← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 133

Sashe 24

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"TabÉ—ijam! Ni zaku yaudara? Ni za ku saka na dinga tura mu ku kuÉ—i a banza ba tare da kun yi min aikin komai ba?. Kun san wacece ni, kun san me kunka É—aukowa kan ku?."

"Kawai ki yi haƙuri ki basar, kuɗi kam sun zo kenan. Ko sama da ƙasa zata haɗe baza mu dawo dasu ba wallahi, gwara ma ki rufawa kan ki asiri a bar maganar."

"Wallahi baku isa ba, dole ku dawo min da kuÉ—ina, tunda baku yi aikin da na saka ku ba. Baku isa ku ci min kuÉ—ina a banza da wofi ba."

"Batun dawowar kuɗin ki babu, sai dai a tara wani lokacin amma ba yanzu ba. Dan wallahi baza mu bada kuɗin nan ba, in kuma ki ka matsa akan sai mun bayar za a yi taɓare."

"Wallahi sai kun bayar, in ba haka ba zan nuna muku bani da mutumci, nima ƴar tasha ce. Abu mai sauƙi ne a wajena na saka ƴan sanda su kama ku."

Ya yi dariyar shaƙiyanci ya ce, "to ki saka a kamu mu ɗin mana, in aka kama mu sai muga damu dake su waye zasu fi shan wahala a wajen ƴan sanda, tsakanin mu dake wa za a tura gidan yari. Aikin sace yarinya ki ka saka mu, kin ga kece babbar mai laifi ba mu ba. Kuma ke kin san ba ki isa mu rufa miki asiri ba, sai kowa ya san aikin sace yarinya ki ka saka samu."

Ta yi shiru ta rasa abinda zata ce, ta rasa abinda zata furta wanda zai yi daidai da abinda suka faÉ—a mata, dan sun É—aure mata baki.

Ya ce, "kawai ki basar a cigaba da harka, zamu cafke a wani lokacin. Amma wannan dai sun zo kenan, kawai ki bar zancen." Kafin ta yi magana ya kashe wayar, tabi wayar da kallo cikin wani irin yanayi na damuwa da tashin hankali.

Ta ajjiye wayar ta kama ƙugu ta ce, "Dani suka baga wasa ba tare sa na sani ba? Meyasa ban nemi ganin Islaha ba tun farko? Yanzu gashi sun ci kuɗina a banza a wofi, ina nan na saki jiki tana hannun mu ashe haukan banza nake yi."

Sai ta dafe kai cikin ƙunar rai, dan an kwance mata lissafi ya farko, an dawo da ita farko, sun warware mata tufkar da ta jima tana yi. Ganin wanda yake yi mata waya ya sakata dafe kanta gabanta yana faɗuwa, a bayyane ta ce, "me zan faɗa masa ne? Me zan ce masa?."

Kiran ya katse bata ɗauka ba, wani ya sake shigowa, ta haƙura ta ɗauka kafin ta yi magana ya ce, "ya haka? Yarinyar nan nake gani fa, ya muka yi dake?. Sai da nace ki bar komai a hannuna ki ka ce zaki iya, gashi kin kasa yin komai."

Cikin damuwa da sanyin murya ta ce, "Wallahi Allah yaudara ta yaran na suka yi, ashe basu ne suka É—auke Islaha ba."

"Waye ya É—auke ta kenan?."

"Wallahi ban sani ba, kawai amfani suka yi da sace ɗin da aka yi suka ce min sune suka sace ta. Suka dinga karɓar kuɗi a hannuna, suka dinga sakawa ina basu kuɗi ace ƙarya suke yi."

"Amma ya aka yi hakan ta faru? Waye ya sace ta É—in?."

"Wallahi ban sani ba, hakan ya nuna min akwai wasu a ƙasa bayan mu."'

"Yanzu meye abin yi?."

"Zan san duk abinda zan yi in Allah ya yarda."

"Ki tabbbatar kin yi abinda ya kamata, kin san halin yarinyar nan, in baza ki iya ba ki faɗa min ni nayi maganinta. Wallahi Allah in na ɗaura ɗammarar yaƙi da yarinyar nan bazata kwana da rai ba."

"In sha Allah zan yi ƙoƙari ranka ya daɗe" bai ce komai ba ya kashe wayar. Ta cillar da wayar a kan kujera ta ce, "kai Islaha! Kina bani ciwon kai wallahi, ko wanne tsautsayi ne ya saka aka karɓe ki a gidan nan oho. Ya Allah ka kawo min mafita, ka fitar dani daga ruɗanin da nake ciki."

       ••••••

Da wuri suka je asibiti saboda aikin Baffa, suna tsaye aka shiga da Baffa da Kawu theater room, su kuma suna tsaye suna yi musu fatan fitowa lafiy. Islaha ta zauna akan kujera tare da yin shiru abubuwa da yawa suna nuƙurƙusar zuciyarta. Mafarkin da tayi a daren jiya ne yake dawowa cikin kanta, ta lumshe ido ta tallafe haɓa ta yi shiru tana tunani kala-kala.

Saheer da Sadik duk suna lura da canjinta, suna kula da yadda take keɓe kanta ta yi shiru tayi tagumi. Ko ka je kana yi mata magana bata ji ba saboda tayi nisa a cikin tunani.

Adda ta zauna kusa da ita ta ce, "Islaha lafiya dai ko?." Ta kalli Adda tana ƙaƙalo murmushi ta ce, "Lafiya lau Adda."

"Amma ki ke tunani?."

"Ina tuna a inda na kasance kwanakin da suka wuce."

"Allah ya isan ki, Allah ya shiga tsakanin ki da waÉ—annan mutane." Ta amsa da amin ta yi shiru bata cewa komai.

Tana ɗaga ido suka haɗa ido da Saheer, sai ta ɗauke kai ta miƙe a sanyaye ta bar wajan tana tafiya a hankali dan bata so ya takura mata da tambaya.

Saheer ya kalli Sadik bayan ta ɓace daga wajen ya ce, "bata faɗa maka komai akan ɓatan nan nata ba? Ni zuciyata tana faɗa min akwai wani abun da ba daidai ba, kamar akwai abinda take ɓoye mana bata so mu san dashi."

Sadik ya kalle sa yama ɗan taɓe baki ya ce, "kamar me ka ke gani?."

Saheer ya kalli inda ta bi, ya kalli Sadik sannan ya ce, "meyasa bata so a cigaba da case ɗin nan? Meyasa ta ƙi bada wata alama da za a gane masu hannu a sace ta?. Na san halin Islaha, tana da wayo da saurin riƙe abu komai ƙanƙantarsa, amma ace ta kasa riƙe wani abu ko yaya ne da zai zamar mana shaida akansu?. Sannan meyasa jikinta yake a sanyaye kamar wacce aka yiwa wani abun?. Kana kallo tunda ta zauna take tunani, meye ya faru a can da bata so mu sani?."

Sadik ya ce, "kai ma baka sani ba, ni ta ya zan sani Saheer? Wannan amsar ai tana wajan ka."

Saheer ya yi shiru kafin ya ce, "akwai abinda yake ba daidai ba, akwai abinda take ɓoye mana bata so mu san dashi."

Sadik bai ce komai ba, a ransa yana ayyana dan ma baka ga maƙudan kuɗin da ta dawo dasu bane, na tabbata da kaima zaka ɗarsa wani abun a ran ka.

Tabbas yana zargin Islaha akan kuɗin nan, dan ya san bata da hanyar da zata samu dala ɗari balle rafar dala, ya yi shiru da maganar ne saboda ta roƙesa akan kar ya faɗa, amma da sai ta faɗa masa inda ta samu. Kuma roƙon nasa da ta yi akan kar ya faɗa ya sake saka masa zargi, dan gaskiya shi zargi yake ta bada kanta a bata wannan kuɗin. Amma kuma sai ya tuna wanne ɗan wahala ne zai bata wannan kuɗin dan ta bashi kanta? A lokaci ɗaya dai bazata samu ba, sai an ɗan saba.

Islaha tana barin wajen elevator ta hau ta yi nisa da floor É—in theater da suke, yana buÉ—ewa ta fita ta tsaya ta jingina da bango cikin rashin sanin abinda ya kamata ta yi a lokacin.

Kuɗin nan da ta ɗauko yana damunta sosai, ta yi danasani yafi cikin kwando, sai dai danasanin bata da amfani, tunda ta riga ta aikata. Danasani akan abinda ya riga ya wuce ɓata lokaci ne. Tana so ta yi focusing akan abinda zai faru a gaba,  amma ta rasa abinda ya kamata ace ta yi.

Ta sauke numfashi tana cire facemask É—inta, ta lumshe ido tana tuna hanyar da ya kamata ta bi wajan ganin ta samo kuÉ—in nan ta biya shi. Dan gaskiya sai ta biya, baza ta zauna da bashi a kanta ba, mutuwa ake yi ko yaushe, in ta mutu da wannan kuÉ—i ta cewa Allah me?. Bashi da yake hana kwanciyar kabari, haka kawai ta jawowa kanta bala'in lahira bayan wanda ta bari a duniya?.

Bata san adadin lokacin da ta kwashe a haka ba, tana zaune ta jingina ta rufe ido ba tare da ta san tunanin me take yi ba.

Maganar da taji a nesa da ita ya saka ta buÉ—e idanunta, ta ga likitoci a zagaye da wani farin mutum ya saka black É—in suit ya juya baya yana magana.

Yadda suka mayar da hankali suka ba sa attension ɗinsu zai baka tabbacin ba ƙaramin girmama sa suke yi, yadda suka nutsu kowa yana magana da girmamawa zaka san ba ƙaramin mutum bane. Islaha mamaki take yi ganin yadda duk suka nutsu, ta ɗan taɓe baki amma still kllon wajan take yi.

A hankali ya juyo yana yiwa na gefen ta magana, a lokacin taga gefen fuskarsa sanye da blue É—in facemask da farin glasses a fuskarsa, kafin ya waiwayo gabaÉ—aya kuma ya yi gaba sun binsa a baya kamar jela.

Ta taɓe baki ta sake rufe idonta, sai kuma ta buɗe da sauri tana shaƙar ƙhamshin turaren da ya dabaibaye wajan da take. Cike mamaki ta ce, "kai! Wannan ai ƙhamshin turaren wancan baturen da ya sace ni ne."

Sai kuma tayi sanyi ta ce, "babu lallai shine kuma ai" ta yi shiru ta gyara zaman ta dan bata san lokacin da zata bar wajen ba.

Wayar ta yi ƙara, ta duba ta ga Hamma ne yake kira a karo na babu adadi, ta yi ajiyar zuciya ta ɗauka ta saka a kunneta. Inda take ta faɗa masa, ta kashe wayar ta yi shiru, bata so yazo ya tsare ta tambayoyin abinda yake damunta, kuma gashi baza ta iya ɓoye masa inda take ba shiyasa ta ɗauka.

A kan idanunta ya ƙaraso inda take, ya zauna a gefenta ya ce, "an yi tiyata cikin nasara."

Ta É—an yi murmushi ta ce, "Allah ya basu lafiya."

"Amin."

Ta yi shiru bata ce komai ba shima bai sake magana ba, ta kalle shi suka haÉ—a ido alamun daman shi kallon ta yake yi.
Chapter 24 · 0% Book details