← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 133

Sashe 124

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya É—an buÉ—e ido ya ce, "fifty millions for you? Oh God!" Ya faÉ—a yana É—an kulle ido.

Inda wata ce ba ita ba kuÉ—in ba komai bane, amma gani yake in ya bata kuÉ—in ta yi nasara kuma ta samu riba akansa, ga aurenta ga kuma kuÉ—in da zai bata. Kamar ma shine ya nemo ta ya ce zai aura, tunda daga aljihunsa zai fitar da kuÉ—in ya bayar, kamar shi ya ke son auren.

Bai ce komai ba ya cigaba da kallon takardar yana karanta rules É—inta bit by bit. Dan ya san sharaÉ—in irin wanna auren, indai ka saka hannu dole ka bi duk abinda mutum ya ce.

Abu na farko da ta rubuta zan cigaba da aikina, ko ƙasar waje aikinna zai ta babu ruwanka. Ina da wanda nake so kuma zan aura, zan cigaba da magana dashi kuma na haɗu dashi a duk lokacin da na ga dama, babu wanda zai yi min iyaka da ganinsa. Zan yi duk abinda nake so, baza a takura min ace sai na bi umarni ba, dan ba auren gaske na yi ba balle na yi biyayya. Ni ba ƴar aiki bace, bazan yi share-share da girki ba. Baza a hana ni fita duk inda na ga dama ba, in kwana ya kama na yi a waje zan yi babu ruwan mutum da ni.

Rehaan ya gama karantawa dan kaf cikin rules É—in bai ga wani rule na kirki a ciki banan ba.

Rule na ƙarshe ya kalla, ya ga shi da capital letter ma aka rubuta shi saboda girmansa, an rubuta NO INTIMACY RELETIONSHIP!.

Rehaan ya É—an É—ago ido ya kalle ta, shi wallahi ya manta da wani intimacy saboda ba ya gabansa a aurenta, ko kaÉ—an bai kawo hakana a ransa ba balle ya yi tunanin saka shi a cikin rules É—insa. Amma ita da yake abin yana zuciyarta gashi har ta rubuta, ko intimacy É—in me zai yi da ita oho mata.

Ya ɗan yi ƙaramin tsaki ya ce, "it's that all your rules?." Ta ɗaga kai alamun eh.

Ya ɗan yi shiru yana tuna alƙawarin da ya yiwa Abba sannan ya kalli Jafar ya ce, "Jazy pen."

Jazy ya ya miƙe masa shi kuma ya yi signing takardar da ta ba shi, sannan ya yi signing akan wata a kusa dashi. Ya sake yin signing akan guda huɗu ya cillar da biro akan table ɗin.

Itama ta ɗauki biron ta saka hannu zuciyar ta ko ɗar babu kamar yadda ya yi. 

Ta ɗauki ɗaya wacce ya rubuta rules ɗinsa, dan ko wacce copy biyu ce, da wacce zata riƙe da wacce zai riƙe, ta saka a handbag.

Daɗi ya cika mata rai dan iya saka hannun sa ya yi ya bata tabbacin zai ba da kuɗin, sai ta ke gani kamar Hamma ya fito ya gama, ta zama silar fitar Hamma daga cikin uƙuba.

Jazy ya É—an yi tafi yana kallonsu ya ce, "Finally, mr and mrs Rehaan."

Islaha ta ce, "ku zama shaida a gaban idanunku aka yi komai, Mr Jafar ka karanta don Allah" ta faÉ—a tana nuna masa takardar.

Ya girgiza kai ya ce, "No need Miss, kar ki damu. Rehaan bazai yi breaking ko wanne rule É—in ki ba, ya san duk abinda yake yi."

"A'a Mr Jafar, bana so a samu matsala nan gaba, dan gaskiya bazan jure ba."

"Baza a samu ba Islaha, tunda kuna ganin auren contract shine daidai da ku shikenan."

Rehaan dai kallon ta kawai yake yi yana mamakin ƙarfin hali irin nata, wai mutum kamar shi take faɗawa irin wannan maganar dan bata da hankali, har tana cewa wai bata so a samu matsala saboda baza ta jure ba.

In ba dan alƙawarin da ya yiwa Abba ba ita ta isa ya zauna yana faɗa tana ja? Ta isa ta sake ganinsa balle har ta samu damar yi masa shirme?.

Ya yi tsaki mai sauti ya miƙe tsaye ya ce, "ki turawa Jazy account details ɗin" ya faɗa yana barin wajan ko takarda ɗaya bai ɗauka ba.....

Nana Haleema.
[7/29, 12:06 PM] KRBBK: RDB2P93
Nana Haleema.

Islaha ta bi shi da kallo cikin takaici da ɓacin rai, kafin ta yi tsaki ta kalli Jafar da yake kallon ta ta ce, "shiyasa na ce ka kasance a nan, saboda ina so ku zama shaida da kai da ƙawata. Bana so a samu matsala nan gaba, duk ƙanƙantar matsala bazan jure mata ba. Na saka hannu na amince da auren nan saboda Hamma, zan rayu tsahon wata biyar saboda shi, in ba dan haka ba da ba mu sake haɗuwa ba."

Jafar ya ce, "saboda wanda za ki aura ki ka amince za ki auri Rehaan?."

Ta É—an yo murmushi ta ce, "ba iya auren yarjejeniya ba, zan iya sadaukar da komai saboda shi."

Ya girgiza kai ya ce, "Wow! Ban taɓa ganin irin wannan sadaukarwa ba. Yanzu fifty millions suka nema kuma za ku basu?."

Ta É—an yi ajiyar zuciya ta ce, "haka suka ce, da farko sun ce one hundrend millions, amma daga baya sun rage ya dawo haka."

"Ƴan sanda fa, kun yi magana dasu?. Haka kawai za ku ɗauki kuɗi a bawa wasu mutane a cikin daji, meyasa baza ku basu dama su yi aikin su ba?."

Islaha ta ce, "an yi komai Mr Jafar, abin ne kamar bazai yi aiki ba. Ni kuma ganin na samu dama sai na ce bara na gwada, in ya yi aiki shikenan, in bai yi ba sai mu nemi wata hanyar."

Jafar ya ce, "shikenan, za a tura miki kuÉ—in."

Islaha ta ce, "Thank you." A lokacin Rehaan ya dawo falon ya É—auki wayarsa.

Jafar ya kalle sa sannan ya kalle ta ya ce, "Thanks him."

Islaha ta kalli Rehaan sannan ta ce, "Da na godewa wannan ai gwara na kwana babu ci babu sha."

Jafar ya yi dariya mai sauti, ya kalli Rehaan da ya É—auki wayarsa ya koma ko kallonsu bai sake yi ba, kamar ma bai san dasu a wajen ba.

Islaha ta miƙe tsaye tana jinta wani iri, sai take ji kamar zuwa ta yi ta roƙosa kuɗi ya bata, sai ta ke jin kamar ta zubar da ajinta a wajensa. Sai kuma ta tuna zama dashi zata yi na wata biyar, shi kuma ya ba ta kuɗi.

Ta kalli Jafar ta ce, "na gode." Bai ce komai ba ya ɗaga mata kai, ta kalli Safeera da ta maƙale a waje ɗaya ko motsin kirki ba ta yi ta ce, "Safeera mu je." Safeera ta miƙe suka fita daga falon.

Tana fita Jafar ya ɗauki takardun yana karantawa, rules ɗin ya dinga bi yana karantawa, dan gabaɗaya shi bai wani nessecery abu a ciki ba, daga nata rules ɗin har nasan. Ya ɗan yi murmushi ya ajjiye musu, ya miƙe tsaye a lokacin Rehaan ya dawo.

Rehaan ya kalli Jazy ya ce, "amma wannan yarinyar nan bata da wani plan a ƙasa? Daga zancen contract sai ta kawo maganar kuɗi?."

Jafar ya ce, "Da gaske an yi kidnapping É—in wanda take so kuma zata aura, a gidanau take rayuwa, shine ya É—auki duk wani responsibilities É—inta. Zata iya É—aukar komai saboda dashi, dan ta yarda ta zauna da kai na wata biyar saboda shi a wajenta ba komai bane."

Rehaan ya girgiza kai cikin ko in kula ya ce, "dole ta yi komai saboda shi, abokin É—an iska shima É—an iska ne."

Jafar ya kalle sa ya ce, "auren ta da dai za ka yi, bai kamata a dinga jin waÉ—anan kalaman a bakin ka ba."

Ya ce, "Ikon Allah, shi kuma ita yake so, ya rasa abinda zai so sai wannan."

Jazy ya ce, "ni na tafi, ina da abinda zan yi. In ta turo min details É—in zan tura maka, ni ba É—an aikin ka bane" ya faÉ—a yana fita daga falon.

Islaha yadda aka ɗauko su haka aka mayar dasu, Safeera duk ta gigice ta kasa cewa komai sai da suka sauka daga motar, suna shiga gidan su Saheer ta riƙe hannun Islaha ta ce, "Islaha daman da gaske ki ke? Wayyo Allah, ban taɓa tunanin zan ga Rehaan ido da ido ba sai yau. Ashe haka yake da kyau? Ashe a zahiri ya fi kyau Islaha. Wow! Gaskiya kina da sa'a ƙawata, ke me sa'a ce."

Islaha ta kalle ta cike da takaici ta ce, "ji don Allah, akan wancan banzan duk kin wani rikice, ni ki sakar min hannu" ta faɗa tana ƙwace hannunta.

Sai kuma ta ce, "Don Allah ki bar wannan shirmen, ni bana so kowa ya ji maganar nan, ki riƙe wannan amanar don girman Allah. Bani da buƙatar a san na yi aure balle a san wanda na aura, ki rufe maganar nan, ko Saleem kar ki faɗawa, na yarda dake shiyasa na je har can da ke."

Safeerq ta ce, "Meyasa bakya so a sani?."

"Kin ga yanayin da auren ya zo, ba aure ne da zai dawwama ba, ba aure ne kamar ko wanne ba. Na rantse da Allah bana son ganin fuskarsa, ko sunansa bana so a kira, ni kaɗai na san wulaƙancin da ya yi min, ni kaɗai na san irin ɗacin da dasa min a zuciyata...."

Ta dakata da maganar tana tuna yadda ya dinga jifanta da kalaman banza sannan ta ce, "amma na amince saboda Hamma kawai, zan je na zauna dashi saboda Hamma, zan dawo saboda Hamma."

"In sha Allah bazan faɗa ba, za ki same ni da riƙe miki amana in sha Allah, kar ki damu."

Sai kuma ta dafe kai ta ce, "Ni wallahi danasani nake yi, sai nake ji kamar na cutar da rayuwata, kamar ban yi daidai ba, kamar abinda na yi zai canja rayuwata, kuma duniya zata ce na aure kafin na auri Hamma, za a dinga cewa bazawara Hamma ya aura. Innallahi, wallahi bana son hakan ko kaÉ—an."

Safeera ta girgiza kai tana binta da kallon daga baya kenan sannan ta ce, "Islaha kenan, sai da na faɗa miki, na ce ki tsaya ki yi tunani, amma ki ka ƙi."
Chapter 124 · 0% Book details