← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 133

Sashe 109

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa ya ce, "Islaha ki nutsu, za a faÉ—a miki duk abinda ya faru."

Ta ce, "Baffa ka faÉ—a min, don Allah."

Baffa ya ce, "É—azu suka kira Sadik akan Saheer yana hannunsu, zasu sake kira a jira su."

Islaha ta ja numfashi mai tsaho ta ce, "innallillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Ta faÉ—a hawaye ya sakkowa daga idonta.

Sai kuma ta juya ta kalli Sadik ta ce, "kuma an tabbatar masu garkuwan ne? Kar a sake maimaita abinda aka yi lokacin da na ɓata."

A sanyaye Sadik ya ce, "da gaske su ne Islaha."

Ta zauna a kan kujera ta dafe kai tana kuka mai taɓa zuciya, hannunta yana rawa saboda kuka ta rasa abinda zata ce.

Baffa ya ce, "mu je a sanar da Æ´an sanda."

Sadik ya ce, "Baffa ka share batun hukuma kawai, a bari aji abinda zasu ce a biya kuɗi a karɓo shi. Haka aka yi da aka sace ƙanwar abokina, ba a iya karɓota ba sai da aka biya wannan kuɗin. Babu abinda hukuma suke yi a wannan gaɓar, in dai sun faɗi kuɗi sai an bayar."

Baffa ya ce, "Duk da haka Sadik, gwara hukuma ta shiga maganar nan."

Sadik ya ce, "ban ƙi ba Baffa, amma abinda suka faɗa shi ya kamata mu yi."

Mama da take kukan rashin Saheer ta ce, "kar a faÉ—a musu don Allah, kar su kashe min Saheer."

Sai abin ya sake karyawa Islaha zuciya, ta yi kuka mai tsuma zuciya, tana ji kamar ta tashi ta yi tsuntuswa ta ganta a gaban Hamma, ta karɓosa ita ta bada kanta a kamata a ɗaure.

Baffa ya yi dauriya ya ce,  "ku daina wannan koke koken, ku je a cigaba da addu'a kawai. Allah ya shiga lamarin mu gabaɗaya." Sadik ne kaɗai ya amsa da amin, su basa cikin nutsuwarsu gabaɗaya..

Adda ta riƙe hannun Islaha suka koma falon Mama, dan yadda take jiri ita kaɗai zata iya faɗuwa.

Ita kaɗai ta shiga ɗaki ta zauna tana ta kuka babu ƙaƙƙautawa, abinda yake ɗaga mata hankali bai wuce in ta tuna yadda suka rabu ba, in ta tuna hakan sai hawaye ya sake sakko mata, cikin wani irin yanayin da bata taɓa jin irinsa ba. 

A lokacin Safeera ta shigo a gigice, Islaha ta miƙe tsaye ta rungume ta sake fashewa da kuka tana faɗin, "Hamma..an kama Hamma Safeera....Zasu kashe min shi, zasu kashe min Hamma!.." Ta faɗa muryar ta tana rawa sosai.

Safeera cikin rauni ta ce, "yanzu Baffa ya yi sallama da Baba yana faÉ—a masa, shine na zo wajen ki."

Islaha kuka kawai take yi a jikin Safeera, tana ganin abin kamar a mafarki, ganin abin take kamar wasa wai an yi garkuwa da Hamma, garkuwa ba irin wacce aka yi da ita ba, garkuwa ta gaske wacce za a iya kashe shi.

Safeera ta ce, "ki yi haƙuri, addu'a yake buƙata ba kuka ba, don Allah ki kwantar da hankalin ki, Allah zai kuɓutar dashi. In ba ki daina kuka nan ba za ki samu attack, kuma kukan ba shine maganin damuwar mu ba." Ita dai bata daina kuka ba, Safeera ta zanar da ita tana rarrashi.

Islaha cikin kuka ta riƙe hannun Safeera ta ce, "In na tuna yadda muka rabu dashi sai na ji wani iri, sai na ji ban kyauta masa ba."

"Haƙuri za ki yi, ki ta yi masa addu'a, ita yake da buƙata yanzu ba wannan kukan ba. Kar ki je ki samu attack a wannan koke-koken, ki yi haƙuri."

"Masu garkuwa da mutane fa Safeera, Æ´an bindiga ne suka É—auke Hamma."

"Na sani, ki yi haƙuri."

Safeera ta dinga rarrashinta har ta samu ta ɗan haƙura, bata koma gida ba ta zauna a tare da ita tana kwantar mata da hankali.

Islaha ta kalli Safeera cikin muryarta da ta dashe saboda kuka ta ce, "Ashe haka ku ka ji lokacin da na ɓace? Ashe haka ku ka ji lokacin da aka sace ni?. Haka wancan banzan ya dasawa mu ku ciwo, kuma ya saka ku kuka?. Me zai saka na so wannan mutumin, har abada wallahi." Safeera dai bata ce mata komai ba, ta dinga rarrashinta har ta nutsu sannan ta tafi.

Ranar gidan haka ya rayu shiru, kowa ya nutsu ya koma ga Allah ana zaman jiran tsammani, gabaɗaya kowa hankalinsa baya jikinsa, ana tunanin ta inda lamari zai sake ɓullowa.

Islaha bata iya baccin kirki ba, da ta yi zata farka ta yi kuka ta koma bacci. Ƙarfe uku ta tashi tana sallah tana roƙon Allah akan ya bayyana mata Hammanta, ta kuɓutar dashi faga hannunsu, ya kare shi daga zaluncinsu.

Da safe da ta tashi haka ta tashi da fuska a kumbure saboda kuka, ko shirin zuwa aiki bata yi ba, saboda bata da wannan nutsuwar a lokacin.

Ta shiga wajan Baffa dan su gaisa, ta same shi shida Sadik da Kawu da Baba a zaune ana ta tattaunawa akan batun.

Ta ƙarasa ta gaishe su, kafin su amsa ta ce, "har yanzu shiru?."

Baffa ya kalle ta cikin tausayin yanayinta ya ce, "har yanzu shiru Islaha, muna ta addu'a a kai."

Ta sauke numfashi ta ce, "Allah ya bayyana mana shi." Suka amsa da amin.

Baffa ya ce, "akwai maganar da nake so zamu yi dake, shigowar wannan lamari ne ya saka ni na manta jiya, amma in kin dawo daga wajen aiki ki zo ki same ni."

"Ai bazan je aiki ba Baffa, bazan iya ba" tana faÉ—a hawaye yana sakko mata.

Ya ɗaga kai ya ce, "shikenan, ki je ki zauna zamu yi maganar in anjima. Ki daina kuka, Allah yana sane da komai, shi ya ƙaddara mana, kuma shi zai ba mu mafita." Ta ɗaga kai ta miƙe ta fita ta bar suna cigaba da tattaunawa.

A harabar gidan ta zauna a inda suka saba zama ita da Hamma. Sadik yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallonsa har ya ƙaraso sannan ta ce, "Hamma Sadik da gaske sace shi aka yi?."

Ya bita da kallo ganin duk ta firgice, sai ya tausasa murya ya ce, "da gaske ne Islaha."

"Kuma zasu sake shi?."

"Za su sake shi in sun faÉ—i kuÉ—i an biya in sha Allah."

"Yaushe zasu faÉ—a?."

Ya sauke numfashi ya ce, "ko yaushe zasu iya yin waya."

Ta É—aga kai ta ce, "an yi magana da Æ´an sandan?."

Ya É—aga mata kai ya ce, "An yi Islaha."

Ta ce, "shikenan Hamma Sadik, amma don Allah kome yake faruwa ka faÉ—a min, ka ji?."

Sadik ya bita da kallo cikin tausayin yanayinta, magana take yi masa amma kuka take yi, gabaɗaya ta canja daga jiya zuwa yau, ta firgice lokaci ɗaya kamar ba ita ba. Tunda ta bar ƙasar yake jin haushinta, amma yanzu sai ta bashi tausayi saboda yadda ta koma wani iri, har rama ta yi akan daga daren jiya zuwa safiya, har ta so ta fi Mama shiga damuwa akan lamarin, dan tunda ya zo gidan ko Mama bai gani ba balle a tambayesa ya ake ciki.

Ya ce, "Zan faÉ—a miki in sha Allah, ki je ki ci abinci."

"Bazan iya cin komai ba."

"In Hamma ya ji bazai ji daÉ—i ba."

Faɗar hakan da ya yi sai hawayenta ya ƙaru ta ce, "ni bazan ci komai ba sai ya dawo."

Ya murmusa bai ce komai ba, dan bazai iya da rigimarta ba, shi yana da saurin hawa yanzu sai ya rufeta da faÉ—a, Saheer É—in ne daidai ita.

Ya fita daga gidan ta bishi da kallo, ta koma ta zauna a wajan cikin tunanin da bata san adadin lokacin da ta É—auka a wajan a zaune ba, yana wajan har sai da rana ta fito sannan ta koma ciki.

•••••••

Su Saheer haka suka buɗe ido a filin Allah, gwara matan ya ga an tattare su an saka su a wata ƙaramar bukka, amma su a wajen suka kwana bayan an ɗaure musu hannu da ƙafa saboda kar su gudu. Suna jere shi da Sudais, dan yaron tausayi yake bashi sosai, bashi da wata magana sai ta ƙanwarsa, hirarsa akan ƙanwarsa ce, indai zai buɗe baki ya yiwa Saheer magana akan ƙanwarsa ne.

GabaÉ—aya wari Sudais yake yi, dan babu batun zuwa yin fitsari sai dai ka yi a wajen, kashi ne in sun ga dama za su kwance ka a kara ka da bindiga ka je ka yi ka dawo.

Suna zane a wannan yanayi na rashin sanin me anjima zata haifar musu. A lokacin Magaji ya zo yana kwance musu hannaye saboda zasu ci abinci. Sudaisa ta kawo abinci a ganye ta ajjiye a gabansu, fuskar ta duk ta tashi, ga cizon sauro da ƙananun ƙwaruka. Saheer ya kalle ta ya ga hawaye kawai take yi, tana ajjiye musu abincin ta koma.

Bayan sun bar wajen Sudais ya ce, "Sune suke dafa abinci, ba ka ji jiya ArÉ—o ya ce a kai su su nemo zogale ba?."

"Na ji."

"To ba a tsaurarawa mata tsaro sosai, an fi tsaurarawa maza saboda kar su gudu."

Magaji ya dawo ya kalle su ya ce, "Akwai wanda zai shiga banÉ—aki? In lokacin shiga banÉ—aki ya wuce babu wanda zamu sake kaiwa."

Kowa ya É—aga hannu a wajen, É—aya bayan É—aya aka dinga raka su da bindiga ana tsayawa su gama abinda zasu yi a dawo dasu. Saheer ya kalli abincin ya ga shinkafa ce fata tas, gabaÉ—aya bata fi spoon uku ba, babu komai a kanta.

Bai ƙi ci ba, dan in bai ci ba bai san zai ci ba nan gaba, aka basu ruwa suka sha. A wajen suka yi taimama suka yi salla kafin a sake ƙulle musu hannu.

Ihuu suka ji daga wajen matan, take Sudais ya zabura yana kallon Saheer cikin tashin hankali, dan ya san ihun Æ´ar uwarsa ne. Suna kallon su sun nufi wajen suna tambayar lafiya. Ita kuwa Sudaisa ta fito tana tsalle tana kiran maciji.

Wani daga cikinsu saboda takaici bai san ya maka mata kan bindiga ba, goshinta ya fashe, jiri ya kwashe ta ta faÉ—i a wajen.

Babu zato babu tsammani suka ji sautin harsashi kawai, take wanda ya buga mata bindiga ya faÉ—i a wajen a mace. Sudaisa saboda gigicewa ta yi baya ta suma.

Nana Haleema.
[7/24, 9:52 AM] KRBBK: RDB2P82
Nana Haleema.
Chapter 109 · 0% Book details