← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 133

Sashe 131

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha tunda suka koma Adda ta saka a gaba da tambaya akan ya aka yi aka yi auren. Adda ta ce, "Ya aka yi? Me yasa Baffa ya yanke hukuncin aura miki wani ba Saheer ba?."

Islaha cikin rauni ta ce, "nima ban sani ba Adda."

"Meyasa ki ka amince bayan kin san wannan hukuncin nan na ki sai ya fi yiwa Saheer zafi fiye da zaman wajen masu garkuwa mutane? Aure fa Islaha."

"Adda babu yadda zan yi ne"

"Ban yarda ba Islaha; Da kin nunawa Baffa bakya son auren da bai yi ba miki ba. Yanzu da ki ka auri wani ya ki ke tunanin makomar Saheer zata kasance?. Daga wajen masu garkuwa da mutane ya fito, kuma dan rashin imani yana farfaÉ—owa sai a ce masa kin auri wani?."

Adda ta ɗora da cewa, "Gaskiya ba a kyautawa Saheer ba wallahi, yanzu shikenan duk yadda ya sakawa ransa auren ki sai dai ya haƙura?."

Islaha bata ce komai ba ta yi shiru, tana so ta faɗa mata babu wanda ya isa ya hanata auren Saheer, aurensa yana nan babu fashi. Tana so ta faɗa mata duk wuya duk runtse sai ta fito daga gidan Rehaan ta zo ta aure shi, tana so ta faɗa mata babu wanda zai rabata da Saheer. Sai dai kash! Bata so kowa ya san sirrin auren ta, bata so kowa ya san irin auren da ta ƙulla, dole ta ja bakinta ta yi shiru.

"Na san dai kuɗi ba sa gaban ki, balle na ce dan ɗan masu kuɗi ne ya saka ki ka amince. Amma duk da haka kin dakusar da kan ki, ba kowa ne zai yarda ba auren kuɗi ki ka yi ba Islaha. Mahaukaci ne fa aka ce, in ya kashe ki ya kashe banza, babu abinda aka isa ayi masa, tunda ba a shari'a da mahaukaci. Kin san da haka ka amince har aka ɗaura aure, ki ka bar Saheer da yake tsananin sonki, yake burin auren ki, yake burin ya ga ya samu kuɗin da zai mallake ki. Ko yaushe maganar bikin ku ce akan harshensa, shine ginin gida, shine lefe, shine kyautata miki, amma ke kuma ba ki riƙe amana ba wallahi!."

Safeera jin Adda ta fara wuce gona da iri sai ta yi caraf ta ce, "Adda duk abinda Islaha ta yi har ki ke ganin laifinta ta yi ne dan taimakon Saheer, ke kin san baza ta zaɓi kuɗi ta bar Saheer ba. Masu kuɗi nawa ne suka nuna suna sonta ta ƙi basu dama? Sai yanzu da aski yazo gaban goshi zata juya masa baya?."

Adda kalli Safeera ta ce, "kamar ya saboda shi ta yi? Ban gane ba, kina so ki ce ta auri wani zata tare a gidansa gobe saboda Saheer? Wannan ma tana daga cikin soyayyar da take yi masa kenan ko?."

Safeera zata yi magana Islaha ta ce, "ni dai ki yi haƙuri kawai, duk abinda ki ke tunani ba haka bane, za ki fahimta nan gaba, amma ban da yanzu."

"Me zan fahimta Islaha? Ai kin riga kin goge min hadda, kin ɓarar da duk yardar da na yi da ke, kin ri ga kin nuna min za ki iya zaɓar kuɗi akan Saheer. Meye Saheer bai yi miki ba?."

Mama da take shigowa falon ta ce, "faɗa mata dai, yau kin tabbatar da tsintacciyar mage bata mage, in ina faɗa miki halinta bakya ganewa, yau gashi ta nuna miki ita ƴar kunama ce. Ta zaɓi auren mahaukaci akan Saheer."

Adda ta kalli Mama ta ce, "wallahi ta bani mamaki, ban yi tunanin zata zaɓi mahaukaci akan Saheer ba. Kawai dan mahaifinsa yana da kuɗi, kuma dan ɗan uwan Rehaan Yola shikenan sai ta zaɓi auresa ta bar Saherr? Yanzu in ya tashi me za a ce masa?."

Hanan ta ce, "a faɗa masa gaskiya mana, ta zaɓi ɗan masu kuɗi mai taɓin hankali a kansa. Daman duk wanda ya siyi rariya ya san zata zubar da ruwa, duk wanda ya kalli Islaha ai ya san zata aikata goman haka."

Safeear fusace ta ce, "ke da ki ke maganar ba dan Islahan ba da yanzu..."

Islaha ta katse ta ta ce, "Safeera mu je gidan ku" ta faɗa tana jan hannunta suka fita da ƙarfi suka fita daga falon.

Suna fita harabar gidan ta fashe ta kuka, ta nemi waje ta zauna ta dafe kanta tana kuka mai tsuma zuciya wanda yake fita da sauti mai ratsa kunne.

Safeera ta tsaya a kanta ta ce, "ki bari a faɗa mu su, ki bari su san kin sadaukar da rayuwar ki ne saboda Saheer, ki bari su san kin yi abinda su basu yi ba saboda shi, ki bari su san kanki ki ka ɗauka ki ka kai wani waje saboda Saheer. Sai wani ƙananun mganganu suke yi, ai kowa ya san baza ki taɓa zaɓar mai kuɗi ki bar Saheer ba. Ban taɓa jin haushin Adda kamar yau ba, na ɗauka zata yi shaidar ki, sai ga shi ta biyewa Mama. Ba dan ke ba da yanzu ai Saheer ɗin bai dawo ba."

Islaha dai bata ce komai ba, kuka kawai take yi tana jin ciwon auren da ta yi da ba Hamma ta aura ba. Tabbas kowa zai ce kwaɗayi ta yi, musamman in aka san asalin wanda ta aura, kuma aka san ta bar Saheer ta aure sa, kowa ya san halaccin Saheer a gare ta, dole a faɗa mata baƙaƙen maganganu a kai.

Islaha kalli Safeera ta ce, "gaskiya ce maganar su, duk wanda ya ji asalin wanda na aura zai ce kuɗi na zaɓa na bar halacci. Na yi danasanin ƙulla yarjejeniyar nan, na yi danasani wallahi. Safeera In wayata?."

Safira ta ce, "me za ki yi da ita?."

"Zan kira Jafar ne."

"Ki ce masa me?."

"Ya haÉ—a ni da Rehaan, zan yi canceling auren nan."

Ta yi mata kallon up and down ta ce, "kuɗin sa da ki ka karɓa fa? Ko kin manta ya ba ki kuɗi dan ki zauna dashi har na wata biyar, ko kina da kuɗin da za ki dawo masa da kuɗinaa ne?."

Islaha ta dafe kai bata ce komai ba zuciyarta tana yi mata É—aci, tana suya, tana zafi da raÉ—aÉ—i mai yawa. Sai a lokacin take danasanin aikata abinda ta aikata, sai a lokacin take tunanin ya Hamma zai ji, sai a lokacin take tunanin me mutane za su ce akan auren da ta yi?.

"Islaha lafiya ki ke kuka?."

Jin muryar Baffa duk sai suka juya a tare, Baffa ya ƙaraso ya ce, "me ya faru ki ke kuka?."

Islaha ta yi bata ce komai ba, amma ƙirjinta bugawa yake yi, jikinta rawa yake yi sosai.

Baffa ya ce, "Safeera me ya faru?."

"Su Mama ne suka ce wai ta zaɓi mai kuɗi ta bar halacci."

Baffa ya girgiza kai ya ce, "shine take kuka?."

Safeera ta ce, "eh Baffa. Suna ta faɗar magana mara daɗi, wai ta zaɓi mai kuɗi ta bar Saheer, ta manta wahalar da ya yi da ita a rayuwa."

Baffa ya yi tsaki ya ce "ku zo mu je ciki."

Safeera ta riƙe hannun Islaha da ta fara jiri, suka bi bayansa har ɓangaren sa.

Baffa ya zauna ya ce, "Islaha kar wata magana ta fatar baki ta dame ki, in ance kin zaɓi kuɗi ki ce kin zaɓa ɗin, waye yaƙi kuɗi?."

Ita dai bata ce komai ba kanta yana ƙasa tana goge ido, kanta yana ciwo, ƙirjinta yana harbawa, numfashinta yana sarƙewa.

Baffa ya ce, "ki kwantar da hankalin ki, ba ina sane na zaɓa miki auren yaron nan ba. Na yi ne dan na tsaraɓar dake daga mahaifiyar Saheer, bana so ki sha wahala a rayuwar ki, shiyasa na aikata hakan. Kin fara shirin tarewar gobe?."

Gabanta ta faÉ—i sosai, ta runtse ido tana girgiza kai alamun a'a.

Baffa ya ce, "ki fara shiryawa. Safira ki taimaka mata, sannan ki faÉ—awa Gwaggon ki Atika za a raka Islaha gidan nijinta gobe. Na san Sa'ida bazata ta fahimta ba itama, tana kishin É—an uwanta baza ta je ba. Iya ku kun isa ku yi mata rakiya, ba taro ake so ba, albarka ake nema."

Safeera ta ce, "To Baffa."

Ya kalli Islaha ya ce, "kar ki wani damu, na san kina tunanin ba ki kyautawa Saheer ba, amma hakan shine daidai."

Baffa ya dinga rarrashinta ita dai jin sa kawai take yi, yana gamawa duk fita ta koma gidan su Safeera dan bazata iya komawa cikin gidan ba. Haka ta zauna da zazazzaɓi da ciwon kai, ta koma shiru bata magana, sai tunani da kuka, Safeera ce mai rarrashinta amma bata rarrasuwa. Safeera ta ba ta magani ta sha, daga nan ta share ta dan ita bata ga abin tayar da hankali akan abinda ba ka da mafita a kai ba.

*Washe gari.*

Abba ne tare da Jazy, ya kira sa suna magana akan É—auko amaryar Rehaan. Abba ya ce, "Jafar kana jina, a je gidansu yarinyar nan a É—auko ta a kawo ta. Na baka ragamar komai, kuma da kan ka nake so ka É—auko ta a kawo ta gidan nan. Kafin a kai maka taka amaryar, ka kawo ta É—an uwanka."

Jafar ya yi murmushi ya ce, "In sha Allah Abba, zan yi yadda ka ce."

"Yauwa Jafar, da kai kaÉ—ai na amince shiyasa na ba ka wannan damar. Don Allah ka kula, yarinyar nan ta shigo gidan nan lafiya, kar a fara da matsala."

"In sha Allah."

"An gyara apartment É—in nasa ne?."

"A'a, ya ce shi baza a canja masa komai ba."

Abba ya girgiza kai yana murmushi ya ce, "ai ya yi ƙoƙari ma, yana da haƙuri sosai, shiyasa bana so na dinga ƙure shi, bana so na dinga yi masa dole akan abinda ba ya so, shiyasa nake ƙyale shi duk abinda ya ce nake bi dan a yi masa yadda yake so. Ba ya son auren nan, ni na tilasta masa ya amince, shiyasa bana son na ƙure shi."

Jafar ya É—an murmusa kawai amma bai ce komai ba. Yana ayyana Abba bai san akan yarjejenuya ya É—ora auren ba, ba don Allah ya yarda har ransa ba.
Chapter 131 · 0% Book details