Sashe 102
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki fito da sassafe, dan cikin ƙauye zamu shiga. Fulani ne mu, akwai wanda ya kai mu surkulle da iya shige shige ne?. Zan yi miki maganin Islaha wallahi, sai dai wata mai irin sunanta, amma ba dai Saheer ya aure ta ba."
Mama ta sauke numfashi cikin jin daÉ—i ta ce, "Allah ya kaimu goben, zamu yi waya" ta faÉ—a tana kashe wayar tana tunani. A bayyane ta ce, "Akan ta auri Saheer wallahi gwara na sabauta ta, gwara ta nemi hankalinta ta rasa."
•••••••••
Abba yana zaune yana amsa waya, Mamy tana gefensa a zaune tana jin duk abinda yake faÉ—a.
Abba ya ce, "Sunan mutumin Mustapaha Maddibo, ka san shi?."
Daga can ɓangaren ya ce, "Sani kai, yanzu haka tare zamu shiga masallaci."
Abba ya ce, "Yauwa, zan iya wakiltaka in babu damuwa."
"Haba dai, faÉ—i kawai babu damuwa."
"so nake a same shi akan maganar yarinyar da yake riƙo, a tuntuɓe shi in ba a yi mata miji ba zan bawa ɗaya daga cikin yaran nan aurenta."
"Islaha ka ke nufi?."
"Eh kamar haka sunan yake."
"Ai kuwa kowa waye ya yi dacen yarinya mai kirki da hankali. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa sosai, dan ta fi yaran da ya haifa tarbiyya da sanin darajar na gaba. Ina ta ya wanda za ka karɓawar auren ta murna, dan ya samu macen kirki."
Abba ya yi murmuahi cikin jin daɗi sannan ya ce, "sai ka saka na ji daɗi da ka ke yabonta. Wallahi Daada ce ta matsa akan sai Rehaan ya aure ta, daga yarinyar ta ganta a hanya ta taimake ta shikenan wai ita Rehaan zai aura. Nayi-nayi a bar batun auren nan amma Daada ta ƙi. Ka san in abu ya haɗu da girma, sai ana yi ana lallaɓawa a rabu lafiya."
"Rehaan da kansa? Kai lallai Islaha ta ta ki sa'a. La la la! Ashe babbar giwar ce da kanta."
"Wallahi shine. Ta dole Daada take son haÉ—a auren nan."
"Kar ka hana, ka ba da goyan baya baka san me Allah ya ɓoye a ciki ba, ka saka a yi ta addu'a, sai ka ga hakan ya zama alkhairi."
"Shiyasa na ji daÉ—i da na ji kana yabonta wallahi. Ka san ya rayuwar Rehaan take, ta ko ina kawo masa suka ake yi."
"Na sani wallahi, ai duk wanda kaga ya ɗaukaka ka kalle sa kawai, ba ka san ƙalubalen da ya fuskanta ba. Amma yarinyar tana da hankali da nutsuwar da zan ce maka baza ta auri Rehaan dan kuɗinsa ba wallahi."
Abba ya ce, "Duk da haka Alhaji Rufa'i, ni so nake kar su san sunan Rehaan, ka je musu a matsayin ban faÉ—a maka sunan wanda nake so na haÉ—a ba, kawai tambaya ce in babu miji za a yi magana."
Alhaji Rufa'i ya ce, "Hakan ma shawara ce. In Allah ya yarda gobe zan same shi, duk abinda ake ciki zan kira ka."
Abba ya ce, "na gode Alhaji Rufa'i." Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar.
Abba ya kalli Mamy da ta yi shiru ya ce, "Kin ji dai, yarinyar ana ta yabonta. Ban taɓa jin wanda ya faɗi aibunta ba tunda na fara sakawa ayi bincike a kanta."
Mamy cikin ko in kula ta ce, "Allah ya kyauta kawai, amma ni kam bana son auren nan wallahi."
"Uwa ce ke, ki yi masa addu'a da fatan alkhairi, ki yi fatan Allah ya sa ta zamar masa alkhairi."
Ta amsa da amin kafin ta ce, "Amma yadda ya bani zaɓi zan zaɓa masa wacce ta dace da rayuwarsa, zan zaɓa masa wacce zai samu farin ciki daga gare ta."
Abba ya murmusa ya ce, "Nadira! Mu fa fulani muna da kara, amma ku indiyawan nan ba ku da kara akan yaranku. Nuna min ki ke yi Rehaan fa É—an ki ne, ni kin cire ni kin ajjiye a gefe."
Ta É—an yi murmushi ta ce, "Bazan yi karar da zata cutar min da É—a ba, ba zan yi abinda zai ji ban kyauta masa ba. Ina so ya samu farin cikin da ya rasa, ina so ya zama ya fi jin daÉ—in zaman gidan nan akan ko ina. Ka duba, saura sati biyu bikin Jafar, amma saboda ba ya son zuwa ba ya maganar dawowa."
Ya yi murnushi ya ce, "zai dawo ne, tsakaninsa da Jafar ai ba a shiga. Kuma dole ya dawo shima ya angwance."
"haka za a yi bikin ba wani shiri? Yanzu an ce nan da sati biyu, ko shirin kayan amarya da ake kaiwa ba a yi ba."
"Kar ki wani damu, wannan duk mai sauƙi ne. Mu jira mu ji mana, in an yi mata miji fa shikenan an huta."
Mamy ta murmusa tana fatan Allah ya sa an yiwa Islaha miji a kuɓutar da ɗanta daga aurenta, dan Allah ya sani bata son auren, dan an fi ƙarfinta ne kawai.
REHAAN KO SAHEER?💃ðŸ»ðŸ”¥
Nana Haleema
[7/22, 10:14 AM] KRBBK: RDB2P75
Nana Haleema.
_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.ðŸ™ðŸ»ðŸ˜_
Sameer ya kalli Mamansu ya ce, "Mama wai meyasa ki ke so auren nan ya yu har haka?."
Mama ta kalle sa ta ce, "yaro yaro ne, yuwar auren nan na Rehaan yana daga cikin cikar birina a gidan nan, shiyasa zan iya bin ko wacce hanya dan ganin na tabbatar da auren nan?."
Sameer ya ce, "ta ya zai zama cikin burin ki? Ban gane ba, ki yi min bayani."
Mama ta murmusa sannan ta ce, "ka zuba ido ka sha kallo, amma babu wanda ya isa ya hana auren nan yuwa matuƙar ina da rai. Ku je ku cigaba da shirin auren kawai."
A lokacin Hamma Zayyad ya shigo, ya zauna a kan kujera ya ce, "Mama ashe wai bikin Riyya saura sati biyu?."
Sameer ya ce, "Abba bai faÉ—a maka ba?."
Ya girgiza kai ya ce, "ban sani ba, yanzu nake ji a bakin masu gadi."
Mama ta kalli ɗan nata tana ji kamar ta juya sama ta dawo ƙasa, da tana da iko da yanzu ta ƙwace ɗaukaka Rehaan ta bawa ɗanta, shine babba amma ya zama kamar shine ƙarami saboda bashi da kuɗin da Rehaan yake dashi. Ba wai kuɗi ne bashi dashi ba, yana da kuɗi kamar sauran ƴan gidan, kawai Rehaan ya fita zakka a cikinsu. Ita kuma kallon talakawa take yi musu saboda Rehaan, shiyasa take baƙin ciki da hakan sosai.
Ta girgiza kai cike da takaici ta ce, "Kaima dai ban da abin ka, meye abin damuwa dan za a yi bikin ka Riyya baka sani ba?."
"Ba damuwa na yi ba, sai meye san an yi ban sani ba. Kawai babu daÉ—i ne Mama."
"Kar ka ji daɗi. Duk ba kai ka jawo ba? Ga hanyar yin kuɗi da shahara nan da yawa amma ka kasa bi ka zama kamar Rehaan. Hannunka kamar rariya, da an ba ka kuɗi da sun ƙare. Haba, ƙannenka wanne irin abun duniya ne basu dashi?."
Hamma Zayyad ya ɗan taɓe baki ya ce, "To Mama zan canja Allah ya yi ni ne?."
Ta ja dogon tsaki, ta cize leɓe tana buga ƙwafa. Auren nan na Rehan shine target ɗinta, shiyasa ta ɓuya ta yi shiru tana jira ayi sannan ta cigaba da aiwatar da abubuwan da suke gabanta, dan wallahi bazata bar Rehaan lafiya ba, sai ta la'anta rayuwarsa ta ɗaiɗaice
••••••
Islaha bata bar ɓangaren Baffa ba sai goma na dare, Baffa ya riƙe hannuta da kansa ya kai ta har ɗaki ya sannan fito. Mama bata ce komai ba dan ta daina ɗaga jiyoyin wuya, ta ƙarƙashin ƙasa zata yi maganin Islaha.
Ita dai Islaha kwanciya ta yi tana tunanin rayuwarta, haka zata yi zaman aure da mijin da babarsa bata ƙaunarta? Anya zata samu farin cikin da take fatan samu a aurensa? Anya zata samu kwanciyar hankali da nutsuwar da take fatan samu?.
Hamma yana sonta, zai bata kulawa irin wacce bata yi hasashe ba. Amma babarsa bata so, duk da ba da Babarsa zata zauna ba amma ita ta haife sa. Tun tana faÉ—a masa aibunta baya yarda, wata ran zai yarda, wata ran za a samu akasin da zata yi abinda zai ce daman Mama ta ce.
Ta girgiza kai Zainab ta faɗo mata a rai, ta miƙe ta kira Suraj a waya amma bai ɗauka ba, ta koma ta kwanta tana tunanin mafita a rayuwarta.
Washe gari da safe bata ji motsin Mama ba, daman bata cika yi mata karanbani ta shiga É—akinta ba sai dole.
Gidan babu kowa alamun Hanan ma bata nan, ta shiga kitchen ta sha tea, dan ya yi safiya baza ta iya cin komai ba sai rana ta fito sosai. Tea É—in kawai ta sha, ta shirya ta fito da niyar tafiya aiki.
Tana fitowa suka haÉ—u da Saheer, suna haÉ—a ido ta É—an yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ina kwana." Bai amsa ba sai kallon ta da yake yi sannan ya ce, "kin ci abinci?."
Ta girgiza kai ta ce, "Ya yi safiya da yawa, zan ci in anjima."
"Ina za ki je da safe haka?."
"wajan aiki zan je."
"Yanzu?." Ta É—aga masa kai alamun eh.
Ya ce, "Ya yi wuri yanzu, na san ba ki da aiki a wannan lokacin. Mu je ki raka ni wani waje, daga nan sai na kai ki." Bata ce komai ba suka fito, bai rufe gidan ba dan Baffa yana ciki.
Tunda suka shiga motar ta lura da yanayinsa ya canja, ya haÉ—e rai sosai kuma ko kallonta ba ya yi. Ta ce, "Hamma motar wajen Sadik É—in ce?."
Kai kawai ya É—aga mata bai ce komai ba, ta yi shiru bata sake kula shi ba. Sun fi mintina goma a haka, shi bai kunna motar ba kuma bai fita ba.
Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Sai na ganki kwatsam, har shekara É—ayan ta yi?."
Islaha ta ɗan murmusa, daman ta san dalilin ɓata ran nasa kenan, babu inda zata raka shi kawai maganar yake so su yi shiyasa ya saka ta shiga mota.
Islaha ta ce, "bata yi ba."