← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 133

Sashe 107

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta share hawayenta tana sauke numfashi ta ce, "Na daina Jafar. Ka samu labarin aurensa ko?."

"Yanzu Abba yake faɗa min, zan ƙara bincike a kan yarinyar in Allah ya yarda."

"Wai Rehaan za a yiwa irin wannan aure, Rehaan ɗin da nake tanadin aurensa, shi za a yiwa wannan wulaƙantaccen auren da ko matar bai sani ba."

"Sai haƙuri Mamy."

Ta girgiza kai bata ce komai ba, sai kuma ta tashi ta sauka daga saman ta barsu a saman.

Ya kalli Riyya da take ta hawaye ya ce, "Meye na kukan kuma?."

Ta ce, "ni kaÉ—ai fa nake shigowa, an zuba masa pioson a drink É—in da na bashi, sannan yanzu ga kayan asiri a É—akin da ni kaÉ—ai nake zuwa. Ba dole na yi kuka ba."

Ya É—ago fuskar ta ya ce, "Kina tunanin za a ce ke ki ka saka masa ne?."

Ta buÉ—e baki zata yi magana ya É—ora yatsansa a kan lips É—inta ya ce, "kar ki ce komai, wannan ba tunani ne mai kyau ba."

Ta cire hannunsa sannan ta ce, "to meyasa suke so su kashe mana shi, kowa a gidan nan ba sauraren mu yake yi ba, laifin mu ne dan mun zo a jinin Mamy?. Shi kaɗai ne Yayanmu, sauran Yayyem ƙannensu ne, meyasa zasu kashe mana shi?."

A ya zauna a kusa da ita ya rungume ta yana pitting bayanta a hankali ya ce, "ki daina kuka, koma meye ai ya wuce, tunda na ƙona da sunan Allah."

Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana kuka sosai yana rarrashinta. Sai da ya ji ta daina sannan ya ɗago ta, ya yi pecking goshinta ya ce, "ki bar kuka, babu abinda zai samu Rehaan in sha Allah, babu wanda ya isa ya yi masa abinda Allah bai yi ba. Ki cigaba da ta ya shi da addu'a, ba wai yana kyautata miki kawai ki ji daɗi ba, ki dinga dagewa da yi masa addu'a kin ji?."

Ta É—aga kai alamun to, ya share mata hawaye ya ce, "Ko ke fa. Yanzu kin gama gyara masa É—akin?."

"Na gama."

"Me za ki yi yanzu?."

"Zan je na wajan wata vendor ne, zan ga wasu samples É—inta."

"Meyasa baza ta kawo miki ba sai kin je?."

"Ai akwai inda zan je."

Ya ɗaga kai ya ce, "Mu je na raka ki." Bata ƙi ba suka sakko daga saman, ta shiga wajan Mamy shima bai bi ta kan matan gidan ba suka fita.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_

Nana Haleema.
[7/23, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P79
Nana Haleema.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ki yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_

••••••••••

Mama tana zaune a gaban Daada tana jira ta idar da sallah dan ta idar mata da abinda yake zuciyarta.

Daada tana idarwa ta kalle ta ta ce, "Saddiƙa lafiya?."

Ta yi murmushi ta ce, "Ga dambun nama."

Daada ta karɓa ta ajjiye a gefe ta ce, "Na gode da hidima."

Ta yi murmushi ta ce, "sai wata magana da nake tafe da ita, ban san ta ya za ki karɓe ta ba."

Daada ta ce, "ina sauraren ki, ko ya take faÉ—a min kawai."

Mama ta sauke numfashi ta ce, "Akan auren nan na Rehaan ne. Daman tambaya zan yi, in ana É—aura auren a ina zai tare da matarsa?."

Daada ta yi dariya ta ce, "Gidajen da Rehaan yake dasu har sai ance a ina zai zauna? Ko mata goma zai aura yana da gidan da ai ajjiye su."

Baƙin ciki ya mamaye zuciyar Mama, amma bata nuna ba ta ce, "gaskiya ne. Amma ni a shawara ta mai zai hana bazai yi zamanasa a gida nan ba, ɓangarensa har mata huɗu zai ajjiye. Kaf gidan nan daga ɓangaren Abbansa sai ɓangarensa ne masu sama, kin ga akwai wajan ajjiye mata a nan."

"Meye amfanin hakan? Yana da gidaje mai zai yi a nan?."

"Amfanin hakan kin ga ba son auren nan yake yi ba, in ya tare a wani gidan Allah kaɗai yasan wulaƙancin da zai yiwa yarinyar nan. Ba a san yadda zasu dinga zama ba, kuma zai iya tsallake ta ya bar ƙasar babu wanda ya sani. Hakan kuma zai taɓa ƙimar ki da ƙimar gidan nan sosai, dan wulaƙanta mutum ba halinmu bane. Kuma ga maƙiyan da ya tara, in ya bar yarinyar nan ita kaɗai a waɗannan tanƙama tanƙaman gidan za a iya cutar da ita. In kuma tana gidan kin ga akwai idonmu, wani wulaƙancin na sa ma zai ragu, kuma ko da ya tafi ya barta muna nan tare da ita, balle ma wani abun in ya aikata za ki tsawatar masa."

Daada ta yi murmushin jin daɗi ta ce, "wato a kaf gidan nan babu mai hankali kamar ki Saddiƙa, babu mai hangen nesa da sanin ya kamata sai ke ɗin kawai. Ai ko ni kin fini zurfin tunani."

Ta yi dariya ta ce, "Wane ni Daada?."

Daada ta yi dariyar jin daÉ—i ta ce, "na ji daÉ—in wannan shawarar ta ki, kuma da ita za a yi amafani. In na bari ya tafi da ita wani waje ai sai ya dinga cin zalinta, nan kuwa ko baya nan muna nan babu abinda zai same ta."

"Abinda na gani kenan, kuma hankali kwance babu tunani mara kyau. Shiyasa na ce bara na zo na same ki, zuwa nan gaba in komai ya warware sai ya tare a inda yake so."

Daada ta ce, "wannan shawara ta yi É—ari bisa É—ari. Haka za a yi ma babu makawa."

Mama ta yi murmushi ta ce, "Bara na je Daada, sai anjima."

"Babu damuwa, in da wata shawarar ina nan ina jiran ki." Ta amsa tana murmushi ta tafi.

****

Islaha haka ta je ta samu Safeera ta dinga yi mata mita skan abinda Saheer ya yi mata Safeera ta yi dariya ta ce, "to ni da ki ke ta yi min mita ni ce Saheer É—in?."

Islaha cike da jin haushi ta ce, "Wallahi Hamma bai taɓa bani haushi kamar yau ba, wai bazai karɓi abinda bai san da kuɗin da aka siya ba. Ni yake faɗawa wannan maganar kai tsaye, yana nufin yana zargin a hanyar banza na samu kuɗin."

"Na faÉ—a miki dole ya shiga ruÉ—ani saboda abubuwan da suka faru."

Ta ja tsaki ta ce, "Shi ya sani. Bazan sake saurarensa ba wallahi, in ya ga dama ya zarge ni É—in sai me."

Safeera bata ce mata komai ba ta yi dariya kawai, dan ta san zasu shirya ne. Kuma ita bata ga laifinsa ba, dole ya zargi wani abun a ransa, saboda abinda ta faÉ—a ita kanta sai da ta kai zucoya nesa sannan ta amince.

••••••••

Motar su tana cikin tafiya a cikin daji da duhuwa, masu bacci suna bacci, masu chating suna yi, masu jin waƙa suna yi. Ƙarar babura da ihuun mutane ya saka kowa ya firgita ya miƙe, kafin wani lokaci babura sun kewaye motar.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Masu garkuwa da mutane ne!."

Jin kalaman driver sai kowa ya ɗauki salati, wasu suka fashe da kuka saboda tsananin tashin hankali. Saheer yana zaune gabansa yana faɗuwa, ya kalli mutanen ya ga a ƙalla baburan zasu kai goma, kuma ko wanne mutum biyu ne a kai. Ya dinga salati a zuciyarsa, hankalinsa ya tashi sosai.

Duk suka sauka daga kan baburan, dukkansu da ƙatuwar bindiga a hannunsu, sun yi carko carko a gaban motar suna kallonsu.

Ɗaya daga cikinsu ne ya buɗe ƙofar driver, cikin muryar fulani amma da yaren hausa ya ce, "Malam Driver sakko."

Driver jikinsa yana karkarwa ya sakko daga motar, suka buÉ—e bayan motar suka ce kowa ya sakko daga ciki.

Duk sauka sakko suka kwanta, suka dinga binsu ɗaya bayan ɗaya suna kallo. Ɗaya daga cikin su ya ce, "Yellow a karɓi waya da kuɗi."

Wanda aka kira da Yellow É—in ya ci sunan nasa yellow, dan yana da haske sosai, gashi É—an siriri mai jikin fulani, ya fara binsu ya ce, "Kawo waya da kuÉ—i." Hannun su yana rawa suke basu, har aka zo kan Saheer ya bayar.

Yellow ya ce, "Magaji wannan matar ciki gare ta" ya faɗa tana nuna masa wata mata da bindiga, tana zaune tana kuka saɓaninsu da suke kwance.

Magaji ya ƙaraso yana kallon yadda take kuka, ga cikinta nan ya fito sosai alamun ta kusa haihuwa. Ya kalle ta ya ce, "Ya sunan ki?."

Muryarta tana rawa ta ce, "Magajiya."

Duk sai suka saka dariya suna sowa. ya kalle ta ya ce, "ki ce sunan mu iri É—aya ne. Kin ci albarkacin sunan ki, baza mu tafi dake ba, kuma baza mu kashe ki ba, zamu bar ki tafi. Tashi ki tafi."

Jikinta rawa yake yi ta kasa miƙewa, ya ce, "ki tashi babu abinda za a yi miki." Ta miƙe tsaye, ya nuna mata hanya ya cr, "ki bi nan, ki ta gudu kar ki tsaya." Bata iya magana ba ta tafi da gudu ɗin kamar yadda ya ce, tana kuka sosai.

A take aka ɗaure hannayensu Hamma ta baya, aka miƙar da kowa a cikinsu suna binsu da kallo. Yellow ya kalli wata babbar mace, a shekaru ta girma kuma tana da jiki sosai. Ya ce, "Magaji wannan fa kaya ce."

Magaji ya kalle ta ya ga tabbas kaya ce, in aka ce za a yi tafiya mai nisa da ita wahala za a sha. Ya kalli Yellow ya ce, "Ka san yadda zaka yi da ita kawai."

Yellow ya saita bindiga a kanta, ta ɗaga hannu sama ta zube guiwa a ƙasa ta ce, "Don Allah kar ka kashe ni, ina da ƴaƴan da suke tsananin buƙaata ta." Kafin ta sake magana bullet ya fasa kanta, a take ta zube a wajen matacciya.

Matan da suke cikin su Hamma suka ƙwalla ihuu, cikin kiɗima da tashin hankali mai tsanani.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭

Nana Haleema.
[7/23, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P80
Nana Haleema.
Chapter 107 · 0% Book details