← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 133

Sashe 88

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin bababr Æ´ar gidan ta zo wajan, Umma ta ce, "Islaha ki yi mata bayani da turanci, ki mata ke Æ´ata ce, kin zo ki ganni ki koma."

Islaha ta kalli yarinyar ta ce, "Mamana ce, na zo na ganta na koma."

Yarinyar ta taɓe baki ta ce, "to ai kin ganta ko? Sai ki koma gida."

Islaha ta haÉ—e rai ta ce, "Ba yanzu ba, ina so mu gaisa kafin na koma."

Yarinyar ta faÉ—awa babarta abinda Islaha ta ce, sai kuwa ta fara zazzaga bala'i da larabci.

Umma ta kalli Islaha ta ce, "ki yi haƙuri, haka suke da wannan tashin hankalin wallahi, gabaɗaya ruɗa ni suke yi, na rasa ya zan yi."

Islaha ta ce, "ke zan bawa haƙuri Umma, na zo na jawo miki faɗa."

"Wannan ma kaÉ—an ki ka gani, shekaean jiya wannan budurwar marina ta yi."

Islaha ta zaro ido ta ce, "Mari Umma?."

Umma ta ce, "Mari Islaha, mu je na kai ki É—aki kafin na gama aiki."

Islshs ta ce, "mu je na ta ya ki."

"Aa, mu je ki huta dai."

"Zan ta ya ki Umma."

Suna tsaye suna kallon su, kamar yadda basa jin me su Umma suke faÉ—a haka suma basa jin me suke faÉ—a, amma kowa ya san maganar juna suke yi.

Zasu wuce kitchen matar gidan ta tare hanya ta hana Islaha wucewa, Islaha ta ce, "ki je Umma, zan jira a nan."

Umma ba dan ta so ba ta wuce kitchen, su kuma suka bar wajan ana bin Islaha da kallo kamar sun ga wata dabba a gidan zoo.

Ita ba ta su take yi ba, tunanin yadda Umma ta rame kawai take yi, gashi dai da hijjab a jikinta amma ta ga ramar da ta yi, ramar ta yi yawa sosai. Ta É—an jima a zaune kafin su bar wajen, Islaha ganin basa nan sai ta bi Umma, ta same ta a tsaye a gaban kayan wanke wanke tana wankewa, ga girki a kan stove.

Islaha ta ce, "Umma kawo na yi miki wannan, ki ƙarasa girki."

Umma ta kalle ta ta ce, "kar ki damu, na saba da haÉ—a aiki."

Islaha jikin ta ya yi sanyi ta ce, "Tunda na zo zan ta ya ki Umma."

"A'a Islaha, daga Jeddah ki ka zo, baza ki yi aiki ba."

"ai ba a mota na zo ba, jirgin ƙasa na hau."

"Duk da haka, ki huta."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, sai ji ana kiran sallah, ta kalli Umma ta ce, "Zan yi Sallah Umma."

Umma ta tsame hannunta ta ce, "mu je na raka ki É—akin sallar."

Suna fitowa suka tarar da matar gidan da yaran gidan suna tsaye suna jiran su, Islaha ta É—aure fuska tana bin su da kallo dan hauka hauka zata yi musu, baza ta bari su latsa ta ba wallahi. Suna wucewa Umma ta ce, "Ikon Allah, na yi mamaki da basu rufe mu da duka ba."

Islaha ta ce, "hauka za ki dinga yi musu Umma, in ki ka zuba musu ido raina ki zasu yi. In ni ce a gidan nan da yanzu na gyara musu zama Umma, sai dai na ƙare a gidan yari.”

Umma ta cire hijjab jikinta ta ce, "ga hijjab ki yi sallar, ni bani da lokaci yanzu, sai zuwa anjima."

Islaha ta ce, "mayafina ma zai yi sallah. Amma Umma na ga kin rame sosai, rashin lafiya ki ka yi haka?."

Umma ta ɗn murmusa ta ce, "na yi ciwon dai na warke, sannan...." Ihun matar gidan da ta ji  ya saka ta ce, "zan dawo Islaha, ki yi haƙuri ban ba ko ruwa ba, ina zuwa" ta faɗa tana fita ita dai Iskaha ta bita da kallo ganin duk ta firgice.

A nan ta yi alwala ta shiga wajan ta yi sallah, bayan ta idar tana zaune tana jiran Umma amma shiru babu labarinta.

Islaha ta miƙe ta fito ta tarar da Umma tana share falon, tana sharewa yarana suna marmasa cake, haka zata dawo ta sake bi ta sharewa.

Duk ta yi wujiga wujiga, sai kuma ta ajjiye ta koma kitchen tana duba abinci. Ta dawo sai ga babbar budurwar da kayan wanki ta watsawa Umman, Umma ta tattare ta shiga laundry room lafin ta fito.

Daƙyar Umma ta samu lokacin sallah, tana idarwa ta kalli Islaha da take kallon ta ta ce, "ba ki sha ruwan ba."

Islaha cikin tausayin halin da Umma take ciki ta ce, "Umma haka ki ke shan aiki a gidan nan?."

Ta sauke numfashi ta ce, "kaÉ—an ma ki ka gani Islaha, komai ni ce, babu abinda aka É—auke min a gidan nan. Bara na kawo miki abinci."

Islaha ta ce, "a'a Umma, wucewa ma zan yi ba sai na ci ba, amma ke ki samu ki ci."

"ina na ga lokacin cin abinci? Tun dafe har dare aiki nake yi kamar agogo. Kalli ki ga" ta faÉ—a tana nuna mata hannunta.

Islaha ta ga hannun Umma duk ya yi wani iri, ta ce, "wanki ne, kin ga dai akwai injin wanki ko, to bashi da amfani, dan dauÉ—ar kayansu sai na saka hannu."

Islaha ta ce, "Amma wallahi wani abun ki dinga ƙin yi, ki dinga yi musu wuta wuta da yaren ki yadda baza su gane ba, zasu dinga shakkar ki."

"Islaha ni zaman ma ya ishe ni, ki dinga yi min addu'a Allah ya kawo silar da zan koma na ƙasata na rungumi yarana. Na watsar dasu a can ban san halin da suke ciki ba, na zo nan na rungumi na wasu ina yi musu bauta. Na bar mijina a Nigeria, na zo ina yiwa mijin wata bauta. Bauta na ke yi a gidan nan ba aiki ba Islaha, bani da banbanci da baiwa. Gashi basa wani damuwa da bani da lafiya sai sun ga dama, ni zan siyi magani na yi jinyar kaina, shiyasa ko bani da lafiya bana faɗa, sai dai na ɗauki ƴan kuɗi na siyi magani. Ga kuɗin babu yawa, gabaɗaya riyal ɗari nake tsira da ita, ɗari biyar ɗin kuɗin ta su Maman Saheer ce."

"Riyar É—ari shida suke ba ki? Aka ce riyal dubu?."

"Roman ba ka ne Islaha, ƙarya ce wallahi. An zuga ni na zo naga duk abinda aka ce ba haka bane. Na zo da niyar na tara kuɗi, amma har yau ban tara riyar ɗari biyar ba. Masifar da nake ciki a gidan nan yawa ne da ita, gwara na koma gida na bawa kowa haƙuri, na riƙe ƴaƴana."

Jikin Islaha ya yi sanyi matuƙa, cikin tausayin Umma ta ce, "Allah zai kawo mafita Umma."

"Allah ya kawo Islaha. Ke kam daga ganin ki an san bakya shan wahala."

Islaha ta ce, "gaskiya bana shan wahala Umma, inda nake aiki basa bani aiki mai wahalar naki, dan bai kai rabin wannan ba, kuma mu biyu ne. Sannan suna da kirki akasin naki, ranar da na samu attack har asibiti suka kai ni da kuɗinsu, yanzu ma da na ce zan zo madina, kuɗin ticket ɗin da na zo nan sune suka biya min. Kuma akwai maƙotansu ina shiga ina aiki, kyautar kuɗi kawai mai gidan yake bani ba albashi ba."

Umma ta goge hawayen da ya sakko mata ta ce, "Kin ji daɗin ki. Ni nan abubuwan sun yi yawa, da girmana amma ban wuce wulaƙanci ba. Babban abinda yake ɗaga min hankali bai wuce mai gidan nan ba, nemana yake yi Islaha.....!" Ta faɗa tana kuka.

Islaha gabanta ya faɗi sosai, Umma ta cigaba ta ce, "kwanaki da suka wuce na yi masa barazana da police ya daina, amma a yanzu ta kai ta kawo in ban rufe ƙofata ba sai dai na ji shi a kusa dani. Babu damar na shiga ɗaki sai ya biyo ni, sai dai ina shiga na kulle, in ba haka ba ya farmin."

Islaha ta ƙame ƙam ta buɗe ido waje cikin mamaki, hawaye suka taru a idonta ta ce, "Umma!." Sai ta kasa faɗa ta fara kuka.

Umman ma tana kuka ta ce, "bai taɓa sanun nasara a kaina ba, kuma Allah bazai bashi iko ba….” Umma ta faɗa cikin kuka mai tsuma zuciya.

Nana Haleema.
[7/17, 7:20 PM] KRBBK: RDB2P64
Nana Haleema.

Islaha ta rungume Umma tana kuka sosai, dan bata taɓa jin abinda ya tayar mata da hankali kamar wanann ba. Mace kamar Umma ace wani namijin yana ƙoƙarin yi mata fyaɗe? Uwa kamar ta, wacce take ƙoƙarin kare mutuncin ƴaƴanta, amma ace ita da kanta wani namiji yake ƙoƙarin haike mata?.

Shine abinda ya saka Islaha kuka, Umma tana shafa bayanta ta ce, "ki yafe min da ƙiyayyar dana nuna miki, ki yafe min Islaha. Na nuna bana sonki ba don kin yi min komai ba, yanzu ga shi kece ki ka ɗauko ƙafa tun daga Jeddah ki ka zo madina da ki ganni. In ban da naka waye zai yi maka haka? Sai mai ƙaunar ka."

Islaha ta É—ago tana kuka ta ce, "Umma ki zo ki bi ni kawai, bazan iya barin ki a wannan halin ba."

Umma ta girgiza kai ta ce, "in bi ki na je ina? Gwara na zauna a nan ɗin, na gama haɗa musu kuɗinsu, daga nan sai na gudu na kai kaina wajan ƴan sanda nace a dawo dani ƙasata."

Islaha ta ce, "yaushe za ki tara kuÉ—in Umma?."

"Nima ban sani ba Islaha, kawai ki ta ya ni da addu'a."

Islaha ta ja numfashi ta goge idanunta ta ce, "Allah yana tare dake Umma."

Umma ta ce, "kar ki faɗawa Safeera, duk da fushi take yi dani, amma hankalinta zai tashi in ta ji ana ƙoƙarin keta min haddi."

Ta É—aga kai ta ce, "ba fushi take yi ba Umma, kewar ki take yi."

"In fushin ta yi ma bata yi laifi ba Islaha, tsallake su na yi na taho nan, sai gashi ina yiwa wasu bauta na bar nawa."

"Umma ga lamabar ƴan sandar ƙasar nan, da zarar ya sake zuwa inda ki ke ki nuna masa lambar, zai tsorata bazai sake yi miki ba."

Umma ta kalla ta ce, "bara na saka a wayata, dan in abin ya ci tura kiransu zan yi."
Chapter 88 · 0% Book details