Sashe 45
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka tana zaune a wajen har aka yi kiran sallar azahar, ta ji kiran ya karaɗe ko ina. Umma ta miƙe daƙyar ta fito ta koma wajan Shafa ta tarar har ta gama abinci ta gama gyara waje komai tsaf.
Shafa ta kalli Umma ta ce, "wai har kin gama wankin?."
Umma a sanyaye ta ce, "sallah na ji ana yi, shine na fito nayi zallah sai na koma."
Ta kalli Umma tana girgiza kaita ce, "hmm, Allah yasa su yi miki wannan uzurin, sufa sun fi so da ance kawai a yi, basa son ɓata lokaci."
Umma ta wara ido waje cikin mamaki ta ce, "har sallar ma?......"
Nana HaleemaâœðŸ»â¤ï¸
[7/1, 1:08 PM] KRBBK: RDB2P31
Nana Haleema
Hajiya Shafa ta yi dariya ta ce, "baki san a ina ki ke bane. Jeki ki yi alawar."
Umma ta juya ta shiga ɗakin da aka nuna mata, daƙyar ta iya alawala ta fito ta yi sallah, Tana idarwa bata san bacci ya ɗauke ta a inda ta idar da sallar ba, ko hijjab bata cire ba saboda yadda baccin ya ci ƙarfinta.
   A firgice ta farka jin ana shafa hannunta, ta buɗe ido tare da miƙewa zaune tana raba ido jin baƙon abu wanda bata saba ji ba.
Suna haÉ—a ido taga mai gidan ne da kansa a tsugune a gabanta yana yi mata murmushi.
Gaban Umma ya faɗi, ta ja baya da sauri tana so ta yi magana amma bata san me zata ce ba, ta san ba yaren ta yake ji, sannan itama ba nasa take ji ba balle ta tambaye sa dalilin zuwan sa waje. Umma ta ruɗe sosai, tashin hankali ya bayyana ƙarara a tare da ita. Shi dai ya bita da kallo kafin ya miƙe ya fita.
Umma ta bisa da kallo sai kuma ta tuna da wanki, ta firgita ta miƙe ta koma ɗakin wankin ta tarar an sake tulo mata wasu.
A haka Umma ta gama wankin, ko gama bushewa basu yi ba ta fito jin kanta yana sarawa kuma ta san yunwa ce. Tana fitowa suka haÉ—u da matar gidan, ta yi mata alama da ta biyo bayanta, Umma ta bita har kitchen.
Ganin kayan wanke-wanken da suke jibge sai da gabanta ya faÉ—i, ta ji hawaye har taruwa suka yi a idanunta saboda tashin hankali da damuwa.
Matar gidan ta nunawa Umma kayan alamun ta wanke, sannan ta nuna nata wani kwano alamun ga abincinta nan. Umma ta bi kayan wanke-wanken da kallo dan kayan suna da bala'in yawa sosai.
Umma ta ƙarasa ta buɗe abincin ganin shinkafar da aka dafa ce sai rabin kaza. Hannu yana rawa Umma ta fara ci a hankali dan yunwa take ji sosai.
Kafin ta ci rabin abincin ta ji ana jan hannunta, taga yarinyar nan da zata yiwa wanka É—azu, Umma ta bi bayanta suka fita sai taga yadda suka lalata falon, kuma taga alama ake yi mata da ta gyara wajan.
Umma ta yi ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi, ta bi dining ɗin da kallo ganin sa kaca-kaca kamar yara ƙananu ne suka ci, bayan cin abincin suka haɗa da dambe a kai.
Ta lumshe ido tana ƙarasa wajan ta ɗauki abinda aka nuna mata na aiki, ta fara share wajan sannan ta goge dining ɗin ta gyara kujuren, ragowar tarkacen kayan da suka bari ta ɗauke ta koma kitchen ta fara wankeawanken dan ta manta ma abinci take ci.
Kamar an tuna mata da wayar ta, gabanta ya faÉ—i ta ji tana so ta yi magana da Æ´aÆ´anta.
Ta juya zata fita ta ɗauko ta ga mai gidan a tsaye a falo shi kaɗai yana binta da shegen kallo da ya saka ta tsaya cak, gabanta ya faɗi matuƙa, ta juya ta cigaba da aikin jikinta yana rawa cikin tashin hankali. Tunani take a zuciyarta ina ta kawo kanta haka?.
••••••
"Sadik ina Islaha ne, ban ganta ba kwata-kwata. Ko ta tafi aiki ne?."
Sadik ya kalli Baffa ya ce, "Wallahi Baffa nima bamu haÉ—u da ita ba, amma na san tana wajan aiki, zata biyo in ta tashi.
Baffa ya ce, "Islaha sarkin ƙorƙari, Allah ya yiwa rayuwa Albarka."
Sadik ya amsa yana fitowa daga É—akin suka haÉ—u da Hanan zata shiga ya ce, "Hanan don Allah ina Islaha?."
Ta ɗan taɓe baki ta ce, "Ban sani ba" ta faɗa tana shiga ɗakin ta bar sa a tsaye yana binta da kallon mamaki.
Sadik ya É—auke kai ya É—auko wayarsa ya kira Islaha amma wayar bata tafiya gabaÉ—aya.
Mama ce tazo zata shiga É—akin, Sadik ya tsayar da ita ya ce, "Mama Islaha tana gida ne?."
Mama ta ce, "Islaha ai bata nan, zaka jima baka ganta ba." Kafin ya sake magana ta shiga É—aki ta barsa a tsaye cikin mamaki.
Sadik ya bi Mama da kallo cikin rashin fahimta, ya fita daga asibitin ya hau mota ya nufi gidansu Safeera.
Yana tsayawa a ƙofar gidan kiran Saheer yana shigowa wayarsa, bai ɗauka ba dan ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ya san bazai wuce yace masa lambar Islaha bata shiga ba, in ya ɗauka bashi da amsar da zai bashi.
Sai bayan wayar ta yanke ya kira Safeera tana É—auka ya ce, "Safeera kina gida ko wajan aiki?." Ya yi shiru alamun ana basa amsa, sai kuma ya fita daga motar ya hango ta ta fito daga gidansu.
Ya ƙarasa wajan sai ya ga motar Saleem ta tsaya, shima ya ƙaraso suka gaisa. Saleem ya kalle Safeera ta ce, "ya jikin ki?."
A sanyaye Safeera ta ce, "Da sauƙi."
Saleem ya ce, "Ana ganin ki an san baki da lafiya."
Sadik ya ce, "Sannu Safeera, ban san baki da lafiya ba da ban kira ki ba."
Safeera ta É—an murmusa ta ce, "ciwon kai ne kawai."
Sadik ya kalle ta ya ce, "Ƙawar ki fa? Na kira ta sau babu adadi bata ɗauka, ga sarkin rashin haƙuri ya fara damuna da waya akan baya samunta."
Saleem ya ce, "A'a, Islaha ba tayi tafiya ba?."
Sadik da mamaki ya ce, "Islahan ce tayi tafiya, to zuwa ina?."
Saleem ya ce, "nima ban sani ba, amma kowa na gidan tv ya san Islaha bata nan, har Safeera."
Sadik ya kalli Safeera ya ce, "Safeera Ina Islaha take?."
Safeera ta sauke numfashi ta ce, "Eh Islaha tayi tafiya Hamma Sadik."
Sadik mamaki ya mamaye masa zuciya ya ce, "ina ta je? Ina ta tafi bamu sani ba?."
Safeera ta É—an yi ajiyar zuciya ya ce, "itace tace bata so ka sani kai da Saheer, shiyasa baku sani ba."
Da mamaki Sadik ya ce, "tafiya zuwa wani gari to? Me ya kaita garin, kuma yaushe zata dawo?."
Safeera ta kalle sa ta ce, "Ƙasar ta bari gabaɗaya ai, ba wani garin ta tafi ba, Islaha bata Nigeria."
A tare suka haɗa baki suka ce, "Kamar ya ta bar ƙasar!?." Safeera ta yi shiru bata ce komai ba, dan bata san me zata ce musu su yarda ba.
Sadik a ƙagauce ya ce, "ki yi mana magana mana Safeera, kalli wayata, Saheer ne yake yi min magana ban san me zance masa ba. Wacce ƙasar Islaha ta tafi? Wacce ƙasar islaha ta tafi bamu sani ba?." Safeera ta sake yin shiru bata ce komai ba, ita kanta gabanta faɗuwa yake yi dan bata san me zata ce ba.
Sadik ya dafe kai ya ce, "Safeera ki buÉ—e baki ki yi magana, kar ki saka jinina ya hau don Allah."
Safeera ta ce, "ta tafi ƙasar saudia, yanzu haka ma tana can. Dan tun safe na ga voice note ɗinta, ta ce min har ta sauka a masauki."
Saleem cikin firgici da tashin hankali ya ce, "Saudia Safeera! Umra ta tafi babu labari?."
Sadik yabi Safeera da kallo dan ya kasa magana, ya girgiza kai cikin mamaki ya ce, "wai me islaha ta ɗauke mu ne? Me take ɓoyewa wanda bata so mu san dashi?. Tunda aka sace ta na lura da akwai abinda ake ɓoyewa wanda bata so mu sani. Yanzu waye ya kai Islaha saudia Safeera? Kin tabbatar ta bar ƙasar nan?."
Safeera ta ce, "Wallahi Islaha bata nigeria, kuma ta tafi Saudia ta ƙarƙashin kamfanin su Mamansu Saheer. Ba ita kaɗai ba, harda Labiba da...." Sai maganar ta maƙale saboda nauyi, ta sunkuyar da kai ta ce, "Da Ummana" ta faɗa hawaye yana sakko mata ta yi sauri ta goge.
Sadik ya dafe kai da hannu biyu ya ce, "aikatau É—in ta tafi kenan?."
Ta ɗaga masa kai ta ce, "ta ce bata so ka san ta tafi, bata so ka san dalilinta sai ta bar ƙasar."
A fusace Sadik ya ce, "wanne dalili ne da ita da zai saka ta yanke wannan hukuncin?. Ni fa ban yarda da ita ba, zuciyata faɗa min take yi yawon banza Islaha ta fara yi, shiyasa ta bar gida ta je ta kwana biyu da sunan an sace ta. Taje ta gama zaman ta a inda ta ga dama, sannan ta dawo da kuɗi masu uban yawa ta ƙi faɗar a inda ta samu, yanzu kuma ta bar ƙasar duk bamu sani ba."
Safeera ta ce, "wallahi Islaha bata fara yawom banza ba, ka daina jifanta da wannan kalaman. Tafiyar ta aikin ma rashim mafita ne ya saka ta tayi ta, ba a son ranta ta tafi ba."
Sadik ya zuba mata ido dan ya kasa magana, hakan ya saka Saleem ya ce, "Wacce mafita ce wannan da zata saka ta tsallake mu ta tafi wata ƙasar aiki a gidan larabawa?."
Safeera ta ce, "Kamar yadda ta faÉ—a mana yadda aka sace ta, da gaske ta hakan aka sace ta. Ranar da zata dawo ta ga kuÉ—in a falon mutumin, shine kawai sai ta É—auko tana tunanin yanayin da ta bar Baffa a ciki, kar ta dawo ba a samu kuÉ—in aikin ba."
"Bayan aikin Baffa ya kammala kuma sai hankalinta ya tashi sosai, ta dinga mafarkai akan kuɗin. Shine ta same ni tana neman hanyar da zata samu kuɗin ta biya sa. Na faɗa mata samun kuɗi kamar wannan a ƙaramim lokaci bazai yu ba, nima ban sani ba, ashe har ta gama shirya komai an yi mata visa, sai tafiyar kawai ta faɗa min."