Sashe 81
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya gyaɗa kai ya fita yana sake kiran wayarta amma bata ɗauka. Ji yake kamar ya shiga cikin wayar ya jawota ta ɗauki wayar, gabaɗaya zumuɗi da shauƙin aura masa ita a ranar ya cika masa zuciya.
(Tofa, ana wata ga wata🤣)
•••••••
Islaha lokacin da Saheer yake yi mata waya suna kitchen ita da Sunaira, ta bar wayar a ɗaki bata san yana kira ba. Sallar la'asar ce ta shigar da ita ciki, kuma bata kalli wayar ba ta yi alwala ta yi sallah ta zauna tana azkhar. Har biyar na yamma tana zaune, Sunaira ta shigo ta yi mata tayin fita su je Mall su dawo, Islaha ta amsa ta miƙe ta saka hijjab suka fita.
A ƙasa suke tafiya a hankali, ba hira suke yi ba dan ko wanne bai iya yareen wani ba, har gwara Islaha yanza ta ɗan iya ƙananun abubuwa a kalmar larabci.
Islaha kallon estate É—in take yi sosai, ya tsaru iya tsaruwa, kai ba sai an faÉ—a maka gidan da suke wajan suna da tsada ba. Sai da suka yi nisa suka hau mota suka tafi. Sai da suka shiga mota ta tuna ta bar wayar ta a gidan, ta ji haushi sosai dan ta so ta É—an yi video ta samu na streaks.
Waye mai nasara? Daada ce ko Baffa?.
Nana HaleemaâœðŸ»â¤ï¸
[7/15, 11:52 AM] KRBBK: RDB2P58
Nana Haleema.
Islaha basu dawo ba sai magrib, a ƙofar gidan Rehaan motar ta ajjiye su, ta harari gidan cikin jin haushin mai gidan da abokinsa, suka shiga ciki suna ajjiye komai a mazauninsa.
Sai da ta yi sallah sannan ta ɗauki wayarta, ta wara ido ganin kiran Hamma babu adadi. Da hanzari ta kira sa, ta yi ringing bai ɗauka ba har ta katse. A bayyane ta ce, "Allah ya sa ba laifi na yi masa ya ƙi ɗauka ba."
Kafin ya kira ta sai ga kiran Umma, Islaha ta É—auka da sallama ta ce, "Umma ina yini."
Umma a sanyaye ta ce, "Lafiya Lau Islaha, ya zaman Jeddah?."
"Lafiya lau Umma."
"Ya ƙawar ki? Kuna waya kuwa?."
"Eh muna gaisawa, bata kira ki ba?."
"tunda na zo sau biyu kawai muka yi waya. Islaha zaman ƙasar nan gabaɗaya ya ishe ni, ina so na samu hanyar da zan koma gida, amma abin ya ci tura."
Islaha ta sauke nunfashi ta ce, "Ina so nazo na gan ki Umma, na yiwa Safeera alƙawarin an ba ki kulawa daidai ƙarfina. Ina so na zo ban san yaushe ba, kuma ban san a inda ki ke ba."
Umma ta ji daÉ—i ya mamaye ta, ta ji kamar an ce Islahan ta zo, ta ce, "Allah ya kawo ki Islaha, sunan unguwar wai Khadiyya, in ki ka shigo sai ki kira ni, an koya min yadda ake tura location ta whatsapp."
Jin yadda Umman take murna daga cewa zata zo sai zuciyar Islaha ta karye, ta ji ranta dole ma ta je Madina ganin Umma. Ta ce, "zan zo in sha Allah Umma."
Umma ta ce, "na gode Safeer....su Islaha, sai na ganki." Daga nan suka yi sallama ta kashe wayar.
Tana kashewa kiram Saheer ya shigo, tana É—auka ya ce, "ina ki ka shiga ne? Tun É—azu nake yi miki waya bakya É—auka."
"Ban ga kiran ba sai yanzu, dan yanzu na dawo daga mall, sallah kawai na yi."
"Baffa ne yake son magana dake tun É—azu."
"Wallahi ban gani ba, yana ina yanzu? Ka haÉ—a ni dashi."
"lokacin sallar magriba ya taho, kin san da huri yake shiga masallaci."
"amma ban ji daÉ—i ba."
"kin san meyasa yake neman ki?."
Kamar tana gabansa ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "ban sani ba."
Ya ce, "bara na kira ki video call."
Bai jira me zata ce ba ya yanke wayar, ya kira ta ajjiye wayar tana kallonsa, ta ɗan yi murmushi ta ce, "Hamma kullum ƙara kyau ka ke yi, meye sirrin?."
Ya yi murmushin da yake ƙara masa kyau, ya ɗan girgiza kai yana kallon ta da fararen idanunsa ya ce, "ni ba ta wannan tsokanar ta ki bake yi ba, Kin san meyasa Baffa yake neman ki?."
"sai ka faÉ—a Hamma."
Ya yi murmushi yana shafa kansa yana kallon ta cikin shauƙi mai yawa, iya faɗa mata maganar da zai yi ma shauƙi yake ji, ina ga an ɗaura kuma?. Islaha ta shagwaɓe fuska jin ya ƙi faɗa mata, ta ce, "ka faɗa min mana."
Ya ce, "Da ace É—azu kin É—auki wayar, daman tambayar ki zai yi, in za ki amince a É—azun za a É—aura aurenmu dake bayan sallar azahar. Shiyasa na dinga jera miki kira amma amma ban same ki ba, wallahi ji na yi kamar na zo na É—auko ki."
Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi matuƙa ta buɗe ido waje tana dafe ƙirji ta ce, "Aure Hamma!."
Shima ya buÉ—e ido kamar yadda ta yiya ce, "Eh mana."
Islaha ta ce, "da gaske ka ke?."
"Na taɓa yi miki wannan wasan?."
"Baka taɓa ba, abin ne na ji sa har jinina, wallahi gabana sai faɗuwa yake yi."
Ya harare ta ya ce, "Meye na faÉ—uwar gaban? Bakya son auren nawa ne?."
Ta girgiza kai ta ce, "Abin ne yazo min coincidences, ban taɓa tunanin hakan ba shiyasa. Kuma da gaske Baffa yake?."
"Wallahi da É—azu da kin É—auki wayar da na yi miki, kin kuma amince, da yanzu kin zama matar Saheer" ya faÉ—a yana zuba mata ido.
Sai kallon ya yi mata nauyi sosai, ta sauke ido ƙasa tana wasa da abin hannun da ya bata.
Saheer ya bita da kallon mamaki ya ce, "Hmm! Da ace Baffan ma ya yi magana dake cewa za ki yi ba ki amince ba ko?."
Ta É—ago ta kalle sa tana zaro idanu ta ce, "Ni haka na ce?."
"Gashin nan kin zama wani iri daga ba ki labari."
"Kawai jikina ne ya yi sanyi, amma da a guje zan amince."
"Meye na sanyin jikin? Aure fa kawai za a É—aura, kina nan Jeddah ina Nigeria. Sai kin dawo sannan za a yi biki."
Ta sauke kai ƙasa ta ce, "Hamma duk inda aka ce za a ɗaura aure, ai dole jiki mace ya yi sanyi."
"yanzu in ya tambaye ki me za ki ce? Kin amince a É—aura yanzu ko sai kin dawo?."
Yadda ya zuba mata ido ya saka ta kasa cewa komai, in dai a ra'ayinta ne baza ta yarda a ɗaura mata aure yanzu ba gaskiya, ta fi so sai ta gama komai da yake gabanta, dan ta san halin Hamma da kishi, in aurensa ya hau kanta wani abun bazai bar ta ta yi ba, musamman ɓangaren da Barr zai shigo ciki. Amma baza ta iya ƙin amincewa ba, zata amince ko dan saboda Hamman yana so, daga jin yadda yake bata labari cikin zumuɗi ta san ya ji daɗin maganar sosai.
"Beddo am!."
Ta kalle sa ya ce, "Tunani ki ke yi akan za ki amince ko baza ki amince ba?."
Ta yi murmushin dole ta ce, "A'a, kawai ina tunanin yadda zan fara rayuwa da auren ka a kaina a ƙasar nan ne, dan ni na hango har an ɗaura auren."
Sai kuwa fuskarsa ta washe, annuri da farin ciki suka bayyana akan fuskarsa sosai. Ya gyara zama ya ce, "Ni kaina ina lissafin yadda zan ji kewar matata a kusa dani, har na siyi bankin da zan fara tara kuÉ—in da zan zo Saudia wajan matata."
Ta yi dariya sosai, shima dariyar ya yi ya ce, "Ni dai kar ki kwafsa min, in Baffa ya tambaye ki ki tausaya min ki amince don Allah. Haɗuwa ta gaba ina so ya kasance da aurena a kan ki, yadda zan nuna miki adadin kewar ki da na yi ba tare da kin ce, Hamma babu kyau fa" ya ƙarasa faɗa yana kwaikwayon muryarta.
Dariya ta yi sosai tana rufe fuska da hannunta, ya yi murmushi yana kallon kyawawan hannayenta marasa kauri dogaye.
Cikin sanyin murya ya ce, "ƙarya na yi, ba haka ki ke faɗa ba?."
Ta cire hannunta tana sunkuyar da kai tana murmushi ta ce, "Amma meyasa Baffa ya ke son a É—aura aurenmu a yau?."
"Mama ce wallahi, itace ta tunzura shi har ya yanke hukunci.....Islaha ana kiran sallah, in an idar zan kira na haÉ—a ki da Baffan." Ta amsa da to ya kashe wayar.
Ta jingina da gado tana tunanin wannan sabuwar chakwakiyar da ta kawo mata kai, Allah ya sani bata ra'ayin wedding fatiha before ceremony. Kuma ana ɗaura auren nan takura ta Hamma zai yi, duk da bashi da matsala da aikin ta amma akwai mutanen da zai iya hanata magana dasu, kuma dole ta hanu tunda matarsa ce. Kuma yadda yake nuna shauƙinta a kwanakin nan bazai iya barinta har sai an yi biki bai yi mata komai ba, ita kuma bata son hakan Allah ya sani. Tana wannan tunanin aka yi sallar i'sha.
Ta san daman bazai kira ta ba sai bayan sallar i'sha ta nigeria, saboda Baffa ba ya dawowa daga masallaci sai ya yi sallar i'sha.
Ko ya wayarta ta yi ƙara sai gabanta ya faɗi, gabaɗaya bata so kiran Saheer ya shigo kwata kwata, dan bata son ya haɗa ta waya da Baffa. A haka ta miƙe ta je suka ci abinci dan har lokacin matar gidan basu dawo ba.
Ƙarfe sha ɗaya na Saudia, wanda ya yi daidai da tara na Nigeria. kiran Saherr ya shigo, tana kalla gabanta ya faɗi ta ji kamar kar ta ɗauka, ta runtse ido ta buɗe, ta ɗauki wayar a sanyaye ta sama a kunne.
Tana sakawa a kunne Baffa ya ce, "Islaha."
Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta ɗan runtse ido sannan ta ce, "Baffa barka da dare."
"Barka dai Islaha, ya aiki?."
"Alhamdu lillah, ya ƙarfin jiki?."
"Jiki ya warware Islaha."
"Allah ya ƙara lafiya."
"Amin Islaha, yaushe ne dawowar ta ki?."
Islaha ta ce, "na kusa in sha Allah."
Baffa ya murmusa ya ce, "Allah ya dawo dake lafiya."
Ta amsa da amin sannan ya ce, "Islaha wani hukunci nake so na yanke a kan ki da Hamman ki, shine na kira na ji ra'ayin ki a kai."