← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 133

Sashe 64

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan ma shawara ce mai kyau. Bayan haka ma akwai abinda nake tunani, amma dole sai na yi bincike na ga ina ta tafi, me ta tafi yi, me ya kai ta garin, yaushe zata dawo?."

"Ka tambayi Salim, na san shi ya san inda take ai."

Ya yi murmushi ya ce, "ta yadda za ki san abun munafurci ne ya ƙi faɗa min, sai ya ce shi bai san inda take ba. Safeera ma da na tambaye ta sai ta ce min ta yi tafiya, nace zuwa ina, wai bata sani ba. Hakan ya jefa min zargi a zuciyata, ya tabbatar min akwai abinda aka ƙulla. Ko dai ba waje na gari ta tafi ba, ko kuma akwai abinda ya faru."

Ummi ta É—an daki table ta ce, "ya kamata ka samo mana inda take, jikina yana bani wani abu akan hakan."

Ya gyaɗa kai ya ce, "dole zan nemo, wannam itace hanya ta farko ta yaƙi da ita. In muka samo labari mara daɗi a kanta, zamu yaɗa sa ya shiga duniya gabaɗaya. Iya wannan zai rage mata farin jini da masoya sosai."

Ummi ta ce, "yaushe zaka nemo É—in?."

Ya bita da harara ya ce, "bana son gaggawa, na ce zan yi ai. Ki tashi ki koma, kar ace muna kulle ƙofa ni dake a office."

Ta miƙe ta ce, "meye in ance ɗin, mun kai mu kulle ɗin ai."

Ya É—an yi dariya bai ce komai ba ta fita. Ya jingina da kujera yana tunanin hanyar da zai bi ya gano inda Islaha ta tafi.

Safeera tana komawa gida ta tarar su Humaira suna nan, ta cire hijjab É—inta, Rukayya ta shiga wajanta ta ce, "Adda Maman su Kausar ta aiko mana da dafaffiyar awara ta ce mu soya. Gata na soya in za ki ci."

Safeera ta murmusa ta ce, "bana jin yunwa Ruky, ki bari sai anjima. Baba ya dawo?."

"A'a bai dawo ba. Nima so nake ya dawo, Maman su Kausar ta ji ina maganar kuɗin handout, shine ta bani kuɗin ta ce na ƙyale Baba ya huta. Kin gansu dubu biyu."

Safeera da mamaki ta ce, "Mamansu Kausar É—in ce ta ba ki?."

Ta É—aga kai ta ce, "itace wallahi."

Safeera ta ce, "Kai hidimar da take yi mana nan ta yi yawa sosai, ta bakin Baba ya kamata ta rage kar ta É—orawa kanta nauyin mu."

Ruky ta ce, "Nima haka na ce Adda, amma bara ya dawo mu ji me zai ce."

Safeera ta É—aga kai ta ce, "bara na É—an huta kafin lokacin sallah. Ko akwai abinda ku ke so?."

Ruky ta ce, "Babu komai Adda."

Safeera ta shiga É—aki ta kwanta sai kuma ya jawo waya ta kira layin Islaha na saudia.

Tana É—auka ta ce, "ki hau whatsapp, yanzu za a janye min É—an katin nawa" tana faÉ—a ta kashe wayar.

Ba jimawa sai ga kiran Islaha video call ya shigo, Safeera ta yi murmushi ta É—auka tana kallon Islaha da take zaune kanta babu É—ankwali tana cin apple.

Safeera ta ce, "Lallai matar nan kina huta, kin ga yadda ki ka ƙara kyau? Ga wani haske, anya larabawa baza su ƙwacewa Hamma ke ba?."

Islaha ta yi dariya ta ce, "ke yanzu kina tunanin akwai halittar da zata iya kasa Hamma? Duk kuɗi da kyaun mutum bazai taɓa kaiwa matsayin Hamma ba"

"Ban da cika baki dai, kar mu ga kin maƙalewa wani balaraben fa."

"Wuce wannan wallahi, Hamma shine farko kuma shine ƙarshe."

"Amma duk da haka kin yi kyau. Waye ya yi miki kitson kan ki?."

"Ni na yi Safeera, ina yi ina kuka saboda sagewar hannu."

"Kema waye ya kai ki, wannan tulin gashin naki mai yawa da tsaho ai tufke shi zai yi miki wahala."

"In san in ina yanayin nan kaina in ba a haka yake ba damuna yake yi wallahi, hasken ma da ki ka ga na yi shine" ta faÉ—a dan bata so su dinga cewa ta yi haske, kar a ga kamar hutawa take yi, ita kuma ta san wahala take sha.

Nana Haleema.
[7/7, 6:26 PM] KRBBK: RDB2P44
Nana Haleema.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L

Safeera ta yi dariya tana kallon Islaha ta ce, "ashe period ki ke yi, to a kan wa ki ka sauke kwandon masifar da ki ka saba?."

Ta É—an yi dariya ta ce, "ni kaÉ—ai na dinga ihu a kitchen, har sai dai mai gidan ya zo yana tambayar lafiya."

Safeera ta yi dariya ta ce, "duk abinda period yake sakawa ban yarda da gaske bane sai a kan ki, in aka faɗa gani nake ƙarya ne, amma a kan ki na yarda. Ya yi spoiling mood ɗin ki, ya canja ki, ki sake komawa masifaffiya daman kuma itace, ya saka ki haske, ya saka ki ciwo, ki zama lazy, ki zama mai rigima......Kai Hamma zai yi fama, Wannan watan waye ya dinga rarrashin ki to?."

"Dallah can ban sani ba. Kin san me?."

"Sai kin faÉ—a."

"yanzu na gama waya da Hamma, ya yafe min mun koma kamar da. Yana ta jaddda min kar na yi abinda zan bashi kunya, na cigaba da riƙe kaina kamar yadda na saba. Ya ce da zarar ya samu kuɗi zai biya su Mama kuɗin da suma kashe a kaina, zai siya min ticket na dawo. In ya so sai mu je a bawa wanda na ɗaukowa kuɗin haƙuri."

Safeera ta ce, "Ke hankalin Baffa ya tashi, ga ciwo ga damuwa, Baffa harda hawaye akan ya ji kin bar ƙasar."

"Allah sarki Baffa, yanzu zan kira Hamma na ce ya bani shi mu gaisa."

"Yana sonki wallahi, yana jin ki kamar Æ´ar cikinsa. Kuma ya san duk gwagwarmayar kin yi ta ne saboda shi."

Islaha ta ce, "ya cancanta ne, riƙe ni ya yi kamar ƴar da ya haifa, ya bani tarbiyya da ilimi."

"Haka ne kam. Allah ya sa ki dawo nan da lokaci kaÉ—an. Kin san hankalin Æ´an da toron guiwa ya tashi, Æ´an commentse section sun buÉ—e wuta su in ba ke ba zasu daina bibiyar mu."

Islaha ta yi siririyar dariya ta ce, "Yanzu Hamma ya bani labari. Ni ban ma duba ba."

"Hankalin Chairman ya tashi, ya ce daga tafiyar ki zuwa yanzu an rasa followers masu yawa, ina ga in aka kwana biyu?. Don Allah shi dai na yi convencing É—in ki ki dawo."

Islaha ta sake yin dariya tana saka hularta ta ce, "na yi kewa sosai."

Safeers ta ce, "ni sai nake ganin me zai hana baza ki ƙirƙiri wani program ba, ki samu topic ki dinga magana a kansa don wayar da hankali. In ya so sai ki yi amfani da sunan tv da kuma logon mu, ki yi video ki watsa. Hakan zai saka a cigaba da ganin fusksr ki, kuma baza a yi saurin mantawa dake ba."

Islaha ta ce, "ina naga cikakken lokacin da zan yi?."

"Za ki samu, kamar yanzu da ki ke zaune za ki iya saka camera a gaba ki ɗan wayar da hankali koda na minti biyar ne, yadda Allah ya saka miki kalaman hikima akan harshen ki yanzu za ki ga kin faɗi abu mai mahimmaci. Don Allah ki yi Islaha, rashin ganin ki zai iya taɓa carrier ki, in ana ganin ki akai akai baza a manta dake ba."

Ta sauke nunfashi tana shafa fuskar ta ce, "zan yi shawara da Hamma, in ya bani dama zan yi Safeera."

"To matar Hamma.."

Islaha ta zuba mata ido ta ce, "Safeera meyasa har yanzu ba ki yi magana da Umma ba?."

Ta kalli Islsha ta ga yadda ta mayar da fuska irin babu wasan nan. Safeera ta yi dariya ta ce, "to tsoron ki zan ji? Wannan haÉ—e fuskar na meye?."

"Ki amsa min kawai."

"Islaha Umma zubar damu tayi ta tafi wata ƙasar neman kuɗi, mahaifinmu ya sake ta saboda hakan, bata saduda ba ta girgije mu ta yi tafiyarta. Neman ta ɗin me zan yi?."

Islaha ta ce, "Mahaifiyar ki ce fa, ko me ta yi miki bata cancanci ki watsar da ita haka ba. Ta damu da rashin magana dake, da mu ka yi waya sai jaddda min take yi don girman Allah na taimaka na saka ku yi magana. Safeera ki ajjiye wannan ciwon da ki ke ji a ranki, ki yi magana da ita, tana son jin muryar ki, don Allah ki yi magana da ita."

"Islaha zafi nake ji a raina, in na tuna ta zaɓi duniya akan mu da mahaifin mu."

"Ke kina da mahaifiyar da zata so ta ji maganar ki, ni kuwa bani da ita. Ban san kowa nawa ba, suna nan ko basa nan ban sani ba. Na tashi cikin marayu, na tashi cikin maraici, ban san kowa na sai Maman da ta raine mu a gidan. Wani lokacin ina ji kamar ina tuna mahaifiyata, amma sai naga kamar a mafarki ne ba gaskiya ba...."

"Nima da da tana nan da ban zo inda nake yanzu ba, da tana tare da ban fuskanci ko wacce matsala ba balle har a ɗauke ni......Safeera! Dan ba ki san abinda nake ji bane a duk lokacin da nake jin kewar iyaye, ke ga ki kina tare dasu suna so ki yi magana amma kin ƙi."

Ta share hawayen da ya zubo mata ta ce, "Safeera ki manta da Umma ta bar ku, ki yi magana da ita matsayin ki na Æ´ar cikinta."

Safeera jikinta ya yi sanyi, tausayin Islaha ya mamaye nata zuciya. Ko sati uku bata yi babu mahaifiya ba, amma ita kaÉ—ai ta san kewar ta da take ji a ranta. To ina ga Islaha da ta rabu da ta ta tun tana yarinya? Ta rayu tsahon shekaru babu ita, kuma bata san inda take ba, bata da tabbacin akwai wanzuwar mahaifiyar ta ta a duniya, wani lokacin tana jin abin a kamar a mafarki. Tabbas Islaha itace ta san meye kewar iyaye.
Chapter 64 · 0% Book details