← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 133

Sashe 77

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta ce, "kamar dai hotunan Hafsa, daga kai sai Safeera, ta ce min ta faɗawa Saleem har ta tura masa saboda gudun ɓata, sai Brr Suraj."

Ta yi tunanin zai yi faÉ—a akan Suraj kamar yadda ya saba, amma sai ta ji bai ce komai ba ya yi shiru kafin ya ce, "lokacin hotonan Hafsa ma iya mu haka muka sani ko?."

Kamar tana gabansa ta É—aga kai ta ce, "A daren kai da Suraj ku ka sani, washe gari Safeera da Saleem suka sani. Ko mintina ashirin ba a yi da saninsu ba aka rasa hotunan."

Saheer ya ce, "Yanzu kuma gashi recording ya fita, ta silar sa har ana ƙoƙarin cutar da Zainab."

Ya sauke numfashi yana ya ce, "Islaha!."

"Na'am!."

A sanyaye ta amsa ya ce, "a tsakanin ni, Suraj, Safeera, Saleem akwai munafuki a cikin lamarin ki. Akwai wanda yake da hannu a cikin lamarin nan, zai nuna yana tare dake amma a bayan idonki yana tare dasu. Tabbas akwai suspect a tsakanin mu."

Islsha ta dafe kai cikin tsananin damuwa, ta kasa furta komai, dan tabbas maganar Saheer gaskiya ce.

Saheer ya katse mata tunani ya ce, "ya zama dole ki nemo waye munafukin a cikin mu, kafin nan ki daina faÉ—a mana komai akan abinda ya shafi binciken ki. Ki dinga ajjiyewa a wajan ki, kar ki yarda da kowa, ki yarda da kan ki. Ko ni É—in kar ki yarda dani, kar ki yarda da Safeera, balle Suraj. Ki nutsu, ki cigaba da abinda ki ke yi ke kaÉ—ai, ko da kin dawo ki daina faÉ—awa kowa damuwar ki."

Islaha a sanyaye  ta ce, "amma ni bana zargin kowa Hamma, wallahi bana zargin kowa a cikin ku."

"Hmm! Ba ki san mutum bane, ni ɗin nan da ki ke gani wataƙila sai ya zama ni ne mai fitar da dukkan sirrin ki. Safeera da ku ke tare ko yaushe zata iya zama itace, Suraj da ki ke kallo a matsayin Yayan ki shima zai iya zama shine munafukin ki. Balle Saleem, da ya kasance abokin aikin ki kawai...."

Ya ja numfashi ya ce, "Ki yarda da zuciyar ki, ko me za ki samu ki daina faɗa, in ba haka ba baza a taɓa bari ki yi achieving mafarkin ki ba. Kuma za a cigaba da cutar da irinsu Zainab ɗin. Kar ki sanar da kowa sai kin tabbatar komai ya kammala. Tunda har aka fara haka zargin ki a kan gidan nan gaskiya ne, wanda yake aikata laifi shine yake ƙoƙarin kawar da duk wani abun da zai kawo masa cikas. In ki ka cigaba da faɗa mana za ki dinga cilla rayuwar mutane a haɗari, tunda bamu san waye suspect ɗin a cikin mu ba."

Ta ja numfashi ta sauke ta yi shiru dan bata da bakin magana. Shima ya yi shiru, dan ya san tana cikin ruÉ—ani mai yawa. Sai daga baya ta ce, "ina son dawowa nigeria Hamma, na gaji da zaman nan, zan dawo gida."

"Dawowa gida ba na ki bane, dole sai kin ƙarasa abinda ki ka fara."

"Bazan iya cigaba da zama ba, zan dawo Hamma!" Ta faÉ—a tana kashe wayar, ta kwanta a kan tiles tana tunani.

Waye abin zargi, wa zata zarga a cikin mutane huÉ—u bayan duk duniya babu waÉ—anda ta yarda dasu kamar su huÉ—un?.

Saheer masoyinta kuma mijinta na gobe, ko aminiyarta Safeera wacce ta rikiɗe ta zama ƴar uwa, ko Suraj aboki kuma Yayanta wanda ya taimake ta tun tana ƙarama, ko Saleem da ya zama ɗan uwa a gare ta? Wa zata ɗauka ta yi cycling sunansa a matsayin munafuki?.

Ni kaina ban san waye na ɗauka waye na bari ba🤔

Nana Haleema.
[7/14, 2:53 PM] KRBBK: RDB2P55
Nana Haleema.

Islaha haka ta kasa komawa bacci, sai tunanin halin da Zainab take ciki take yi. Ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a nigeria, zaman ya gama isar ta, ta gaji tana buƙatar komawa gida. A haka ta kwana cikin tunani, haka ta tashi kanta ya yi nauyi ta rasa me zata yi. Tana idar da sallar asuba ta kira Saheer amma bai ɗauka ba, sai a lokacin ta tuna ashe fa su asuba bata yi ba.

A hankali ta ji ana buga ƙofar, ta miƙe ta buɗe suka haɗa ido da Maleek da Maryam. Maryam ta shiga ciki tana kallon ta, Islaha ta ce, "good morning madam."

Maryam ta riƙe fusksr Islaha ta ce, "you look so stressed, i hope you are feeling well?."

Islaha ta ɗaga kai ya ce, "Ahamdu lillah! I'm feeling better. Good morning" ta faɗa  tana kallon Maleek da yake kallon ta.

Ya É—an murmusa ya ce, "Ya jikin ki?."

"Alhamdu lillah."

"Ma sha Allah. Ki kwanta ki huta, kar ki damu kan ki." Ta É—an yi murmushi suka fita dan ta san bacci zasu je su yi, dan tana jin su tana jinsu sai uku na dare suka dawo daga yawo.

Ita kam kasa baccin ta yi gabaɗaya, tunani kawai take yi cikin rashin mafita da rashin sanin abinda ya kamata ta yi. Ta jima a haka, sai ga Sunaira ta kawo mata breakfast har cikin ɗaki, tana murmushi ta karɓa ta yi mata godiya ta koma. Tea ta sha, sai kuma arabian rice ɗin ta burge ta, ta ɗan ci kaɗan sannan ta sha maganinta ta koma ta cigaba da tunani mara ɓullewa.

A haka ta miƙe ta yi wanka ta ɗan kwanta ta yi bacci, zuwa sha biyu na rana ta farka, a lokacin ta ga kiran Hamma dana Safeera da na Suraj.

Hamma ta fara kira, yana É—auka ta ce, "Hamma an samu Zainab É—in?."

Ya ce, "ba a same ta ba islaha, amma ana bincikawa."

Zata fara yi masa kuka ya katse ta ya ce, "Allah in ki ka yi kuka zan ƙi nemo ta ɗin, baki da lafiya fa, in wani abun ya same ki fa?."

Islaha ta goge ido ta ce, "na damu ne."

"Ai na faɗa miki zan yi ƙoƙari ko? Ko ba ki yarda dani ba?."

"Na yarda."

"To ki kwantar da hankalin ki, saboda wannan maganar zan koma nigeria, in na zauna a nan bamu san inda lamarin zai je ba, tunda ke bakya nan gwara na koma kafin abin ya yi nisa."

Ta yi ajiyar zuciya jin zai koma gida saboda haka ta ce, "To Hamma, Ina kwana."

Ya É—an murmusa ya ce, "Matar Hamma, sai yanzu za ki gaishe ni?....."

Ta É—an yi murmushin da ya ji sautinsa, amma ya san murmushin bai kai zuciya ba, ta yi ne kawai dan ya ji daÉ—i.

Saheer ya ce, "lafiya lau, ya jikin ki?."

"Da sauƙi sosai, na ji daɗin maganin."

"Haka ake so. Allah ya ƙara lafiya."

"Amin Hamma."

"Zamu yi magana anjima." Ta gyaÉ—a kai sannan ya kashe wayar.

Sai ta É—an samu nutsuwa, jin Hamma zai koma Nigeria a nemo Zainab sai ta ji daÉ—i sosai, ta san in sha Allah rayuwar Zainab baza ta salwanta ba.

Sai a lokacin ta samu ƙarfin guiwar iya zuwa gidan Rehaan, ta miƙe ba tare da ta saka uniform ba, ta yafa mayafi a kanta tana kallon kanta. Atamfa ce a jikinta mai kyau, rigar bata kamata ba amma bata yi mata yawa ba, daidai jikinta, irin mai tsaga a gefen nan, an ɗan yi nata adon stones a waya, sai dogon hannu da ya zo har tsintsiyar hannunta.

Ita kanta ta san ta ƙara haske a zamanta na Jeddah, fatarta kamar madubi saboda ɗaukar ido da santsi.

A bayyane ta ce, "ina zaune waje É—aya dole na yi haske." Ta faÉ—a tana É—aukar wayarta, ta fita daga gidan zuwa gidan Rehaan.

Yau a falon downstairs ta tarar dasu duka biyun a zaune, abinda bata taɓa gani ba, bata taɓa ganinsa a ƙasa a zaune ba, ko yaushe yana upstairs.

Babu da wanda bata haɗa ido dashi a cikinsu ba, ta ɗauke kanta ta sunkutar da kai ƙasa ta ƙarasa ciki ta ce, "Good morning."

Jafar ya wani kalle ta ya ce, "morning! Yanzu safiya ce?."

Ta É—an yi shiru bata ce komai ba ya ce, "haka housemaid suke zuwa aiki sai lokacin da suka ga dama?."

Ta É—an sauke nunfashi ta ce, "bani da lafiya ne, shiyasa hakan."

Rehaan ya É—ago ya kalle ta jin wai bata da lafiya, kai tsaye suka haÉ—a ido, sai ta ga ya sake yi mata wani haske mai É—aukar ido, gashi ya rage gashin kansa, ya dawo da iya wuyansa, kuma an datse shi ya zama daidai babu inda ya fi wani tsayi.

Shi kallon ta yake yi jin ƙaryar da ta zabgawa Jafar, wai bata da lafiya bayan ya ganta jiya da Ubaid yana ja mata kunatu tana dariya. Sai kuma ya yi tunanin ina ruwansa, ya taɓe baki ya ɗauke kai bai ce mata komai ba.

Jafar ya ce, "Okay." Daga haka ya yi shiru bai ce komai ba.

Ita dai ta ga ji da tsayuwa ganin duk sun share ta sai ta kasa motsawa, bata son yin abinda zasu dizga ta dan ba É—auka zata yi ba, gwara ta cigaba da tsayuwar.

Jafar ya É—ago kai ya kalle ta ya ce, "ki je ki yi aikin ki, ki samar mana da wani abu mai daÉ—i."

Ta É—an É—aga kai ta ce, "Okay."

Rehaan ya miƙe tsaye, ya kalli Jazy ya ce, "Ta samar maka dai, ni kam bana so" ya faɗa yana ɗaukar wayar sa ya hau sama bai sake kallon ta ba. Islaha ta bi sa da kallo, dan da fulfulde ya yi maganar, tana ta mamaki dan ita bata ɗauka yana ji ba.

Kitchen ta wuce bayan ya bi shi da harara, ta shiga ta ja kujera ta zauna dam bata san me zata dafawa Jazy ba.

A lokacin Jafar ya shigo da sallama, ta amsa tana kallon sa, ya É—an tsaya daga gefen ta ya nuna mata screen É—in wayarsa ya ce, "Are you?."

Islaha ta kalli wayar, ta ga content É—inta na farko da ta yi magana akan zuwa hotel, wanda ya fi samun views da É—aukaka sama da ko wanne. Ta kalle sa ta ga ita yake kallo, sai ta É—aga kai ta ce, "Eh ni ce."
Chapter 77 · 0% Book details