Sashe 40
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk suka yi musabaha kafin su fara tafiya ciki a hankali, Labiba ce kaɗai take murna amma Islaha da Umma kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki a haka haka suka ciki.
Basu sha wani wahala ba dan ba kaya ne sosai a ciki ba, aka gama auna kayan aka basu tag aka tafi boarding room. A nan Islaha ta ga akwai banÉ—aki, bata yi duhun kai ba ta yi alwala ta yi sallolin da suke kanta.
Ganin tayi ya saka Umma ma ta yi, suka dawo suka yi jugum suna kallon jirgi ta glass É—in da yake gabansu.
Basu jima ba aka fara shiga jirgi, wanda yake tare da su ya ce, "mu je."
Ba musu suka miƙe a sanyaye suka fita daga wajan suna takawa kamar basa so. Labiba ce take ta video da selfie, su kuwa a hankali suke takawa cikin wani yanayi.
Lokacin da suka shiga jirgi ganin abun suke yi kamar a mafarki. A econamic class suke, kujeru huÉ—u ne, Islaha ce a ciki har ta tana kallon Window. Sai Umma a kusa da ita, sai Labiba sannan shi.
Duk sun yi shiru babu wnada yake magana, Islaha ta kunna data ta turawa Safeera cewa sun shiga jirgi.
Ba jimawa aka rufe jirgi, aka fara yi musu bayanin da komai da komai na mintina ashirin, daga nan aka kunna jirgi ya fara juyawa a hankali. Islaha ta runtse ido lokacin da jirgin ya fara gudu, ta riƙe hannun kujerar lokacin da ya ɗaga ya lula zuwa sararin samaniya, tana ji kamar jirgin ya ɗaga da duk wani burinta na duniya…..
Safe flight mutanen Saudia🙌ðŸ»â¤ï¸
[6/30, 9:54 AM] KRBBK: RDB2P28
Nana Haleema.
Safeera tunda ta koma gida take kuka, ƴan uwan Umma suna tayi mata waya suke yi amma ta ƙi ɗauka, a ganinta babu amfanin ɗaukar tunda dai Umma ta riga ta tafi.
Tana tsaka da wannan tunanin ƙanenta suka dawo, Rukayya ta shigo a hankali ta ce, "Adda Safeera baki da lafiya ki ke kuka?." Jin muryar ƙanwata ya sake karya zuciyar Safeera, ta cigaba da kuka babu ƙaƙƙautawa.
Yaran duk suka zageye ta suna kallo, Ruƙayya ta ce, "Adda ki daina kuka, naga Umma bata nan, bara na faɗawa Baba baki da lafiya" ta faɗa tana miƙewa ta fita.
Babu jimawa suka dawo da Baba, ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallon ta cikin tausayawa sa karayar zuciya ya ce, "Safeera!."
Jin muryar Baba ya saka ta É—ago fuskarta ta yi kaca-kaca da hawaye.
Baba ya bita da kallo ya ce, "ki bar wannan kukan, ki yi haƙuri ki tashi ki rarrashin ƴan uwanki. Ke ce uwa a gare su a yanzu, shigar ki damuwa zai dame su. Ki daure ji kawar da duk abinda yake damun ki, ki zama jaruma ko dan saboda su."
Rukayya cikim mamaki ta ce, "Baba Umma bata nan ne?."
Ya kalle ta ya É—aga kai ya ce, "Umman ku tayi tafiya, kuma zata jima bata dawo ba."
Humaira mai biye mata ta ce, "Katsina ta tafi Baba?."
Ya girgiza kai ya ce, "Umman ku ta É—an yi nisa da ku, zata kwana biyu bata nan. Ku kwantar da hankalin ku, zaku dinga waya da ita in sha Allah."
Rukayya gabanta ya faÉ—i, dan sai take ji kamar Umman mutuwa ta yi ta ce, "Baba ina ta je?."
Ya kalle ta a tausashe ya ce, "kar ki damu, zo ki dafa muku abinci dan ko girki ba a yi ba. In akwai abinda babu ki faÉ—a min sai a siyo."
Rukayya ta fito a hankali ƙannenta suka biyo bayanta cikin damuwa mai tsanani.
Baba ya kalli Safeera bayan sun fita ya ce, "ki bar wannan kukan kar ki jawowa kan ki ciwo, kukan ki bazai saka babar ki ta dawo ba tunda ta yi niya sai ta yi. Ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai faru in Allah ya yarda. Tafiyar ta babu abinda zata rage daga cikin farin cikin gidan nan, dan ta tafi ba hakan yana nufin mun daina walwala da farin ciki ba, zamu cigaba da yin komai kamar yadda muka saba in sha Allah. In kina zama a haka ya ƙannen ki zazu kasance? Ke kin samu sallama da ita, su kuwa basu san ma zata tafi ba sai yanzu."
"Rukyya zargi take yi kamar babar ta ku mutuwa tayi aka ɓoye musu. Sai kin saki jiki kina walwala sannan suma zasu sake, in kina a cikin damuwa suma zasu shiga damuwa. Ke ce babba, duk halin da suka ganki a ciki suma a ciki zasu kasance.
Safeera ta goge hawayenta ta ce, "To Baba."
"Mun yi waya da mutanen Katsina, sun ce suna ta yi miki waya bakya É—aukar wayar. Ki É—auka ku yi magana, rashin É—aukar wayar zai dame su sosai. Ko kin É—auka ko baki É—auka ba Maimuna ta tafi, gwara ki É—auka ku yi magana dasu."
Safeera ta kuma É—aga kai ta ce, "zan É—auka Baba."
Baba ya ce, "Yauwa. Ki fito wajan Æ´am uwanki ku dafa abinci ku ci, ba sai kun ajjiye min nawa ba, bana jin yunwa. In akwai abinda za a siya sai ki faÉ—a min."
Hawaye ya sake sakko mata, ya bita da kallo ya ce, "ki daina kuka, ki É—auka kamar taje Katsina ta dawo ne, kin ji?." Ta É—aga kai alamun to Baba ya juya ya fita.
Sai da ta jima a zaune sannan ta fito, ta tarar har sun gama jollop ɗin taliya sai ƙhamshi take yi.
Rukayya ta bita da kallo ta ce, "Adda mun gama, kizo ki ci."
Ta girgiza kai tana zama a kan kujera ta ce, "bana ci Ruky, ku ci kawai."
Rukayya ta yi sak tana kallon ta, cikin sanyin jiki ta ce, "Adda don Allah me ya faru?."
Safeera ta lumshe ido ta buɗe ta ce, "Babu komai, ku ci abinci kawai." Rukayya ta zauna suna ci a tray ɗaya, basu jima da fara ci ba Safeera ta miƙe ta shiga ɗaki.
Rukayya ma ta tsame hannunta bi bayanta, ta same ta a tsaye a É—aki ta ce, "Adda don Allah ki faÉ—a min abinda yake faruwa, ki taimaka min ki sanar dani hankalina ya kasa kwanciya wallahi."
Safeera ta kalle ta ta ce, "Rukayya Umma ta tafi saudia aiki, ta bar gidan nan bamu san ranar dawowar ta ba."
Rukayya ta ce, "Yanzu sai da Umma ta tafi?."
Safeera ta É—aga kai ta ce, "Ta tafi Ruky. Ki je ku cigaba da cin abincin saboda su Aysha."
Rahma jikinta a sanyaye kafin ta ce, "To wa ta bari wanda zai dinga kula da Baba?."
Safeera ta ce, "Umma bata yi wannan tunani ba ta tafi. Mu kwantar da hankalin mu, tunda Baba yana nan komai zai zo mana da sauƙi."
"To Adda ta ya hankalin mu zai kwanta kina nan kina nan kuka? In baki kwantar da hankalin ki ba mu ma hankalin mu bazai taɓa kwanciya ba."
Safeera ta yi ajiyar zuciya ta ce, "kaina ne yake ciwo, magani zan sha zuwa anjima zan dawo mu zauna mu yi hira."
"to Adda, Allah ya ƙara lafiya" ta faɗa tana fita a sanyaye.
Ba jimawa ta dawo, ta kalli Safeera ta ce, "Adda Abba na Katsina yana son magana dake."
Safeera ta buɗe iso ta yi mata alama da ta ce bacci take yi. Rukkya ta juya ta fita Safira ta kwanta, bata ga amfanin magana da dangin Umma ba tunda dai Umma ta riga ta tafi balle su dakatar da ita, shiyasa babu da wanda zata yi magana, kowa bata buƙatar magana dashi tunda maganar bazata dawo mata da Umman ta ba.
••••••••
*KING ABDULAZIZ INTERNATIONAL AIRPORT JEEDAH.*
Awansu shida da rabi a sama suna tafiya, Islaha tunda aka tashi bata iya motsi ba, abincin jirgin ma bata iya ci ba, cake kaɗai taci sai ruwa. Ƙarfe shida na safiyar Saudia suka garin Jeddah.
Dukkansu suna bayansa suna tafiya a hankali, sai da suka ƙaraso wajan da za a buga musu stamp sannan ya kalle su ya ce, "ku je ku hau layi, ga wannan ku miƙa musu."
Basu musa ba suka hau layi suna kallon wajan cikin burgewa. Kaf ma'aikata mata ne, wasu sun rufe fuska da niƙab wasu kuma fuskar su a buɗe. Sai larabci suke yi, ga mutane mabanbanta ana ta kai kawo a wajen, komai nasu very neat babu dauɗa ko ƙazanta.
Islaha ta ƙarasa ta miƙa passport ɗinta, matar ta karɓa Islaha ta bugawa Islaha Stamp ɗin shiga Sauida bayan ta yi thumb print, Islaha ta koma gefe ta tsaya tana jira a gama dasu. Ba jimwa suka tafi wajan da zadu ɗauki kayansu.
A lokacin ya kalle su ya ce, "in kuna da kayan siyarwa a cikin jakukunan ku zasu iya ƙwacewa a wajan nan, ku nutsu kawai."
A hankali suka wuce cikin ikon Allah babu wanda aka buÉ—ewa kayan har suka fita dags screnning É—in.
Bayan sun fita ya juyo yana kallon su ya ce, "wannan rumfar zamu shiga, in kuna da kayan siyarwa akwai waÉ—anda zasu siya. In an gama sai mu tafi."
Labiba dai kallon wajan take yi cikin burgewa, mamaki take yi wai itace a ƙasar Saudia cikin garin Jeddah. Larabawa suna ta kai kawo, tana ta jin yadda suke yarensu abin yana sake burge ta. Ta ce, "eh akwai kayan Mama, nima kuma ina da kaya."
Ya nuna musu ciki ya ce, "mu shiga ciki ku huta, sai a siyar da kayan."
Islaha dai ta kasa magana, a sanyaye suka ƙarasa ciki suka zauna. Abinda ya bawa Islaha msmski jin suna ta hausa kamar ba a Jeddah suke ba, sai a lokacin ta lura duk hausawa ne masu zaman can.
Labiba ta kalli Islaha ta ce, "kin ja kin zauna kin yi tagumi, kin san akwai kayan Mama a kayan ki."
Islaha ta sauke numfashi dan ita ta manta, ta buɗe ta ɗauko ta miƙawa Labiba bata ce mata komai ba. Tana ji suna ciniki da mutumin, aka gama aka basa kuɗin, Oga Musa ya ce musu zai turawa Mama naira shi zai riƙe riyal ɗin. A nan suka yi sallar asuba, bayan sun idar basu jima sosai ba suka miƙe suka fito zuwa harabar wajan.