Sashe 18
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Ba fa sata zaki yi ba Islaha, kuÉ—in wahalar dake da yayi zaki É—auka, ko banza kin fashe zaman da ya saka ki ka yi ba tare da kin yi masa laifin komai ba. Ki É—auka kawai, ai bai san kin É—auka ba, Allah ya san ba sata ki ka yi masa ba._
Da wannan shawarar zuciyar ta ta miƙa hannunta wajen kuɗin, hannun yana rawa ta ɗauki rafa ɗaya tana juya ta a hannunta. Bata taɓa riƙe dala ba balle rafar ta, sai dai ta ganta a waya ko a wani abun, amma bata san ya take a zahiri ba.
Tsoro ya mamaye ta, ta mayar ta ajjiye tana tunanin abinda ya kamata ace ta yi.
_Islaha in baki É—auka ba a ina za ki sake samu wannan damar? Ki ara kawai, in yaso sai ki biya shi wani lokacin. Ba sata zaki yi ba, aro zaki yi kawai. Bashi ki ka ci, kuma gwamnati ma tana cin bashi, kema dan kin É—auki bashinsa ai ba wani abun bane. Haka kawai ya kawo ki ya ajjiye ki a gidansa, da ya bar ki ai da yanzu kin nemo kuÉ—in. Dan haka ki É—auka kawai, Allah ya san baki da mafita ne._
Da wannan tunanin ta sake saka hannu ta É—auki guda É—aya cikin wani irin yanayi na bugun zuciya.Â
Ta sake mayarwa ta ajjiye tana furzar da iska, ta dafe kai tana tuna yanayin da ta ga Baffa a mafarki, kuma ta san tashin hankalin ɓatanta bazai bari su nemi kuɗin aikin Baffa ba. Kuma ga kuɗi tana gani, in ta ɗauka ma ba sata ta yi ba, kuɗin wahalar da ita da ya yi ne.
Islaha ta sake miƙa hannu ta sake ɗaukar kuɗin, tana kallonsu a hannunta jikinta da zuciyarta suna rawa.
Ta ɗaga kai sama taga cctv tana ɗaukar ta, ta sake ajjiye kuɗin gabanta yana faɗuwa matuƙa, abin ka da baka saba gani ka ɗauka ba, duk ta ruɗe ta firgice.
Sai ta kuma ɗauka kuɗin tana kallon camerar, ta nunawa camerar kuɗin ta ce, "Aron kuɗin nayi, ba satar maka kuɗi nayi ba, zan dawo dasu in na samu. Ni ba ɓarauniya ba ce, ban taɓa sata ba. Wannan ma aro nayi, zan dawo maka dasu duk daren daɗewa..... in ma ban dawo dasu ba, fansar wahalar da ka bani ce."
Sai kuma dafe kai ta ce, "To kuma ai baya jin hausa" ta faÉ—a still tana kallon camerar.
Shams ya leƙo ya katse mata tunani ta ce, "Yar jarida ke nake jira."
Ta zubura tana neman inda zata boye kuÉ—in hannunta, shi kuma bai kawo komai ba dan ya san kaÉ—an daga cikin aikin Rahaan ya bata kyautar kuÉ—in.
A sanyaye ta ɓoye kuɗin a rigarta tana takawa a hankali, sai kuma ta tsaya tana tunanin ta mayar da kuɗin, tana sake tunawa sata ce ba bashi ba, zuciyarta tana sake zugata akan ta tafi da kuɗin kawai ai kuɗin fansar sace ta da ya yi ne. A haka ta saka ƙafa ta fita daga falon.
Ta ganshi a tsaye a jikin range rover baƙa, ya buɗe mata gaban motar shiga, ya zagaya ya shiga suka bar gidan gabanta yana faɗuwa sosai, ta waiwayo tana kallon gidan tunawa da ta bar undies ɗinta a ciki.
_Hmm rashin mafita da neman mafita, ya kan ja mutum ya aikata abinda zai yi danasani. Kamar dai Islaha🥺_
Nana Haleema
09030398006.
[6/19, 5:37 PM] KRBBK: RDB2P12
Nana Haleema.
Tunda suka tafi take kallon hanyar, bata taɓa shiga mota irin wacce take ciki ba, ji take kamar ba tafiya suke yi ba saboda daɗin motar. Abin mamaki sai taji wayar jikinta tana ta ƙara alamun shigowar saƙo. Tana dubawa taga services ɗin wayar ya dawo, abin ya bata mamaki, tana tunanin da gangan aka kashe mata services ɗin wayar kenan. Ta girgiza kai tana jinjina girman makircin mutumin, ta tabbata ba ƙaramin mutum bane tunda ya saka aka kashe mata services.
Tana shiga camerar wayar sai taga ta daina nuna mata blank ta dawo aiki, ta riƙe haɓa cikin mamaki da ɗaure kaita ce, "kai!."
Shamas ya juya ya kalle ta, ta girgiza kai tana kallon inda suke shiga suna fita, wani babban estate ne da dole ya rikita ka in baka san kansa ba, kusan gidajen duk iri É—aya ne, layikan ma duk iri É—aya.
"Ina zan kai ki?."
Ta wani kalle sa, irin kallon ban sani ɗin nan ba ta ce, "inda ku ka ɗauko ni."
Ya yi dariya ya ce, "Ƴar Jarida, kina bani dariya sosai."
Ta girgiza kai ta cs, "na baka dariya a yanzu, da na koma gida kuma zan baka kuka, dan kaine mutum na farko da zan fara kai ƙara, in yaso sai kazo ka faɗi sunan ogan naku a kama shi shima."
Ya yi dariya yana ta mamakin rashin sanin fuskar Ogansa da bata yi ba ya ce, "kina tunanin a ƙasar nan akwai hukumar da zata iya kama sa?."
Cike da gadara ta ce, "Shi ba mutum bane?."
"Mutum ne kamar kowa ƴar jarida, amma yana da ƙarfin ikon da bazai kamu ba a ƙasar nan ba."
"Hmm, za a fara daga kaina kuwa, in ban zama silar kama shi ba kace ba sunana Islaha ba."
Ya yi dariya bai ce komai ba, ƙarfin halinta da rashin tsoronta ya burge shi, sai yake ji ina ma ta shiga harkar tsaro, ta zama jami'a a hukumomin tsaro na nigeria.
Islaha ta kalle sa ta ce, "Kai baka jin tsoron nayi maka hoto na nunawa Æ´an sanda fuskar ka?."
Ya É—an kalle ta ya ce, "wanda ki ka yi min fa? Ko kina tunanin banga kin É—auke ni a hoto ba?."
Ta bisa da kallon mamakin ya aka yi ya gane, ya yi dariya ya ce, "ba zauna gari banza bane ba ni ƴar jarida, na wuce tunanin ki. Kar ki ga ba kallon ki nake yi ba, ina sane da duk abinda ki ke yi." Ba tace komai ba tayi masa banza, sai gani tayi ya tsayar motar a ƙofar gidansu.
Ta kuma kallonsa ta ga É—aure fuska kamar ba shine yake murmushi ba, ya nuna mata gidan ya ce, "ki shiga gida."
Bata ce komai ta buÉ—e ta fita, sai da ta tabbatar ta fita daga motar, yadda ko sake kamata zai yi kafin ya fito ta shiga gida sannan ta ce, "ai daman zan shiga gidan, ba sai ka bani umarni ba. Kuma dukkan ku sai Allah ya saka min, kuma wallahi bazan bar maganar nan ta tafi a banza ba, ku jira na kammala abinda yake gabana ku ga abinda zan aikata. Sai na bawa ogan naka mamaki, sai na saka ya kwana a cell akan case É—in nan. Mu zuba nu gani" tana gama faÉ—a ta bar wajan da sauri ta shiga gida.
Shams ya bita da kallo yana dariya, ya girgiza kai ya ce, "Ko ina Oga ya samo wannan Æ´ar rigimar oho, yarinya kamar mai aljanu? Babu tsoro ko kaÉ—an a idanunta." Yaja motar ya bar unguwar da gudu.
Islaha da sallama ta shiga falo, sai ta É—auke kai ganin abinda yake faruwa a cikin falon. Hanan ce da wani saurayi, tana zaune akan cinyarsa yana bin ko ina na jikinta da kiss.
Ganin Islaha babu zato sai ta zubara ta miƙe daga jikinsa, cikin borin kunya ta ce, "Islaha! Kin dwwo? Su waye suka sace ki?."
Takaici bai bari Islaha ta bata amsa ba ta wuce ɗaki ta kulle kanta. Ta ƙarasa ciki a sanyaye, ta ajjiye kuɗin da ta ɓoye a rigar ta, ta shiga wanka a gaggauce. Ta fi minti talatin tana wanka sannan ta fito ta shirya ta yi sallar azahar.
Kuɗin da ta ajjiye ta ɗauka da wayarta, sai ta kai su hancinta ta ji ƙhamshin turaren mutumin kawai suke yi, musamman wayar ta kamar shafa mata turaren ya yi. Ta yi tsaki tana hararar wayar, ta fita daga gidan da sauri.
Tana fita ta hangi motar Saleem a ƙofar gidansu Safeera, da sassarfa ta ƙarasa ƙofar gidan, tana zuwa ta ga Saleem da Safeera a tsaye yana rarrashin Safeera tana ta kuka.
Islaha ta ce, "Safeera!."
Da hanzari Safeera ta juyo jin muryar Islaha, suna haÉ—a ido tayi murmushi ta ce, "Hamma Saleem rarrashi ka ke yi kenan, to na dawo ai."
Safeera ta fito da sauri ta ce, "Islaha!" Tana faÉ—a ta rungume ta cikin tsananin kewa da farin ciki.
Islaha ta yi murmushi ta ce, "na dawo, ki daina kuka."
Safeera ta É—ago tana kallon Islaha ta ce, "Ina ki ka shiga? Su waye suka yi garkuwa dake? Ya aka yi suka sake ki ba a biya kuÉ—in fansar ba?."
Ta kalli Saleem da yake kallon ta a rikice cikin mamaki ya kasa magana. Islaha ta ce, "kuÉ—in fansa kuma? Wanne irin kuÉ—in fansa?."
Saleem ya ce, "Islaha an kira mu an nemi naira miliyan ashirin kuÉ—in fansar ki, ko mu bayar ko a kashe ki."
Ta É—an yi shiru tana nazafi kafin ta ce, "kuna ji, mu je asibiti wajan Baffa."
Saleem ya ce, "wajan Æ´an sanda ya kamata mu fara zuwa kafin mu je can."
"A'a Hamma Saleem, mu fara zuwa asibitin akwai abinda zan yi a can da gaggawa, in mun gama daga can sai muje duk inda zamu."
Safeera ta bita da kallon mamaki ta ce, "ni ban ga alamanun an yi garkuwa dake ba, gabaÉ—aya baki yi kama da wacce aka sace ba. Islaha daga ina ki ke?."
"Duk za ku ji komai, muje kawai" ta faÉ—a tana shiga motar Saleem, shima ya shiga yaja suka tafi asibiti.
A kan hanya ma bata ce komai ba har suka je asibitin, tana shiga wajansu Mama duk suka taso ana tambayar ta abinda ya faru. Bata basu amsa ba ta ce, "Lafiya lau nake Mama, ina Hamma Sadik?."
A lokacin Sadik ya ƙaraso ya ce, "Islaha! Ke ce?."
Ta É—aga masa kai ta ce, "ni ce Hamma Sadik, ya batun kuÉ—in aikin Baffa?."
"Mu fara da gama case É—in nan naki, ya aka yi ki ka dawo? Waye ya sace ki?."
"Na fi so mu gama da batun aikin Baffa, in yaso komai sai ya biyo baya, kazo muje" ta faÉ—a tana yin gaba ya bi bayanta da hanzari.