← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 133

Sashe 11

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kyakykyawam mari ya sauke nata akan kuncinta, Ummi ta fasa ihu ta koma jikin mahaifiyarta tana kuka sosai.

Mahaifinta ya ce, "shashasha mara hankali, tunda nake ban taɓa shiga police station ba sai yau. Ke kin san furuci akan sai kin ga bayan mutum? Kin san girman kuskuren da ki ka aikata kuwa?."

Yayanta da yake tsaye ya ce, "wallahi akan wannan maganar sai ta yi zaman gidan yari."

Abba ya sake fusata matuƙa ya kalle ta ya ce, "meya kai ki, waye ya aike ki furtawa wani sai kinga bayansa?."

Ummi tana kuka a jikin babarta ta ce, "kuskure ne Abba, wallahi ni ban faÉ—a da niyar zan aikata ba."

"Yanzu sai ki fito da yarinyar, sai ki faÉ—a mana uban da ki ka saka ya sace ta."

Ta É—ago tana kuka ta ce, "wallahi Allah ni ban saka ayi mata komai ba, ban yi mata komai ba Abba. Tun daga lokacin ban sake tunawa na yi wata magana ba sai É—azu."

Abba ya ce, "ƙarya ki ke yi, tunda ki ka ce sai kin ga bayanta ke kika saka a sace ta, dan haka ki fito musu da yarinya."

Ta fashe da kuka ta ce, "wallahi ban saka a sace ta ba!."

Cikin faÉ—a Yayanta ya ce, "wannan ke kika sani, kotu bata san ba ke bace tunda kin furta. An samu shaida kuma kema kin amsa da bakin ki, iya wannan ya ishi kotu tura ki zaman gidan yari."

Mamanta ta ce, "ke waye ya aike ki? Waye ya faÉ—a miki ana wasa da irin wannan maganar?."

Ta share hawaye ta ce, "wallahi sai dai in wani ne ya yi amfani da kalamaina ya aikata, amma wallahi ni ban aikata komai ba."

Abba ya girgiza kai ya ce, "wannan ke kika sani, abinda hukuma ta sani kin fi kowa hannu a ɓatan yarinyar nan, kuma koda ta bayyana case ɗin bazai mutu ba, ko ya ya wai abun ya same ta za a ce ke ce."

Yayanta ya ce, "Abba in ta rasu fa? Ai tana mutuwa a hannunsu wallahi ita ta kashe ta, gidan yari zata tafi a É—aure ta É—aurin rai da rai."

Ummi cikin kuka ta ce, "na shiga uku! Wallahi ban yi komai ba. Ni haushi take bani ne kawai, na riga ta fara aiki amma tazo ta mamaye komai, ba a saka mu yin komai sai ita. Mu da muka rigata zuwa ba a yi mana abinda ake yi mata, akan idanunmu ake É—aukaka, ta koma kamar bamu rigata fara aiki ba."

"Ranar ma katin gayyatar Mr Ray aka bata, kuma ni chairman ya yiwa alƙwarin zan yi hira da duk wani babban baƙo, amma sai bai bani ba ya bata. Shine na ji haushi na tare ta har na faɗi maganar, amma wallahi Allah ban saka ayi nata komai ba."

Abba ya fusata ya ce, "rufe min baki ko na ɓalla ki, daman baƙin ciki ki ke yi nata kenan ko? Hassada ce take damun zuciyarki ko?."

Yaya ya ce, "ga illarta nan ta fara gani yanzu, dan wallahi babu mai fitar dake a case ɗin nan sai Allah, ki yi addu'a dan daƙyar baki yi zaman gidan kaso ba. Kin ga sai ki ƙara hankali, nan gaba kar ki sake furtawa wani kalma makamanciyar wannan balle ki ce sai kin ga bayansa."

Ita dai kuka take yi sosai ta ce, "Abba ka bani dama na gudu Lagos, don Allah."

Yaya ya harare ta ya ce, "ai in kika kuskura ki ka gudu kin ƙarawa wutar fetur wallahi, dan duk inda ki ke sai an nemo ki kuma baza a sassuta miki ba. In kina wannan tunanin ma ki daina, shashasha mara hankali."

Shi dai Abba bai ce komai ba ya bar wajen saboda ɓacin rai, Ummi ta cigaba da kukan rashin mafita, sai dai ta yi alwashin in har aka rufe ta to wallahi sai ta zama silar da za a kulle Muslim, sai dai ayi mutuwar kasko, a mutu har liman, baza a a rufe ta ita kaɗai ba wallahi.
[6/17, 11:58 AM] KRBBK: RDB2P07
Nana Haleema

Islaha bacci ta yi mai tsaho har asuba tana bacci, sai bayan an yi sallah sannan ta miƙe tana riƙe wuyanta da ya riƙe, sannan ga bayanta ya riƙe sosai saboda kwanciyar kan kujera. A hankali take sake kallon ɗakin tana tuna abinda ya faru, ita dai ta san ta tare masa hanya daga nan bazata iya tuna komai ba.

Wani tunani ya ɗarsu a ranta, ta miƙe a firgice tana duba jikinta, tana tatttaɓa wuyanta da fuskar ta amma bata ji wani canji da zai nuna an yi wani abu da ita baz Ga kayan jikinta a yadda ta kwanta, alamun ba a taɓa su ba, babu alamun an buɗe wani ɓangare na jikinta. Sai lokacin ta yi ajiyar zuciya, hankalin ta ya ɗan kwanta, tana sauke ajiyar zuciya a hankali.

Tana dafe da kanta, ta duba wayar ta taga lokacin sallar asuba ya yi, ta miƙe a sanyaye ta nufi inda ta yi alwala jiya da niyar sake yi.

Kayan jikinta duk sun dame ta, musamman undies ɗinta har wani zafi take ji a jikinta saboda yadda suka yi dauɗa, duk ta ƙyamaci kanta.

A haka ta shiga banÉ—aki sai kawai ta haÉ—a da wanka, ta yi wanka ta cire undies É—in ta fito dasu a hannunta, ta tsaya tana kallon kayan ta rasa me zata saka. Ta san dai bata da kayan sakawa, su É—in ne kawai. Rashin mafita ya saka ta mayar jikinta amma bata mayar da undies É—in ba, dan gaskiya baza ta iya mayar dasu jikinta ba, musamman pant É—inta, yafi komai damunta. Ta jawo bedside drawer ta cilla undies É—in a ciki, ta kalli undies É—in da ta saka da niyar duk ranar da zata bar gidan zata É—auke abinta. Ta kalli kanta tana tunanin anya ma kayan zasu yi sallah.

Tunawa bata da mafita ya saka ta fito ta dawo inda aka ajjiye ta tayar da sallar asuba jikinta a snayaye.

Ta ji daɗin jikinta, babu ciwon kai kuma zazzaɓin ya sauka gabaɗaya. Ta jingina da kujera tana lumshe ido tana tunanin halin da Baffa yake ciki, tana tunanin halin da masoyinta yake ciki. Ta san zuwa yanzu Hamma ya san an sace ta, ta san yana can cikin tashin hankali mai tsanani. Wayar ta ta ɗauka amma still no service, ta cillar da wayar a wajan tana sauke numfashi a hankai.

Kallon abincin jiya ta yi, duk suna wajan babu abinda aka taɓa, kuma Allah ya sani yunwa take ji, ta daure ta ɗauke kai daga kallon abincin ta rufe ido, tana ji kamar ta dinga dukan kanta har sai ta daina jin takaicin da yake damun zuciyarta.

A hankali ta ji an buɗe ƙofar, ta juyo tana kallon wanda ya shigo. Baturen Chef ne, ɗaure da apron a ƙugunsa sai wata maid a bayansa.

Ta zuba musu ido tana kallo suka É—auke abincin jiya, suka ajjiye mata sabo suka fita basu ce mata komai ba itama bata ce ba. Ta yi banza da abincin, ta rufe ido cikin rashin sanin abinda ya kamata ta yi.

Har gari ya yi haske Islaha bata motsa ba, sai ma gyara zama da ta yi a wajan. Sai da ta ji zata kashe kanta sannan ta ƙaraso ta zuba tea ta sha, bata sake kallon komai na wajan ba ta kwanta a kan carpet hawaye yana zuba a idanunta.

Rehaan kuwa da ya farka lokacin sallar asuba sai da ya dubata ta camera record É—in wayar sa, bai É—auko ta dan ta yi rashin lafiya ba, dole ya so ya ga ya take tunda ya san ta suma. Da ya duba ya ga yadda take bacci sai ya ja tsaki ya ajjiye wayar.

Bayan an idar da sallar asuba bacci yayi mai aji, hakalinsa a kwance kamar bai É—auke Æ´ar mutane ba, ya jima sosai yana bacci dan har rana ta fito bacci yake yi.

Sai gab da sallar azahar ya tashi, ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya, ya kwance gashinsa ya sauka har wuyansa. A lokacin ya ɗauki wayarsa daidai lokacin kiran Jazy yake shigowa.

Ya yi tsaki ya share bai ɗauka ba, ya fito falon tare da sakkowa ƙasa cikin takun isa da ƙasaita.

A kan kujerar dining ya zauna, babu abinda ba a ajjiye masa akan dining ba, komai yana ajjiye yana jiransa kamar banza.

Kiran wayarsa da aka sake yi, ya zubawa wayar ido ganin Jazy yana yawo a kai,ya ɗan girgiza kai ya ɗauka Jazy ya ce, "na san daman zaka ƙi ɗaukar wayata, kuma bazan fasa faɗa maka gaskiya ba Ray, ajjiye yarinya a gidan ka babban hatsari ne wallahi."

Bai kula shi ba, dan bashi da lokaci bashi amsa, dan bazai É—auki maganar sa ba sai ya yi maganinta. Jazy yana ji yana wasa da cokali ya san abinci yake ci, dan ya san lokacin cin abincinsa ne, dan shi yafi damuwa da yin lunch akan breakfast ko dinner.

Jazy ya ce, "malam kana ji ina magana fa." Nan ma ya yi masa banza bai ce komai ba.

Jazy ya ce, "Wallahi zan haɗa ka da Mamy. Allah in na sake yin magana ka yi shiru sai na kira Mamy na faɗa mata, sai na ce mata ka saka an ɗauko maka mace kana abinda ka ga dama da ita, Allah sai na haɗa ƙarya da gasakiya na faɗa mata."

"Daman ai kai maƙaryacin ne" ya furta a hankali yana cigaba da cin abincinsa.

Jazy ya ce, "kai ka san ya ka ke a gidanku, maganar nan tana fita an samu dama, yanzu za a dinga yaÉ—awa ana cewa daman halin ka ne ka saba. Meye amfanin ajjiye yarinya budurwa don Allah? Kai ko tsoron ta mutu a hannun ka baka ji? Ko dan kana ji da kanka, kai ga matashin mai kuÉ—i ko ta mutu a gidan ka babu abinda za'a yi maka?."

"Look Jay or Jazy. FaÉ—i matsalar ka."

"ga matsalata nan ina faɗa maka, ka ƙyale yarinyar nan ta tafi."

"In na ƙi fa?."

"Zan faÉ—awa Mamy."

"Wani ya riƙe maka hannu? Ka kira ta mana."
Chapter 11 · 0% Book details