Sashe 85
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jazy ya ce, "tana bani labarin yadda ka sace ta ka kaita gidan ka ne."
Ray ya ja tsaki ya É—auke kai cikin takaici mai yawa, sai daga baya ya ce, "yarinyar tana da mental disorder, ta dinga magana ita kaÉ—ai, kai kuma ka biye mata kun zama É—aya."
Jazy ya kawar da maganat ya ce, "gobe zan tafi Madina."
Rehaan ya fusata ya ce, "ina yi maka magana akan kana cin amanar ƙanwata kana zancen gobe za ka tafi madina? Na riƙe ka ne? Yanzu ma ka tashi ka tafi mana."
Jazy ya bi shi da kallon mamaki jin ya fusata lokaci É—aya, ya ce, "calm down, me ya fusata ka haka Ray?."
Ya ja tsaki bai ce komai ba, yana jin zafi haushin Jazy da ya biyewa Islaha suna hira.
Jazy ya ce, "Ni ban ga abin faÉ—a a nan ba Ray, dan na yi hira da ita ban ga dalilin da zai saka ka fusata kana faÉ—a haka ba. Yau na saba hira da mata?."
"You were talking in a low voice so I wouldn't hear, right?. Me ka ke faÉ—a da baka so na ji?."
Jazy ya bi sa da kallon mamaki ya ce, "wait! Ya ka ke magana kamar wanda yake kishi?."
Wani banzan kallo ya yi masa, kafin ya yi tsaki ya miƙe ya bar wajen. Jazy ya bi sa da kallo yana dariya, dan shi bai ga abin ɗaga hankali ba.
Nana Haleema.
[7/17, 11:50 AM] KRBBK: RDB2P61
Nana Haleema.
Islaha a sanyaye ta fita daga gidan, ta sake kallon ƙofar gate ɗin ta ga Dr Rehaan a rubuce, ta yi ajiyar zuciya, ta shiga gidan Maleek.
Tana tafiya tana tunani, ganin abin take yi kamar a mafarki wai wannan mutumin da take rainawa hankali, take faÉ—a masa duk abinda ta ga dama, wai shine Rehaan Yola da kowa yake son yin magana dashi.
Ta zauna a gefen gado tana tuna yadda ta dinga faÉ—a masa magana, da yadda Chairman ya ke son a kawo shi channel É—in su, da yadda kowa yake son ace ya ga Rehaan Yola.
Ta ɗan taɓe baki ta dafe kai ta ce, "Shiyasa Hamma yake yawan yi min faɗa, yana cewa na iya harshena, ban san mutanen da zan haɗu dasu ba, amma bana jin magana."
Ta É—auki wayarta, ta sake yin searching Rehaan Yola ta ga dai shi É—in ne ya fito, a bayyane ta ce, "Anya Jafar É—in nan ba raina min hankali yake yi ba?."
Sai kuma ta kalli wayar ta É—an gyaÉ—a kai ta ce, "kuma dai É—in ne, kenan da gaske shine Rehaan Yola? Wanda na fita tun asuba ina nema, muka haÉ—u ya zuba min tea" ta nuna wayar da yatsanta ta ce, "wai duk shine ashe?."
Ta girgiza kai ta ce, "Allah mai iko, Allah gwanin hikima. Ko kaɗan ban taɓa hararowa shine Rehaan Yola ba, ko da na ga Jafar ban ji a raina shine Rehaan ba. Ashe wannan soloɓiyon mai jikin matan shine Rehaan Yola, amma dai an yi ragon maza."
Ganin Hamma yana yi mata waya sai gabanta ya faɗi, ta tuna da batun ɗaurin aurensu gobe, sai ta kasa ɗaga wayar tana kallo ta lumshe ido tana jin ƙirjinta yana bugawa sosai.
Ya sake kiranta ta kasa É—auka, sai ma komawa da ta yu ta kwanta tana tunanin da gaske dai wancan shine Rehaan?. Rehaan Yola dai da yake yiwa mutane wahalar gani, shine ya zama kamar purewater a wajenta, shine ya zama kamar wani toy a wajen ta. Ta lumshe ido tana tuna waye shi a Yola, ta girgiza kai tana ganin abin kamar a dream.
Jazy a tsaye ya samu Rehaan yana kallon wani waje daban kamar mai tunani, Jazy ya kalle sa ya ce, "ina faÉ—a maka gobe zan tafi Madina kana share ni."
Ya juyo ya kalle shi, kamar zai yi magana sai kuma ya yi masa banza. Jafar ya yi dariya bai ce komai ba ya wuce É—aki, dan in ya biye masa faÉ—a zasu yi, mamaki ma yake bashi da yake wannan abun, kamar yau ya saba hira da mace bayan Riyya.
Haka suka zauna Rehaan yana jin haushin Jafar ba tare da ya san me ya yi masa ba, ba su haɗu ba har dare kowa yana ɓangarensa.
Shigowar Jafar kenan ya siyo turare ya zauna yana buÉ—ewa bai kula Rehaan ba, dan yadda ya share shi shima haka ya share sa.
Rehaan ya É—an kalle sa, kamar baya son magana ya ce, "meyasa baza ka jira mu je tare ba?."
Jazy ya yi masa banza kamar bai ji ba, dan sai ya rama wulaƙancin da ya dinga yi masa. Rehaan ya ce, "magana nake yi maka."
Ya yi masa shiru bai ce komai ba, buɗe turarensa yake yi kamar bai san yana yi masa magana ba. Rehaan ransa ya sake ɓaciya girgiza kai yana jan ƙwafa kafin ya cigaba da danna wayarsa. Yana ji Jafar yana waya da wanda suka sani a Madina, yana faɗa masa hotel da room ɗin da zai yi masa reserving kafin ya zo.
Sai a sannan Jafar ya kalle sa ya ce, "Abba ya ce yana ta kira ka baka É—auka ba, in ka ga dama ka kira shi, in ba ka ga dama kar ka kira."
Rehaan ya kalle sa cikin ƙuluwa ya ce, "wai akan waccan yarinyar ka ke yi min magana haka?...."
Jazy ya É—ago ya kalle sa ya ce, "Rehaan me na yi maka?."
"Me ba ka yi ba?."
"Sai ka faÉ—a na ji ai."
"Ka zauna da ita kuna hira harda dariya kama wata sister ka, ka manta yarinyar Ubaid ce, zama da ita a waje É—aya ma babban zunubi ne. Dan na yi maka magana ka ke jin haushina?."
Jafar ya ce, "sai me ye dan yarinyar Ubaid ce? Ni bai dame ni ba, kai ka ga hakan zai dama ka bani ba. Ko ganinta na yi da Ubaid ido da ido ba damuna zai yi ba, kaima kuma ban ga dalilin da zai dame ka ba. Kamar yadda ka ce ba sister na bace, kai ma ba sister ka bace. Ban ga abin É—aga hankali dan tana yarinyar Ubaid ba, balle har ka ji haushi kana daina yi min magana."
"Kuma ni yarinyar nan tausayi ta bani, da na saka aka yi min bincike a kanta, sai na gane rayuwar ta gabaÉ—aya a maraici ta tashi. Kuma kai da ka san taimakon da ta yi maka, da baka ce mata haka ba" ya faÉ—a yana cigaba da abinda yake yi.
"Taimako! Ita wacece da zata taimake ni?."
"Ƴar adam ce kamar kai, zata iya taimaka maka a ko wanne hali. Ba maganar kuɗi ko iko ake a nan ba, maganar taimako ake yi."
"Kai ka san duk duniya babu yarinyar da nake jin haushi kamar ta, dan baka da class, ka zauna da ita kana hira, bayan ga matar da zaka aura can a Yola."
"Kai wai dan zan auri Riyya shikenan bazan yi hira da ko wacce mace ba?."
"Ka yi hira da matan duniya ma Jazy, amma ban da wannan."
"ita meye laifinta? Kawai dan kana zarginta akan abinda baka da tabbaci a kai?."
Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, Jazy ya ce, "In ma kana da tabbacin yarinyar Ubaid É—in ce, abinda ka ke zargi ta aikata, sai me? Ina ruwan ka, rayuwar ka ce ko rayuwar ta?."
Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, Jazy ya taɓe baki ya ce, "Ni dai gobe zan wuce, kafin ka tashi daga wannan wahalallan baccin naka na hau train na wuce."
Ya É—an hararesa sannan ya ce, "In ka je a binne ka a can, kar ka dawo da rai."
Jafar ya yi dariya ganin ya ƙular dashi, kuma shi dai bai ga abin jin haushi a lamarin nan ba, ya tayar da hankali kamar wata sister sa ce.
Ya ce, "Inyee, jinin indiyawa ya ji hausa. Na ji, dan an binne ni a can ai ba komai bane, garin da Annabi yake kwance ai abin so ne nima na kwanta. Kuma wallahi duk bala'in ka bazan ɗaga tafiyata ba, in ka ga dama ka biyo bayana, in baka ga dama ba ka sha zaman ka" ya faɗa yana haɗa kayansa ya miƙe ya bar masa wajan. Ya bi sa da harara yana ji kamar ya je ya yi msa dukan tsiya.
Washe gari Friday, tunda Islaha ta farka take cikin fargaba da bugawa ƙirji. Da safe sai kallo agogo take yi tana tunanin aurenta da Hamma saura awanni kaɗan. Haka take yin komai sukuku babu ƙarfi, a haka suka gama haɗa breakfast suka fara shirin zuwa masallaci.
Sunaira ta ta takurawa Islaha akan su je sallah, babu yadda ta iya, ta saka sabuwar abayar da aka bata suka tafi da wuri dan su samu huÉ—uba.
Lokacin da suka dawo a lokacin wayarta ta fara ringing, gabanta ya faÉ—i ganin sunan Hamma yana yawo akan wayar.
Ta san lokacin sallar juma'a bai yi ba a Nigeria, amma haka kawai take jin faÉ—uwar gaba mai tsanani.
A hankali ta ɗauka ta saka a kunne, daga can ɓangaren ya ce, "Ya dai Matar Hamma? Saura lokaci kaɗan ko?."
Ta É—an yi dariya kaÉ—an ta ce, "ina yini Hamma."
"Lafiya lau Matar Hamma, kin ganni ina shirya kaina cikin farar shadda, saboda yau za a bani auren Islahata."
Ta É—an murmusa, cikin son kawar da abinda yake ranta ta ce, "ai gwara ka shirya da kyau, dan ma bana kusa ne."
Ya yi dariya ya ce, "ai ni ko bakya nan É—in, indai za a ce Islaha matar Saheer ce Allah ya yi min komai. Zan zauna na jira ki, duk lokacin da ki ka dawo a yi biki, a kai min ke mu fara shimfiÉ—a rayuwar aure mai tsafta. Ke ba sai an yi bikin ba ma, a bani ke haka."
Ta sake yin murmushi ta ce, "Yanzu dai yau za a É—aura?."
"In sha Allah, saura lokaci kaÉ—an."
Ta yi shiru bata ce komai ba, Saheer bai damu ba ya ce, "zan je wajan Baffa, ana ɗaurawa zan yi miki message, ki kasance active." Ta amsa da to a sanyaye, ya kashe wayar cikin shauƙi da zumuɗi..