Sashe 106
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baffa ya ce, "Waye bai san gidan Alhaji AbdulAziz ba? Ai ba ɓoyayyen mutum bane, da halayensa dana ƴaƴansa duk basa su ɓuya ba. Zan yi magana da Islahan, in ta amince zan kira ka na faɗa maka, in bata amince ba ma zan sanar da kai. Ka san yaran yanzu, ba kasafai suke amincewa da irin wannan haɗin ba, ni kuma bana so na yi mata dole dan ta kasance ba ni na haife ta ba."
Alhaji Rufa'i ya ji daɗin kalaman Baffa ya ce, "wannan gaskiya ne. Ka faɗa mata zai zo su ga juna, ta ɓangarensa daman mahaifinsa ya bawa zaɓin fitar masa da mata, ka ga ita ake jira a yanzu."
"In Allah ya yarda zamu yi magana da ita, ta tafi aiki da yanzu zan kira ta."
"Babu komai, ayi abun a nutse. Muna da saura kwanaki a gaba. Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Baffa ya amsa da amin, ya raka shi har ƙofar gida sannan ya dawo.
Baffa ya sauke nunfashi yana jin daɗi a ransa, domin mafita Allah ya kawo masa a lokacin da yake tsaka da nemanta. Ya ji daɗi da Saheer baya nan, yana fatan kar ya dawo har sai an ɗaura auren Islaha da wannan yaron da ko sunansa bai sani ba. Mama sai ta jiƙa Saheer ta shanye, Allah ya ɗaga Islaha ya kai ta babban gida, inda rayuwarta zata yi haske, inda zata yi farin ciki ta samu cigaban rayuwa.
(me ya canja Baffa ne?😱🤔).
_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.ðŸ™ðŸ»ðŸ˜_
Nana Haleema.
[7/23, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P78

••••••••
Abba yana zaune a gaban Daada yana faÉ—a mata yadda aka yi. Daada yi guÉ—a cikin murna, ta yi hamdala sannan ta ce, "An yi nasara a matakin farko da ya kasance ba a yi mata miji ba. Yanzu sai jiran amincewarta, in Allah ya yarda zata amince da auren nan." Abba ya yi murmushi kawai bai ce komai ba.
Daada ta ce, "An faÉ—a musu bikin bazai wuce kwana sha uku ba dai ko?."
"An faɗa Daada, shiyasa mai riƙonta ya ce bazai yanke hukunci ba sai ya yi magana da ita, sanann sai ta ga Rehaan ɗin ta tabbatar zata aure sa. Dan ba a faɗa musu sunansa ba, na saka an ɓoye ne dan mu gwada yanayin su, kuma gashi ya bamu mamaki ya amince."
Ta washe baki ta ce, "Ai daga ganin laraba ka san da juma'arta, ni na san yarinyar nan ta samu tarbiyya mai inganci wallahi. Yau kwana zan yi akan sallaya ina faÉ—awa Allah, sai Ishlaya ta shigo ahlina sannan hankalina zai kwanta."
Abba bau ce komai ba, amma yana jin daÉ—i in ya ga Daada tana farin ciki. Daada ta ce, "a je a cigaba da shiri kamar yadda ya kamata." Ya amsa yana tashi ya fita.
Yana fitowa suka haɗu da Jafar zai shuga wajan Daada. Jaazy ya duƙa har ƙasa ya gaishe da Abba, Abba yana murmushi ya ce, "Ango ka dawo ashe?."
Jazy cikin da kunya da girmamawa ya ce, "Na dawo Abba."
Abba ya ce, "Jeka ku gaisa da Daadan ka zo ina neman ka."
Jazy ya amsa da to, Abba ya fita shi kuma ya shiga wajan Daada. Bai wani jima a wajenta ba, dan ba fuska yake samu a wajanta ba, kawai ya shiga ne dan Mamy tana cewa ya shiga, amma da bazai je ba.
Yana fitowa ya shiga ɓangaren Abba ya same shi a zaune a kan kujera. Shi kuma ya zauna a akan carpet yana jiran Abba ya yi magana.
Abba ya ce, "Jafar ina É—an uwan naka? Yaushe zai dawo?."
Jazy ya ɗan murmusa ya ce, "ya ce min nan da jibi in sha Allah zai shigo, daƙyar na saka zai zo ma, ya ce shi ba sai ya zo ba."
Abba ya murmusa yana gyaÉ—a kai ya ce, "Baturen bafulatani kenan, jini uku ne yake yawo a jikinsa. Ga jinin fulani, ga na indiyawa, ga jinin turawa tunda a burtaniya can ya girma, dole a samu iyayi kala kala a tare dashi."
Jazy ya yi dariya sosai amma bai ce komai ba. Abba ya ce, "Ai kuwa zuwa ya zamar masa dole, dan tare za a haÉ—a aurenku da kai dashi, kamar yadda Daada ta ce."
Da mamaki Jafar ya kalli Abba ya ce, "Tare kuma Abba?."
Abba ya ce, "Tare kuwa Jafar, dan har an yi magana da dangin yarinyar da Daada ta nace a kai, amma sun ce sai sun yi magana da ƴarsu in ta amince. Hmmm a ganinka akwai wacce zata ƙi wannan tayin ne?."
Jafar ya ce, "gaskiya babu Abba."
"Ka ga shima aurensa ya zo kenan."
Jafar ya ce, "Amma Abba wacece yarinyar? An yi bincike mai kyau a kanta?. Kar a biyewa Daada a yi abinda za a yi danasani, wacce zata zama natar Rehaan dole a tsaurara bincike a kanta, musamman irin wannan auren."
"An yi sosai Jafar, yanayin yadda Rehaan yake dole ayi bincike kafin ayi auren. Na yi bincike da kaina kuma na saka anyi, babu wanda ya buɗe baki ya faɗi aibun yarinyar. Duk wanda zai buɗe baki yabonta yake yi, kowa in zai yabe ta zai ce tana da kirki da hankali. Kuma marainiya ce gaba da baya, a gidan marayu ma ta tashi har ta girma. Daga baya ne ta dawo gidan su wanda ya yi adopting ɗinta, da shi zai aure ta amma ance mahaifiyarsa bata so an haƙura. Duk da ance gidan da take babu wata tarbiyyar kirki, matar da take riƙonta tana harkar kai yara ƙasar waje aikin gidajen larabawa, amma duk da haka ana yabon halinta fiye da na yaran da ya haifa. Wajen aikinsu, mutanen unguwa, gidan marayun da ta tashi duk na bincika, kuma alhamdu lillah!."
Jafar ya gyaÉ—a kai sannan ya ce, "ma sha Allah! Wacece Abba?."
Abba ya ce, "Sunanta Islaha Maddibo, ƙaramar ƴar jarida ce a wata ƙaramar gidan tv, ban riƙe gidan tv ba gaskiya, amma yarinyar ta ɗaukaka a idanun mutane, musamman matasa.
Jafar ya zaro ido ƙirjinsa yana bugawa ya ce, "Islaha Abba!."
Abba ya kalle sa ya ce, "haka aka ce sunanta. Ka santa ne?."
Jafar ya ce, "Na santa Abba, na taɓa ganinta a wani waje, har muka yi magana tana so na kawo mata Rehaan su yi interview."
Abba ya É—an girgiza kai yana murmushi ya ce, "to itace."
Jafar ya girgiza kai yana mamakin ikon Allah, yana mamakin wannan kwaÉ—o da chakwakiya, yana hango yadda abin zai kasance, yana hango rigimar da Rehaan zai yi akan wannan abun. Lallai Allah Allah ne, in ba Allah waye zai haÉ—a Islaha da Rehaan a matsayin mata da miji?."
Jazy ya ce, "itace wacce Daada take ta magana daman a kanta?."
Abba ya ce, "Wallahi itace, yarinya kamar ta yiwa uwata asiri, gabaÉ—aya hankalinta ya tashi a kanta. Kuma babban abin mamakin har yanzu yarinyar bata san da maganar auren ba, bata san za a yi aura mata wani daga gidan nan ba, balle kuma ta san Rehaan zata aura."
Jafar ya ce, "Ikon Allah!."
Abba ya ce, "me ka sani a game da ita?."
"Babu laifi Abba, ana yabonta sosai. Amma zan saka a yi bincike na musamman, in na ga wani abu mara kyau ko lokacin auren ya yi za a san yadda za a yi a fasa. Dan gaskiya bazai yu a yi auren mutum kamar Rehaan da wacce ba a san halinta sosai ba, zan tsaurara bincike mai kyau, in aka samu akasin alkhairi za a fasa."
Abba ya cr, "hakan yana da kyau, ka saka a bincika yadda ya kamata, bana so ayi abinda za a zo ana danasani."
Jafar ya ce, "Gaskiya ne kuwa."
Abba ya ce, "amma kar ka faÉ—a masa sai ya dawo, na san halinsa, ana faÉ—a masa ya fasa zuwa."
Jafar ya yi dariya yana hango dramar da za a kwasa dashi, musamman da ya kasance Islaha ce. Ya ce, "Bazan faÉ—a masa ba in sha Allah." Suka yi sallama Jafar ya shiga wajan Mamy.
Da Banisha suka haÉ—u a falon Mamy, ya yi murmushi hancinta kamar yadda Rehaan yake yi mata ya ce, "Kiddo ina Mamy?."
Ta ce, "Uncle Jazy Mamy tana apartment É—in Hamma Rehaan."
Ya riƙe hannunta ya ce, "zo ki raka ni."
Tare suka je har part É—insa, ya hau sama ya tarar da Mamy a zaune a falon Rehaan na sama, Mamy ta dafe kai ga Riyya tana rarrashinta.
Ya shiga da sallama ta ɗago ta kalle sa ta ce, "Jafar ƙaraso, ƙaraso ka ga abubuwan da na samu a ƙasan gadon ɗan uwanka."
Gaban Jafar ya faɗi, ya ƙarasa yana kallon layoyin da suke ajjiye akan center table. Ya kalli Riyya da take kuka, ya kalli Mamy dan itama kukan take yi.
Ya sanyaya murya ya ce, "A É—akinsa aka samu wannan Mamy?."
Riyya ce ta ce, "Eh! Mun zo yi masa gyara, shine Mamy ta samo wannan."
Ya kalli layoyin ya sake kallon Riyya ya ce, "Samo ashana da reza yanzun nan, ki taho da plate." Ta É—aga kai ta É—auko ta kawo masa.
Ya ɗauki layoyin bayan ya kira sunan Allah, ya farke ya zaro takardar ciki, bai tsaya karantawa ba ya saka musu wuta akan plate ɗin suka ƙone, yana ƙonawa yana karanta Auzubika bi kalmatillahil tammaat min sharri ma kalaƙ.
A kan idonsa suka ƙone ƙurmus ya ɗauki tokar, ya shiga banɗaki ya zuba a masai ya yi flushing. Ya fito yana kallon Mamy, cikin son kwantar mata da hankali ya ce, "Koma meye Mamy ya koma kansu in sha Allah, don Allah ki daina kuka."
Kamar jira take ta sake fashewa da kuka ta ce, "Jafar kashe Rehaan suke so su yi ne?."
Ya sauke numfashi ya ce, "waye yake shigowa nan?."
Riyya ta ce, "Babu kowa, ni ce kaÉ—ai nake zuwa, wani lokacin sai Janan ko Ikram."
Ya gyaÉ—a kai ya ce, "Kar ku damu, za a yi maganin koma waye. Mamy ki daina kuka."