← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 133

Sashe 13

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha haka ta zauna falom ta rasa me yake yi mata daɗi, ga jikinta duk babu daɗi saboda bata saba zama babu komai a jikinta ba. Ta ɗan sauke numfashi a lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo mata da abinci, ana ajjiye abincin a inda suka saba ajjiye mata, ta kalli abincin ta kalli wanda yake shigowa ta ce, "Don Allah ina ogan ku?."

Da mamaki yake kallon ta jin tana tambayar ogansu, kuma yau magana take cikin sanyi babu hayaniyar da ta saba ya ce, "waye?."

"Wanda ya fita yanzu, wani fari haka" ta faÉ—a tana kallonsa.

Ya bita da kallo yana mamaki, yana tunanin wa take tambaya, ba dai Mr Rehaan ba?. In shine mai zai kawo shi inda take? Shi fa bai gane kan Ogan nasa ba, mace ta farko da aka taɓa kawo masa gidan. Ko Chef namiji ne, house maids ɗinsa kaf maza ne, indai ba abokan kasuwancinsa ba, mata basa zuwa inda yake. Amma ga wata ƙaramar ƴar jarida, ya saka an ɗauko ta ya ajjiye har yana zuwa inda take. Tana faɗa kuma sai ya ji ƙhamshin turarensa, ya ɗan ɗaga kai yana mamaki, bai nuna mata ba.

Ya ce, "ban gane wa ki ke nufi ba."

"Mai gidan ku mana, wanda ya saka ku ka sato ni ku ka kawo ni nan."

Shams ya É—an yi murmushi kaÉ—an yana girgiza kai ya ce, "baki san sunansa ba?."

"In na sani zan tambaya ne?" Ta tambaya a fusace tana kallonsa.

Ya yi Æ´ar dariya ya ce, "ni ban san wa ki ke nufi ba."

Ta lumshe ido kawai bata ce komai ba, har zai fita sai ta tuna Baffa, ta ga in bata kwantar da kai ba baza ta samu ta bar gidan ba, in bata yi laushi ba baza a bari ta koma su cigaba da fafutukar neman kuÉ—in aikin Baffa ba.

Ta ɗan sanyaya murya, tana jin haushin sauke kai ƙasa da zata yi, ta ce, "Don Allah yana ina? Ka faɗa min inda yake naje na same shi, wallahi Allah ina da mara lafiya a asibiti, babana za a yiwa dashen ƙoda, ana buƙatata a wajen, ina da mahimmaci a wajen aikin. Ku bar ni na tafi, ban san me na yi muku ba."

Ya dakata ya juyo ya kalle ta, dan shine ya yi bincike a kanta, kuma ya tabbatar da abinda ta faÉ—a gaskiya ne. Shams ya ce, "babu inda za ki iya zuwa daga gidan nan, kina wajan nan da aka ajjiye ki."

"Na sani, nima ba guduwa zan yi ba, magana nake so na yi dashi, ka taimaka min na ganshi don Allah."

Ya ɗan yi shiru yana kallon ta, sai kuma ya gyaɗa kai ya ce, "lokacin hutunsa ne yanzu, amma zuwa anjima na yi miki alƙawari da kaina zan same shi na faɗa masa, in ya amince zan zo na kai ki."

Hawaye ya sakko mata ta ce, "na gode." Ya buɗe ƙofar ya fita, ta yi tagumi tana kallon ƙatuwar tv da take ajjiye.

Shams bayan ya fita kiran wayar Jazy ya shigo wayarsa, yana É—auka Jaafar ya ce, "yarinyar nan tana nan har yanzu?."

Shams ya ce, "tana nan Sir."

Jafar ya yi tsaki ya ce, "ba nace ku sallame ta ba?."

"Ka faɗa Sir, amma bai bamu umarnin hakan ba, ka yi haƙuri."

"Yana ina yanzu?."

"Yana ciki yana hutawa."

"Zan yi magana dashi, zuwa anjima ko bai baka umarni ba ka sake ta ta tafi gida, babu abinda zai faru."

Shams ya gyaÉ—a kai ya ce, "To sir." Daga haka ya kashe wayar Shams ya bi wayar da kallo yana mamaki ya ce, "maganar wa zan É—auka wa zan bari?" Ya faÉ—a yana zama cikin tunani.

Bayan ya idar da sallar isha yana zaune a falo yana shan ice macha, Shams ya yi kocking ƙofar kamar bazai amsa ba, sai daga baya ya ce, "Yeah."

Ya shigo da sallama, Rehaan ya amsa Shams ya ajjiye masa abinda ya aike shi ya kawo masa, ya koma daga gefe ya ce, "Sir."

Ya É—an juyo amma bai ce komai ba, alamun amsawa ce hakan. Shams ya ce, "yarinyar nan...."

ÆŠago kan da ya yi ya kalle shi sai Shams ya nutsu sosai, kar ya yi tunanin wani abu ya ce, "ÆŠazu da na kai mata lunch, ta ce min tana so ta yi magana da kai."

Ya É—auke kai daga kallonsa ya cigaba da abinda yake yi kamar bazai yi magana ba, sai da aka yi minti biyu a haka sannan ya ce, "what next?."

Shams ya ce, "as you said Sir."

Ya ɗan kaɗa ƙafarsa da take ajjiye akan table ya ɗago ya kalle sa ya ce, "meyasa ka faɗawa Jazy maganar ta?."

Gabansa ya faɗi matuƙa, ya ɗan sunkuyar da kai ya ce, "Sir...."

Kafin ya basa amsa ya ce, "Sir what?."

Shams ya yi shiru dan ya san baya so ka yi kuskure ka ce masa sorry.

Rehaan ya gyaÉ—a kai ya ce, "meyasa ka faÉ—a masa?."

"Saboda komai ina faɗa masa, kuma baka taɓa complain akai ba."

Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba dan ya san gaskiya ya faÉ—a, ko kisan kai ya yi dole Jafar zai sani balle kuma É—auko wata yarinya.

Rehaan ya yi masa banza kamar bazai yi magana ba, sai daga baya ya ce, "ta zo."

"Thank you sir" ya faÉ—a da hanzari yana fita kar ya sake kunno masa ruwa.

Yana fita wayar Rehaan ta yi ƙara ya duba ya ga Mamy ce, ya gyara zama ganin video call ne ya ɗauka ya ce, "Mamy."

Mamy tana kallonsa ta ce, "Rehaan me ka ke yi a nan ne?."

"Aiki Mamy."

"Aikin me? Me ka ke yi har yau baka gama ba? Kasan bana son zaman ka kai kaÉ—ai a waje ko?."

"Mamy har yanzu ban gama ba, yanzu m meeting nake yi."

"bayan Jafaar ya faÉ—a min babu wani aiki da ka ke yi. Rehaan in ka san babu abinda ka ke yi ka dawo gida please."

Rehaan ya ce, "ina aiki, ƙarya yake yi."

Ta É—an yi shiru ta ce, "Okay Allah ya taimaka. Amma gobe kazo gida, ka zo mu yi lunch, ina so na ganka."

Rehaan ya gyaɗa kai ya ce, "Mamy gashi kina ganina, ai ba sai na zo ba" ya faɗa cikin shagwaɓa yana kallon ta. Dan baya son komawa gidansu, ya fi jin daɗin zama nesa da gida.

Mamy ta yi murmushi ta ce, "Mamies Boy, ina so in yi hugging É—inka Baby, ka dawo ka ji?."

"In sha Allah."

"Take care."

Ya yi murmushi bai ce komai ba ta yanke wayar.

Tana kashewa Jafar ya kira shi, ya bi kiran da kallo kamar bazai É—auka ba, ya yi tsaki sannan ya É—auka ya ce, "Sai me?."

Jafar ya ce, "inyee lallai, hausa ta fara fita yadda ya kamata a harshen ka."

Rehaan ya yi tsaki ya ce, "ina da abinda zan yi, ka faÉ—i damuwar ka ko na kashe wayata."

Jafar ya ce, "baka ƙyale yarinyar nan ba ko? Wai meyasa ka ke da taurin kai ne?."

"Wait! Wai sister ka ce?."

"Not at all..."

"So why are you bothering yourself about it?."

"Saboda kai ne malam, meye na ajjiye mace a gidan ka for god sake?."

"Na faɗa maka ina so ta san waye ni, har yanzu bata sanni ba, ina so ta sani. Duk lokacin da ta sani zan ƙyale ta, ni ban ɗauko ta dan cutarwa ba."

Jafar ya ce, "wallahi zan faɗawa Mamy, ɗazu dai ban faɗa mata ba, amma in na tabbatar baka ƙyale ta ba wallahi sai na faɗa mata. Tunda baka jin magana, in ita ta yi maka magana zaka ji ai" yana gama faɗar hakan ya kashe wayar.

Ya bi wayar da kallo yana taɓe baki ya ajjiye ta a gefe yana rufe ido.

Tunda suka taho wajansa da Shams gabanta yake faÉ—uwa, girman gidan ma tsoro yake bata, bata tsaya tana kallo ba dan ba kallo ne a gabanta ba.

A hankali take tafiya har suka ƙarasa babbar ƙofar, Shams ya nuna mata ya ce, "in ki ka shiga yana falo a zaune."

Ta É—aga kai ta ce, "na gode."

Bai amsa ba ya juya ya fita, ita kuma ta ƙarasa wajan ƙofar a hankali.

Ƙofar a buɗe take, ta tura a hankali sanyi da ƙhamshin turarensa da ya gauraye waje ɗaya ya daki hancinta, ta ɗan lumshe ido dan ƙhamshin ya yi mata daɗi, kuma sanyin bai yi yiwa yanayinta yawa ba.

Slowly ta shiga da sallama, tana sake gyara mayafinta dan gani take kamar tsirara ake kallonta.

Ya amsa sallamar a iya laɓɓansa dan bai bari ta ji ba, ta ƙaraso a hankali ta tsaya daga gefe tana ƙarewa falon kallo.

Dakatawa ta yi daga kallon falon, ta kalle sa ganin ya canja shiga ba ta ɗazu bace, yanzu baƙar riga ce a jikinsa mai dogon hannu, sai baƙin jeans da baƙin slippers. Gashin kansa a sake, ya saka har wuyansa.

Ta É—auke kai daga kallonsa, ta É—an sauke numfashi tana tattaro nutsuwar ta gudun kar ya raina ta, ta sauke numfashi tana kallonsa.

Ta daure ta ce, "Ban san sunan ka ba, amma don Allah ka barni na tafi ina da abu mai mahimmaci wanda ban yi ba. Ban ga amfanin ɗauko ni ka ajjiye ni a nan ba, iyayena suna can suna ta nemana cikin tashin hankali. Ban san me nayi maka ba, ban san me na aikata maka ba, ka bar ni na tafi gaban iyayena. Babana bashi da lafiya, za a yi masa dashen ƙoda, ka bari na je a gama ya samu lafiya sai ka sake aikawa a ɗauko maka ni."

A hankali take maganar babu rashin kunya ko tsiwa kamar yadda ta saba, shi kuma jira yake ya ji tace ya yi haƙuri, amma shegen taurin kai ya saka taƙi faɗa. Tana cewa yi haƙuri ko minti goma baza ta sake yi a gidan ba zai saka a mayar da ita, in kuma bata faɗa ba wallahi ta zo gidan kenan.

Ya É—ago ya kalle ta ya ga kanta a sunkuye tana wasa da abin hannunta kamar wata mutuniyar kirki, ta wani nutsu kamar ba ita ba:
Chapter 13 · 0% Book details