilaihir raji'un!."
Shine abinda take maimaitawa cikin kiÉ—ima da tashin hankali, jikinta har rawa yake yi, kanta yana sarawa saboda tashin hankali.
Zagaye É—akin take yi, duk da akwai sanyin ac amma gumi tsatstsafo mata yake yi cikin tashin hankali da tsananin firgici mai yawa.
Ta kira lambar Zainab amma bata shiga, ta yi mata voice note amma babu alamun datar ta a kunne take. Ta É—ora hannu a kanta ta fashe da kukan damuwa da rashin sanin abinda zata yi.
Sai kuma ta zabura ta kira lambar Safeera, daga can ɓangaren Safeera ta gama shirin kwanciya kenan tunda suma dare ya yi.
Ganin kiran Islaha sai ta murmusa, daman tana da niyar kiran ta bata labarin auren Baffa da Atika.
Tana É—auka Islaha cikin kuka ta ce, "Safeera na shiga uku, zasu kashe Zainab Safeera. Ki taimaka min ki je ki gano ta, ki taimaka ki je gidan ki ga in tana nan!. In zainab ta rasa ranta ta silata bazan yafewa kaina ba."
Hankalin Safeera ya tashi ta ce, "Ban gane zasu kashe ta ba, su waye zasu kashe ta É—in?. Ki nutsu, ki yi min bayani yadda zan gane."
"Safeera ki fara zuwa ki gano min in tana nan, bazan taɓa samun nutsuwa ba indai ba lafiyar Zainab na ji ba."
"Goma na dare ta wuce Safeera, Baba bazai barni na fita ba. Kuma ko da na je kin san a rufe gida gate, baza a bar ni na shiga ba. Ki kira Æ´an uwanki na gidan ki ji in tana ciki mana."
Islaha ta sake fashewa da kuka ta ce, "Bata nan, An ce min ta bar gidan Safeera!. Ina zan saka raina in wani abun ya samu Zainab?."
Saferra jin yadda Islaha take kuka sosai sai hankalinta ya sake tashi sosai, ta ruÉ—e itama, cikin taushin murya ta ce, "ki faÉ—a min me ya faru?."
"Komai ma ya faru, na lalata rayuwar Zainab, tunda ni na bata shawarar ta dinga yi min recording tana turo min, da ban saka ta yi ba da bata yi ba, da ba a yi ƙoƙarin kashe ta ba. Ina zan saka raina in aka cutar da ita ta silar hakan?." Safeera zata yi magana Islaha ta kashe wayar tana kuka sosai.
Ta nemi number Saheer ta kira sa, bai ɗauka ba ta ajjiye wayar ta cigaba da kuka mai tsuma zuciya. Tashin hankalin ta bata ƙasar balle ta je ta ɗauke Zainab, damuwar ta ta yi nisa da Zainab balle ta kai mata ɗauki.
Babu jimawa Saheer ya kira ta, tana É—auka ta sake saka masa kukan da yake jin sautinsa sosai.
Shiru ya yi mata bai ce komai ba, yana jin yadda take sauke numfashi tana fitar da kuka mai sauti. Ya san in ya ce zai yi magana bazata ji sa ba, gwara ya yi shiru ta gama kukan sai su yi magana.
A hankali ya ji tana sauke nunfashi alamun kukan ya tsaya ya ce, "ki nutsu, kar ki jawo numfashin ki ya sarƙe. Kin san ba cikakkiyar lafiya ce dake ba."
A hankali take sauke numfashi kafin ta ce, "Hamma!."
Jin yadda ta kira sa ya saka ya ce, "Na'am, ya aka yi?."
Ta lumshe ido ya buÉ—e, a sanyaye ta ce, "Hamma Zainab!."
"Me ya samu Zainab É—in?."
"Za su kashe ta Hamma."
"Kisa kuma! Su waye?."
"Su Maman orphage."
"Mafarki ki ka yi akan hakan?."
Hawaye ta sakko mata ta ce, "wayar nan da muke yi mafarki ce?."
Ya ce, "Aa, a gaske ne."
"To da gaske ne abinda na faÉ—a maka, za su kashe Zainab Hamma."
Saheer cikin rashin fahimta ya ce, "da gaske ne me? Ki yi min bayani yadda zan gane. Ki nutsu, sai ki faÉ—a min abinda ya faru."
"Hamma sun samu recording É—in da Zainab ta turo min har na tura maka na ce ka ajjiye min, saboda shi zasu kashe Zainab saboda ta naÉ—i muryar Mama ta turo min."
Saheer ya ce, "su waye suka samu recording É—in?."
"Maman orphanage."
"ya aka yi ki ka san sun samu har zasu kashe ta?."
Hawaye ya sake sakko mata ta ce, "Zainab É—in ce ta faÉ—a min, kuma an tabbatar bata cikin gidan yanzu, na saka a n duba an ce bata nan."
Saheer ya ce, "Islaha anya ba mafarki ki ka yi ba? Ba fa film mu ke kallo ba, zahiri ne." Islaha sai ta yanke wayar, ta tura masa voice note É—in Zainab.
Sai da ta tabbatar ya gama ji sannan ta kira sa, ya kiÉ—ime ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yaushe ta tura miki?."
Islaaha ta ce, "tun É—azu, ban gani ba sai yanzu dana farka daga bacci. Hamma in wani abun ya samu Zainab mutuwa zan yi, ni na saka ta ta dinga yi min recording ko yaushe, ni na saka Zainab ta dinga tura min duk abinda ya faru. In suka yi mata wani abun bazan yafewa kaina ba, ko meye ya same ta ni ce sila, Hammaaaaaaaa!" Ta ja sunan cikin heart breaking, muryarta tana cracking cikin tashin hankali.
"Kwantar da hankalin ki, in Allah ya yarda babu abinda zai same ta. Yanzu zan saka Sadik ta je ya sanar da hukuma halin da ake ciki, zan saka a baza neman ta ko za a dace a ganta. Kar ki damu, ki kwanar da hankalin ki, zan yi komai kamar kina ƙasar, kin ji?."
Ta girgiza kamar yana gabanta ta ce, "bana so hukuma ta shiga maganar nan tun yanzu, na fi so na gama tattara komai sannan hukuma ta sani."
"Shikenan, zamu bayar da cigiyarta. Amma na tambaye ki."
Kafin ya yi tambayar ta ce, "Ya aka yi aka san ta yi recording É—in, har aka san ta turo min ko?."
Saheer ya ce, "haka zan tambaya. Ya aka yi suka san da recordong É—in a wajan ki?."
Ta ce, "ban sani ba Hamma, wallahi ban sani ba......" ta faɗa tana kuka, sai kuma ta ce, "Ka ga kenan lokacin da aka goge hotunan Hafsa shima masaniya suka samu a akan hakan, shine aka saka wani a cikin office ɗin su Safeera ya goge."
Saheer ya É—an yi shiru yana tunani sannan ya ce, "bayan ni, waye ya san da recording É—in a wajan ki?."