Sashe 90
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A daidai lokacin mararta ta murɗa sosai, bata san ta riƙe hannunsa ta matse ta saka kuka mai ƙarfi ba.
Kukan ta duk sai ta jawo hankalin mutanen da suke zaune a train ɗin, da sauri ma'aikatan suka ƙaraso wajan ta ana tambayar ta abinda yake damunta.
Shi dai takaici ya gama mamaye masa zuciya, gashi ta riƙe masa hannu ga mutane a kansu sai kallonsa ake yi kamar wani tv.
Ya ja siririn tsaki dan bai san me zai ce musu ba, gabaɗaya zaman jirgin ya ishe shi, ba ya son ganin fuskar yarinyar ko kaɗan. A lokacin wani ma'aiakcin train ɗin ya ƙaraso, ganin hannunta a cikin na Rehaan, sai ya kalli Rehaan sai ya ce, "Me yake damun ta?."
Rehaan ya É—ago ya kalle sa, ya harare sa ya yi masa banza bai ce komai ba, dan indai a kanta ne bazai yi magana ba, bai ga dalilin da zata shiga shiga rayuwarsa ko yaushe ba.
Train staff É—in ya ce, "she's your wife?."
Nan ma ya share sa yana ƙoƙarin zame hannunsa a hankali ba da ƙarfi ba, amma ta riƙe sosai ga zafin da hannunta ya yi yana ratsa fatar hannunsa.
Ta daina kukan sai hawaye kawai take yi, tana jan numfashi kamar mai naƙuda, a hakan ma dauriya take yi, ita kaɗai ta san adadin ciwon da yake nuƙurƙusar ta.
Ganin sun kafe shi da ido sai ya É—an kalle ta, muryarsa a hankali ya ce, "suna tambayar ki, ki faÉ—a musu me yake damun ki."
Islaha idonta yana rufe, ta buÉ—e ido ta kalle sa suka haÉ—a ido dan ita yake kallo, yadda ya ga fuskar ta ta koma sai jikinsa ya É—an yi sanyi, ba sai ance maka bata da lafiya ba, kana kallon ta kasan babu lafiya.
Ta ɗan miƙe zaune sosai sannan ta ce, "paracetamol za a bani kawai."
Da gaggawa aka kawo mata aka bawa Rehaan dan ya bata. Kamar ba ya so haka ya karɓa, ya miƙa mata yana kallon ta. Islaha hannunta yana rawa ta raba hannunta da nasa ta karɓa ta sha, ta koma ta kwanta ta lumshe ido, sai kuma ta tattare ƙafarta, ta haɗe da ƙirninta ta saka kanta a ciki.
Wayarsa kawai yake dannawa kamar bai san abinda yake faruwa ba, sai daga baya ya kashe ac tana kwance a haka tana jin sauƙin ciwon a hankali sai ciwon kai da ya dame ta.
Dan ita bata san irin ta ba, bata son ac a mota balle kuma a jirgi. Yanzu sai ac mota ta saka ta ciwon kai, ko za a saka tafi son a saka kaɗan, kar ta yi yawan da zata dame ta. Kafin su je Jeddah ta ɗan ji sauƙi, train yana tsayawa ya fita bai sake waiwayenta ba, itama ta miƙe tana tafiya a hankali, larabawa suna ta yi mata sannu, sai dai ta ɗaga kai tana fatan Allah ya sa bata yi staining wajan ba.
A haka ta fito, a lokacin rana ta buÉ—e sosai, ta tsaya daga can gefe tana ji kamar jiri yana É—aukarta. Bata san inda zata bi ta hau mota ba, dan ba a nan suka zo da Sunaira ba, nan arrived area ne, gabaÉ—aya bata gane wajen ba, ga ciwon da yake damunta.
Rehaan kuwa kai tsaye inda ya bar motarsa ya je ya ba da pass É—in ajiyar aka bashi, yana zaune yana kallon ta. Kallon ta yake yi, ba sai an faÉ—a ba, kai da ka ganta ka san gaske bata jin daÉ—i, yana so ya taimake ta amma kuma ba ya son abinda zai haÉ—asu a waje É—aya, shiyasa yake kaucewa, amma Allah ya sani yana so ya taimake ta musamman da take tsaye a kan titi kamar zata faÉ—i.
A hankali ya ƙarasa da motar kusa da ita, ya sauke glass a hankali yana kallon ta. Islaha idanunta a rufe suke, amma tunda motar ta zo kusa da ita ta ji ƙhamshin turarensa, ta buɗe ido suka haɗa ido, ta sunkuyar da kai ƙasa tana ji kamar ta faɗi.
Kamar ba ya son magana ya ce, "mu je."
Bata da yadda zata yi, in a son ranta ne itama baza ta shiga motarsa ba, amma da yake neman taimako take yi sai ta motsa daga inda take, ta yi kamar zata faÉ—i ta yi saurin dafa motar.
Rehaan ya ce, "ki shiga back seat" ya faɗa ganin kamar kafin ta ƙaraso front ɗin zata iya faɗuwa.
Islaha a hankali ta shiga bayan motar, ƙhamshin turarensa ya mamaye motar, ta jingina a hankali shi kuma ya ja motar suka tafi.
A hankali yake tafiya, babu sautin komai a motar, sai ƙarar wayarsa kuma baya amsawa. Idonta a rufe suke, tafiya kawai take ji ana yi, tafiyar mai laushi babu gargada, sai zaman ya yi mata daɗi sosai, dan ba a motsa ta balle ta ji wani abu.
A har suka je unguwar ya tsayar motarda yana kallonta ta mirror, idanunta a rufe suke har lokacin, yanayinta gabaɗaya ya koma na marasa lafiya, yana so ya ji me yake damunta amma sai ya ga kamat bai shafe shi ba. A lokacin ta buɗe ido suka haɗa ido, ta sauke ido ƙasa ta kalli unguwar ta ga har sun zo.
Ta ɗauki jakarta ta kalle sa ta ce, "Na gode." Bai ce komai ba ta buɗe ƙofar ta fita, shi kuma ya danna remote ɗin gate ɗinsa ya buɗe ya shiga, bai tsaya ya ga inda ta shiga ba.
Islaha tunda ta shiga ta kwanta a kan gado, Sunaira ta zo tana yi nata sannu da zuwa ganin bata da lafiya sai ta fita ta ƙyale ta.
Shi kuwa Rehaan yana ajjiye motar ya shiga cikin gidan, ya hau sama ya shiga wanka bayan ya fito ya yi sallar azahar ya kwanta bacci. Sai la'asar ya farka, ya sake yin wanka ya saka jallabiya ya sakko ya shiga masallaci ya yi sallah sannan ya fito. Yana fitowa ya shiga coffee bar É—in da yake kusa da gidan su, ya zauna tana duba menu, kafin ya yi order aka kawo masa black coffee da brownie, sai kuma biryani rice.
"Hii Rehaan." Aka faÉ—a ana zama a kusa dashi.
Ya É—ago kai suka haÉ—a ido da Ubaid, sai ya basa hannu suka gaisa kafin ya ce, "Hii."
Ubaid ya ce, "kwana biyu ina ka je? Bana ganin ka."
"Madina" ya bashi masa a nutse yana cigaba da cin abincinsa.
Ubaid ya ce, "Nima na je, mun je tare da Babyna, na rigata dawowa ne kawai."
Rehaan ya kalle sa yana mamaki, ya rasa meyasa Ubaid ya raina sa, ba ya iya ɓoye yana neman mata, har faɗa yake yi ya je da wacce ba matarsa ba Madina suna aikaita saɓon Allah, ko kunya ba ya ji faɗa yake yi kamar ba babban abu ya aikata ba. Sai kuma ya tuna shi ƙasar ce, ba wani abu bane a wajansa.
Ubaid ya ce, "wallahi ina son ƴan matan ƙasar ku, Allah ya yi musu wata baiwa ta musamman, wacce sai ka shiga za ka gane. Rehaan black sun haɗu sosai, akwai albarka a tare dasu. Irin abinda za ka samu a tare dasu bazai misaltu ba wallahi."
Rehaan ya ji kamar ya shaƙe masa wuya, ba ya son wannan maganar ko kaɗan, ɓata masa rai take yi ta fusata shi lokaci ɗaya. Ya daure ya share bai ce komai ba, haka kawai ya ji abincin ya fita daga ransa, ya kalle sa ya ce, "na faɗa maka ka daina bani labari ko?."
"Ina so kaima ka ɗanɗana ne shiyasa. In kana so zan turo maka ita ta kwana biyu a wajan ka, na yi maka alƙawarin za ka so hakan."
"No need"
Rehaan ya faɗa yana harararsa Ubaid shi kuma yana dariya, dan wani lokacin da gangan yake tsokanarsa, dan ya san ba ya so. Rehaan ya miƙe ya biya kuɗi ya fita yana jin haushi.
Yana shiga gida ya ji wayarsa ta yi ƙara alamun shigowar saƙo, da ya ga Ubaid ne sai ya yi tsaki ya jawo laptop ya fara abinda yake gabansa dan gobe yana da morning duty.
Waya yake yi ta ko ina, maganar harkar kasuwancinsa yake yi, gabaÉ—aya ya takura saboda amsa waya, wannan ya kira sa wannan ya kira sa. Ya jima a haka, sai dai ya tashi ya yi sallah ya dawo, har aka yi sallar i'sha yana a haka.
Maganar Ubaid ce ta faɗo masa a rai, sai ya tuna da saƙonsa ya ɗauki wayar ya ga ƙaramin video ne, kuma viewonce ya tura masa.
Kamar ya share kar ya buÉ—e sai kuma ya buÉ—e, video yana loading shi kuma yana kallon laptop É—insa.
Wani irin yarr ya ji a jikinsa lokacin da ji abinda yake fitowa daga video, ya kalli wayar sai ya yi saurin ɗauke kai ya kashe video, ya dafe kansa ya yi shiru cikin takaicin Ubaid wanda bai taɓa ji ba.
Ƙaramin video ne, babu fuskarsu amma akwai muryarsu cikin fitar hayyaci wanda ya ke nuni da dukka basa hankalinsu.
Wani irin dum dum dum haka ya ji zuciyarsa tana yi, ya runtse ido ya saki wayar ta faɗi a ƙasa, jin muryoyin yake yi yi har tsakiyar kansa, ya sauke numfashi yana jin haushi da tsanar Islaha tana mamaye masa ko wanne ɓangare na jikinsa.
Bai taɓa jin tsana mai muni lokaci ɗaya kamar tsanar ta ba, danasanin taiamka mata ya mamaye masa rai. Sai yanzu ya ke tunawa ashe ma tare suka je Madina da Ubaid ɗin, tunda ga shi ya ganta ita kaɗai babu shi.
Ya cize bakinsa cikin takaici, baƙin cikin taimaka mata yana yi masa dirar mikiya, ji yake kamar ya dawo da wajen baya, ya jawota ya zabga mata mari sannan ya cilla ta kan titi mota ta take ta. Da ana dawo da abinda ya wuce, da ya dawo dashi ya goge taimaka mata da ya yi a ranar.
A bayyane ya ce, "Allah ka yi maganin matan da suke zuwa ƙasar waje suna lalata mana sunan matan ƙasar mu, Allah ya shiga tsakanin mu dasu, ka yi mana tsari dasu gaba da baya."