Sashe 29
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita dai bata ce komai ba sai kiran Zainab da ya shigo wayar ta, ta É—auka take sanar da ita su haÉ—u a asibiti dan fita zata yi bata da aiki. Bata jima sosai ba suka fita ita da Safeera zuwa asibiti wajan Baffa.
A can suka tarar da Umman Safeera ita da Mama suna tattaunawa akan abinda ya shafe su. Suka gaisa da Islaha daga nan suka wuce wajan Baffa dan ance sun farka.
Da suka shiga Baffa idonsa biyu amma yana cikin raÉ—aÉ—i, dan a lokacin yankan yake yi masa ciwo sosai, kana ganinsa ka san yana cikin yanayi na zafi da ciwo. Dan haka basu jima a ciki ba, suka koma wajan Kawu suka tarar yana bacci.
Kiran Safeera aka yi a waya ta tsaya tana amsawa, ita kuma ta koma wajan su Umma da Mama. Daga can gefe ta hangosu a tsaye Umma tana miƙawa Mama wata baƙar leda, sai ta matsa kusa dasu dan ta ji me za a ce, bata sani ba ko akan tafiyar Umma ne, tana so ta ji dan ta sanar da Safeera su yiwa tufkar hanci.
Umma ta ce, "fasko ne kamar yadda ki ka ce, gashi nan nayi komai, visa za a buga min na tafi."
Mama ta karɓa ta ce, "kin tabbatar zaki iya? Kar sai na yi asarar kuɗi an yi visa da ticket ki ce baza ki je ba."
"Mai zai hana ni zuwa? Wallahi zuwa babu fashi sai dai in bani da rai."
Mama ta saka a aljihun doguwar roga ta ce, "tunda akwai gidan aikin a ƙasa ko yaushe za a iya cewa ki fito. Visa ba wahala take yi yanzu ba, dan haka ki zama cikin shiri. Na karanta miki tsarin ko?."
"Na haddace tsaf a kaina."
"Kar a same ki da saɓa wani abun. Gidan aikin ki duk wata a kuɗin najeria naira rubu ɗari biyar za a baki. Ɗari uku ta kamfani ɗari biyu naki."
"na amince da wannan."
Mama ta girgiza kai ta ce, "tare zaku tafi da Labiba, yadda Babanta yake kwance a nan tsaf zata je ta samo mana abin arzuƙi. Itama ta yi komai, lokaci kawai ake jira."
Umma ta ce, "godiya mu ke woman leader."
"Ko kefa, yanzu ki ka fito a mace, da kun zauna namiji yana sarrafa ku bayan ba wata tsiyar ku ke samu ba a wajensa ba?. Ƙarshen cika bakin namiji fa saki ne, to sai meye dan ya sake ki? Mtsww! A kan ki aka fara saki ko a kan ki za a gama?."
Mama hango ƙawarta na ƙarasowa, sai ta kalli Umma ta ce, "Jeki kawai Maimuna, za mu yi magana kawai." Umma ta fita a lokacin ta ƙaraso wajan.
Tana zuwa ta ce, "komai ya kankama kenan ko?."
Mama ta ce, "an sanu biyu, Labiba da babar Safeera."
"Na taɓa ki da alkhairi, an kuma samun wani gidan a Jeddah. Albashinsa har ya fi na gidan da Labiba zata je wallahi. Dan a wata ɗaya miliyan ɗaya da rabi zasu bayar, ban da alkhairin yau da kullum."
Mama ta zaro ido ta ce, "wayyo Allah, anya bani zan shirya mu tafi ba?."
Ta girgiza kai ta ce, "yarinya suke nema, mai jin turanci, mara ƙiba, mai son aiki. In zai yu a samu mai kyau, ƴar gayu dan basa son ƙazama."
Mama cike da zumuÉ—i ta ce, "a ina zamu samu wacce zamu tura musu?."
"Hanan baza ta je ba?."
"Bana tunanin Hanan zata je, dan tana samu a nan sosai. Baza su tafi su biyu ba, saboda babansu."
"Kin ga da Æ´ar rikon nan ta ki zata yarda itace daidai da abinda aka lissafa, yadda take da shegen iyayin nan da wuri zata yi saurin shiga."
Mama ta taɓe baki ta ce, "kar ma ki ɓata min rai, mu koma ciki mu cigaba da magana."
Islaha ganin suna tahowa tayi saurin komwa baya, ta yi shiru tana lisssafi a zuciyar ta. Miliyan ɗaya da rabi za a bayar duk wata, hakan yana nufin zata iya tara kuɗin wanda ta aro a ƙasa da shekara ɗaya.
Ta yi ajiyar zuciya tana tunani, ta É—an sauke numfashi cikin tunanin abinda ya kamata ta yi, dan gaskiya sai ta biya kuÉ—in nan hankalin ta zai kwanta. Ya kamata ta yi tunanin da ya kamata, indai zata samu kuÉ—i ta sauke nauyin bashi ko meye zata yi.
Dafata ta ji anyi daga baya, ta juya a firgice tana kallon wanda yake tsaye a bayan ta.....
[6/25, 11:14 AM] KRBBK: RDB2P20
Nana Haleema
Tana juyawa suka haÉ—a ido da Zainab, Islaha ta É—an sauke numfashi cikin tsoro ta ce, "kin bani tsoro Zainab." Zainab ta bita da kallo, kafin ta rungume ta cikin kewar ta ta ce, "na yi kewar rashin ki sosai Adda Islaha, na yi kewar ki."
Islaha ta riƙe hannunta tana murmushi ta ce, "nima na yi kewar ki Zainab. Ya na ganki haka, akwai matsala ne?."
Zainab ta É—an yi shiru kafin ta ce, "Adda Islaha Mama ce ta saka a sace ki, na ji da kunnena tana waya tana cewa a tabbatar an É—auke ki."
Islaha ta ja hannunta suka zauna a inda babu jama'a sosai, ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce, "ban gane ba, yi min bayani yadda ya kamata."
Zainab ta ce, "Ina nufin Mama ce ta saka a sace ki, saboda kina saka mata ido akan abubuwan da take aikatawa."
Islaha ta yi shiru tana tunani cikin ruɗani, kenan mutanen da suka sako ta a gaba suna da yawa, tunda ga wata maganar ma ta sake ɓullowa daga inda bata yi tunani ba. Bata nunawa Zainab firgici akan haka ba sai ta ce, "faɗa min damuwar ki Zainab."
Zainab ta sauke nunfashi ta ce, "Zaman gidan ya yi min zafi Adda, na gaji da zaman gidan wallahi. Abubuwan da ban yi zato ba suna ta faruwa, na kasa tsallake wasu abubuwan."
"Me ya faru?."
"Adda gabaɗaya kowa na gidan da kowa na gidan canjawa yake yi, ma'aikatan gidan Mama ta siye su, kowa a ƙarƙashin ta yake, shiyasa ba a taɓa jin ɓarnar da take cikinsa a bakin kowa ba. Da zarar maganar kuɗi ta shiga shikenan sai a canja.."
"Akwai wata mata da ta takurawa Mama akan a kaini gidanta, kullum sai an takura min da maganar matar. Wai in na je za a canja min makaranta, za a yi kaza da kaza. Ni na gaji, da kin yi aure gidanki zan dawo da zama kawai, gabaÉ—aya zaman gidan ya fita daga raina."
Islaha ta É—an yi shiru sannan ta sauke numfashi ta ce, "in aka kai ki gidan me zaki yi a can?."
"Nima ban sani ba, amma kamar ba abin arzuƙi zan aikata ba, dan matar kwata-kwata bata kwantan min a raina ba."
Ta girgiza kai ta ce, "kina ji, ki kwantar da hankali ki, babu abinda zai same ki sai alkhairi. Ina tare dake a ko yaushe a ko ina. Ki nutsu ki ji abinda zan faÉ—a miki."
Zainab ta ɗaga kai Islaha ta ce, "kar kuɗi ko wani abu ya ruɗe ki kamar Hafsa, ki cigaba da bijirewa, duk abinda za a ce miki kae ki yarda, ki nuna kw bakya ra'ayi. In aka takura ki amince ki je gidan, da zarar an tafi kai ki ki yi min waya ki faɗa min inda aka kai ki. Ni kuma a wannan lokacin zan haɗa hujja da nake son haɗawa akan su Mama da ma'aikatan gidan, in abin nan ya tabbata wallahi sai na yaɗa ta a ko ina, sai gwamnati ta san abinda take aikatawa da sunan riƙe marayu."
Zainab ta share hawaye ta ce, "in na bisu babu matsala?."
"Babu komai, Amma kafin ki tafin ki tabbatar kin sanar dani, yadda zan shirya komai na biyo sawun ki."
"Zan yi duk abinda ki ka ce Adda."
"Yauwa Zainab. Allah yana tare dake, bazai taɓa bari ki wulaƙanta ba in sha Allah."
"Allah yasa."
"Amin."
"Adda kayana duk sun yi min kaÉ—an, bani da kayan sakawa sosai."
Islaaha ta dafa ta, tasan yadda ake ƙarancin kaya a gidan marayu, ta san yadda kayan sakawa suke yankewa, ta san yadda yaran da basu kai matakin sana'a ba suke rasa kayan sakawa. Wani lokacin sai masu ziyara sun zo sun kawo kaya, a nan ne za a zaɓi wanda bashi da kayan sosai a bashi ya rage ko ya ƙara. Ita kanta ta shiga irin wannan yanayin, har ta kai ta kawo tana cire kaya ta wanke da daddare ta shanya,washe gari ta kuma mayarwa jikinta.
_(Ƴan uwa ga wanda Allah ya bawa dama, in an haɗa kayan sakawa na bayarwa, a dinga tunawa da yaran da suka tashi a gidan marayu. Kayan yara ko na manya, na maza ko na mata, a dinga taimkawa ba a san inda za a dace ba. Allah ya sa mu dace amin.)_
Islaha ta ce, "Akwai kayan da zan baki, sannan akwai kuɗin da zan tura miki, ki shiga kasuwa ki siyi ƙananun atamfofi ki bayar a gidan a ɗinka miki. Ba su Kamila suna ɗinki ba?."
"Suna yi Adda."
"To ki bayar a É—inka miki, nawa da zan baki ki basu su rage miki. Zan tambayi Safeera ma in tana dasu ta sake haÉ—o miki, indai ina da rai babu abinda zaki nema ki rasa Zainab."
Ta yi murmushi ta ce, "Allah ya bar min ke Adda Islaha, Allah ya baki miji na gari, mai kuÉ—i wanda zai É—auke ni na koma gidansa."
Ta yi murmushi ta ce, "Amin Zeey. Ina auren Hamma zan É—auko ki, kin gama zaman gidan nan in sha Allah." Zainab ta yi murmushi, suka cigaba da hirar gidan, har Zainab ta yi mata sallama ta tafi.
Bayan tafiyar Zainab Islaha ta yi shiru tana tunani, abubuwa uku suna yi mata yawo a cikin kanta, abubuwa uku suna kai kawo a tsakiyar ƙwaƙwalƙwar ta. Zainab, Mama da ta da ta saka a sace ta, uwa uba kuɗin mutumin da ta ɗauko, dan ya fi komai ɗaga mata hankali a halin da ake ciki.
Ta yi ajiyar zuciya cikin nauyin ƙirji, a lokacin Safeera ta ƙaraso ta zauna, suka ɗan cigaba da hira duk da hankalin Islaha baya tare da ita ko kaɗan, wani abun daban take tunani.
••••••