Sashe 20
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sadik ya juyo ta kalle ta ya ce, "Islaha kar ki ce min saboda kuÉ—in aikin Baffa ki ka je kika sadaukar da kanki aka baki wannan kuÉ—in?."
Da sauri ta ɗago ta kalle sa tana buɗe ido cikin firgici, ta dafe ƙirji ta ce, "Hamma Sadik! Zargin zina ka ke yi a kaina?."
"Dole a zarge ki Islaha, bani kaɗai ba, ko Saheer in yaji wannna tatsuniyar taki dole wani abun ya ɗarsu a ranki. Haka kawai wanda ya sace ki zai ɗauki waɗanan kuɗi ya baki ba tare da ya ƙaru dake ba?."
Ta goge hawayen da suka taru a idanunta ta ce, "Wallahi Allah ni ban aikata komai ba, abinda ku ke zargi ba haka bane. Mutumin nan ban san shi ba, ko sunansa ban sani ba, kuma ni ko hannuna bai riƙe ba."
Saleem da ya cika da mamaki ya ce, "To wani ɓangare daga sassan jikinki ki ka siyar masa? Na tabbatar haka kawai namiji bazai ɗauki wannan kuɗi a baki ba."
Ta dafe kai ta ce, "Ku yarda dani, wallahi sace ni yayi, sannan duk zargin ku a kaina ba haka bane. Rantsuwa nake yi muku da wallahi, ku yarda dani."
Safeera a sanyaye ta ce, "Islaha ba ƙin yarda muka yi dake ba, mun ji ya sace ki, kina nufin bayan ya sace ki da ya tashi sakin ki sai ya baki kyautar kuɗin? Kuma ya aka yi ki ka bar hannunsa? Sannan waye shi?."
"Na faÉ—a muku ban san sunansa ba."
"Meyasa ki ka ce a rufe case É—in?."
Ta sauke numfashi ta kalli Safeera a sanyaye ta ce, "kema zargina ki ke yi?."
Ta girgiza kai ta ce, "bana zarginki da fasiƙanci, amma zuciyata tana faɗa min kin san wani abu akan case ɗin nan. Meyasa zaki ce a kulle case ɗin? Ki bari hukuma tayi bincike a gano mai hannu a ciki mana."
Islaha ta ce, "Wallahi Allah ban san komai akan case ɗin nan, kawai na buɗe ido na ganni a wani gida, daga nan aka dinga kawo min abinci kamar ina gida. Abinci ake bani mai rai da lafiya kamar na hotel, shiyasa baku ga wahala a tare dani ba. Ac nake kwana nake tashi, tsabar sanyi sai da numfashina ya fara riƙewa. Sai daga baya naga asalin wanda ya saka aka ɗauko ni."
Sadik ya ce, "akan wanne dalili ya saka aka É—auko ki?."
"Saboda kawai nayi masa rashin kunya, yana so ya nuna min yana da ikon da zai iya É—auke ni. Shine kawai."
Sadik ya ja tsaki jin tana raina musu hankali, tana wata magana kamar a drama ko a tsatsuniya, ya kawar da kai dan tsaf zai iya zaginta, haushinta yake ji sosai, baya a dinga magana cikin rainin hankali.
Saleem ya girgiza kai ya ce, "kawai dan kin yi masa rashin kunya sai ya sace ki?...."
Ta sunkuyar da kai bata amsa ba, Saleem ya ce, "Hmm Islaha ba fa film muke kallo ba, ya kamata ki faÉ—a mana abinda ya faru, in kuma kina ganin sirrin ki ne ba sai mun san maganar ba sai mu cigaba da sabgar mu."
Sadik ya ce, "shine kawai, kai tsaye ta ce mana bata buƙatar mu san komai, shikenan sai muyi shiru. Rayuwarta ce ai ba tamu ba, ita ta ga zata iya ai."
Islaha ta yi shiru, bakin ta yayi nauyi ta kasa ce musu É—auko masa kuÉ—in tayi, nauyin kalmar take ji sosai a zuciyar ta shiyasa ta kasa magana.
Amma dan ta fitar da kanta daga zargi sai ta ce, "ni dai na faɗa muku wallahil azim ko hannuna bai riƙe ba, kuma ban siyar da ko wanne sassa na jikina ba. Wanda ya ɗauke ni kuma ban san sunansa ba, amma na san fuskarsa a yanzu. Kuma kuɗin nan aronsu na karɓo, kuma......" sai ta kasa ƙarasawa ta yi shiru tana kallon ƙasa.
Sadik ya yi murmushin takaici yana binta da kallon kin raina mana hankali ya ce, "kar ki damu Islaha, tunda Allah ya bayyana ki abinda muke fata kenan daman. Ummi ta fita daga zargi, yanzu waÉ—anda suka yi waya suna neman kuÉ—in fansa za a nemo. Ko da yake, tunda kin ce a rufe case É—in ai case close."
Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce, "Don Allah Hamma Sadik kar ka bari Hamma ya san labarin nan, don Allah kar ka ce masa ni na biya kuÉ—in aikin Baffa, ka ji?."
Ya É—aga kai ya ce, "akan me zan yi shiru, bayan ban san daga inda ki ka samo kuÉ—in ba?."
"Wallahi ban yi abinda ku ke zargi ba."
"Shikenan Islaha, bazan faÉ—a masa ba." Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "na gode."
Ta kalli Safeera da itama ita take kallo ta, ta mayar da ido ta rufe tana jin haushin kanta akan akan É—auko kuÉ—in da tayi. Danasani ya cika mata zuciya, da bata É—auko kuÉ—in ba da yanzu ta faÉ—awa hukuma kamanninsa an kamo shi.
Sadik ya ce, "Na kira Saheer bana samunsa, ina jin ya taho ne."
Ita dai ta yi shiru bata ce komai ba tana tuna yadda komai ya kasance a can gidan.
Saleem ya ce, "na faÉ—awa Muslim ya yi update akan bayyanar ki, mutane sun damu da rashin ki sosai."
Ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, ta jinginar da kanta a jikin ƙofar motar tana tunani kala-kala. Bata san haka kuɗin da ta ɗauko suke da yawa ba, da ta san haka suke da matuƙar yawa da bata ɗauko ba. Yanzu wacce hanya zata bi ta samo masa kuɗinsa ta biyasa? Yanzu a ina zata samo kuɗin da zata biyasa? A ina zata gansa har ta basa kuɗinsa?.
A ƙofar gida suka tsaya Saleem ya ce, "ki je ki huta." A sanyaye ta buɗe ƙofar ta fita ita da Safeera.
A hankali aka buÉ—e gate É—in gidan aka fito, tana kallon gate É—in idonta ya faÉ—a cikin na Saheer, da dawowarsa kenan ya shiga ya ajjiye kayan hannunsa ya fito.
Suna haɗa ido ta ji hawaye ya taru a idonta, gabanta ya faɗi tana tunanin da wacce kalma zata kare kanta a wajensa? Ta san bazai taɓa yarda a rufe case ɗin ba, dole sai an yi bincike ita kuma bata so. Saheer ya zuba mata ido yana kallonta cikin wani irin yanayi na kewa.
A hankali ta taka ta ƙarasa inda yake ta ce, "Hamma!."
Ya runtse idonsa cikin wani yanayi na rauni da sanyin zuciya, bai san lokacin da ya riƙo hannunta ya rungume ta tsam ba.
Duk da tana cikin wani irin yanayi, amma hakan bai saka ta ji abin baƙo ba. Duk da son da Hamma yake yi mata bai taɓa rungume ta baa, sau ɗaya ya taɓa haɗa jikinsa da nata lokacin da ta samu attack, amma tana hayyacinta bai taɓa aikatawa ba.
Sadik ne ya ƙaraso ganin ya riƙe ta gam yana lumshe ido yaƙi sakin ta, ya kalli inda suke yaga babu jama'a sosai, ya ƙarasa daidai kunnensa ya ce, "A kan hanya ka ke Malam, ka sake ta."
Kasa sakinta ya yi, dan ji yake in ya sake ta kamar za a sake cewa ba a ganta ba. Ita ta fara ƙoƙarin raba kanta daga garesa, jin hakan sai ya sake ta ya riƙe hannunta suka shiga cikin gidan.
Ya zaunar da ita a inda suka saba zama a harabar gidan yana binta da kallo. Sai ta sunkuyar da kai, dan a yau idanun Hamman nata ba irin wanda zata tsaya kalla bane.
"Matar Hamma, kina lafiya? Su waye suka É—auke min ke!?" Ya faÉ—a cikin murya mai sanyi yana kallon ta.
Ta É—ago ta kalle sa, a sanyaye ta ce, "Lafiya lau nake Hamma. Amma kai ma ka rame."
"ta ya hankalina zai kwnata ina can an ce min ba a ganki ba? Ga Baffa babu lafiya, ga ki kema kin ɓace. Ai dole na rame."
"Yanzu na dawo ai."
"Waye ya É—auke ki? Ina suka kai ki, basu yi miki komai ba?. Kin faÉ—awa Æ´an sanda komai akai?."
A sanyaye ta ce, "babu abinda suka yi min, kuma ni ban san wanda ya É—auke ni ba Hamma."
Ya ce, "Amma kin yi bayani yadda ya kamata a gaban Æ´an sanda ko?" Sai ta juyo ya kalli Saleem da Sadik da Safeera da suke tsaye suna kallon su ya ce, "anje wajan hukuma? Sun É—auki bayaninta yadda ya kamata?."
Sadik ya ce, "anje, amma ta ce a rufe case É—in."
Da mamaki ya ce, "Kamar ya a rufe case É—in?."
"Haka ta ce."
Ya kalle ta ya ce, "kamar ya a rufe case É—in, meyasa za a rufe matar Hamma?."
Ta sauke numfashi ta ce, "Saboda ni ban san shi ba, hasalima ba yaren mu bane ba fa, baya jin fulatanci kuma baya jin hausa. English ɗin da yake yi ma british ne, kana ji ka san ba ɗan ƙasar nan bane."
Saheer ya ce, "saboda haka kawai sai a kashe case ɗin? Saboda kawai ba ɗan ƙasar nan bane sai a kashe case ɗin?. Mu mun isa mu je ƙasar su mu yi abinda ya yi, sai shine zai yi ya ci bulus?."
Ta É—an É—aga kai ta ce, "kawai bana so ai ta wahala ne, domin baza a iya kama sa ba wallahi, babban mutum ne sosai. Kuma ni nafi so mu mayar da hankali akan rashin lafiyar Baffa shiyasa na ce haka."
Saheer ya bita da kallo yana ɗaga kai ya ce, "saboda hakan kuma sai waɗanda suka sace ki a ƙyale su sun sace banza kenan? So ki ke a rufe case ɗin, shi kuma ajjiye ki ɗin da yayi ya yiwa banza ko?." Ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba dan tasan bazai fahimce ta ba.
Ya kalli Sadik ya ce, "ku ji fa abinda take faÉ—a."
Saleem ya ce, "haka ta faɗa a police station, ta ce bata buƙatar a yi bincike akan case ɗin."
Ya bita da kallo tuhuma yana rolling idanunsa a kanta ya ce, "Islaha meyasa bakya so a bibiyi case É—in, kin san shi ne?."
Zata bashi amsa ya ɗaga mata hannu ya ce, "kar ki maimaita abinda ki ka faɗa min a farko, ki bani dalili mai ƙarfi wanda zai saka na amince."