Sashe 28
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na jira ki kenan?."
"Eh, zan zo mu tafi."
"Allah ya kaimu. Ni zan wuce." Islaha ta miƙe ta rako ta har bakin gate jikinta a sanyaye.
Safeera zata yi magana Hamma ya shiga gidan, bai ce musu komai ba ya wuce ya shiga ciki. Islaha ta bi sa da kallo har ya wuce, sannan ta kalli Safeera ta ce, "fushi yake yi Safeera, ban san me zan faÉ—a masa ba."
Safeera ta ce, "ki bashi haƙuri kawai."
"Bazai haƙura cikin sauƙi ba wallahi, sai yaji dalilina, kuma kin san bazan faɗa ba."
"Ki gwada."
Ta sauke numfashi sannan ta ce, "ki gaida Umma." Safeera ta É—aga kai ta fita daga gidan ita kuma ta koma ciki a sanyaye.
Da ta koma abinci ta tarar suna ci, bata ce komai ba ta wuce ciki ta zauna ta zabga tagumi, ta rasa abinda yake yi mata daÉ—i. Har lokacin bata yarda sata tayi masa ba, ita aro ta É—auka. Dole ta bisa kuÉ—insa, dan ta san nauyin bashi akan mutane.
Nana Haleema.
[6/24, 11:32 AM] KRBBK: RDB2P19
Nana Haleema.
Rehaan yana tsaye sun gama sallama da Abba ya shiga wajan Mamy, ya tsaya yana jiran fitowarta dan bazai shiga É—aki ba, in ya shiga zama zai yi. A lokacin ta fito ta bi shi da kallo ta ce, "Baby sai Jeddah?."
Ya É—aga kai ya ce, "in sha Allah Mamy."
Mamy ta yi murmuahi ta ce, "Allah ya kiyaye hanya."
"Amin Mamy. Ina suke?."
Kafin Mamy ta ba shi amsa ƙannensa suka fito, suka ƙaraso wajansa ya riƙe hannun Banisha ya ce, "i promise zan turo a ɗauke ki, ki zo ki yi one week ki dawo."
Ta yi murmushi ta ce, "Okay, Safe trip my love."
Ya yi pecking goshinta ya ce, "thank you my love."
Ya kalli Riyya da ta sunkuyar da kai ya ce, "are you Okay?."
Mamy ta ce, "wai tayi maka milk cincin ne, tana tsoron kar ta baka ka sake cin poison."
Ya É—an murmusa ya ce, "com'on Riyya, kawo min kawai."
Ta juya a sanyaye ta kawo masa, ya buÉ—e ya É—auki É—aya ya ci sannan ya ce, "ki kai wa Shams ki ce ya saka min a cikin box."
Ta karɓa ya ce, "thank you Riyya."
"Zamu yi kewar ka."
"Nima zan yi kewar ku."
Ya ƙarasa ya rungume Mamy ya ce, "Mamy sai na dawo."
Ta shafa kansa ta ce, "Allah ya kiyaye min kai Babyn Mamy, Allah ya baka nasara a duk inda ka ke."
"Amin Mamy" ya faÉ—a yana raba kansa da ita ya fito zuwa inda motarsa take.
A lokacin Mamy ta ce, "ka yiwa sauran iyayen ka sallama ne?."
Ya É—an yi shiru alamun bai yi ba, Mamy ta ce, "bai kamata ba, ka je ka yi musu sallama."
Ya ɗaga kai ya riƙe hannun Banisha, Riyya tana bayansa suka nufi bangaren Mama.
Ita da babban ɗanta suka same ta, sai Sameer da Janna da suke zaune. Ya shiga da sallama suka amsa, ya ƙarasa ya ce, "Mama zan tafi Jeddah."
Ba yabo ba fallasa ta ce, "a dawo lafiya." Ya É—aga kai ta kalli babban yayyansu ya ce, "Sai anjima Hamma."
Ya kalle sa ya ce, "Allah ya kiyaye Rehaan."
"Amin."
Ya kalli Sameer da ya wani haÉ—e rai kamar bai san shi ba, sai bai ce masa komai ba ya kalli Janan da ta haÉ—e rai ta kawar da kai.
Ya san fushi take yi dan bata san zai yi tafiya ba, ya É—an saki fuska kaÉ—an ya ce, "Little Jan zan tafi?."
Sai a lokacin ta kalle sa, kafin ta yi magana ya ce, "i'm sorry, zo mu je mota." Bata musa ba ta miƙe suka fita tare. Mama ta buga ƙwafa tana gyaɗa kai ta ce, "ayi dai mu gani."
Æangaren Umma suka shiga suka tarar tana gyarawa Salman farcensa. Yana ganin Rehaan ya zabura zai gudu, ta buga masa tsawa ta ce, "koma ka zauna malam, uban ka ne shi da ka ke rawar jiki in ka gan shi?."
Rehaan shi kansa sai da ya tsorata da tsawar da ta yi, bai ce komai ba ya yi mata sallama ya fita zuwa wajan amarya Abba. Bai jima a wajan ta ba ya dawo ya shiga wajan Daada, Allah ya taimake sa ya samu bacci take yu. A bakin mota suka yi sallama da ƙannensa ya shiga mota suka nufi airport.
Motarsa tana fita, wani da yake tsaye a estate É—in gidan ya É—auki waya ya ce, "Motar Rehaan ta fito, kun tabbatar an kwance burkin motar?."
Ya yi shiru alamun ana basa amsa sannan ya ce, "Dakyau, bana so ransa ko lafiya sa ta tsira a wannan lokaci, a tabbatar da ya rasa É—aya daga cikin waÉ—annan."
Ya kashe wayar ya yi shiru yana kallon indai motar Rehaan ta bi. In ba mutuwa Rehaan ya yi hankalin sa bazai taɓa kwanciya ba.
  Rehaan basu yi nisa ba ya ji an tsayar da motar, ya buɗe ido ya ce, "ya dai?."
Shams da yake gaban motar ya ce, "Sir burkin naji yana rawa, shiyasa aka samu aka tsaya a nan.."
"Kamar ya kenan?."
"Bamu san ya aka yi hakan ya faru ba, amma yanzu zan yi waya a kawo mota."
"Alright" ya faÉ—a a hankali yana lunshe idonsa.
Ba jimawa aka kawo wata motar, suka canja mota suka wuce airport tsaye.
Washe gari da safe Islaha da wuri ta shirya dan tana so taje wajan aiki, bayan ta shirya tana falo ta gama shan tea Saheer ya shigo da sallama.
Islaha ta amsa sallamar tana kallonsa, sannan ta ce, "ina kwana Hamma."
Saheer daƙyar ya ce, "Lafiya. Ina Mama?."
"Bata fito ba."
"In ta fito ki faÉ—a mata na tafi wajan Baffa."
"To. Amma wajen aiki zan tafi, nima babu lallai mu haÉ—u."
"Okay" ya furta yana ya fita.
Haka ta gama abinda zata yi a sanyaye, ta fito tana kallon ƙofar gidan cikin tunani. Motar da suka shiga jiya ta gani, bata ƙarasa wajan motar ba, sai da ta kira Safeera take faɗa mata ita ta wuce.
Horn ta ji yana yi mata, ta kalli wajan kafin ta ƙarasa a hankali dan ta san shine ta buɗe ta shiga suka tafi. Ta kalle sa taga ya haɗe rai kamar ba Hammanta mai yawan murmushi ba, ko kallon inda take ba yayi balle ta saka ran zai yi mata magana.
"Kina fama da kanki ki ka saka wannan turaren mai ƙarfi, kin kyauta." Ta kalle sa jin abinda ya ce sai ta yi shiru bata ce komai ba.
Sai da suka tsaya Islaha ta kalle shi taga glass É—in gabansa yake kallo alamun ta fita babu abinda zai ce mata. Islaha a sanyaye ta ce, "Hamma!."
Ya yi mata banza kamar bai ji ba, cikin shagwaɓa ta ce, "Hamma ka yi haƙuri, ka daina fushi dani don Allah." Tsaki taji ya yi bai ce komai ba, ta sake kallonsa ta ce, "Hamma don Allah."
Ya kalle ta ya ce, "bani da mahimmanci a rayuwarki ne kawai, dan haka ki fita ki bani waje."
"ka yi haƙuri" ta faɗa hawaye yana sakko mata.
Bata son fushin Hamma ko kaɗan, matuƙar ya yi fushi da ita to tabbas ta ɓata masa rai da yawa, baya iya fushi da ita sai abin ya ƙure sosai.
Jin tana kuka sai ya sauke ajiyar zuciya, ya É—an tausasa murya ya ce, "in baki faÉ—a min dalilin ki na son a kashe case É—in nan ba bazan saurare ki ba, Islaha."
Ta goge hawayenta bata ce komai ba, ya kalle ta ya ce, "za ki jefa min zargi a zuciyata, zan ga kamar da gagan ki ka gudu daman ba sace ki aka yi ba. Shaiɗan yana faɗa min abubuwa marasa kyau akan hakan, na ƙi bada damar da zan ɗarsa zargina a kan ki, amma in ki ka cigaba da ɓoye ɓoyen nan zan zarge ki Islaha!."
"Wallahi Hamma ban san komai a kai ba, ban san shi ba balle na haÉ—a baki dashi ya sace ni, kuma ni ban aikata komai ba."
"Nima ban ce kin aikata wani abu ba, amma in kika cigaba da ɓoye ɓoyen nan zuciyata zata amince kin yi, ko meye ya ɗarsu a raina zan amince kin aikata!."
"Hamma!."
"Islaha."
"Hammana!."
"Islahaaa!" Ya faÉ—a yana jan sunan yana kallonta.
Ta girgiza kai tana langwaɓar da kai, cikin sanyi ta ce, "Hammana!."
Ya zuba mata ido na wani lokaci kafin ya ce, "Matar Hamma."
Ta lumshe ido hawaye yana cigaba da zuba daga idonta. Ta buɗe ido ta kalle shi ta ga shima ita yake kallo, ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ka bani dukkan yardar ka, wallahi bazan taɓa cin amanar ka ba."
Ya taɓe baki yace, "kina san dawo a dawo bara bana kenan, indai baki faɗa min dalilin ki ba bazan karɓa. Zuciyata zata faɗa min akwai wani abu mara kyau da ki ke ɓoyewa."
"Ina da dalili."
"Am all ears."
"Ka yi min alƙawari zaka saurare ni."
"Ina jin ki."
"Zan faÉ—a maka dalilina, amma ka bani kwana biyu don Allah."
Ya zuba mata idanu yana kallonta cikin mamaki, da gaske zuciyarsa ta fara ɗarsa masa abubuwa marasa kyau, da ya yi tunanin raping ɗinta suka yi, amma yadda take ɓoyewa sai ya ga ba lamarin rape bane, abin ya girmi haka a tunaninsa.
Saheer zai yi magana ta tare shi da sauri ta ce, "don Allah ka yi min wannan alfarmar."
Ya ɗaga kai ya ce, "Allah ya kaimu. Jeki wajan aikinki." Ta ƙi fita, sai da ta tabbatar ya daina fushin sannan ta shiga.
Tun daga gate take gaisawa da mutane har ciki, haka aka cika table É—inta ana gaisawa tana murmushi tana amsa gaisuwa da addu'a.
Bayan mutanen sun watse Safeera da Muslim suks ƙaraso wajan ta, Muslim ya ce, "Islaha ashe mai keken nan ƙoƙarin watsa miki acid ya yi?."
Ta É—aga kai alamun eh, Muslim ya ce, "amma bashi da kirki, nan yazo ya same ni fa ya ce yaga lokacin da aka sace ki, yana so ya ba da shaida ashe shima mugu ne."
Safeera ta ce, "mugun gaske ma kam."
"Kuma wallahi ya gudu, an nemesa an rasa."