← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 133

Sashe 36

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta yi dariya mai sauti, ta kalle sa tana murmushi amma bata ce komai ba. Sai dai tana jin daÉ—i ya sake ya daina fushi da ita.

“Har zan tafi baki faɗa min komai ba akan maganar case ba.”

Islaha ta yi shiru bata amsa, ya ɗan murmusa ya ce, “Na sake baki lokaci ko?.” Ta ɗaga kai alamun eh, ya girgizaa kai ya yi kafin ya ce,

“Ki je ki huta kanki yana ciwo, in sha Allah da asuba zan tafi. Na faɗawa Sadik kar wani abu ya sake faruwa a ɓoye min, in hakan ya faru bazan yafe ba.”

Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, amma ta daure ta ce, “in Allah ya yarda babu abinda zai faru.”

“Allah ya sa, nima haka nake fata matar hamma. Ki je ki huta.”

Ta ɗaga ido tana kallon kyakykyawar fuskarsa mai cike da haske da kyayawan idanu ta ce, “To Hamma, da asuban zan fito mu sake yin sallama.”

Ya bita da kallo ya ce, “To matar Hamma.Ina ƙaunar ki.”

Ta sauke ido dago kallonsa ta ce, “ina ƙaunar ka Hamma.”

Murmushi ya yi yana ji kamar ya rungume ta, sai yake jin wata irin kewar ta mai yawa tana ratsa jikinsa, sai yake ji kamar rabuwar su ta ƙarshe kenan a duniya.

Ya kalle ta ya ce, “ina jin kewar ki a raina wacce ban taɓa ji ba, ina ji zuciyata tana bugawa fiye da duk lokacin da zan yi tafiya.”

“nima haka haka nake ji Hamma” ta faɗa a sanyaye tana ji kamar ta kwantar a jikinsa, tabbas da zata samu zarrar jawo sa jikinta babu abinda zai hana bata ware hannayenta ta rungume sa ba. Amma kai tsaye bazata iya ba, da ace shi zai yi mata zata so hakan sosai a lokacin.

Ya ɗan matso kusa da ita yana kallon idanunta da bakinta da yake ɗaukarsa ya ce, “ina ji kamar na rungume ki matar Hamma, kin bani dama in yi?.”

Ta sauke iso ƙasa tana sauke numfashi a hankali zuciyar ta tana bugawa da ƙarfi. Da zata iya magana da ce masa eh, da ta faɗa masa ta bashi dama dan ita kanta tana so, amma baza ta iya furtawa ba.

Bata iya cewa komai ba tana tsaye ƙyam bata motsa daga inda take ba. Yana jin sirritaccen ƙhamshin da yake fita a hankali daga jikinta, kasancewar ta mai yawan samun attack bata cika amfani da turare mai ƙarfi ba, sai ka zo kusa da ita zaka ji tashinsa a hanlkali yana shiga hancin ka.

Jin shaiɗan yana neman tsirga masa wani abu sai ya yi sauri ya ja baya, amma sai ya riƙo hannunta duka biyun ya ce, “na sake yin haƙuri, sai kin zama mallakina, amma ko hmm” ya faɗa yana murmushi ita dai kunya duk ta cika ta.

Ya ɗan shafa fuskarta ya ce, “ki je ki kwanta.”

Ta ɗaga kai ta ce, “sai da safe.”

Ya saki hannunta a hankali sannan ya ce, “sai da safe.” Ta juya tana hankali ta koma tana jin wata irin kewarsa tana ratsa zuciyarta. Tana ji kamar bazasu sake haɗuwa ba, kamar daga lokacin baza su sake furtawa junansu suna ƙaunar juna ba, kamar bazasu sake tsayuwa a matsayin masoya ba. A haka ta kwanta cikin tunani da buguwar zuciya, kewa da tunani kala kala a ranta.

Nana Haleema
09030398006.
[6/29, 11:53 AM] KRBBK: RDB2P025
Nana Haleema.

Da asuba basu haÉ—u ba, sai text ya yi mata ya ce ya tafi, ta ji haushin rashin haÉ—uwarsu sosai sai take ji kamar baza su sake haÉ—uwa ba.

Bayan ta fito ta ga Mama da iyalanta suna karyawa, ta gaishe da Mama ta amsa tana kallon ta ta ce, “ki fa shirya kayan ki, tafiyar ku gobe ce.”

Gabanta ya faɗi ta ce, “To Mama.”

Labiba ta ce, “ashe maganar duk ta ƙarya ce, da an yi magana ta ce ita bazata je ba, sai gashi zata tafi ba tare da Hamma ya sani ba.”

Hanan ta ce, “bar munafuka, ita wai ga ta gari. Mtsw kamar bamu san dawar garin ba.”

Islaha dai bata ce musu komai ba dan bata cikin yanayin magana. Ta juya ta koma ɗaki ta zauna tana tunani, taƙi bawa zuciyar ta damar tunanin abinda take niyar yi ba daidai bane, bata so ta zauna ta yi nazari a akai har ta gani kuskure zata aikata. Gudun hakan sai ta miƙe da hanzari ta shiga banɗaki ta yi wanka ta fito ta shirya ta wuce wajan aiki.

A can ma bata da walwala, kowa ya lura da ita Safeera ce kaÉ—ai ta san halin da ake ciki.

Tare suka je wajan chairman suka same sa a zaune Islaha ta ce, “Chairman barka da aiki.”

Da murmushi ya ce, “barka dai ƴar jarida mai ƙwazo.”

Ta murmusa ta ce, “daman wata magana nazo da ita.”

Ya gyara zama ya ce, “Allah ya sa labarin da zamu fara fitarwa ne. Kin san ya kamata ki koma ɓangaren da ki ka baro, ɓangaren wasanni ana ta tambayar ki.”

“Ba akan aiki bane Chairman.”

“To meye?.”

Ta kalli Safeera sannan ta ce, “zan ɗan yi tafiya na wani lokaci, zan yi dropping aikina in na dawo zan cigaba. Ba barin aikin zan yi ba, zan tafi za a daina biyana, in na dawo zan ɗora daga inda na tsaya.”

Mamaki ya saka Chairman miƙewa zaune ya ce, “ban gane ba, kina nufin zaki daina aiki damu?.”

Islaha ta ce, “aikin gabaɗaya zan bari na wani lokaci, kuma ba gidan wata jaridar zan koma ba, zan yi ƙaramar tafiya ne zuwa wani waje. Da zarar na dawo zan ɗora in sha Allah.”

Chairman ya ce, “Islaha ina zaki je haka? Ina zaki tafi ki bar ɗaukakar ki?. Kin san labaran da ki ka yi jiya adadin mabiya da masoya da mu ka tara? Islaha kece ƙwarin mu, saboda fuskar ki da muryar ki mutane suke bibiyar mu. Yau in aka ce bakya nan ina zamu saka ran mu?.”

Islaha ta kalle sa a sanyaye ta ce, “Chairman tafiyar ta zamar min dole, ni kaina wallahi ba a son raina zan yi ba, kawai dan babu yadda zan yi ne. Amma na yi maka alƙwarin zan dawo.”

Chairman ya ce, “in kika tafi kika canja wajan aiki fa?.”

“Babu inda zan canja, ina nan bakin rai bakin fama in Allah ya yarda. Tafiyar ta zama dole ne, nima da bazan tsallake aikina na tafi ba.”

Ya yi shiru yana sauke numfashi cikin damuwa ya ce, “Shikenan Islaha, Allah ya kiyaye, ya baki abinda ki ka je nema.”

Ta yi murmushi ta ce, “amin, na gode.”

“Yaushe ne tafiyar?.”

“Gobe in sha Allah.”

“Yanzu labaran goben ma baza su samu ba?.”

Ta ɗan yi dariya ta ce, “in sha Allah zan shigo, nima ina so na yi na bankwana kafin na dawo.”

Ya yi dariya ya ce, “shikenan Islaha. In kuma Mr Rehaan ya amsa gayyata bakya nan fa?.”

Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba, bata nuna ba ta ɗan murmusa ta ce, “sai a samu madadina.”

Ya yi dariya ya ce, “duk wahalar da ki ka sha ta tashi a banza? Zan yi fatan Allh yasa ya jinkirta amsawa har sai ki dawo.”

Ita dai bata ce komai ba ta miƙe suka fito ita da Safeera. Da Ummi da Muslim suka haɗu, suka gaisa da Muslmin Ummi kuwa bata ce komai ba suka wuce.

••••••

Yadda fuskarsa take a ɗaure ya saka Alma shiga hankalin ta, a rayuwarta tana tsoron baƙin mutum kuma ɗan nigeria, musmaman irin waɗanda deal irin nan ya haɗa su.

Cike da ɓacin rai ya ce, “meye amfanin saka ki aikin da na yi, ace har yanzu an kasa samun ƙaramin videon Rehaan ko ya ya yake, har yanzu kin kasa yin komai game da hakan?.”

Alma ta ce, “Im sorry sir, Rehaan ya bar Uk kuma bai dawo ba. Ina yawan zuwa apartment ɗinsa amma sai na tarar brother ɗinsa ne kawai shi baya nan. Ni kaina na damu da raahin dawowarsa, kuma tunda ya tafi yaƙi picking call ɗina. But na duba location ɗinsa a snapchat na ga yana Jeddah.”

“To me ki ke jira baki bisa Jeedah ba?.”

“Sir Saudia baza su bani damar zama tare dashi ba tunda ni ba matarsa bace.”

“A apartment ɗin ma’aikata yake?.”

“Aa, a gidansa na Jeddah yake.

“To ina ruwan Saudia da zaman ki? Ki haɗa kayan ki kawai tafi can ku zauna tare. Bana son kuskure Alma, wannan lokacin ki tabbatar da kin samu Rehaan, ki tabbatar da kin turo min video.”

Alma cike da ƙarfin guwa ta ce, “okay sir, i will try my best.”

Ya yi tsaki ya tashi ya futa ya barta a wajan. Ta sauke numfashi tana haɗa plan ɗin tafiya Jeddah, dan ko babu wannan aikin itama ta yi missing ɗinsa sosai, tana da buƙatar ta je ta gan shi a duk inda take.

•••••••

Tun bayan tafiyar Yaya daga wajan Umma bata sake nuna wani abu ba, ta nuna kamar ta bar tafiyar, nan kuwa shirin tafita take yi hankali kwance babu wanda ya sani sai ƙawar ta.

Ranar da zasu tafi da safe take ta shiryawa tana kallon Æ´aÆ´anta da suke shirin tafiya makaranta. Sai take jin tausayinsu, dan ta san kafin su dawo ta tafi, kuma gashi bata san ranar da zata dawo ba, bata san ranar da zata sake haÉ—a ido dasu ba. A haka suka gama shiryawa, suka yi mata sallama suka tafi, Safeera ce ta tashi bata jin daÉ—i tace baza ta fita ba.

Ƙarfe goma na safe, jirginsu kuma zai tashi ƙarfe sha ɗaya na dare, ya rage saura awa sha uku zuwa sha haɗu jirginsu ya tashi, Umma ta shiga wajan Baba ta same sa a zaune yana duba wayarsa.

Ta zauna a kusa dashi ta ce, “magana nake so mu yi.”

Baba ya kalle ta ya ce, “ina jinki.”
Chapter 36 · 0% Book details