← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 133

Sashe 80

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha tana daga tsaye ta ce, "Alhamdu lillah, na ji sauƙi sosai

"Good. Have a seat" ya faÉ—a yana nuna mata kusa dashi.

Bata zauna ba ta cigaba da tsayuwa ya ce, "Kina da kyau sosai." ÆŠan kawar da kai tayi tana haÉ—e rai cikin takaicinsa.

Bata farga ba sai gani ta yi ya tsaya a kusa da ita, ya miƙa mata hannu alamun su gaisa ya ce, "Can i be your friend?."

Ta É—an ja da baya kaÉ—an ta ce, "Sorry Dr, i'm not interesting. Thank you" tana gama faÉ—a ta bar wajan cikin jin haushinsa har zuciyarta

Shi kam fita ya yi yana neman hanyar da zai bi ya ga Islaha ta saba dashi sosai. Gidan ya koma, ya shiga ɗaki yana kallon window cikin damuwa mai yawa. Sai kuma aka buɗe ƙofar aka shigo, ya juya ya kalli wacce ta shigo ya ga Labiba ce, ya yi tsaki yana kallon ta da yarinyar tana tsaya masa a ransa. Tunda ya ga Islaha ta fara sire masa, amma yana jin daɗin mu'amala da ita sosai.

Zama ya yi akan sofa, ta zauna a kusa dashi ta ce, "Me yake damun ka?."

Ya gyara zama ya kalle ta ya ce, "Kin san haousemaid É—in gidan Maleek? Sunanta Islaha, itama Æ´ar nigeria ce, kuma fulani ce."

Gaban Labiba ya faÉ—i, ta É—an haÉ—e rai ta ce, "Eh na santa."

Ya yi murmushin jin daɗi ya ce, "Ina sonta, ina son kasancewa da ita, ina jin yanayi mara misaltuwa a akanta. In dai za ki jawo min hankalin ta, zan ba ki kuɗaɗe masu yawa, zan ba ki kuɗin da ban taɓa ba ki kamar su ba."

Labiba ta ɓata rai, cikin jin haushin Islaha ta ce, "Ni ba ƙawata ba ce."

"Amma za ki iya sakawa ta zo nan, Indai ki za ki saka ta ta zo..." ya dakata ya ɗauko kuɗi masu yawa ya bata ya ce, "zan ƙara miki wasu."

Ta kalli kuɗin, ko lokacin da ya fara kwanciya da ita bai bata wannan kuɗin ba, amma gashi yau saboda Islaha yake bata wannan kuɗi masu yawa har yana cewa wai zai ƙara mata.

Bata ƙi karɓar kuɗin ba, ta riƙe a hannunta sannan ta ce, "zan yi, amma tana da taurin kai, babu lallai ta amince."

"Zan jira, ko yaushe ne indai zata amince. I like her, tana da kyau sosai." Labiba ta girgiza kai sai ta miƙe ta fita.

Tana shiga É—aki ta kira Mama, Mama yana É—auka ta ce, "Mama sai kin tashi tsaye, balaraben da yake yi min kyauta ya gano Islaha Mama, Shikenan Mama, zai daina bani komai."

Daga can ɓangaren Mama ta ce, "ban gane ya gano Islaha ba, a ina ya ganta?."

Daidai lokacin Saheer ya kai abinci bakinsa, jin abinda Mama ta ce sai ya tsaya cak ya kasa ci ya zubawa Mama Ido kallon ta.

Labiba ta ce, "Ban sani ba Mama, amma shekaran jiya an ganta a motarsa, yau kuma ya zo yana faɗa min indai zan saka ta zo gidansa ta kwana dashi kamar yadda take kwana da saura abokinsa zai bani kuɗi masu yawa. Mama kin ga kuɗin da ya bani saboda ita? Kin ga yawan kuɗin, har yana cewa zai ƙara min in dai ta zo gdain?. Mama shikenan ta mu ta ƙare, don Allah Mama ki yi wani abun."

Mama ta ce, "ke dallah kar ki damu, islahan ta isa ta shiga tsakanin mu da arzuƙin mu?. Ki kwantar da hankalin ki, zan yi maganin abin wallahi. Amma in ya ba ki kuɗi akan ki kawo masa ita ki karɓa, amma ko da wasa kar ki bari ta kusanci gidan, ta je ta ƙarata da abokinsa, shi kam ya fi ƙarfinta. Sannan me ya kaita shiga motarsa?."

"Mama ko ni ban taɓa shiga ba, amma ita ta shiga. Sai gano su na yi ta camera yana yi mata kiss. Kin san ta da farin jinin maza, inda take aikin ba ki ga yadda mai gidan yake rawar jiki a kanta ba, ita tsabar haɗama namiji ɗaya ya yi mata kaɗan, har wani gidan take zuwa kullum, nan ma ta samo kuɗi. Wallahi Hamma bai yi dacen mata ba, gabaɗaya Islaha ta gama zubar da mutuncinta, ta zama ƴar iska mai lasisi."

"Farin jinin samarin banza ba, ai in saurayi na kirki ne bazai kalli Islaha ya ce yana so ba, ke da ganinta ka san babu irin duniyancin da bata aikata ba, yadda idanunta suke a kakkafe akan mutane, babu iskancin da basu gani ba. Yanzu dai ki kwantar da hankalin ki, ta je ta ji da wasu amma wannan na ki ne ke kaÉ—ai, ke kaÉ—ai zai dinga yiwa kyauta, baza ta hana mu rawar gaban hantsi ba."

"Kuma Mama ta ci a can, ta ci a nan kenan? Ni ina zuwa gidan da take ne?."

"Bar shegiya tsintacciya, zan yi maganin abun."

"yauwa Mama, Yanzu zan je na canja kuÉ—in xuwa naira sai na turo miki." Mama fara saka mata albarka kafin ta kashe wayar.

Saheer ya ƙame ya kasa yin komai, ya ajjiye cokalin yana juyasa a plate yana jin duk abinda dukkansu suke faɗa, har wanda Labiba ta faɗa ya ji.

Baffa da ya shigo yana tsaye shima duk ya ji abinda ta ce, ya girgiza kai cikin ƙunar zuciya da ɓacin rai ya ce, "a cikin samarin banza da suke kula Islaha, ina so ki san ɗanki ne lamba ɗaya, ɗanki ne babban ɗan iska tunda shine zai aure ta."

Mama ta kalli Baffa ta ce, "yanzu ban da lalacewa yana ji an ce ta zama Æ´ar iskar larabawa sai ya É—auka ta ya kai gidansa a matsayin mata? Ya aure ta ya ce ya auri me? Gwangwani ko fanko?."

Baffa ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "ina guje miki ranar da za ki yi danasani akan harshenki, ranar da rashe zai juye da mujiya, ranar da kalaman bakinki zasu zamar miki izina akan Islaha. In kina da rabo, daga lokacin da fari zai koma baƙi, za ki yi hankali ki san me zaki dinga faɗa a kan ƴaƴan wasu."

"ai babu wannan ranar kuwa, yarana na gari ne gaba da baya. Kuma aure tsakanin Saheer da Islaha babu, indai ni na haife sa."

Baffa ya gyaÉ—a kai, ya kalli Saheer ya ce, "Kai Saheer ba dai ginin gidan ka ya kammala ba?."

Cikin wani yanayi na damuwa ya ce, "saura kaÉ—an Baffa, an gama komai, kawai kayan wuta za a saka."

Baffa ya kalle sa ya ce, "zan yi waya da Islahan,  juma'ar jibi za a ɗaura auren ka da ita in sha Allah, in ya so duk ranar da ta dawo nigeria sai ta tare."

Mama ta miƙe ta ce, "a ɗaura aurensa da wa, Ragowar wasu mazan? Ai wallahi indai ina da rai bai isa ya auri yarinyar nan ba, in ka ga na bari ya auri Islaha, to ka ɗauka bana numfashi!."

Baffa ya murmusa, ya kalli Saheer ya ce, "Saheer kira min Islaha a waya."

Saheer ya ce, "Baffa ka kwantar da hankalin ka, ka ga ba wata lafiyar kirki ka ke da ita ba, kuma ba a son abinda zai saka ka a damuwa, ka yi haƙuri."

Baffa ya ce, "ni ba a damuwa nake ba Saheer, ka kira min wayar Islaha kawai."

Saheer ya sauke numfashi ya kira lambar Islaha ta ƙasar Saudia amma bata ɗauka ba, ya sake kiranta ta whatsapp amma bata ɗauka ba. Saheer ya ce, "Bata ɗauka ba Baffa."

Baffa ya ce, "sake kiran ta." Saheer bai musa ba ya kuma kira amma bata É—auka ba. Ya kalli Baffa ya ce, "bata É—auka ba Baffa."

Baffa ya ce, "daga nan zuwa ko yaushe indai ta ɗauka ka sanar dani, ni Mustapha Maddibo, na rantse da girman Allah, daga yanzu zuwa sallar azahar, indai har Islaha ta ɗauki waya mun yi magana da ita, ba za a ƙara mintina goma ba sai ta zama matar Saheer. Daga lokacin da igiyoyin auren ɗanki suka ɗaure Islaha, sai zubawa kan ki fetur ki ƙona kan ki da kanki. In kin ga hakan bai faru ba, ki ɗauka kawai Islaha bata ɗauki wayar nan ba, amma indai ta ɗauka sai na nuna miki ni ne uban Saheer!...."

Baffa ya juyo a fusace ya kalli Saheer ya ce, "mu je" ya faÉ—a yana kallonsa suka fita daga falon.

Mama ta da ki kujera ta ce, "in ɗana Saheer ya auri Islaha Allah ya tsine min albarka, wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma bazan taɓa bari Saheer ya auri Islaha ba!" Tana faɗa ta shiga ɗaki dan nemo mafita.

Baffa bayan sun fita ya kalli Saheer ya ce, "ba ka gama haÉ—a lefen ba?."

Saheer ye ce, "an gama Baffa, daman kuɗin aikin ka ne ya tsayar da komai. Amma ka yi haƙuri kar ka yanke hukunci cikin fushi, ka kwnatar da hankalinka saboda lafiyar ka."

Baffa ya kalle shi ya ce, "kana son Islaha ko babarka ta saka maka zargi ta?."

Ya girgiza kai ya ce, "Har abada bazan taɓa zargin Islaha ba, na san halinta fiye da kowa."

"Kana sonta ko baka so?.

"Baffa kaima ka san amsa ta akan hakan."

"Ka shirya karɓar aurenta a yau?."

"Ko yanzu ne a shirye nake?."

"Za ka iya jira har sai ta dawo da auren ka akanta ko baza ka iya ba?."

Ya sauke numfashi ya ce, "akwai yarda a tsakanina da ita, wallahi ko shekara dubu zata yi da aurena a kanta zan jira har ta dawo."

Baffa ya murmusa ya ce, "da zarar ta kira ka ka sanar dani, zamu yi magana da ita, bana so na yanke hukunci ya zama kamar ban kyauta mata ba. Amma da yanzu yadda zan fita masallacin nan, wallahi bazan dawo ba sai igiyoyin auren ka uku sun hau kanta, daga nan sai babarka ta saka bindiga ta kashe kanta."

Saheer ya murmusa, wani irin daÉ—i yana mamamaye masa zuciya, Allah Allah yake ya fita ya sake kiran Islaha.

Baffa ya ce, "Jeka, in ka same ta kazo ka haÉ—a mu."
Chapter 80 · 0% Book details