Sashe 10
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Throw the vein ya yi mata pcm ya haɗa mata da allurar bacci, ya miƙe yana kallon ta yana taɓe baki. Shi ba dan ta suma ya ɗauko ta ba, ya ɗauko ta saboda dalilinsa amma ba dan ta yi rashin lafiya, wannan dalilin shine ya saka ya tsaya ya taimaka mata, kar ta mutu a hannunsa.
Ya É—an ja tsaki yana kallonta, yana tuna abinda ta faÉ—a masa sai kawai ya fita daga falon bai ce komai ba.
Wayar sa ya É—auka ya shiga camera record É—in gidan yana kallon yadda aka shiga da ita falon, tun lokacin da suka ajjiye ta da haukan da ta dinga yi. Da lokacin da ta tashi sallah, ta shiga ciki ta yi alwala ta fito ta yi sallah ta dawo.
Yana ganin faÉ—an su da Shams da duk abinda ta ce, ya yi murmushi yana girmama girman taurin kai da rigima irin ta yarinyar.
Ya sake dawo da inda take yiwa Shams Allah ya isa, ya sake yin murmushi yana shafa kansa ya girgiza kai ya ce, "Za ki ba da labarin waye Rehaan, daga wannan lokacin baza ki sake cewa waye ni ba. Babu inda zaki je sai na ga dama, kuma babu wanda zai san kina nan. If i like, zan bar ki ki shekara a nan, babu abinda aka isa ayi min" ya faÉ—a yana fita daga record É—in, sai kiran Jazy ya shogo wayarsa.
Kamar bazai É—auka ba sai kuma ya É—auka, Jazy ya ce, "Ray wacce yarinya ce a guest house?."
Ray ya É—an yi tsaki ya ce, "ni bani da pravicy ne? Komai sai ka sani?."
Jafar ya ce, "ka bani amsa kawai, wacce yarinya ka sace?."
"Bai shafe ka ba."
"Ya shafe ni malam, ka faÉ—a min ko in kira Mamy na faÉ—a mata ka fara kawo mata gidan ka."
Ya É—an yi tsaki ya ce, "ina ruwanka da sanin wacece?."
Jazy ya ce, "ya zama dole na sani, ina so na san yaushe ka samu gut É—in kawo mata gidan ma? Yaushe ka samu courage na fara aikata wannan shirmen?. Infact me ka É—auko ta ka yi da ita?."
"Ciki, ko ban kai nayi bane?."
Jazy ya yi dariya jin amsar da ya basa, duk da ya san Rehaan ba mutum ne mai dirty talks ba, tunda ya faÉ—a ya san yana da dalilin sa. Jazy ya ce, "ka kai ka yi ciki, kana da lafiyar da a rana zaka iya yiwa mata goma ciki. Dan ka kawo ta dan ka yi mata ciki tsaf zaka iya."
Ray ya yi banza bai amsa ba, Jazy ya ce, "i'm not joking Ray. Wacece yarinyar da ka saka a ka É—auko maka?."
"Wata ce."
"me zaka yi mata?."
"ba ka ce na fara iskanci ba? Ciki zan yi mata."
"Ray ba wasa nake yi ba, ka faÉ—a min."
"Nima ba wasa nake yi ba."
"Please."
"Kana magana kamar wani Yayana, ka yi magana a tausashe mana, ka daina É—aga min murya."
"Okay my bad. Wacece?."
"She is the girl from that hotel, she is the one I told you to find for me."
Jazy ya ce, "Okay ina jin ka, itace wacce ka ke nema. Meye na É—auko ta? Me zaka yi mata?."
Rehaan ya ce, "I brought her here so she would know who I am. She always keeps asking who I am. I want her to know who Rehaan is."
"is that all? Shikenan dalilin naka?."
Ya yi masa banza bai amsa ba, Jazy ya ce, "wannan shine dalilin da zai saka ka É—auko yarinya daga gaban iyayen ta? Ka san halin da iyayenta zasu shiga saboda raahinta?."
"Ina ruwana da iyayenta? Ni abinda yake gabana kawai na sani. Ina so na tabbatar mata da ni waye, ina so ta san ina da ikon da zan yi mata duk abinda naga dama babu wanda ya isa ya hana ni."
Ya ɗan dafe kai yana lumshe idanunsa ya ce, "Ina so ta san zan iya barinta over a year a nan babu abinda zai faru, ina so ta san in na kashe ta na kashe banza!....." ya ƙarasa faɗa cikin sanyi.
Kafin Jazy ya ce wani abu Rehaan ya ce, "Yadda take a gidan nan, in na so a ciki zan yi nata kabarinta babu wanda zai san tana ciki. Who is she? Ta san waye ni? Ni take kallo tana faɗawa maganganu marasa daɗi, kuma sai na zuba mata ido ina kallonta?!" Ya faɗa cikin fusata, amma da yake muryar ƴan gayu ce dashi in ba sanin halinsa ka yi ba baza ka taɓa cewa faɗa yake yi ba.
Jazy jin yadda yake faɗa ya san ransa ya ɓaci akan abinda yarinyar ta yi masa, kuma tunda har ya ɗauki mataki abin ya taɓa ransa sosai.
Ya san shi mutum ne wanda zaka zage sa a gaban idonsa ma ya ɗauke kai kamar bai ji ba, bai cika mayar da ƙarami abu babba a wajansa ba. Yana da haƙuri da kawar da kai, duk abinda zaka yi masa sai ya ga dama zai ɗaga kai ya kalle ka, kawai baya so ka shiga rayuwarsa, yadda bai shiga taka ba, kaima ka ka shiga tasa.
Tunda ya ji ya fusata har ya yi hukunci ya san ta taɓa masa rai, kuma ya yi mamaki sosai. Dan karo na farko kenan da wani abu ya taɓa haɗa sa da wata mace har ya yi mata irin wannan hukucin. Ray ba shi da saurin fushi ko kaɗan, yana da haƙuri, yana da kawaici, amma in ya yi fushin sai ka gwammace bai yi ba.
Jazy ya ce, "kwantar da hankalin ka Ray, na san ta ɓata maka rai, amma meye na sakawa a ɗauko yarinya ƙarama don Allah?. Wannan ba girmanka bane, in sunan ka ya fita a kan wannan lamarin ka san abinda zai faru ko?."
"So what? Babu wanda ya isa ya yi min wani abun, kaf danginta babu wanda zai iya ja dani. In na kashe ta na kashe banza, haka zan binne a nan, ta ko na bawa kare ya cinye namanta."
"Amma haƙƙinta ai yana kanka, shi kuma akwai wanda zai rama mata ko?."
Ray ya yi masa shiru bai tanka ba, dan ko me Jazy zai ce wallahi bazai bar Islaha ba sai ya ga damaX Jazy ya ce, "don Allah ka ƙyale ta tayi tafiyar ta. Wannan abun ba girman ka bane wallahi, ka ƙyale ta rashin sanin waye kai ne ya saka ta yi maka rashin kunya har ta ce waye kai, amma nan gaba ko kuɗi aka bata akace ta yi baza ta yi ba. Please, allow her to go."
Ray ya yi tsaki ya ce, "So is that all you have to say to me? Should I hang up now?."
Jazy ya ce, "calm down Mr Ray, don't do anything that will ruin your reputation, don't smeer yourself with black paint. Don Allah, ka ƙyale ta ko dan iyayenta, na tabbatar suna can gida suna nemanta. Ko Mamy in ta ji ka ɗauke yarinyar mutane kawai dan ka nuna mata who you are zata yi maka faɗa."
Ray ya É—an yi shiru kamar ya ji nasihar, sai ya kuma yin tsaki ya ce, "i don't have your time" yana faÉ—a ya kashe wayar ya cillar da ita gefe yana shafa fuskarsa da hannayensa, yana ji kamar a lokacin take yi masa rashin kunya, ya yi alwashin sai yarinyar ta san waye shi kamar yadda take tambaya.
Babu wanda ya taɓa kallonsa ya ce masa waye kai, a ko ina girmama shi ake yi in yaje waje, kafin ya je sunansa ya riga shi zuwa. Amma sau biyu suna haɗuwa tana raina masa hankali, in ya ƙyaleta ma ai bai nuna mata capacity da yake dashi a Nigeria ba. Zai nuna mata yana da ikon da zai saka a ɓatar da ita gabaɗaya, kuma in ta ɓata ta ɓata kenan har abada, ko cigiyar ta baza a sake yi ba.
   ******
Sadik yana komawa asibiti bayan sallar magrib Mama da Adda Sa'ida da Labiba suka fito daga reception zuwa waje.
Adda ta ce, "Sadik ya labarin Islaha, an ganta ko an samu labarinta?."
Ya É—an yi shiru yana girgiza ka ya ce, "wallahi babu labari Adda. Kawai an samu wani ya faÉ—a yadda abin ya faru, ya tabbatar mana da É—auke Islaha aka yi."
Adda ta ce, "innalillahi! Aka É—auke ta Sadik?."
Ya É—aga kai ya ce, "tabbas, a gaban asibitin nan kaÉ—an aka yi garkuwa da ita."
Mama jikinta y yi sanyi matuƙa, ta kalle sa ta ce, "yanzu me ƴan sandan suka ce?."
"Sun bamu tabbacin za a yi bincike, duk abinda yake akwai zamu ji. Yanzu muna jira mu ji ta inda za a ɓullo, in an yi waya an nemi kuɗin fansa to masu garkuwa da mutane ne, in ba ayi waya ba kuma wani ne ya ɗauke ta bisa dalilin kansa."
Adda ta ce, "daman islaha ta tara maƙiya akan aikin jaridar nan da take yi, wataƙila ta tsayawa wani ko wata a rai."
"tabbas kuwa, dan har an kama mace ɗaya, wata yarinya ce da ta yi iƙirarin sai ta ga bayanta."
"Ka ji ko? Kai innallahi wa'inna ilaihir raji'un!. Saheer ya sani?."
"Ya sani, mun yi dashi da gobe zai taho ma, to na ga gwamnatin ƙasar ta hana kowa fita saboda matsalar tsaron da ake samu, kin ga shima an rufe dashi sai lokacin da suka buɗe zai samu damar fitowa."
Labiba ta ce, "Allah ya bayyana Islaha."
Suka amsa da amin duk jikinsu ya yi sanyi, Mama da bata ƙaunarta ita kanta ta ji babu daɗi jin an yi garkuwa da ita, abin bai yi mata daɗi ba ko kaɗan.
Adda ta ce, "ya batun kuÉ—in aikin Baffa? An dace?."
"Wallahi ɓatan islaha ne ya ɗauke min hankali, amma in Allah ya amince za a dace, komai zai zo da sauƙi in sha Allah."
Adda ta ce, "Allah ya sa. Nima zan turo maka wani abu da yake hannuna, sai a san abinda za a yi."
Ya ɗaga kai kawai bai ce komai ba, dan jikimn a sanyaye yake akan ɓatan Islaha, ganin abin yake yi kamar wasa.