← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 133

Sashe 37

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ta sauke numfashi ta buɗe wayarta ta shiga whatsapp ta buɗe wani hoton ta haska masa ta ce, “waɗanda suka ri gasuka yi min visa da komai sun ri ga da sun siyi ticket ɗin tafiya, sun ce dole sai naje bazan saka su asarar kuɗi ba. Maganar da nake maka nan da awa sha uku zuwa huɗu jirgi zai tashi. Ana jirana zamu tafi Abuja, da mun je zamu wuce airport mu hau jirgin saudia.”

Baba ya zuba nata ido yana kallon ta cikin firgincin maganar ta, ya ɗan ɗaga kai ya ce, “ina jin ki.”

Umma ta ce, “tafiya ta zamar min dole, babu yadda zan yi dole sai naje. Kaima shaida ne tunda Yaya ya yi min faɗa na ajjiye batun zuwan, amma yanzu dole na tafi saboda bazasu yi asarar kuɗinsu ba.”

Baba ya katse ta ya ce, “bata zama dole ba, babu wanda zai yi miki dole tunda kin ce bakya so. Nawa suka kashe, ba sai a biya su ba?.”

Ta wani kalle sa ta ce, “ka san nawa ce visar? Ko iya ticket yafi miliyan balle a haɗa da visa. Bamu da kuɗin da zamu iya biyansu.”

Baba ya ce, “ba dai matar Alhaji Mustapha bace Hajiyan ta ku ba? Nawa ne kuɗin.”

Umma ta ƙufule ta ce, “biya fa bai tashi ba, kawai tunda haka ya riga ya faru zanje na dawo kawai, kamar yau zaka ga naje na dawo.

Baba ya murmusa yana kallon ta ya ce, “zaki je ina?.”

“Saudia ɗin mana.”

Ya bita da kallon baki da hankali bai ce komai ba ya yi shiru. Umma ta miƙe ta fita a lokacin kiran Mama ya shigo wayarta tana shaida mata da ta haɗo kayanta ta taho gidanta zasu tafi Abuja gabaɗaya.

Sai a lokacin gaban Umma ya faÉ—i, tsoro ya mamaye mata zuciya, tausayin Æ´aÆ´anta ya É—arsu a ranta, ta shiga tunanin ya zasu ji in suka buÉ—e ido bata nan?. Amma babu yadda zata yi, duk abinda take yi ma dansu take yi, saboda gobensu.

Safeera ce ta shiga wajanta neman maganin ciwon kai, ta ga Umma tana rufe jaka gata da hijjab tana sakawa alamun fita zata yi. Safeera da mamaki take kallon ta ta ce, “Umma ina za ki je da safiyar nan?.”

Umma ta kalle ta tana harararta ce, “aikin da ki ƙi zuwa ni zan je. Islaha da ta dinga zuga ki akan kar ki je, to yau da ita zamu tafi.”

Kan Safeeera ya sara, daman gashi yana yi mata ciwo, ta dafe kai ta ce, “Umma ban gane ba, kina nufin tare da Islaha da Labiba zaku tafi yau?.”

Umma ta ce, “ga zahiri kina gani, daga nan sai Madina in Allah ya yarda. Ki kula da ƙannenki kafin na dawo, in buƙatar kuɗi ta tashi zan dinga tura miki, daman nemansu zan tafi.”

Safeera ta ƙarasa ta riƙe mahaifiyar ta tana kuka ta ce, “Don Allah Umma ki ce wasa ki ke yi, ki ce wasa ki ke yi min ba tafiya zaki yi ba.”

Umma ta ce, “tafiya zan yi Safeera, zan je na nemo kuɗin da zan aurar dake da ƙanneki. Ki kula da kanki da ƙannenki kafin na dawo.”

Safeera ta duƙushe ta riƙe ƙafarta ta ce, "Don Allah Umma kar ki yi mana haka, mun fi buƙatar ki sama da komai a rayuwar nan. Ni na yarda zanje, na amince zan je ba sai kin je ba."

Umma ta kalle ta tana hararar ta ta ce, "lokacin da nake lallaɓa ki ai iskanci ki ke yi min, dan haka ki sakar min ƙafa na wuce."

Baba ya É—aga labulen ya shigo yana kallon ta da mamaki da É—aure kai ya ce, "Maimuna da gaske tafiya za kiyi?."

Ta kalli Baba duk da faÉ—uwar gaban da take ji, amma hakan ta daure ta ce, "yanzu na gama yi maka bayani fa."

"Duk abinda Yayanki ya faÉ—a miki daman baki ji ba?."

"Ni fa ta dole zan tafi, ba dan son raina zan je ba."

"Yanzu dai sai kin je É—in?."

"Jirana ma suke yi zamu tafi Abuja, ta can zamu hau jirgin saudia mu tafi Madina.”

Baba ya girgiza kai ya ce, "Maimuna kin zaɓi ki watsar da ƴaƴanki mata ki tafi wata ƙasar aikin gidan larabawa, kin zaɓi ki barsu a nan ki je inda baki da kowa saboda neman duniya?. Ki bar naki yaran, ki je ki yi bautar yaran wasu?."

Umma ta ce, "ga Safeera nan, meye baza ta yi musu ba? Ai ba lallai sai ni ba."

Baba ya bita da kallo dan bai ga alamun zata fasa ba, bai ga alamun tana jin tausayin Æ´aÆ´an ba balle shi ta ji tausayinsa a matsayin mijinta. Zuciyarta ta bushe, kuÉ—i kawai take kallo.

Baba ya gyaɗa kai ya ce, "na faɗa miki baza ki bar ƙasar nan da aurena akan ki ba, anyi haka ko?."

Sai a sannan ta ji gabanta ya faɗi matuƙa, ta ɗago ta kalle sa taga ita yake kallo sai ta kasa cewa komai.

Baba ya daure ya ce, "tunda kin zaɓi tafiya a kan aurenki da ƴaƴanki da ƴan uwanki baki ɗaya, ki je Maimuna, ki je ki nemo duk abinda ki ke ganin zaki samo a aikin gidan larabawan saudia."

"In kin bar gida nan ki taho da duniya gabaɗaya, ƙarewar arzuƙin da ki ke hangen zaki samu a aikatau. Kin zaɓi yin aikatau a wata ƙasa akan zama da yaranki…..”

Baba ta dakata yana gyaɗa kai, ya ɗago ya sake kallon ta ya ce, “Kamar yadda na faɗa miki, indai ki ka zaɓi barin ƴaƴanki ki ka tafi neman kuɗi Saudia, ni kuma na rantse baza ki bar ƙasar da aurena kan ki ba. Ki tafi saudia, amma ki sani, na sake ki Maimuna!."

Wata irin ƙara Safeera ta yi, tana ɗora hannu a kanta cikin gigicewa da tashin hankali.

Su Umma za a tafi aiki, sai mu ce Allah ya sa a dace.😁😁
[6/30, 9:54 AM] KRBBK: RDB2P26
Nana Haleema.

Islaha haka take yin komai a sanyaye, ji take kamar ta cewa Mama ita ta fasa tafiyar, gabaɗaya tafiyar ta fita daga ranta, daman ba a ran nata tafiyar take ba lallaɓawa kawai take yi. Amma yanzu da tafiyar tazo sai raunin ya yi mata yawa, ta sake zama mai rauni sosai.

Tana ganin Labiba sai hidima take yi tana shiga ta fita, harda su yin sabon kitso. Ita dai kallon ta kawai take yi, zuciyarta tana saƙa mata abubuwa da yawa, tana ji da tana da dama da iko zata fasa tafiyar da ta yi niya, dan Allah ya gani gabaɗaya tafiyar ta ta fita daga ranta ko kaɗan. Ranar ko asibiti basu je ba, suna gida suna hidimar tafiya.

Islaha tunda ta dawo daga wajan aiki ta kasa yin komai, tana zaune sai dai ta kwanta ta tashi ko kayan ta kasa haÉ—awa. Jikinta ya yi sanyi, ta rasa abinda yake yi mata daÉ—i, komai ya tsaya mata cak, bata jin daÉ—in duniyar gabaÉ—aya.

Buɗe ƙofar da aka yi hakan ya saka ta ɗago ido ta kalli Labiba da har wanka tayi, ta shirya cikin doguwar riga kuma tayi mata kyau sosai.

Ta bi Islaha da kallo ganin babu alamun shiri a tare da ita ta ce, "ke bama ki shirya ba kenan, jirgi dai ha mota bace balle a jira ki. Gashi nan in ji Mama, ki saka mata a kayan ki" ta faÉ—a tana cilla mata kayan ta fita ta barta.

Islaha ta sauke numfashi ta miƙe a sanyaye, ta buɗe kayanta tana kallo ta kasa taɓa komai balle ta san abinda zata ɗauka. Kamar mara jini haka ta dinga jawo kayan tana zubawa, ita kanta baza ta ce ga abinda take zubawa ba, kawai ta san ta saka dogayen riguna da hijjabai.

Tana gama zubawa ta zauna a kan gado ta yi tagumi, ta rufe idanunta ta rasa abinda yake yi mata daÉ—i a lokacin. Tana zaune Mama ta shigo tana faÉ—in, "Yauwa Islaha kizo kuci abinci, motar tafiya Abuja tana jiran mu, gabaÉ—aya zamu tafi sai kun tashi sai mu dawo."

Mama ganin yanayin Islahan sai ta bita da kallo mamaki ta ce, "ke jirgi ne fa ba adadaita sahu ba ne, akwai tafiya miƙaƙƙiya a gaban mu, daga nan Abuja zamu wuce ba jimeta ba. Ki tashi ki shirya, dan wallahi in ki ka rasa jirgi kamfani bai san asara ba, sai kin biya abinda aka kashe miki." Islaha ta ɗaga kawai bata ce komai ba Mama ta fita ta barta.

Bata an shigo ba, kawai ji ta yi an faÉ—o kanta ana kuka, a firgice Islaha ta kalli Safeera da ta rungume ta tana kuka mai tsuma zuciya.

Islaha cikin tashin hankali da tsoro ta ce, "lafiya Safeeraa, me ya faru ki ke kuka haka?."

Safeera bata yi magana ba sai kuka da take yi mai sauti, Islaha ta yi shiru ta bar ta tana kuka, dan itama haka kawai take ji tana da buƙatar zubar da hawaye. Taso ace tana da iyayen da zasu hanata abinda take niya, taso ace tana da uwa ko uba da zasu yi rantsuwa su ce baza ta je ba kamar yadda Baba ya hana Safeera zuwa. Amma ita bata da kowa, ita kaɗai take yanke hukuncin da ya yi mata a zuciyar ta, ita kaɗai take saƙawa kuma take warwarewa.

Safeera sai da ta gaji da kukan sannan ta koma jan numfashi, islaha ta bata ruwan da yake kusa da ita ta ce, "ki sha." Bata ƙi ba ta karɓa ta sha tana sauke numfashi.

Islaha ta ce, "me ya faru?."

Safeera ta ce, "Islaha Umma da Baba."

"Me ya faru?."

"Ashe da Umma zaku yi tafiyar nan?."

"Na sani Safeera, ban faɗa miki bane dan babu amfanin na ɓata miki rai. Amma na san da Umma za a yi tafiyar tun ba yau ba."

Safeera ta goge hawaye ta ce, "Islaha ni kaɗai na san abinda nake ji a raina. Baba ya hana Umma tafiyar nan, har Yayanta na Katsina ya kira har gida ya zo ya hanata. Amma ga Umma can ta haɗa kaya zata taho gidan nan. Islaha...." Sai ta kasa magana tana jan nunfashi cikin ƙunar rai da ɓaci mai yawa.
Chapter 37 · 0% Book details