← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 133

Sashe 5

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dafe kai cikin takaici ta ce, "gaskiya ni ban so hakan ba wallahi, a barta ta je ta can ta ƙarata har Allah ya ɗauki ranta gabaɗaya mu huta da annabo."

Muslim ya ce, "in so samu ne nima haka nake so, amma bazai yu ba dole hakan ya faru, dole mu nuna mun damu da ɓacewar ta."

Ta harare sa ta ce, "ka je ka faɗa masa. In kuwa ta bayyana, baza mu rusa plan ɗin mu ba gaskiya." Ya gyaɗa kai ya ce, "watsa mata acid baza mu fasa ba, sai mun lalata fuskar nan, ina zuwa"ya miƙe ya fita zuwa office ɗin Chairman.

Cikin lokaci kaÉ—an kowa ya san ba a ga Islaha ba, hankalin ma'aikata abokan aikinta ya tashi, dan Islaha ta kowa ce bata da matsala ko kaÉ—an. Bar ta da rashin kunya da tsiwa, shima sai ka shiga sabgar ta, in ba haka ba zaku zauna lafiya lau.

Hankalin kowa ya tashi, aka tambayi kalar kayan da ta fita dasu, aka nemi Safeera ta bada hoton Islaha guda ɗaya, nan da nan aka yaɗa hotonta a kafafen yaɗa labarai. Da ka shiga duniyar yanar gizo hoton Islaha zaka fara gani, ana cigiyarta da daidai lokacin da ta ɓace. Da lambobin wayar da za a kira in an ganta...

Nana Haleema
09030398006.✍🏻
[6/15, 3:57 PM] KRBBK: RDB02P3
Arewapen@nanahaleema11

Rehaan yana zaune ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, waya ake yi masa amma bashi da lokacin kallon wayar balle ya É—auka. Tunani ne kala-kala a ransa, ya rasa wanda zai kama ya yi nazari a kai.

Mamy ce ta shigo falon nasa da sallama, hakan ya saka ya buɗe ido yana kallon ta har ta ƙaraso ta zauna a gefensa. Tana zama ya zame ya kwanta, ya kwantar da kansa a kan cinyarta yana lumshe idanunsa, ta ɗora hannunta a gashin kansa tana shaafawa a hanakali.

A sanyaye ya ce, "Mamy wani abu yana damuna."

Mamy ta ce, "meye shi?."

Ya ɗago ya kalli idanunta  ya ce, "Mamy Salman..."

sai kuma ya miƙe zaune ya ce, "jiya dashi na kwana a raina, ina so in tafi dashi Jedda a nema masa lafiya."

Mamy ta sauke numfashi ta ce, "Abba ya faÉ—a min duk abinda ya faru, duk abinda ya faru a falon Daada ya sanar dani...."

Ta riƙe hannunsa duka biyun ta ce, "bazan taɓa hanaka yiwa ƴan uwanka alkhairi ba, kome zaka yi musu ka yi, zumunci ka yiwa. Amma tunda uwarsa tace bata so sai ka ƙyale su ai babu dole ko?."

Ya É—an rausayar da kai ya ce, "Amma Mamy...."

Ta dakatar dashi ta ce, "Allah ya ga zuciyar ka, Allah ya baka ladan niya. Yaushe zaka tafi Jedda?" Ta faÉ—a dan ta kawar da waccan maganar.

Ya É—an sauke numfashi ya ce, "na kusa."

"Nima ina so na je gida amma mahaifin ka ya hana, kai ina so ka je. Na samu labarin an samu inda Sofia take."

Ya É—aga ido ya kalle ta ya ce, "Mamy har yanzu ba ku fitar da rai da samunta ba?."

"Ta ya zamu fitar da rai? Har yanzu a jikina ina jin za a ga Sofia. Ka je gidanmu, ina so na san asalin abinda yake faruwa.

Ya rausayar da kai ya ce, "Mamy ni bana son zuwa ƙasar nan taku fa."

Ta harare sa cikin harshen hausa ta ce, "sai ka je, É—an rainin hankali kawai.

Ya yi dariya ya rungume ta ya ce, "Mamy har yanzu hausar ki bata zauna ba, kowa ya ji ya san koya ki ka yi ba da ita aka haife ki ba."

"Kaima haka taka take, gwara ni akan ka."

"Well, in na samu lokacin zan je."

Ya kalli agogon hannunsa sannan  ya ce, "ina da baƙi a guest house, zan je can mu tattauna. Zan iya yin kwana biyu a can."

"Kawai kana so ka gudu ne, ba wasu baƙi."

"Allah ina da baƙi Mamy."

Ta É—aga kai ta ce, "shikenan. Ka ci abinci?."

"Mun ci tare da Riyya."

Ta shafa fuskarta tana pecking É—insa a kumatu ta ce, "Allah ya cigaba da baka nasara, Allah ya cigaba da kare ka daga sharrin duk mai sharri. Ya baka É—aukaka da zuciyar taimakon wanda ya cuce ka."

Shima ya yi pecking ɗinta ya ce, "Amin Mamy. Ki cigaba da yi min addu'a, daƙyar nake yi zaman ɗakin nan, sai na ji kamar ana bin bayana."

Ta shafa kansa ta ce, "tsananin addu'ar ce ta kawo ka haka, kar ka damu. Kai mai nasara ne a ko yaushe. Shiyasa na so na saka maka sunan mai nasara, amma Kakar ka ta hana."

Murmushi ya yi kaɗan, ya kwantar da kansa a ƙirjinta yana jin ƙaunarta tana sake shiga ransa. In ba wajen ta babu inda yake samun nutsuwa, daga ita sai Jazy, sai kuma Abba da yake yawan fahimtar sa. Amma Mamy daban take, ko ransa a ɓace yake da ya kwanta a jikinta sai ya manta, tunda shi bashi da riƙo, kana yi masa ya wuce.

Ta shafa kansa ta ce, "aure zaka yi Rehaan, ya kamata ka rage wannan son jikin nan. Har yanzy baka girma da kwanciya a jikina ba. In kuwa ka yi aure sai ka kwanta a jikin matar ka."

Ta ɗan yi murmushi ta ce, "matar ka zata sha wahala, kafin ta saba da wannan shagwaɓar ta ka, kamar wani last born."

Ya sake narkewa a jikinta ya ce, "ni babu wani aure da zan yi."

Ta yi dariya tana shafa bayansa ta ce, "tunda Kakar ka ta faɗa sai an yi, ka yi haƙuri kawai."

Ya miƙe daga jikinta, hular da take bayan rigarsa ya ja ya rufe kansa ya ce, "zan tafi Mamy."

Ta miƙe tsaye ta ce, "ka yi parking kayan ka ne?."

"No need."

"okay my billionaire, Allah ya raya min kai, na ga Æ´aÆ´anka."

Jin sunan da ta faɗa ya basa dariya, ya sake rungume ta sannan ya ɗauki wayarsa ya bar falon, ta bi sa da kallo tana jin alfahari a zuciyarta mai matuƙar yawa.

      Islaha alarm ɗin wayarta ne ya tashe ta, ta miƙe a firgice tana sake jin sanyi yana sake dabaibaiye jikinta.

Ta buɗe ido a hankali ta ganta a kwance a inda bata saba ganin kanta ba, a firgice ta miƙe tana jin sautin agogo, tik tik tik da yake aiki a falon.

Ta ɗaga kai ta kalli agogon, ta ga ƙarfe uku da rabi na dare, ta sake kallon ƙofar falon tana tuna a inda take, sai ta zabura da hanzari ta nufi ƙofar tana jijjigawa amma ƙofar ko motsi bata yi.

Ta koma wajan window ta buÉ—e tana kallo, gidan yana nan da hasken sa tar amma babu kowa a wajen.

Hawaye suka sake gangaro mata, daman ga ciwon kan da ta kwanta dashi, ta dafe jijiyoyin kan ta zame a wajan tana kuka sosai. Bata san a in a inda take ba, bata san waye ya kawo ta ba, bata san a ina take ba.

Ta numfashinta sai ta ji yana sarƙewa, ta ɗan ja sa da ƙarfi, ƙirjinta ya yi nauyi numfashin baya sauka yadda ya kamata.

A hankali ta miƙe tsaye, ta ƙarasa wajan ac falon tana kallon a.c, sai ta bi wayar da kallo har ta ga inda switcg ɗin yake, ta kashe tana numfashi da  daƙyar.

Ta sake zamewa a wajan tana kuka sosai, sai da ta gaji dan kanta sannan ta miƙe zuciyarta tana bata umarni ta miƙe ta yi alwala ta yi sallah kawai.

Ta inda Allah ya taimake ta ta gama preiod, da ace tana kai ne da bata san halin da zata kasance a inda bata san ina ne ba.

Wata ƙofa ta gani a falon, ta nufi wajan a sanyaye cike da tsoro ta murɗa handle ɗin ƙofar. Duhu ta gani babu haske ko kaɗan, ta ɗan taɓa gefe kawai ta ji ta kunna wutar wajan, ta bi wajan da kallo.

Dogon corridor ne sai falo daga ciki, sai wasu ƙofofin da suke wajan a kulle.

Ta taka a hankali ta buɗe ƙofar farko, ta yi karo da babban bedroom mai kyau da girma, ta kunna haskensa dan ta san baza'a rasa banɗaki a ciki ba.

Ta ƙarasa ta buɗe bathroom tana kallonsa, bata tsaya ƙare masa kallo ba dan ba abinda yake gabanta ba kenan, ta shiga ta yi abinda zata yi ta fito ta dawo babban falon.

Jin sanyin ya yi mata yawa sai ta ɗauki wayarta ta koma falon da ta baro, da application ɗin wayarta ta ga alƙibila sannan ta tayar da sallah.

Sallah take yi tana kuka, bata san adadin sallolin da ta yi ba, ta dai san ta yi sallah da yawa tana faÉ—awa Allah damuwarta da neman ya fitar daga inda bata san waye ya kawo ta ba.

A haka ta ji wayarta tana kiran sallar asuba, ta idar da sallar ta yi shiru ko zata ji kiran sallah amma ɗuf babu alamun kiran sallah a unguwar, ta miƙe ta tayar da sallah tana jin jiri yana ɗaukarta saboda ciwon kai da yunwa.

Bayan ta idar ta jingina da kujera tana sauke numfashi cikin ciwon kai da yunwa.Tunaninta ya tsaya cak, tunaninta da hankalinta ya tsaya waje É—aya ta rasa abinda ya kamata ace ta yi.

Ta sake duba wayarta ta ga no service, ta sake fashewa da kukan takaici tana ji kamar ta samu wuƙa ta sokawa kanta ta mutu kowa ya huta.

Bata san adadin lokacin da ta É—auka a wajan ba, ta san tana jingine da kujera idanunta a tufe tana karanta azkhar.

Ɗan taɓa ƙofar ta ji anyi, ta zabura ta fito tana fitowa ana kulle ƙofar main falon. Ta saki ƙara ta ƙarasa tana jan ƙofar amma an riga an kulle har an fita.

Ta buɗe window tana cewa, "Don Allah ku buɗe ni, ban yi mu ku komai ba meyasa za ku kawo ni nan ku ajjiye kamar kayan wanki? Don Allah ku taimaka min ku buɗe min, Babana bashi da lafiya yana asibiti. Don Allah ku taimaka ku buɗe min!" Ta faɗa da ƙarfi tana kuka sosai.
Chapter 5 · 0% Book details