Sashe 17
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kawai ta fashe da kukan rashin mafita, ta cusa kanta a ƙafafunta tana kuka mai sauti. Ta san ko bata yi mafarki ba Hammanta yana cikin wani irin yanayi, ta san Hamma yana cikin yanayin da dole hankalin sa zai tashi saboda rashin ta. Duk wanda zai damu da ɓacewar ta a bayan Hamma yake, duk wanda zai ɗaga hankalinsa akan hakan a bayan Hamma yake.Tasan tabbas zai iya yin kukan rashinta, balle kuma basu san inda take ba balle a ɗauki matakin nemo inda take.
Rauni ya sake mamaye mata zuciya, tana tuna yanayin da Hamma zai shiga, tana cigaba da kuka cikin baƙin ciki da ƙunar zuciya. Haushin baturen da bata san sunansa ba, suna sake mamaye mata zuciya.
Sai da ta gaji ta É—ago a hankali tana cigaba da kallon falon, sai a lokacin ta kula ashe ba inda aka ajjiyeta take ba, a falon da tazo neman ya fitar da ita take a zaune akan carpert, a haka bacci ya É—auke ta.
Ta lumshe ido hawaye yana cigaba da zuba daga idanunta, ta kalli agogo taga dare ya yi sosai har asuba ta kusa. Ta fara kalle-kalle tana neman inda zata ga banÉ—aki ta yi alwala ta kai wa Allah kukan ta akan halin da take ciki.
Ƙofa biyu kaɗai ta gani, sai stairs ɗin da taga ya hau a daren jiya, ta miƙe ta nufi ƙofa ɗaya ta buɗe a hankali taga bedroom ne mai girma sosai, ta taka kamar bata so ta shiga inda take tunanin banɗaki ne, ta shiga tayi alwala ta fito ta dawo inda take zaune.
Kallon jikinta tayi ta É—an tsaki, ji take kamar kayan jikinta baza su yi sallah ba, duk da basu yi dauÉ—a sosai ba amma sai take ji kamar basa su yi sallah ba. Tunawa da babu yadda zata yi sai ta tayar da sallah har lokacin asuba sallah take yi.
Footstep take jiyowa a hankali, ta juya ta gansa yana sakkowa kunnensa maƙale da airpot, yana motsa bakinsa alamun magana yake yi.
Hannayen sa duka biyun suna kansa yana tattare gashin kansa ya ɗaura band, sannan ya saka hular jallabiyar da take bayansa. Baƙar jallabiya ce a jikinsa mai dogon hannu, waccs ta yi masa kyau sosai ta haska fatar da take jikinsa. Tun kafin ya ƙaraso turarensa ya rigasa zuwa wajanta, ƙhamshinsa ya dabaibaiye falon cikin ƙaramin lokaci.
Yana juyowa suka haɗa ido da ita, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi sosai, sai take so ta tuna inda ta taɓa ganin fuskarsa ko da sau ɗaya ne. Tunani take yi a ina ta taɓa ganinsa, kamar ba a hotel ta fara ganinsa, zuciyar ta tana faɗa mata ta san shi a wani waje, kawai bata san a inda ta ganshi ɗin bane, kuma gashi ta kasa tunawa.
A lokacin taji ya ce, "Alright."
FaÉ—ar hakan da ya yi sai ta dawo hankalinta, ta kawar da tunanin inda ta san shi ta cigaba da kallonsa tana so ta ga ko zai yi mata magana.
Bai kalle ta ba, ta taka a hankali ya nufi ƙofa ya buɗe ya saka thumb print ɗinsa, ƙofar ta bada sauti kaɗan samnan ta buɗe, ya fita daga falon bai sake kallon inda take ba balle ta saka ran zai yi mata magana.
A sanyaye ta daina kallon sa, ta kalli gabas ta tayar da sallah tana hawaye, tana idaarwa ko addu'a bata yi ba ta ƙarasa wajan ƙofar tana ja ko zata buɗe amma bata buɗe ba.
Ta ƙarasa wajan window amma ta kasa ɗaga labulen wajan dan ba normal labule bane da ta saba gani, ta koma ɗaya tagar nan ma ta kasa dan duk iri ɗaya ne bata san ta ake amfani dasu ba, bata taɓa ganin irinsu ba. Ta glass ɗin window take hangosa tsaye da yaransa, sai murmushi suke yi shi kuma bata ganin fuskar sa.
Sai kuma taga ya juyo takowa zuwa falon, ta lumshe ido tana ji kamar da zuciyar ta yake tahowa, duk taku ɗaya da zai yi bugun zuciyar ta ƙaruwa yake yi, kamar wacce ta aikata masa laifi take jin tsoron zai kamata. A daidai lokacin ta ji an buɗe ƙofar an shigo, ta juyo tana kallo sa ganin ko kallon falon bai yi ba yana niyar wucewa sama.
Da sauri ta ƙarasa inda yake, muryar ta tana rawa ta ce, "ban san sunan ka ba..." Sai ta kasa ƙarasawa saboda hawayen da take riƙewa suka sakko daga idanunta.
Ta ja numfashi mai tsaho ta ce, "Babana yana asibiti........" tana faÉ—a ta fashe da kuka tana zubewa akan guiwar ta tana kuka sosai.
Kamar an dakatar dashi ya tsaya bai hau saman ba, ya juyo ya ga yadda take kuka kamar wacce aka yiwa rasuwa a lokacin. Ko maganar ta bata fita yadda ya kamata, kuka take yi sosai tana haÉ—e hannunta waje É—aya.
Islaha ta ce, "Ban san me na yi maka ka kawo ni nan ba, ban san me na aikata ka saka aka kawo ni ba. Da nace bazan ba ka haƙuri ba, tunda ban yi maka laifin komai ba, kaine ka yi min laifi bani ce nayi ba. Amma na haƙura, saboda rayuwar Baffa zan sauke kai ƙasa, saboda rayuwar Baffa zan yi abinda ban taɓa yi ba. Baffa ya cancanci fiye sa haka a gare ni, ya cancani nayi komai saboda shi."
Ta ja numfashi tana goge hawayenta ta ce, "ka yi haƙuri....." Ta faɗa tana lumshe ido hawaye yana cigaba da zuba a idonta. Hawayen baƙin ciki da takaicin sauke kai ƙasa da tayi, amma bata da mafita dole ta saka ta bashi haƙuri.
ÆŠan murmushi ya yi, ya É—an girgiza kai ya ce, "finally."
Islaha ta kalle sa ta ce, "Don Allah ka bar ni na tafi, ka ƙyale ni naje na cigaba da abinda yake gabana. Tunda na baka haƙuri, komai ya ƙare daga wajen nan."
A lokacin ya juyo a hankali ya kalle ta, bai yi magana ba sai É—aga kai da ya yi kawai, ya hau sama bai sake kallonta ba.
"Mugu kawai, Allah ya isa tsakanina da kai, kar ka bari na tafi ɗin, in ka ga dama ka bari sai naman jikina ya koma ƙashi sai ka bawa karnuka. Saboda Baffa kaɗai na baka haƙuri, wallahi da baka isa na sauke kai ƙasa ba. Bana bada haƙuri akan haƙƙina, in ka ga na bada haƙuri nasan laifi. Zamu sake haɗuwa wani lokaci, a lokacin zaka tabbatar da bana sauke kai ƙasa wallahi."
Rehaan yana jin ta, ya yi murmushi dan shi kallon mai taɓin hankali yake yi mata, yanzu zata yi maganar hankali in anjima ta yi maganar shirme.
islaha tun tana kukan da ƙarfinta har ta gaji, ta koma sauke nunfashi idanunta biyu har gari yayi haske. Shiru gidan babu motsin kowa, ko ina tsitt kamar babu mutane a cikinsa.
Motsi ta dinga ji, ta zubawa wajan ido sai ta ga an fito daga wata ƙofa an shigo inda take da sallama, ta kalli wanda ya shigo ganin Chef ne bature, ɗaure da apron a ƙugunsa, ya ƙaraso ya ajjiye mata tray bai ce komai ba ya koma ƙofar da take tunanin kitchen ne.
Ta kalli abincin ta ga gabaÉ—aya english breakfast ne, sai wani munafukin kofin shayi kamar na yara. Ta yi tsaki ta É—auke kai ta cigaba da zama har bacci ya É—auke ta.
Shi kam Rehaan tunda ya hau sama ya manta da wata Islaha, bai tashi daga bacci ba sai sha biyu na rana. Ya shiga ya yi wanka ya shirya zai fita, tunawa sun yi da Mamy zai je su yi lunch a gida.
Tsaf ya shirya cikin ƙananun kaya, riga red colour, sai saka black ɗin jeans, ya kawo jacket black ya saka. Ya ɗauki comb ya gyara gashin kansa da gashin fuskarsa, ya zubawa kansa ido, har zai naɗe gashin sai ya fasa ya bar gashin sa ya sauka har wuyansa. Ya kawo face cap ya saka, yana gyara ta yana kallon kansa.
A hankali yake sakkowa ƙhamshin turarensa ya mamaye ko ina. Islaha ta ɗago kai ta kalle sa dan tashin ta daga bacci kenan. Basu haɗa ido ba dan hankalinsa yana kan waya yana dannawa, sai da ya ƙaraso falon sannan ya ganta ya yi kamar bai ganta ba.
Ya É—an yi tsaki dan ya manta da ita, yaso yace su mayar da ita tun asuba sai ya yi bacci, daga nan bai sake tunawa da ita ba.
Ganin ta zuba masa ido tana kallonsa sai ya kira kira Shams, ya ƙarasa ya buɗe ƙofar Shams ya shigo yana gaishe sa cikin girmamawa, da kai ya nuna masa ita yayi alamun a fita da ita.
Shams ya ce, "Okay Sir."
Rehaan ya fita Shams ya ƙarasa ya ɗauki tarkacen kayansa da suke ajjiye, waya ce guda ɗaya, zai laptop. Ita dai bata motsa ba har suka fita tana kallon su. A haka Shams ya dawo yana kallon ta da fara'a ya ce, "ƴar jarida kin yi free, mu je a mayar dake gida."
Ta miƙe a zabure ta ce, "da gaske ka ke ko wasa?."
"Da gaske nake, Æ´ar jarida Islaha."
Ta gyaÉ—a kai cikin tabbatarwa ta ce, "Wallahi sai nayi repoting É—inku a wajan Æ´an sanda."
Da mamaki yake kallon ta yana É—an murmushi ya ce, "Lahh, lallai yarinyar nan kina tsaurin ido, shikenan sai kin dawo" ya faÉ—a yana dariya sosai, dan shi kam tana bashi dariya.
Ya ce, "ina jiran ki" ya faÉ—a yana fita ya bar ta a falon dan ta É—an kimtsa yadda ya kamata.
Islaha duk ta ruÉ—e saboda murna, ta gyara hular kanta ta gyara zaman mayafin kanta, har zata wuce sai ta dawo da baya ganin rafar dalolin nan suna wajan har lokacin.
_Islaha monday ta kusa, kuma lokacin aikin Baffa ne. Na tabbatar har yanzu Sadik bai samu kuÉ—in aikin Baffa ba, kuma in ba mu biya kuÉ—in nan ba daidai yake da mun rasa Baffa._
Magana take da zuciyarta tana kallon kuɗin gabanta yana faɗuwa matuƙa a karo na farko a rayuwar ta.